Free chapter 路 Read without an account

Chapter 19-20

by Amanarcool 路 AKWAI SILA

馃挦 AKWAI SILA 馃挦


BY AMANARCOOL 


YOTA ID/021

*SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KU茒I 茦ALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA 茦WAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DA茒EWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTU苼A TA KAI TSAYE KU TUNTU苼E NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA ****.


PAGE 19-20


Tana dur茩ushe a gabansa, ba tare da tunanin komai ba, ta bu蓷e jakar makarantar ta ta 蓷auko kwalbar ruwa da biskit ta mi茩a masa hannunta na rawa ta ce "Kar蓳i ka ci don Allah".

Ya kalli ruwan a hankali ya kar蓳a ya sha ka蓷an ya ajiye, da 茩yar yake iya motsa hannunsa, Joriyya ta bu蓷e masa biskit 蓷in ta mi茩a masa ya amsa.

Direba ya matso kusa yana cewa "Shalele mu tafi, wallahi ina cikin matsala idan aka gan ki a nan fa".

Cike da tsiwa ta juya tana kallonsa ta ce "Bazan tafi ba, taya zan tafi na bar shi a haka? Ka jira ya gama ci sai mu tafi".

Kar蓳ar biskit 蓷in ta yi ta fara karya masa shi 茩ananu tana bashi, amsa ya yi yana ci a hankali, idanunsa na kallon ta ko 茩iftawa baya yi.

"Baka da suna ne?" ta tambaya murya a sanyaye

Shiru ya yi mata, ta kuma cewa "Ko ka manta da sunan naka ne?".

Ya girgiza kai ka蓷an, ya bu蓷e baki kamar zai yi magana sai ya fasa, yana jin yadda hannunsa ke yi masa ra蓷a蓷i, ya 蓷aga shi sama yana huci. Joriyya ta kalle hannun hawaye na ci gaba da zubo mata ta ce "Wannan hannu ciwo yake maka sosai ko? Zan sa Dady ya kai ka asibiti".

Da jin kalmar asibiti ya janye hannunsa da sauri, tsoro ya bayyana a fuskarsa, ya fara girgiza kai yana ja da baya.

"Baka son asibiti ne? To ba za a je da kai ba, za a siyo maka magani kasha ka ji dama". Ta fa蓷a tana matsowa kusa da shi.Kallon ta yake yi sosai, idanuwansa sun yi ja, hawaye sun taru a ciki, bakinsa ya fara motsi a hankali "Ki tafi..." Bai 茩arasa ba ya yi shiru.

Ta tsaya cak, zuciyarta na bugu da sauri ta ce "Kana magana da ni ne?"

Direba ya dafe kansa ya ce "Wannan yarinya 拼ar bala'i ce, ko tsoron ya sha茩eta ba ta yi". 

Wata tsohuwa ta zo wucewa ta tsaya tana kallonsu, ta ce "Ke yarinya kin san ko waye shi kuwa?".

Joriyya ta 蓷ago ido cike da hawaye ta ce "Ba na san shi ba, sai dai bai kamata ya kasance haka ba, dubi hannunsa babu wanda ya taimaka masa, kuma jama'a na kiran sa da mahaukaci".

Tsohuwar ta girgiza kai ta ce "Shi ba mahaukaci ba ne, abin da ya same shi ne ya fi hauka muni".

"Me ya same shi?" Joriyya ta tambaya da sauri

Tsohuwar ta yi murmushi ta ce "Yariya tashi ki wuce gida kin ji".

Kafin Joriyya ta sake yin wata maganar direba ya ce "Shalele wallahi lokaci yana tafiya, ki taso muje ka da ki saka ni a matsala".

Ta kalli mahaukacin ta ce "Ka yi ha茩uri zan dawo, za a baka maganin wannan ciwon".

A hankali yake tu茩in zuciyarsa a cunkushe. Idanunsa sai shawagi suke yi a titi, motar da ya gani a gefen titi kusa da bola ya sa zuciyarsa ta buga da 茩arfi.

Ya rage gudu yana kallon motar sosai "Joriyya?" ya furta a ransa, taka birki ya yi, ya fito daga motarsa ya tsaya can nesa, ji ya yi zuciyarsa na harbawa da sauri, idanunsa suka sauka a kan Joriyya dake dur茩ushe a gabansa tana kuka, mutumin da kowa ke gudu, wanda Duniya take kira da mahaukaci, shi ne yarinyar da yake yi wa kallon uwar 拼a拼ansa take yin wannan abin a gabansa? Take ransa ya 茩ara 蓳aci ya ce "Haba Joriyya, me kike nema a gurinsa ne? Me yasa kike kusantar shi haka?" ya tambayi kansa cikin 蓳acin rai. "Ba zan bari wannan abin ya ci gaba da faruwa ba". Yana kallo Joriyya ta mi茩e ta shiga mota direba ya ja suka bar gurin.

Shiga tashi motar ya yi, zuciyarsa cike da ba茩in ciki ya rufa musu baya.

Suna isa gida ta fito da sauri ta shiga ciki zuciyarta cike da damuwar halin da ta baro shi a ciki, tana shiga falo ba ta ma lura da Momy ba ta fara 茩o茩arin hawa saman bene. "Auta" Momy ta kira ta "Ina kuka tsaya tun 蓷azu? Me ya faru kika dawo cikin wannan yanayin?". "Momy shi ne fa" kafin Momy ta yi magana Jiniyo ya shigo falon fuskarsa a murtu茩e, idanuwansa sunyi jajur.

"Jiniyo?" Momy ta furta da mamaki "Lafiya ka shigo haka kamar wanda aka je fo?". Bai ba ta amsa ba, kai tsaye ya nufi Joriyya da ta tsaya cak a tsakiyar falon "Me kika je yi gurinsa?" ya tambaye ta cikin fushi. Joriyya ta kalle shi ta ce "Shi wa?" "Karki raina mini hankali Joriyya! Na ganki da idona, na ganki gurin mahaukaci nan, kina dur茩ushe a cikin bola kamar wata mara galihu".

Momy ta ce "Subhanallah! Jiniyo me kake nufi? Ba dai gurin wannan mahaukacin ka ganta ba" . "Can na ganta Momy, baki ga a yadda na ganta ba. Momy Joriyya na son zubar da mutuncin gidan nan". Joriyya ta 蓷aga kai tana kallonsa idanunta cike da hawaye, cikin rawar murya ta ce "Ba mahaukaci ba ne, ka da ka sake kiransa da wannan sunan!". "Me kika ce?" Ya tambaya cikin fushi da zafin kishin da yake jin yana nu茩ur茩usar sa.

"Na ce ba mahaukaci ba ne, mutum ne kamar kowa, kawai an manta da shi ne" ta fa蓷a da 茩arfi, 茩ara har zu茩a ya yi ya ce "Ke Joriyya ki shiga taitayin ki, wannan mahaukaci ne, kin san irin hatsarin da kike jefa kanki a ciki kuwa? Bana son damuwar nan da kike yi akan sa, wannan ai hauka ne". Ya 茩arasa maganar cikin hargagi

"Idan tausayin sa ne da nake ji ya zama hauka, na ji 蓷in ni mahaukaciya ce" Joriyya ta maida masa martani.

Mutuwar tsaye Momy ta yi, ganin abin zai zama rigima a tsakaninsu ya sa ta ce "Ya isa haka, ku daina wannan rikicin ba na so. Auta wuce ki bani guri kafin in sa蓳a miki". "To Momy zan wuce" ta dubi Jiniyo ta ce "Ka da ka sake shiga harka ta, kuma ka daina kiransa mahaukaci". Jiniyo ya girgiza kai cikin takaici ya ce "Na yi tunanin kina da hankali ashe ba haka ba ne, yau kin karya mini zuciya Joriyya".

"A'a bayanka dai na karya ba zuciya ba, ina naga zuciyar taka da zan karyata? Bana son sharri kuma ka daina shiga harka ta". Tana gama fa蓷ar haka ta haye sama da sauri.

Cike da ba茩in ciki Jiniyo ya juya ya fita ransa a matu茩ar 蓳ace, yana 茩ara jin 茩iyayyar mahaukacin nan mai tsanani a zuciyarsa, take ya sha alwashin sai ya 蓷auki hukunci mai tsanina a kansa, sai dai komai zai faru ya faru.


Momy ta zauna a falon idanunta sun canza launi "Wannan wace irin masifa ce? Yarinya gaba蓷aya ta rikice, anya ba malami zamu samu ya yi mata addu'a akan wannan lamari ba?" Tana tsaka da tunani ta ji ana kiran wayarta ko da ta duba Na'ima ce, 蓷auka ta yi jiki a sanyaye 

"Hello Momyna"

"Na'am Na'ima ya kuke?".

"Alhamdulillah Momy ya gida? Ya Dady da kuma rigimamiyar ku?". 

"Kowa yana nan lafiya, Auta yanzu ta dawo daga school, ina Ummie ne tana lafiya?".

Na'ima ta ce "Ummie yanzu ta fita da Dadyn ta. Momy ina fatan dai Auta ta daina rigimar da take yi 蓷in?". Momy ta nisa ta ce "Tsakanin jiya da yau kafin ta je school ta yi sau茩i duk da abin na ranta, amma daga fitar ta makaranta kinga yanzu ta dawo a rikice, ashe da aka tashe su daga school sai da ta biya gurinsa kafin ta dawo gida, baki ga rigimar da suka gama yi da Jiniyo ba da ya ganta a gurin. Na'ima al'amarin nan ya fara isa ta, na fara tunanin ko malamai za mu sa suyi mata addu'a. Yanzu fa hadda fa蓷in take yi wai ha mahaukaci ba ne, an manta da shi ne, ban san me take nufi da wannan maganar ba. Yaro kamar ba mutum ba gaba蓷aya yarinya ta rikice akansa, kuma fa sai kin ganshi ba wani babba ba ne, matashi ne kamar Jiniyo".

Na'ima ta ce "To Momy ya aka yi ta je gurin sa? Ba tare take da direba ba?".

"Na'ima sai ka ce baki san halin Auta ba, tare take da direba kin san dai halin tsiwarta idan ta tashi, ina tunanin tursasa masa ta yi, dole ba yadda ya iya ya je 蓷in".


"Duk da haka Momy bai kamata suna biye mata ba, tunda sun san ba ku son hakan da take yi, sannan Momy na ce idan kunga da matsala ta dawo gurina da zama mana, ina ga idan aka nisanta ta da shi ai za ta ha茩ura".

 "Ina ga hakan za a yi, duk da ta ce ba za ta je gurinki ba, amma dai yanzu bari Alhaji ya dawo na ji yadda zamu yi da shi, a fara saka malamai su yi mata addu'a tukuna mu ga abin da hali yayi, idan ba ta daina ba dole za ta bar 茩asar nan".

Na'ima ta ce "To shikenan Momy, duk yadda ake ciki ki sanar dani, ai ba dole sai ta yarda ba" ci gaba da tattauna matsalar suka yi daga 茩arshe suka yi ajiye wayar.


Joriyya na shiga 蓷aki ta zauna idanuwanta cike da hawaye, zuciyarta na bugawa da sauri, ta yi shiru tana tunanin yadda taga hannunsa ya 茩ara kumbura "Dole ne nasa Dady ya siya maka magani, ba na son ganin wannan ciwon a hannunka" ta 茩arasa maganar tana matsar 茩wallah.

Da yamma sosai Dady ya dawo gida, bayan ya yi wanka ya ci abinci. Momy ta ce "Alhaji Auta fa ta koma gurin mahaukacin nan yau". "Kamar ya? Ban gane ba? Ba yau school ta je ba? Taya aka yi har ta fita ta je gurin sa?" Ya yi maganar yana tsare Momy da ido. 

"Alhaji daga school 蓷in ta wuce gurinsa, bayan an tashe su".

"What! Taya aka yi ta je can 蓷in? Ina direba ne ko ba aje 蓷aukar ta ba ne?" 

"Tare fa da direba take, tare suka je gurin" Momy ta fa蓷a tana kallonsa. Cikin tsanin fushi Dady ya mi茩e tsaye zai fita, da sauri Momy ta ce ''Alhaji ina za ka je ne?" .

"Zan je in ji dalilin daya sa zai kai mini yarinya gurin wannan banzan" . Momy ta ce "Haba Alhaji kafa san halin Auta, ni yanzu ba zanga laifinsa ba, ina da ya茩inin takura masa ta yi, ka yi ha茩uri ka da je yanzu, idan ma magana za ka yi masa ka bari sai gobe. Alhaji lamarin nan ya fara 蓷aure mini da kai, yau dalilin zuwanta gurin nan sai da na shiga tsakaninta da Jiniyo, baka ga rashin kunyar da ta yi masa daga ya yi mata maganar ta daina zuwa inda yake, ka yi ha茩uri koma ka zauna ina da shawara". 

Komawa ya yi ya zauna yana jin zuciyarsa na yi masa zafi sosai "Duk da haka Shafa bai kamata ya biye wa Shalele ba" ka yi ha茩uri Alhaji, yanzu dai ina da shawara, ni a ganina mu saka malamai su fara yi mata addu'a, saboda ina tunanin kamar yaron nan ba mutum ba ne, yarinya gaba蓷aya ta rikice". Shiru ya yi yana nazarin maganarta kafin ya ce "Kin kawo shawara, zan yi wa Malam Nura magana ya ri茩a zuwa yana yi mata addu'a ko Allah zai sa a dace". 

Kafin Momy ta yi magana, kamar daga sama suka ji Joriyya ta ce "Dady nima aljanu ne dani irin na Anty Teema ta makarantarmu? Ru茩iyya za a fara yi mini? Dady bari na kwanta na fara birgima irin yadda Anty Teema ke yi sai a kira Malam ya yi mini ru茩iyya".



Amanarcool
***










Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.