Free chapter · Read without an account
Chapter 3
INA MUKA DOSA?
S-Reza✍️
Page 3️⃣
Sosai Abdul yayi murna harda kuka, kuma lokaci ɗaya ya ƙara tsoron Allah, domin kuwa lokacin da suka je buɗe banki abokinsa ya bashi shawarar ya cuci su Alpha ɗin kuɗi, ganin kuɗin da ya wa, farko yaji tsoro amma abokin ya nuna masa hanyar da suka saci kuɗin sama da miliyan biyar. A daren yayi tunanin hakan bai dace ba, kuma a kullum idan suka fita wani guri Alpha ɗin yana basa Kuɗi kusan dubu hamsin banda kuɗin mai. Hakan yasa ya mayar masa da kuɗin sa, bayan ya faɗawa abokin cewar ba zai iya ba. Yanzu kuma gashi an siya masa gida na sama da miliyan goma, shi da yake gidan haya yanzu an gwangwaje shi da nasa. Cikin sati ɗaya matar Abdul mai suna Bintu da tayi jagoranci wajen siyan kayan gida, irin na mata. Sauran kuma irin su kujeru da gado kamfani ne suka zo har gida suka shirya musu kaman yadda suke so. Kwana na tara gida ya zama gidan ƴan gayu. Dama Alpha ba dai son gayu da gyra ba. Muddin Alpha suka fita shida Abdul haka Bintu zata zo su zauna da Laila, duk da cewar ta girmi Laila ɗin amma haka take bata girmanta, kuma take ƙara godiya ga Ubangijin da ya halicci Laila, domin bata gajiya da kallonta, Allah yayi mata kyau mai daukar hankali sosai wanda ko da take Mace Laila na bata sha'awa. Kwanansu goma sha shida da tarewa aka ɗaura musu aure a masallacin juma'ar dake saman layin nasu bayan Alpha yaje ya musu nasa bayanin. Shi kansa Abdul bai sani ba sai ranar kuma lokacin ya san da cewar ba matarsa bace. Sosai yayi mamaki jin wai ashe ba matarsa bace sai ma yanzu za'ayi auran. Ai kuwa a daren ranar suka angwance da junan su, tun daga lokacin kuma Alpha baya fita waje, kullum yana gida suna tare, izuwa yanzu hankalinsu ya kwanta sai kuma rainon ciki da suke yi. Watansu ɗaya a Nigeria wanda yayi daidai da watan cikin Laila biyu kenan, har Kuma lokacin cikin nata bai bar laulayin da take fama dashi ba. Yana da son yin sex sai dai cikin nata yazo mata da wani irin abu da bata buƙatar sa. Shi kuma baya iya jurewa, hakan yasa kusan kullum ba'a jinsu sai a kan haka idan dare yayi. Sosai take daurewa amma idan yana yi sai taji kamar ana tura mata sanda a jikinta, wani lokacin ma sai taji kamar ana zungurin ɗan cikin nata ne, hakan yasa yana cikin yi sai ta fara turesa ko ta fara kuka tana ihu, idan ya tambaya tace bata so ne kuma bata jin daɗi. Tun yana mata uzuri har kuma shima ya kai ƙrashe yake ganin kamar dai iskancin tane kawai. Yauma kamar kullum duk yadda taso ta hana shi farawa amma bata iya ba, domin tana sonsa sosai kuma tana jin nauyin sa har lokacin, da yayi mata kalaman soyayya sai ta yarda amma da zarar ya fara sai taji wannan abun ya dameta. Tun yana yi tana jin dad'i har ta fara jin abun da wannan karan taji kamar zai shaƙe ta ta mutu ne, hakan yasa da wani irin karfin da bata san tana da shi ba ta ture shi gefe, shima da baiyi tunanin hakan daga gare ta ba, sai gashi a ƙasan gadon tim ya fado. Tsabar zafi har sai da yayi ƴar ƙara. Ita kuwa Laila da sauri tayi Toilet tana kakarin amai ga gabanta da yake mata wani irin zugi. Sosai ransa ya ɓaci ya bita da kallo yana mamaki. Yana zaune dafe da baya ta dawo ta masa kallo ɗaya ta koma kan gadon ta cigaba da barcin ta. Duk yanda ya kai har wuya bai ce mata komai ba saima tashi da yayi ya shiga Toilet. Bayan ya fito ya saka kaya ya koma wani ɗakin. Washegari ma da safe haka bai nuna mata komai ba suka cigaba da rayuwar su a haka, kullum idan zai yi sex sai sunyi faɗa domin ko minti goma baya samun damar yi. Hakan yasa yau yaci alwashin ko bata so sai ya biya buƙatar kansa da ita. Koda ya fara bata hana shi ba, amma tana fara jin abun ta fara kuka da ihu da duka da yakushi har sai da ya gangara gefe ita kuwa ta shige Toilet ya bita da kallo.
Sosai abun ke cigaba da faruwa tsakanin masoyan har dai cikin ya kai wata shida. A wannan lokacin kuma sai ta fara buƙatar sa sosai har fiye da kowani lokaci, hakan yasa zaman nasu ya ƙara gyaruwa domin dama abun da yake haɗa su faɗa kenan. Daga lokacin kuma ta fara kumbura kamar mai shan maganin sha ka fashe, sosai cikin nata ke hurata kamar mai cikin ƴaƴa goma sha biyu. Zuwa lokacin kuma ba ƙaramin sabo ne ya shiga tsakaninta da Bintu ba, kasancewar itama bintun bata da matsala domin kuwa irin matan nan ne masu hakuri sosai ko daga fuskar ta ma zaka gane hakan. Bintu iya secondary school ta tsaya kasancewar itama ba ƴar manya bace, amma da yake a cikin garin Abuja suke da zama da iyayenta sai turanci ya zauna a bakinta, hakan yasa suke hira sosai da Laila har take ƙoƙarin koya mata yaren Hausa, sai dai bata iya wa sosai, ita kuma bata gajiya da yi mata magana, koda bata zo gidan ta ba, haka zata dinga mata magana a waya ko suyi video call, sannan ta sakata a cikin group ɗin su na family's ba tare da kowa ya ankara ba, tayi hakan ne domin ko zai taimaka mata wajen gane Hausar. Ita kanta Bintu ba wasu group take shiga ba hakan yasa bata saka ta a wasu ba. Haka dai suke rayuwa har cikin Laila ya kai wata bakwai, izuwa yanzu kuwa ta zama wata gari guda, zama da ƙyar tashi sai da dabara, hakan yasa Bintu ta tare a gidan idan ta dawo gidan sai dare. Shi kuwa Alpha a wannan lokacin ya fara tunanin abun yi, yana son zaman Nigeria ganin yadda komai yake zuwa masa babu taƙura, sai ya fara tunanin fara abun yi, ko dai ya fara sana'a ko kuma ya naimi aiki koda kuwa koyarwa ne kaman yadda Abdul ya taɓa basa shawara. Ita kuwa Laila dukda halin da take ciki bai hana ta yin lissafin idan ta aihu zata koma gida ba. Izuwa lokacin wani irin mafarkin Abi da Ummi da Abdulhi take yi sosai, ga kewarsu da ta gama kamata, har kuka take idan ta tuna dasu, hakan yasa hankalinta gaba ɗaya ya koma Saudiyya. Sosai ta iya cin abincin Hausawa tun bata so har Bintu ta koya mata, sannan Hausar ma takan iya kwaɓawa Bintu kuwa taita mata dariya, wani lokaci sai tace ba zata yi hira da kowani yare ba sai Hausa, hakan kuwa ba ƙaramin nishadi yake saka Bintu ba, domin harshen nata baya iya karyewa kwata-kwata, idan tayi magana kamar ƴar chana zata fara koyan Hausa, tana ganewa, amma gurin furtawar ne dai sai a hankali, ita kuwa Bintu kasancewar tayi karatun Alkur'ani mai girma sosai, domin kuwa har sauka tayi, kuma babu laifi tana iya fassara wasu guraren a cikin Alqur'ani mai girma, hakan yasa larabcin da take koya baya bata hawala, a da bata iya yin magana da larabci ba, sai dai takan fadi sunan wasu abubuwa kaman yadda ta tsinta a islamiyya, amma haɗuwarta da Laila sai take iya yin magana kaman yadda take koya mata. Ita kanta Laila tana mamakin yanda Bintu ta iya larabci amma ita Hausar Tata bata fita. Izuwa lokacin wasu daga cikin ƴan uwansu Bintu ita da Abdul sun zo gidan kasancewar su ƴan uwa ne. Kuma kowa yazo yaga Laila da Alpha sai ya buɗe baki tsabar kyawun halittar su. Shi kuwa Alpha sosai yake ƙara fahimtar Nigeria da yadda garin yake. A cikin wata bakwai ɗin da sukayi ya gane cewar Nigeria babbar ƙasa ce mai ɗauke stest talatin da shida (36) ya san sunan wasu daga cikin kuma har labarin wasu yaji, harma zuwa wasu yayi ya gani. Sosai yake ƙara jinjina wa kansa na haukan da yayi na cewa zai gano ƴan uwan mahaifinsa a wannan ƙasa mai girma haka, kuma mai cike da al'umma iri daban-daban, wani lokaci sai yaji cewar to ta ina zai fara, sannan ga ita Laila ta fara maganar koma gida, shima baya jin zai iya komawa Saudiyya yanzu, kai shi yana ganin nan da shekaru masu yawa ma ba zai koma ba. Ta bangaren sa, sosai ya koyi abubuwa da yawa fiye da ita, aciki kuwa harda Hausa da ya iya fiye da ita, duk da cewar shima idan ya furta sai anyi dariya amma dai ya fita, sannan cin abincin Hausawa ya ƙware sosai, harma ya zaɓi ɗanwake daga cikin irin abincin da yake so.
Lokacin da cikin Laila ya kai wata tara hankalin kowa ya tashi, domin gaba ɗaya asbinti suka tare, ta kumbura sosai har ma ta koma a bar tsoro kamar an hura balun, hakan yasa hankalin Alpha tashi sosai, domin har suma take yi, tana kuka yana kuka, tana faɗa masa cewar dan Allah yace wa Abi da Ummi su yafe mata mutuwa zatayi. Tsabar rudewa har yana mata alƙawarin cewar tana aihuwa zasu koma Saudiyya, ita kuwa tasan ba zata ƙara shaƙar iskar duniya ba, domin ita kadai tasan mai take ji. Shi kansa Abdul da matarsa sun tashin hankali su sosai, domin idan kaga yanda cikin Laila yayi dole ka ƙara tsoron Allah. Su kansu likitocin sun ce basu taɓa ganin ciki irin wannan ba, gashi duk iya gwaje-gwajen da sukayi basu ga komai ba, bayan lafiyar cikin da suke da tabbacin yake. Kwanansu biyar a asibiti ta ƙara kumbura sosai fiye da farkon zuwansu, sannan kuma naƙuda ta tashi mata ganga-ganga, zuwa wannan lokacin kuwa babu baki gurin Laila sai dai tuba da take yi a zuciya, tana ƙara jin tsoron Allah, sai yanzu take ganin Kuskuren da tayi na bin Alpah yazo da ita garin da zata mutu bataga kowa nata ba, ita kaɗai tasan halin da take ciki, sai yanzu take jin inama ta tsaya ta aihu a gaban iyayenta, inama ta yarda taji kunyar al'ummar da take gudu akan wannan wahalar da take ciki. Shi kansa Alpha ya cire rai da ita ganin yadda ta koma kamar ba mutum ba, ji yake inama da yadda zaiyi ya Kaita gida ta mutu a gaban iyayenta kamar yadda ta ce. Sosai fuskarsa tayi jaa, yana ƙara jin tsoro a ransa. Babu abun da yake tunowa sai yanzu fa wannan cikin bada aure aka samar dashi ba, yanzu idan sun haifa mai zasu cewa yaron ko yarinyar idan ta girma, to ko dai duk saboda laifin ne Allah yake hukunta su ta hanyar kumburan da Laila take yi. Kwana biyu ta kwashe tana abu guda gashi Alpah ya ce ba za'a mata aiki ba, kasancewar a rikice yake. Cikin ikon Allah kuwa cikin yammacin rana ta biyun Laila ta sulluɓo jaririnta ƙato mai kama da ita, minti biyar sai ga na biyun shima ƙato da shi masu kama da juna.
Alhamdu lilliha bini'imatika ya Allah! Shine abun da Alpha ya fara faɗa lokacin da yaji ta sauka lafiya amma babu ƙarfi ko guda ɗaya a tare da ita domin kuwa bata ƙara sanin ina kanta yake ba sai washegari da asuba. Shi kuwa Alpha lokacin da yayi tozali da yaran nasa sai yaji duk wani tsoro da faɗuwar gaba da ya shiga suna zubewa, sosai yake jin ƙaunar yaran a ransa kamar ya haɗiye su. Su kansu su Abdul da Bintu farin ciki suke sosai kamar ba gobe. Yara kuwa kana kallonsu kaga jinin larabawan asali na Saudiyya domin babu abun da suka baro na Laila kamar an tsaga kara. Cikin kwana uku wannan kumburin na Laila ya sace kamar ba itace tayi wannan girman ba. Sannan gashi babu wani abu da take ji a jikinta sai dai hankalinta da yayi gida. Gaba ɗaya gida take san zuwa ta gaji ba zata iya ba, domin ji take kamar lahira ta leƙo ta dawo, ita bata ma jin zata ƙara yarda ta aihu karo na biyu ba. Kwana biyar aka sallamosu suka dawo gida cikin farin ciki. Nan kuwa Bintu ta dawo gidan da zama gaba ɗaya, suna kwana a ɗaki daya da Laila. Sai dai ita kanta ta kula da rashin walwalar da Laila ɗin ke ciki. Amma jin bata yi mata maganar ba yasa itama taja baki tayi shiru. Sai da yaran suka yi sati biyu kafin akayi suna wanda ba wani taro a kayi ba, a cikin masallacin da aka ɗaura musu auren aka raɗawa yara suna, kuma babu wani taron suna da zasu yi domin basu da kowa, sai naman sunan da Bintu ta dinga aikin soyawa, domin har sai da wasu biyu daga cikin ƙannenta suka zo suka taya ta. Yara sukaci sunan Hakim da Ziyach. Hakim shine Babba sai Ziyach mai bi masa.
Wannan ƙaruwa da ma'auratan suka samu sai ta fara zama babbar ƙofar ɓullowar dukkanin matsalolinsu domin kuwa daga wannan lokacin zanen gaddarar su ta fara aiki kaman yadda Allah ya tsara musu ba tare da sanin ko wannensu ba. A bangaren Alpah ya ɗauki son duniya ya ɗora akan yaran nan, wanda har yaji baya sha'awar komawa gida, domin yana tsoron yaje a fara sheganta masa yara, yana jin zasu zama masa family's ɗin da ya rasa dasu dama wanda zasu ƙara haifa a nan gaba shida matar tasa, hakan yasa tun washegarin ranar da suka dawo gida yayi shawara da Abdul akan zai yi zaman Nigeria dan haka wacce sana'a yake ganin zai buɗe. Abdul ya bashi shawarar siyan babban guri ya buɗe mayan shaguna na siyar da kayan sakawa bama a iya garin Abuja ba harma da wasu garuruwan tunda dai Alpah ɗin yace a kwai kuɗi. Ai kuwa cikin kwana huɗu suka samu ƙaton fili ya siya da tsada, kuma yasa aka fara masa gini. Hakan yasa kusan kullum yana gurin aikin domin ya kula yanzu Laila bata son zaman lafiya. Sosai ya sallama da zaman Nigeria ba domin komai ba sai dan yaransa, kuma ma ai babu abun da yake bukata, ga mata ga yara ga zaman lafiya to me ya rage. Ita kuwa Laila gaba ɗaya ita dai gida take da burin tafiya, hatta yaran nata ma idan ta tuna da cewar bada aure aka samesu ba sai taji wani abu kamar na tsoron yaran na shigar ta. Ita dai yanzu tunda ta rabu da cikin kawai zata tafi gida koda shi ba zai koma ba, ta gaji ba zata jure ba. Duk lokacin da suke su biyu babu abun da take masa sai kuka akan ita gida zata koma dan Allah ya mayar da ita, shi kuwa tun yana ɓoye mata har ya sanar mata da ƙudurinsa akan fa zaman Nigeria dole ne. Ai kuwa a ranar yaga sabuwar Laila domin kuwa a cikin borin Yaren larabawa babu irin wanda ta mance batayi masa ba. Wasu kalaman larabcin ma ya manta ranar da yaji wasu sun yi amfani da shi. Hauka tuburan irin na wanda ya samu zaucewar tunani Laila keyi kai ka rantse da Allah satota yayi ba itace ta biyosa ba da kafarta ba. Wannan dalilin yasa ko yaran bata wani kula dasu, daga ya shigo gida sai kuka ita dai Saudiyya zata koma gurin Abi da ummi. Ganin dai ya mayar da ita majnun ɗin gaskiya kaman yadda yake ce mata ne yasa ta fara neman ina zata saka kanta, duk ta saka damu a ranta har ramewa take yi. Shi kuwa hankalinsa kwance yana mayar da hankalisa ga ginin sa da aka fara. Haka har wata guda izuwa lokacin kuwa abun sai yaci uban nada, domin yanzu idan ya shigo gidan tayi masa magana yayi mata banza sai kawai ta chakumesa tana dukansa, wasu lokutan ya yageta daga jikinsa yayi wurgi da ita, wasu lokutan kuwa sai dai ya rabu da ita har sai ta gaji da kanta. Su kansu su Abdul sun kula da rashin zaman lafiyan dake faruwa tsakanin su, amma jin basuyi magana da kowa ba sai suma suka zuba musu na mujiya. A lokacin da Hakim da Ziyach suka cika wata uku, a lokacin aka gama gina katafaren flazar da taci sunan Alpha plaza a cikin garin Abuja. A wannan lokacin ne kuma Alpha ya fara magantuwa da buƙatuwa da matarsa, amma tayi tsalle ta dake tace bata san wannan ba, wallhi sai dai ya mayar da ita gaban iyayenta muddin yana son zama da ita. Nan fa yace wannan kuwa tayi ƙarya domin shi ba zai koma Saudiyya ba, kuma itama ba zata koma ba. A cikin wannan daren komai ya ƙara lalacewa, domin daga wannan daren zaren rayuwar gidan Alhaji Alpah ya tsinke wanda su da kansu basu san ina suka dosa ba, basu san yaya tafiyar gidan zata kasance musu zuwa gaba ba. A cikin daren tana kuka tana zagin sa, shima yana sanar da ita ko mutuwa zatayi sai ya ƙarbi hakkinsa, domin kuwa harda duka ya haɗa mata, itama bata tsaya ba tana zagi tana mayar da martani iya yadda zata iya. Haka ya tsalleketa bayan ya samu gamsuwa yayi wanka ko ta kanta bai bi ba.
Ita Laila babban abun da take tsoro bai wuce aihun da tayi taji irin raɗaɗin dake cikin sa ba, sannan kuma tana jin ba zata iya sakewa ba idan bata ga iyayenta ba. Hakan yasa washegari da sassafe ta kira Bintu ta ce mata ta shirya zata rakata asibiti. Bayan fitar Alpha suka shirya Bintu ta ɗauki Hakim Laila ta rika Ziyach. Bayan ta samu ganawa da likitane tayi masa bayanin abun da take bukata a tare da shi. Likitan yayi shiru yana kallon ta, kallo ɗaya yayi mata ya gane cewar yarinya ce ƙarama, domin kuwa babu komai a tare da ita sai zallar ƙuruciya da rashin wayo. Farko ma yayi tunanin ko ba matar aure ba ce ganin tayi yarinya ƙarama da irin wannan maganar. Ya ce "Kina da aure ne?" Ya faɗa da kyakkyawan turancin sa. Ta ce "Eh ina da shi? Ya ce "Kin taɓa aihuwa? Nan ma tace "Eh. Ya sake kallonta sosai kamar zai ce wani abu amma yayi shiru yana ɗaukar kiran da ya shigo wayarsa. Sai da ya gama wayar kafin ya dawo da kallonsa ga Laila da har ta fara gajiya da wulaƙancin da yake mata. Cikin harshen da yasan tafi ganewa ya fara mata magana cike da kulawa da mutuntawa. "Muddin kina son muyi miki wanna aikin dole sai kinzo da mijin ki, kuma ina baki shawarin cewar idan ma mijin naki ne ya baki wannan shawarar to karki yarda, su maza basu da tabbas, kina cire mahaifarki wata zai auro ta cigaba da haifa musa yara ke kuma ko oho, kuma baki tunanin cewar zaku iya rabuwa da shi, ko mutuwa ko rabuwar aure ba'a fata. To shi wanda zai aure ke me zaki ce masa. Ina mai baki shawara a matsayin likita akan ki sake tunani. Likitan ya ƙarasa yana karantar fuskar Laila ɗin. Sosai take tunani, haƙiƙa tayi mamakin jin yadda likitan ya iya larabci sosai, sannan maganar ƙara aure da yayi nan ma sai yanzu hankalinta ya kai gurin. Amma idan ta tuna da azabar da tasha sai taji ba zata iya ba. Haka dai ranar suka koma gida duk ta rasa abun yi. Washegari kuwa aka fara kawo kaya cikin Alpha plaza. Cikin kwana na uku suka koma wani asbintin wanda yanzu ta sake shawara daga cire mahaifar zuwa a tsayar da aihuwar har na tsawon shekaru goma. Shi kansa likitan yayi mamaki amma ganin kuɗin da ta bashi nan take yayi mata aiki bayan ta saka hannu. Sai yanzu taji hankalin ta ya kwanta ta wannan ɓagaren sai kuma batun yadda zata koma gida, koda kafin ta tafi ya samu ya kwanta da ita bata da matsalar ɗaukar wani cikin. A cikin wannan kwanakin sai ya zama baya samun zama, domin hada-hadar kayan da ake kawo masa. Sosai ya zuba dukiya masu yawa dan saida aka ƙaro masa kuɗi kasancewar harda kayan Saudiyya yake so ya haɗa kuma duk cikin sirri tsakanin sa da shi amintancen nasa. Cikin ikon Allah komai ya kammala shaguna guda goma sha biyu, shida a sama shida a ƙasa sai wasu ƙanana guda biyu a gefen su, kuma gaba ɗaya babu wanda yasa haya, duk kayansa ne a ciki, gashi gurin a bakin titi yake kuma ginin yayi kyau sosai. A kwai bangaren abayoyi da na jallabiyoyo, sai turaman zani, da hijjabai da ta ƙalma da bangarori akwati sarƙoƙi laishe kayan maza. Duk wani abu da ya shafi sutura kam idan kazo Alpah plaza zaka samu. Sannan ya biya kuɗin gidan jaridu da gidan talabijin harda selebiritis duk suka yi masa talla, lokaci ɗaya kuwa kasuwancin nasa ya haɓɓaka sosai. Cikin kasa da wata biyar ya tada wani irin ginin a Kano wanda dama ya siya gurin. Sosai Abdul ya samo masa ma'aikata masu amana wanda suke masa aiki sosai domin Allah. Cikin ƙasa da shekara ɗaya sunan Alpha ya zagaye Nigeria domin yanzu har gidan mai yake son budewa.
Dukda wannan nasarori da Alpha yake samu a bangaren gida kuwa komai sake lalacewa yake yi, domin rayuwar tasa tsakanin sa da matar gidan dai babu daɗin ji bare kuma gani. Izuwa yanzu idanun Laila ya rufe bata kunya kutuntuma masa zagi a gaban yaransu da yanzu suma suka fara wayo, shima kuma Alpha baya jin kunyar lakada mata duka idan ta kaishi bango, gashi sun iya wasu irin zagi da sukewa junansu da yaren nasu na gado, yanzu-yanzu zakaji taje Allah ya la'anci shi, ko tace Allah ya la'anci yaran nata idan ta haɗo su akan yaran, ko kuma tace Allah ya la'anci uban uban yaren. Zagi dai mara daɗin ji ga wanda yake jin yaren. Yanzu da suke cimma shekara biyu da zuwa Nigeria sosai Hausar Laila tayi ƙwari dukda haka dai a kwai tuntuɓe idan har zata furta, amma dai anfi da, kuma tana iya yin duk wani nau'in girkin Hausawa sosai. Sosai ta ɗauki tsangwama ta ɗora a kan yaren da idan gori ya tashi bata kunyar gayawa ubansu cewar su ɗin bada aure aka samesu ba domin bata mantawa da irin azabar da ta sha gurin haifar su. Akan wannan abun sosai yayi mata gargadi har dai yanzu ta daina ganin sun fara wayo. Shekarun su Hakim da Ziyach uku flazar Kano itama ta tsaya daram izuwa lokacin suna tafiya harda magana sosai, kuma sun tashi da larabci a bakinsu sosai kasancewar da shi ake musu magana. Sai dai wani sabon al'amari da yaran suka tashi da shi na ƙiyyayyar junansu kamar abokan gaba. Kullum kuwa sai kaji kukan ɗaya daga ciki idan suna faɗa, domin kuwa Laila ko a jikinta ko da zasu kama faɗa ko kallo basu isheta ba. Dukda kuwa wani lokacin idan suna faɗan har jini ana fitarwa da wani a cikin su, gasu yara amma faɗan nasu kaman na manya, domin faɗa sosai kamar yaran zakuna ga su da baiwar yin ƙofi idan an ɓata musu rai. Wani lokaci idan suna yi Alpha ya shigo ya gani sai ya hauta da faɗa itama ta hayayyako masa, babu kunya za'a dambatu su kuwa yaran su tsaya suna kallosu, wani lokaci ma iyayen nayin nasu suma suna yin nasu. Kuma daga cikin irin zagin da Laila ke yawan musu suma sukewa junansu da idan suna faɗa, wani lokacin ma harda ita idan ta bata musu rai zagin nata suke yi, ita kuwa tayi musu shegen duka. Ai kuwa a ranar bata gane kanta domin kuwa haka zasu tsayar mata da duk abun da take yi ba tare da tasan sune suka tsayar ba har dai ta gano cewar ƙofi suke mata. Ita dai ta sa a ranta tunda ya raboto da nata iyayen to wallhi babu wanda zaiji daɗi da ita har sai ya Kaita ga iyayenta. Wanda yanzu babu ɓoye-ɓoye har iyayen nata yake zagi, itama ta zagi nasa. A zahiri Laila tana da damar da zata iya komawa Saudiyya amma shi Alpha ɗin ne ya toshe duk wata hanya, sannan ita kanta tana so idan zata je su tafi tare za'a fi ganinta da mutunci domin ta rubuta a jikin wasiƙar da tayi wa su Abi cewar tare suka gudu.
Lokacin da su Ziyach suka cika shekaru biyar kuwa Anan kuma ciki ya baiyana a jikin Laila wanda bata ankara da shi ba har sai da yayi wata uku domin bai zo mata da wani laulayi ba. Anan fa tace uban kuturu yayi katan bare na makaho, hakan yasa tace sai ta zubar. Alpha kuwa da yake jin ba'a zubar da cikin shege ba sai na halak, ai kuwa bata isa ba...📝
Kuci gaba da bin wannan labarin a hankali har mu kamo bakin zaren. Kusan S Reza baya rubuta littafin banza. In sha Allah zakuji daɗin sa sosai.