Free chapter · Read without an account

Chapter 4

by Salis M Reza · INA MUKA DOSA?

INA MUKA DOSA?

                   S-Reza ✍️

                Chapter 4️⃣
Dama tun kafin samuwar cikin kullum a ƙorafi yake akan me ya hanata yin wani cikin har yanzu, ita kuma sai ta ce ai dama shine mai bada cikin sai yazo ya saka mata shi idan ya isa, sosai yake ƙin yarda da ita, sun sha zuwa asibiti likitoci suna tabbatar masa da cewar babu ciki a jikinta. Kuma bai taɓa kawo cewar tayi tsarin iyali bane, kuma bai isa yace ko bata aihuwa bane domin kuwa ta haifa ya gani. Kafin samun wannan cikin har magana yake gasa mata na cewar da yake cikin shege ne ai ta iya buɗe jiki tayi ciki a yaɗuwar farko amma yanzu anyi aure shegiya ta kasa yin wani cikin. Idan ya faɗa mata haka sai itama ta ce da shi "Ai kaima da yake ɗan iska ne, ka iya bawa mace ciki a waje amma gashi anyi aure ka kasa. Kai rayuwar gidan Alhaji Alpah sam bata da alƙibla, ba zaka taɓa yarda cewa suna da ilimi na addini ko ɗaya ba, kuma alhalin duk cikin su babu wanda bai haddace Alqur'ani mai girma ma, kuma idan suna maka ƙira'a tamkar kar su tsaya tsabar daɗin murya da kuma iya bin tajwid daidai. Amma sam basa amfani da shi. Gashi yanzu da suka fara samun yara sai abun ya ƙara lalacewa. Su kansu su Abdul da Bintu lamarin gidan Alpah ɗin yafi karfin su, domin ko a gabansu basa kunyar yin uwaka ubanka. Amma koda kuskure basu san cewar Hakim da Ziyach bada aure aka samesu ba. Sun san dai Laila na faɗin ya gudo da ita daga gurin iyayenta, shima yace itace ta biyosa da kanta ba satota yayi ba. A haka dai suka gane cewar giyar soyayya ce ta kwashe ta har ta biyo shi wata duniyar da babu kowa nata a ciki. 

Hakim da Ziyach sun taso da banbancin ra'ayi kaman yadda suke a komai nasu, hatta kaya basa taɓa saka iri ɗaya, idan kuwa wani ya taɓa na wani ko a rashin sani ne to fa ranar babu mai iya raba wannan yaƙin da za'ayi a gidan Alhaji Alpah har sai uncle Abdul yazo, shima sai sunga dama. Bangare guda ga gata da suke samu daga ubansu, domin babu abun da zasu ce suna so bai mallaka musu shi ba, dukda kuwa babu wani girmamawa dake tsakanin sa da yaran tun ma yanzu, domin kuwa idan yayi musu abun da basa so haka zasu ƙunduma masa zagi da yaren nasu na gado, kuma haka zaiyi dariya ya ƙyalesu. Ita kuwa Laila dama cen babu shaƙuwa a tsakaninta da su sai ma ta zama kamar itama a bokiyar faɗan tasu ce, gaba ɗaya babu dama dama a cikin su. Shi Hakim wanda shine babba, Allah ya bashi zuciya sosai gashi da ɗan banzan ruƙo, zai yi wahala ya manta da abu muddin ya dame shi, sannan ya tashi da sha'awar yin ƙwallon kwando wato ( Basketball) Shi kuwa Ziyach wanda shine ƙarami shima Allah yayi masa zuciya harma fiye da ta Hakim amma shi bashi da ruƙo kamar ɗan uwansa, muddin abu ya wuce to tabbas sai dai idan kaine ka sake dawo masa da wannan abun, shi kuma ya tashi da sha'awar buga ƙwallon ƙafa wato ( Football) Hakan yasa tun suna yara koya Alpah yasa aka buɗe masa ɗan karamin filin wasan sa a cikin gidan da suka sauya shekarar da ta gabata. Wato yanzu dai basa tare da su Abdul sai dai idan sun zo gidan nasu. Ko a makarantarsu kowa bangaren support ɗin da ya zaba daban, kuma kowa ana ji dashi a bangaren sa. Sai dai wani abu guda biyu da suke yi wanda suke burge kowa shine basa yarda wani ya taɓa ɗaya daga cikin su koma waye, nan fa zasu haɗu ayi taron dangi, wani lokacin ma kafin a bar gurin faɗan yake juyewa ga junansu. Abu na biyu kuwa shine dagiya kar wani yafi wani a komai. Ko bangaren karatu da kuma abubuwan rayuwa kama daga kayan sawa ko kuma dai wani abu da zai nuna cewar wani yafi wani to kowa baya son hakan ta faru. Babu ta gun da zaka iya banbance Hakim da Ziyach sai ta wajen magana idan a waje ne, ko kuma banbancin kaya, domin Ziyach yafi son kore wato (Blue) shi kuwa Hakim yafi son Jaa wato (Red) Haka dai suke rayuwar a gidan kamar ba babba.

Zaune take a Falon gidan nasu wanda har yanzu basu da ƴar aiki, bayan mai musu wanki da direba da mai gadi babu kowa a gidan, domin indai girki ne Laila da yanzu su Hakim suka mayar mata da suna "Ummu Shi kuma Alpha ya koma Abba. Yanzu ta gama waya da Bintu akan tazo yanzu zata rakata wani guri kuma ba ko'ina bane sai asibiti domin ba zata iya aihuwa a karo na biyu ba wallhi ko ana ha Maza ha mata ne sai ta zubar da wannan cikin, bata manta da abun da ya faru da ita a aihuwar farko ba. Yanzu haka ta shirya ne tana jiran isowar Bintu sai ga Abba ya shigo gidan. Kallo ɗaya yayi mata ya karance ta hakan yasa ya manta da abun da yazo yi gidan ya ce "Laila ina ƙara sanar dake cewar karki yarda cikin nan ya salwanta, idan kuwa hakan ta faru na rantse da ubangijin Ka'aba na kusa da ɗakin Katii sai na shayar dake ruwan mamaki wallhi. Ya faɗa yana nuna mata hannu har idanunsa sun ƙada sunyi jaa sosai, domin kuwa tabbas yana son yara sosai. Itama da dama abun da take jira kenan ta ce "Wallhi sai na zubar sai dai duk abun da zaka yi kayi, idan aihuwar wasa ne kai kazo ka aihu ɗin mana, haka kawai a aihuwar baya nayi kamar na mutu gashi yaran ma shegu tsinannun duk masu halin ubansu babu mai jin ƙaina ba mai tausaya mini, na kusa mutuwa a kansu amma babu wacce suka raina sai ni, to wallhi ba zan ƙara ba, kuma ciki ne daga yau sai ya bar jikina, idan kuma kana da gurin da zaka zuba to ka biyoni sai a juye maka kayan ka, amma dai ni na rantse maka da Allah yau sai wannan cikin sai ya bar jikina. Ta ƙarasa tana nuna masa cikin nata da ya ɗan nuna kaɗan daga cikin rigar. Abba da zuciyarsa tayi zafi kamar ta soye ya ce "Laila idan kin haifu a cikin Khadijah da Abdul Aziz dan Allah ki zubar da wannan cikin dan uwarki. Yayi maganar da larabci wannan karan. Ai Kafin ya gama rufe baki Itama cikin jin zafi da harshen da yayi magana na larabci tace "Alpha idan ka haifu a cikin Katii da Jamal kazo ka hana ni zubar da wannan cikin. Karf kuwa sai a kunnen Bintu da zata shigo Falon. Ai kuwa dama kamar ta sani tana addu'ar Allah yasa ba akan zubar da cikin bane, hakan yasa ta kira Abdul ta sanar masa domin Laila ɗin ta dameta, shine Abdul ɗin ya ce idan taji maganar zubar da cikin ne ta faɗa masa shi kuma zai sanar wa da Alhaji Alpah ɗin domin kuwa yasan yadda Alpha ke mutuwar son yara. Hakan da taji tun kafin ta shiga cikin gidan ne yasa ta godewa Allah da yasa Alpah ɗin yana gidan kuma yanzu yasan komai, ai kuwa haka ta juya ba tare da kowa ya ganta ba ta bar gidan. Wani sauƙar mari Ummu taji mai zuwa da hucin tafiyar mota irin mai gudun wuce sa'ar nan da zakaji suna bada sauti shuuu-shuuu!. Sai da ta ɗauke wuta na daƙika ɗaya kafin ta fara jin zafin marin. Sosai ta ke kallon sa da ya kafe ta da ido yana nuna mata hannu. Ya ɗora da faɗin "Lokacin da zaki biyoni nan ban miki dole ba, kuma lokacin da kika boɗe ƙafa kika bada kai kafin aure da har kike cewa kin sha wahalar aihuwa shima ban miki dole, sannan sunan Katii ya zama na ƙarshe a bakinki da zaki dinga kira babu ladabi domin ita ɗin uwata ce, kuma ina sonta fiye da komai a duniya, ciki kuma kaman yadda nace dan Allah Kiyi gigin zubar min dashi ki gani sai kin gane Allah shine Ubangijin dabbobi. Yana faɗa ya kama hanyar sama. Amma kamar a tunani ko a bazata yaji ta chakume shi kuma ta kama sunan Katii da ƙarfi ta kutuntuma mata wani irin zagi mai wahalar fassarawa sannan ta ɗora da faɗin "Ai uwa bata fi uwa ba, ita Katii ɗin fin Ummi ta tayi da ka zageta ita kace ba za'a zag" Bata ƙarasa ba ya shaƙe mata wuya, itama ta shaƙe masa. Daidai lokacin kuma Hakim da Ziyach suka dawo daga school da direba ya shigo da su. Suma tun a hanya suke zagin juna akan ruwan sha da Hakim ɗin ya wanke ƙafa da na Ziyach.

Lokacin da Alpha ke zagin Laila lokacin yayi daidai da ture Ziyach da Hakim yayi dalilin ƙin ƙarasa shigowa Falon da yayi  kuma yana zagin sa. Hakan yasa juyawar da Ziyach zai yi ya buga masa kular ruwan dake ɗaya hannun nasa, lokaci ɗaya gurin ya kawo ji, kuma Ziyach na tsaye a gurin ko gizau. Hakan yasa Hakim lailayo wani zagi mai laƙabi da uwa ya makawa Ziyach kuma ya nufo gurin sa da niyar faɗa. Ita kuwa Laila jin shaƙun yayi yawa yasa ta cije shi a hannun tana zagin sa. Shi kuma ya shiga kiran Hakim da har ya kai gurin Ziyach an kaceme da faɗa. Ummu ta haura sama tana kuka tana faɗin magana marasa daɗi ga mijin nata yayin da shi kuma ya shiga raba wannan faɗan. Shi kuwa Hakim ganin kansa na jini yasa yaƙi haƙura da abun har sai shima yaga ya fitar wa ɗan uwan nasa jini. Amma karshe dai shi ake ƙara cin galaba. Ganin kamar Abbu ɗin yana riƙe shi ne yasa shi faɗin "Abbu kana riƙe ni shi kuma yana dukana to wallhi ba zan yarda ba mugu. Ya faɗa cikin kuka. Hakan yasa Abbu ɗin komawa da baya. Daidai lokacin ita kuma tana sakkowa. Ta ce "Yara biyu kawai kenan sun zama maka masifa da bala'i, ka kasa kula dasu amma hakan kake so wai sai na ƙara haifo maka wasu, to ba ni Laila ba wallhi. Abbu ya tsaya yana kallon yadda yaran suke ta dambe sosai kowa na ƙokarin ganin yaci galaba akan ɗan uwansa. Abbu ya buɗe baki da ƙyar ya ce "Kinga abun da kika jawo mana ko?" Ta ce "Abun dai da ka jawo wa kanka, kuma dama ba dai ƴaƴa kake so ba gasu Allah ya baka . Ya buɗe baki zai yi magana yaji sun fado kansa da damben hakan yasa ya mayar da maganar tasa yana kallo har ta bar gidan. Leƙawa waje yayi ya kira mai gadi ya ce ya kira masa Abdul yanzu dan Allah. Ai kuwa sai da uncul Abdul yazo kafin wannan faɗan ya rabu, kowa na sauke ajiyar zuciya.

Haka dai Ummu taci gaba da rainon cikin da duk inda tace sai ace ai ya shiga wata biyar cire sa hatsari ne zata iya rasa ranta idan ta dage, hakan yasa ta hakura. Sosai rayuwar take gara musu, ana faɗuwa ana tashi, uncle Abdul yazo akan zai tafi da Ziyach gidan sa domin rage wasu abubuwan amma firr yace ba zai je ba sai dai ya tafi da Hakim. Shima Hakim ya ce sai dai a tafi da Ziyach.  Cikin ikon Allah wannan karan batayi wannan kumburin ba, sai dai tayi nauyi sosai, domin saida Anty Bintu ta sake dawowa gidan domin yi mata girki da dai sauransu, babu yadda batayi akan ta ɗauki mai aki ba amma taki yarda. Kuma ba komai ya hanata ba sai yanayin yaran gidan da kullum basu da saiti zagi a bakunansu kamar ƴaƴan maguzawa. Cikin ikon Allah ta Haifi ƴa mace mai kyau da ita, mai kama da ƴan uwanta. Sai dai wannan karan bata sha wannan wahalar da take tunani ba, kuma cikin ikon Allah lokacin da ta haɗa ido da yarinyar sai taji wani irin sonta ya shigeta har sai da ta lumshe ido. A ranta tana jin sai yanzu ta san ta haifi ƴa tata ta kanta. A washegari aka sallamosu kuma ranar suna yarinya taci sunan Nadiya. Ba ita kaɗai ba kowa na gidan Allah ya ɗora masa son Nadiya domin tana da shiga rai sosai. Haka suka cigaba da rainon ta har lokacin ba'a zama lafiya a gidan Alhaji Alpah. Rikicin Hakim da Ziyach sai ƙaruwa yake, yayin da suma iyayen har zuwa lokacin babu jituwa. 

*Bayan shekaru biyar*

Filin ƙwallon ya cika sosai da makallata wannan babban wasa da kowa yake son ganin yadda zata kasance domin kuwa yau shine wasan karshe wanda suka ci sune zakarun gasar. Yara ne wanda ake kira da ondar 15. Wato yan ƙasa da shekaru goma sha biyar. Masu jajayen kaya da masu fararan kaya ne tsaye a tsakiyar fili suna jira alƙalin wasa ya busa wusir ɗin sa a fara fafatawa. Daidai lokacin da filin wasan ya natsu ana jiran alƙalin wasa ya bada dama ne muryar wata ƙaramar yarinya ya karaɗe filin tana kiran sunan ɗaya daga cikin yan wasan da zasu fara ɓarje gumin su a gurin. Sanye yake da farar riga mai ɗauke da lamba bakwai ga kaftin a ɗaure da hannunsa na hagu, yana gefe guda yana ɗan mommotsa jikinsa kafin a fara. "Ziyach!. Shine sunan da yarinyar ta kira a daidai lokacin kuma alƙalin wasa ya bada umurnin fara wasan. Sai dai kuma hankalin mai sunan ya tafi ga mai kiran sunan nasa. Nan take ya shiga dube-dube har aka bugo masa fasin bai sani ba kwallon ta dangana da waje. Sosai Koch ɗin nasu yake kiran sunan Ziyach ɗin yana masa ihu kasancewar dashi suka dogara a team ɗin nasu. Da yawan yan kallo ma kowa na mamakin meye ya ɗaukewa tauraron team ɗin hankali haka. Su kansu ƴan team ɗin su Ziyach ɗin magana suke masa ganin kamar ma ya manta da kansa ne. Shi kuwa Ziyach gaba ɗaya neman ta inda zai hango yarinyar yake amma ya kasa hangota. Yana haka yaji an face shi da ball ɗin a goshin sa hakan yasa ya dawo da kallonsa ga cikin filin da har abokan karawar tasu sun nufi ragar tasu amma Allah yasa mai tsaron ragar su Ziyach ɗin ya kama Ball ɗin ba tare da anci ba. Hakan yasa yan wasan nasa suka samu damar tsayawa suyi masa faɗa. Hannu kawai ya daga musu yaci gaba da buga wasan , sai dai har lokacin yakan waiga baya ko zai hango ta. Minti goma da farawa aka zurawa masu fararen kaya ƙwallo ɗaya, hakan yasa duk filin ya hargitse da murna ga magoya bayan masu jajayen kaya. Lokacin kuma magoya bayan Ziyach ɗin da yaki sakewa ya buga wasan yadda yake yi suka fara ƙoarafi. Har ƴan kallo na tambayar anya kuwa Ziyach lafiya yake. Haka dai aka cigaba da wasan har aka tafi hutun rabin lokaci ɗaya ba ko ɗaya. Sosai Koch ɗin yake tambayar sa ko bashi da lafiya a sauya shi. Ziyach yace lafiyar sa lau. Ya ce "To meye yake damun ka, kasan cewa wannan shine wasan karshe amma ka tsaya kana abu kamar mai tunani, kana yaro da kai mai zaka tsaya yiwa tunani haka? Ko dai ka fara soyayya ne? Ziyarci dai bai sake cewa komai ba. Haka dai aka dawo wasa sai dai wannan karan sosai yake ball ɗin ganin dai zasu iya rasa wannan nasarar da ita ce mafarkin sa a kullum, bashi da wani buri da yafi ace yau ya ɗauki wannan kofin ko dan ɗan uwansa kar ya samu damar goranta masa, kasancewar shi Hakim sunyi nasu wasan ƙwallon kwandon kuma sunyi nasara, to hakan yasa shima yake da wannan burin. Minti uku da dawowa Ziyach ɗin ya rama musu ƙwallon da tasa kowa farin ciki domin kuwa mutane da yawa domin sa suka zo kallon wasan kasancewar ya iya Ball ɗin sosai, domin idan yana wasa da Ball dole kayi nishadi. Haka dai wasa ya ɗauki zafi ko wani bangare suna neman damar da zasu ƙara kwallo ɗaya domin suyi wannan nasarar. Ziyach ne ya ɗauko wata kwallo wacce daga shi sai mai tsaron gida wato kifa. Gudu yake sosai ƴan kallo kuwa kowa ya tashi domin suna da tabbacin cewa Ziyach sai ya zura wannan kwallon domin kuwa sun yarda da shi. Sai dai kuma cikin muryar kuka ya sake jin muryar wannan yarinyar ta sake kiran sunansa wanda yana ɗaga kai ya hangota tsaye a bakin filin wasa idanuwanta duk cike da ruwan hawaye. Ziyach bai san lokacin da ya bar Ball ɗin ba ya nufo gurin yarinyar da tana ganin sa ta juya da gudu tana kuka. Hakan da ya gani yasa yabi bayanta shima yana tsayar da ita da gudu. A cikin fili kuwa sosai yan kallo suka bisa da kallo ganin ya bar Ball ɗin ya fita waje. Shi kuwa Koch ɗin su harda faɗuwa a ƙasa tsabar rudewa ganin wannan abun da Ziyach ɗin yayi. Hakan kuwa da Ziyach yayi ya bawa abokan karawar tasu damar daukar ball ɗin da gudu basu tsaya a ko ina ba sai cikin ragar su Ziyach ɗin kasancewar dayawa yawan ƴan wasan su Ziyach ɗin hankalin su ya tafe ga abun da Ziyach ɗin yayi. Ai kuwa take magoya bayan su suka fara ihu suna murna. Sosai filin wasan ya rikice da ihu ana kiran sunan yaron da ya ci wannan Ball ɗin. Kasancewar a karshen lokacin tashi ne yasa yan wasan su Ziyach suka fara zama a cikin filin sun gama saddaƙarwa wasu ma har sun fara kuka domin kuwa bai fi minti biyar ya rage a tashi ba. Shi kuwa Koch nan take ya ɗauko wani wanda zai sa a matsayin chanjin Ziyach ɗin da ba wanda yasan ina yayi, domin kuwa babu wanda yaji kiran sunansa da yarinyar tayi sai shi ɗaya domin yana kusa da ita. A daidai wannan lokacin Koch ɗin su Ziyach da ƴan wasan suna jin cewar da Ziyach zai zo gurin nan babu abun da zai hana basu haɗa masa jini da majina ba, domin kuwa sun saka rai da wannan kofin, yanzu haka wasu kuka suke yi sosai akan abun da ya faru. Shi kansa mai horar da su ɗin idanunsa sun yi ja kamar zai fashe da kuka, tabbas badan shi babba bane da yanzu shima kukan yake kamar yadda yaran suke ta kuka bayan alƙalin wasan ya busa tashi a wasan gaba ɗaya wanda aka tashi 2-1. 

Bangaren Ziyach kuwa sai da suka ɗanyi nisa da gurin wasan kafin ya iya cafke yarinyar da take gudu kamar itama yar wasan ƙwallon ƙafan ce. Rikota yayi ya juyo da ita suna kallon juna cikin harshen Ingilishi ya ce "Tell me ina kika shiga yau? Me ya faru tun ɗazu ina jiran ki, ina kika je? Ya jera mata tambayoyin yana kallon cikin idanun ta da suke cike da ruwan hawaye. Ta ce "I'm hungry" Ta faɗa hawayen nata na ƙara zurarowa daga cikin idanun nata. Hannunta ya kama suka karasa gefe guda ya share mata hawayen ya ce "Ina kika je tun ɗazu nazo ina neman ki kuma na faɗa miki yau muna da wasa karfe huɗu idan nazo ban ganki ba zan tafi amma ban same ki ba?" Ya faɗa yana dosar wata mai sayar da abinci da ya gani nesa da su, duk da kuwa babu ko sisi a jikin sa, hasali ma kayan jikinsa babu aljihu."Ta ce "Mommy ce yau tace sai nabi Daddy mun koma gida, shi kuma yace ba zai tafi dani ba sai dai na zauna a gurinta, shine fa suke ta faɗa kowa yace ba zai zauna da ni ba. Ta ƙarasa tana share hawayen ta. Ya ce "Shine kika tsaya kina kallonsu baki zo ba? Ta ce "Sunki bari na fita ne wai dole sai na haɗa kayana na bisa, shi kuma yaki yarda. Ta faɗa daidai suna isowa gurin mai abincin. Yasa aka haɗa mata abinci harda abun sha ya zaunar da ita tana ci yana kallon ta...📝

Muje zuwa yan amanar S Reza.

One love 
One house 
Comment's 
And shering
Love my fans 
By S-Reza ✍️

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.