Free chapter · Read without an account

Kamar da wasa pg 21

by Fatima Isah · KAMAR DA WASA

KAMAR DA WASA💘


                 Fatima Isa 




                    Page 21





Washegari. 
Tun fitowar alfijir,Naana ta nufi kitchen tare da kukunsu domin shirya abinci.
Naana na zaune tsakiyarsu tana gyara musu uniform na makaranta.

Shattima ya fito daga ɗakinsa sanye da kaya masu sauƙi amma masu ɗaukar ido, farar riga mai kyau da wando navy blue. Fuskar nan tasa a ɗaure kamar kullum, amma akwai wani sabon annuri a idanunsa da ba kowa ke iya hango shi ba.

“Good morning Abie!” cewar Iman tana tsalle ta nufe shi.

Ya ɗaga ta sama sannan ya rungume ta cikin ƙarjishi. 
“Morning princess. Kin shirya zuwa school?”

“Yes!” ta amsa tana dariya.

Minal kuwa tana tsaye tana turo baki Shattima ya kama hannunta cikin tsantsar ƙauna ya ce:
“Come on, my baby. Time to get ready fushi na meye kuma?”

Naana ta miƙe da nutsuwa tana ƙoƙarin share gumin da ya bayyana a goshinta saboda aikin safe. Idanunta suka haɗu da nasa na ɗan daƙiƙa, ta yi saurin kau da kai. Duk da haka zuciyarta ta ɗan tsaya saboda irin kallon da ya sauke a kanta,  ya isar da sako.

“Naana.” 
ya kira sunanta cikin murya mai sanyi
.
“Na'am Hamma Awali jam” 
ta amsa da ladabi.

“Kin tashi lafiya?"
 "Alhmadullilah "
 "Masha Allah ki tabbatar sunyi breakfast kafin su fita. Ni kuma I’ll be in my office. If you need anything, talk to Waziri. Clear?”

“Ok Sir.” 
Ta amsa tana lumshe ido, zuciyarta na cike da farin ciki da izzar mijin nata.

Khalid ya kallesu da murmushi  ya ce

“Sir, akwai takardun briefing daga Abuja. Na baro su a ƙasa.”

Shattima ya ɗaga kai ba tare da kallonsa ba

“I’ll check them before noon. Keep everything ready.”

Ya juya ya nufi ƙasa da takun da yake sa kowanne ɗa namiji nutsuwa. Har ƙofar falon, sai ya sake waiwaya ya kalli Naana, bai ce uffan ba, amma murmushi ƙarami ya bayyana a gefen leɓensa.

Wannan safiya ya zama sabon babi ga Naana tsakanin soyayyarta da ta samu amincewa, da kuma izzar da ke sa zuciyarta ta ƙara jawo shi cikin ruhinta.

***

Yau Shattima sai daya tabbatar ya gama komi ya yi handing and taking over ga sabon commender daya zo Sannan hankalinshi ya kwanta
Dare ya fara yi  nutsuwa mai kama da fassararsa komai shiru ya fara sauka, sai ƙarar ƙudan zuma a gefen fitilar baranda. Iskar Lagos mai sanyi tana busowa cikin natsuwa, tana motsa labulen falon cikin salo.

Shattima ya dawo daga office da misalin ƙarfe tara na dare. Ya gama komai, ya sallami ma’aikatanshi, ya bar ofis ɗin da takardun da yasan bai karasa wasu ayyukan ba a cikin su. Kamar yadda zuciyarsa ma ta gaji.
Haka ya shigo gidan da takun da kowa ke gane shi da shi, ba da sauri ba, amma cike da iko.

Naana tana zaune a falo  cikin doguwar riga mai launin cream, kanta a ɗan daure da veil mai launin peach. Hasken fitila ya daki fuskarta ya zame mata wani irin kyalli tare da bayyana hasken fatarta mai laushi.

Lokacin da ya shigo, ta ɗan miƙe da girmamawa ta ce.

 “Welcome, Sir.”

Dan ɗan zaman da ta yi da yar uwarta duk ta fahimci wasu abubuwa nashi da yake so.
Ya ɗan kalle ta na ɗan lokaci ba tare da ya ce komai ba. Sai ya cire hulanshi ya ajiye, sannan ya nufi kujerar gefenta ya zauna, ya jingina da baya yana sauke numfashi.

Naana ta tsaya a gefe, tana kallonsa da idanunta masu taushi. A yadda ya jingina, sai ta gane akwai gajiya, akwai tunani. Tana son ta tambaye shi, amma tsoro da kwarjini suka hana ta.

Sai ta ce a hankali
  “Zan kawo maka ruwa”

Ya ɗan jinjina kai “Hmm.”

Ta juya cikin natsuwa, tana tafiya  ba jimawa ta kawo masa ruwa cikin glass cup mai sanyi. Lokacin da ta miƙa masa, hannunta ya shafi nasa na ɗan daƙiƙa kaɗan, amma ya ishe shi ya sa zuciyarsa ta yi wani irin bugawa da bai so ba.
Ya karɓi ruwan yana sha, idonsa kafe a kan fuskarta.
Hasken fitilar ya ci gaba da haskaka fatar hannunta, yana ɗaukar hankalinsa har sai da ya yi ƙoƙarin juya kai gefe.

 “Kin gama shirya su yaran?”
Ya tambaya a hankali, kamar ba ya son ya yi magana ba.

“Eh, sun tafi bacci. Iman tana ɗakin Mama Binta nasan ita ma ba jimawa zata kawota ɗaki.”

 “Good.”
Ya ce yana jingina kansa, yana kallon sama.

Shiru ya rufe falon. Sai sautin agogon bango da ƙarar shassheƙar iska suka cika sarari. Naana na tsaye a gefe, zuciyarta cike da bugun da ta kasa bayyana ko na meye.
Ganin iska ta taso na hadari sosai yasa.
A hankali ta isa wajan labulen gefen window ta rufe, sannan ta juya da nufin wucewa sai murya tasa ta dakatar da ita

 “Naana.”

Ta tsaya cak, da sauri ta amsa shi

“Na’am, Sir”

 “Kin tabbata komai lafiya dai ko?” 
 “Lafiya lau.”
Ta amsa da murya mai rauni, amma idanunta sun kasa kame rawar motsin da ke cikinsu.
Ya jinjina kai, bai ce komai ba, amma idonsa ya tsaya a kanta na fiye da daƙiƙa goma. Wani irin shiru mai nauyi ya mamaye falon, wanda yake cike da abin da kalmomi ba su iya faɗa.
Ta sunkuyar da kai cikin ladabi ta ce
  Bari na je na yi shirin barci me za'a kawo maka nasan dai baka cin abu mai nauyi daddare"

 Ido ya ɗan lumshe a hankali ya buɗe a kan fuskarta ya ce.
  "No  bana bukatar komi idan kin gama dai kizo zamu yi magana"
  "To"
 ta ɗan murmusa kawai, sannan ta nufi cikin ɗakinta.
Shattima ya bita da ido har ta ɓace a jikin labule.
Ya runtse ido, yana furta a hankali

  “Allah Ka bani ikon fahimtar yarinyar nan kada na shiga hakkinta”

Sai ya miƙe, ya ɗauki takardunsa, amma ransa ya kasa daidaituwa  ba saboda aikin da ya baro ba, saboda yanayin da ba zai iya fassara shi ba.
Sai da ta gyara jikinta ta fesheshi da turare kala kala kafin ta ɗauki wasu shegun kayan barci ta saka ita kanta tasan kayan sun amshi jikinta kafin a hankali ta nufi ɗakin shi ta kwankwasa.
A take ya bata izinin shigowa shima har ya sauya kayan jikinshi zuwa na barci. Kallo ɗaya ya yi mata ya lumshe idanunshi take yaji wani abu ya tsarga ɓargon jikinshi.
Ido ya buɗe a hankali ya sake sauke su a kanta ɓoyaya a jiyar zuciya ya sauke a hankali ya ce.

 " Come in"
Yana mai nuna mata gefen shi. 
Cike da nuna ita ma ɗin ba daga baya ba ta karaso cikin sauya wata tafiya mai ɗaukar hankali.
Inda ya nuna mata dab dashi nan ta zauna tare da sadda kanta kasa.
 "Come on my friend  ki saki jikinki ki daina wani nuna kina jin kunya ta bayan jiya kamar yanzu na yage wannan kunyar ciki da bai" 
 Murmushi ta sake tare da rufe fuska tana cewa.
  "Kai Hamma Sham babba da kai"
  "Au karya na faɗa ke fa kin fi ni sanin komi tunda kin taɓa aure kinsan meke tafiya a wannan yanayin"
 
Shattima ya ƙasa magana yana mai kai hannun yana ɗan daga fukarta suka haɗa ido, cike da sauke mata wasu sakonni ya Matso da fuskarshi dab da tata suna musayar numfashin juna.
Sun ɗan dauki min 5 kafin ya manna mata kiss a goshi ya ɗauko wayanshi yana mai kiran sunanta a hankali.
  "Naana"
  "Na'am"

Ajiyar zuciya ya sauke ya ɗan kwantar da kanshi jikin kan gado a hankali ya ɗan kwantar da ita jikin shi ya ce.

 "Naana tomorrow in shaa Allahu morning flight ɗinmu zai tashi zan wuce Katsina so ina fatan dan Allah komi ya taso just call me ga yarana nan nasan kema yaranki ne ko babu aure a tsakanin mu, ki rike su amana bana son bayan tafiyata naji wani abu ya taso kuma any moment zaku iya bina akwai driver da zan bar maku duk inda zaku zai dinga kaiku. Ki duba account ɗinki na saka maki kuɗi ki aje wajen ki ko wani abu ya taso kinji ko"

Cikin sanyin murya ta ce.

 "In shaa Allahu Allah yasa kaje a sa'a"
  "Amin ya rabbi yanzu me zan samu kinsan ya kamata ayi min ban kwana mai kyau"
 Ya karasa magana yana mai tura hannunshi cikin rigarta dariya ta yi ta ce.

 "Hamma komi nawa naka ne"
  "Hmm are you sure?"
  Gyada mashi kai tayi cikin kashe murya ta ce
  "Am very sure"
Ida rugumeta ya yi jikinshi tsam daga nan labari ya sauya ......


Da gudu na fito na baru ɗakin

#Son zuciya 
#Makirci
#Yaudara
#Soyayya
#Bemty

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol