Free chapter · Read without an account

002

by Fatima Muhammad Gurin · SAFARA A TAƁO

SAFARA A TAƁO 


FATIMA MUHAMMAD GURIN 

*GUREENJOH*


*ADABI WRITERS ASSOCIATION*


*PAID BOOK*


*002*


Dukan kawo wuƙa Aunty Kubrah ke yi mata gabaɗaya ɗakin an rasa mai ƙarbar ta sai ma masu kuka don kusan friends ɗin cousins nasu ne, ganin har jini na fita a jikinta ya sa Hudah da take ji kaman jikinta ake zubawa bulalun ta shiga da gudu ta rungume 'yar uwarta tana kukan fitan rai kaman yadda Hibbah ke yi, sam ba zata taɓa cewa zafin bulalar ya fi na zuciyarta ba, zuciyarta gabaɗaya ji take ta tarwatse kanta ya mata nauyi a wurin bata da maraba da saƙago don bata fahimta, bata ji kuma bata gani abinda kawai ke dawo mata tamkar a talabijin bayan hotunan sai fasa Aurenta da Mahmud yayi.


Wani irin balae'en rikici ne ya barƙe a gidan abin ka da kishiyoyi kuma dama Momma a wuyansu take a maƙale, hakanan Hibbah tafi kowani ɗa a gidan shiga ido masu Allah ya ƙara na yi masu Allah ya kyauta ma suna yi, Alhj Mudassir ne ya shigo gidan bayan an samu ya farfarɗo mutum ne shi mai tsananin zafi da faɗa bashi da sauƙi sam, kuma kap cikin yaranshi babu wanda yake yiwa son da yake yi wa Hibbah, shine zata ɗibi ƙasa cikin trela ta watsa mai a ido? Shine za ta muzanta a gaban dubban jama'a? Shi zata kunyata a idon duniya? A haukace ya ci karo da su Mumtaz da Aunty Kubrah da wasu 'yan uwan Momma sun dauƙeta ranga ranga don duk irin dabarar da za'a yi an yi ta ƙi farkawa hankalinsu ba karamin tashi yayi ba, ba shiri ya juya suka nufi asibiti.


Fitansu gidan kaman sabon gurmi ne don tuni su Hajiya Kamila sun cike gidan da zagi da cin mutunci babu mai bakin magana bare amsa cikin 'yan uwan Momma don kunya tabbas Hibbah ta bar masu abin kunya, Daddy Rabi'u ne babban wan Alhj Mudassir ya shelanta cewa biki ya watse kowa ya kama gabanshi kawai a bar 'yan gida komai da zai faru ya riga ya faru kafin awa ɗaya gidan ya zama sai su ya su ahalin gidan kuma har lokacin Hibbah bata bar wani irin kuka da take yi daga ƙasan zuciya ba tana yi tana girgiza kai hannunta ɗaya akan zuciyarta da take ji kama zai tsagata ya fita kunnuwanta na ji mata irin rashin kunyar da ƙanwarta Aina'u ke yi mata, wai yau ita ce Aina'u dai Aina'u dake bi ma Mumtaz a haihuwa take gayawa magana duk saboda kuskurenta... Duk saboda wautarta...

   "Wallahi kika kashe mana uwa sai kin bi ta, ashe baki da tausayi? Ta ji da sharri da bala'in Hajiya Kamila da Hajiya zakiya ta ji da baƙin taurin kanki da rashin jin maganar ki da kullum sai kin ja mata magana a gidan nan kuma yanzu ke da abin kunya ita da mutuwa? Ba zai yiw...."


"Will you shut up Aina'u??"

Hudah ta daka mata tsawa tana kuka akan muryarta, itama Aina'un cikin tsawa tace

"Ba zan yi shiru ba Adda Hudah ba ita kaɗai ba ce! ba ita kaɗai Momma ta haifa ba, ashe ba zata sararawa uwarmu ba? In ta mutu mu waye zai ragar mana? Tirrrr tirr da halinki Hibbah"

Tana kai nan ta fice tana kuka sossai.

Tuni su Amal dama sun tattafi sashen iyayensu gurmi da mayar da magana ya saura Hudah ne da Hibbah.... Ta kasa barin 'yar uwarta duk yadda mijinta ke kiranta a waya ta kasa dagawa, ta kasa shiru da kukan da take yi Dukda na Hibbah ya fi nata sau hamsin sai dai ciwon ƴar uwar haihuwar ta nata ne, dama sun saba duk abin da zai samu daya na sharri ko alkhairi tare suke raba wa amma Hibbah ta fi janyo musu abin kuka Hudah mai haƙuri ce tsantsa.


A chan asibiti kuwa likitoci ne suka rufu a kan Momma saboda ganin sun ceto rayuwarta abin ya daketa sossai hakan yayi sanadiyar hawan jininta ainun da suke tunanin in ba sa'a ba zata iya samun paralyze.

Sai safa da marwa Daddy Zubair da ya tuko su yake yana call Shi ɗin babban DSS ne yana ganin ko da yadda za'a yi a taking pictures ɗin down kuma ayi tracing daga inda ya fito don ya shiga mota zai tafi office kenan ya ga su Alhj muddasir ɗin afujajan tsabar rikicewa duk motocin sun bari gida suka fito da kafa shine ya tsaya kawai aka sanya ta ciki.


"Yaya ka kwantar da hankalinka don Allah kar kaima ka shiga wani hali komai zai yi daidai in shaa Allahu"

Alhj Mudassir dake hadiye wani irin baƙin ciki ya kalli Daddy Zubair hawaye na shirin sauƙo mishi yace 

"Zubair ba zaka gane ba... Nan"

Ya nuna kirjinshi

"Kaman zai fito nake ji, why Hibbah?? Meyasa Hibbah zata mana haka? Me na ragi yarinyar nan da ta zaɓi tozarta ni a idon duniya, yanzu abokan gaba sun samu makami a kaina rasa kujerata kila zan yi, hakan bai wani dameni ba kaman yadda mutuncin gidana da sauran ahalina ya zube don ko za'a mutu wani ba zai taɓa yarda cewa ita ɗin ba 'yar iska bace kaddara ma bata taɓa aikata hakan ba kenan"

Tari ya fara 

"sakayyar kenan? Na nuna mata ƙauna fiye da duk 'ya'yana na fifitata na bata duk wani gata sannan na bata tarbiya Zubair sakayyar da zata yi min kenan"

Kan a ankara jini ya fara fita masa a hanci hankali tashe Zubair ya riƙe shi yana jijjiga shi 

"Yaya..! Doctor...!! Someone please helppp"

Ai da gudu aka yi kanshi shima aka tura shi emergency.

A mugun zuciye Zubair ya fita asibitin haka ya isa gidan kaman zai tashi sama ya haura ɗakin yaran, har lokacin kuka suke wani irin hankado kofa da yayi shi ya saka su duka Miƙewa tsaye, wani irin bugawa zuciyoyinsu yayi.


"Ashe ke ƴar iska ce? Kashe mana ɗan uwa kike so ki yi? Hibbah me kika nema a duniya kika rasa da kika zabi wannan hanyar? Don ubanki kin ce aure kike so ne aka ƙi yi miki?"

Girgiza kai kawai take yi don sun san irin zafi da tsananin shi, shi a gidanshi matanshi ma tsoron motsi me karfi suke

"Don ubanki ki buɗe baki ki yi min magana..! Kin ce a miki aure an ki?"

"Aaa.a..ah"

"Uban me ya saka ki aikata hakan?"

"Wal...."

Wani gigitaccen marin da ya so kurumtata ya sauƙe mata, zata iya rantsuwa ta yi suman wucin gadi ta dawo kan ta gama ganin taurarin marin ya rufeta da mugun duka da belt da ya zaro...


Ihu take yi Hudah na taya ta ganin zai iya kashe mata 'yar uwa kuma babu mai taimako Alhali mutanen gidan sarai zasu iya jin su yasa tayi shahada ta riƙe kafafunshi da ƙarfi 

"Don Allah...Don darajar Allah kayi hakuri Daddy Z, tayi kuskure amma kayi haƙuri jikinta ya farfashe ka tausaya don Allah..!"

Hudah yarinya ce mai hankali da ladabi kowa ya sani tun haihuwar su akan mixer su don ba'a gane wacece wacce a cikinsu sai da suka fara wayo halayensu ya sha bambam nesa ba kusa ba.

"Waye shi ɗin kika ba wa jikinki??"


"Ba...ban yi b...a"

Cikin wani irin wahala take kakaro maganan 

"Nace uban waye kika tambaɗe dashi har yake da shaidah kan ki..?"

Tsawar da ya daka mata ya haɗu da mummunan yanayin da take ciki na jiki da zuciya ta buɗe baki da niyyar magana sai numfashi ya ƙi fita, tamkar mai ciwon asthma haka take kokuwa da numfashinta hannunta ɗaya dafe da zuciyarta tana dannawa saboda ji take kaman ana daddatsawa she's disappointed, betryed, deeply hurt duka a lokaci ɗaya tun tana fahimta har ta zo ta daina fahimtar komai ta tafi luuuuuu ta faɗi ƙasa kanta ya bugi jikin gado shima ya fashe...


Daddy Rabi'u da ya shigo da hanzari saboda shiga da yayi magana da masu aiki akan su zo su gyara gidan

Fitowan da zai yi sai ya ga motar Zubair kuma ya san shine ya tafi da su Momma asibiti hakan ya sa ya hauro da hanzari kar yayi aika aika kowa ya sanshi da zafin zuciya irin Alhj muddasir amma nashi ya haɗu da aikin khaki da yake ya ninka na Alhj muddasir ɗin ihun da Hudah ta tsala daidai faɗuwar yar uwarta yasa ya shigo da gudu, ɗaukarta kawai yayi suka fito da gudu gudu zuwa mota iliya yayi hanzarin buɗe mishi suka shiga da ita kusan duk matan da yaransu kowanne na kofar side ɗin shi suna murmushi yayinda Aina'u ta riƙe autocinsu da suma 'yan biyu ne maza Fadil da Fareed a jikinta tana kara karfin kukanta.


Itama Hibbah emergency aka yi da ita Dr. Najeeb Kabir ne yayi kanta da wasu nurses aka rufu don ceto ta.

A chan ɓangaren Momma an samu ta farfarɗo da kyar an yi mata allurar bacci likitocin suka fito suka kwantar musu da hankali haka ma na Daddy dama yana da 'yar matsalar zuciya amma ba chan ba kuma yana kan samun kulawa kan wannan abu ya faru shima an samu ya lafa ya yi bacci, duk da basu damu da sanin Halin da Hibbah ke ciki ba sai dai kukan Huda da yadda take ta je-ka-ka-dawo sai ya basu tausayi, nan Aunty Kubrah ta janyota jikinta tana rarrashi sai da aka samu awa kan Dr. Najeeb ya fito ya dube su sai dai sam bai yi magana ba don ya karanci yarinyar ya fahimci daga gidansu ne koma mene ya sameta don tana farkawa da haƙuri ta fara tana ambatan sunayen Momma Daddy da su Aunty har ma da Hudah.


Office nashi kawai ya wuce riƙe da file ɗinta a hannunshi, zama yayi yana sake karantar file ɗin da yanayinta nan ya kira wata Nurse ya ba da umarni a je a yi mata gwajin kirjin nan ya gani don kaman ta samu issue da numfashinta, sam bai natsu a kan lamarin ta ba don haka kawai yanayin nata ya mugun taɓa shi Dukda bai san laifinta ba sai zirga-zirga yake yi a ɗakin babu kowa kusa da ita ko a kanta har aka kwana, Washegari da safe yana tsaye kanta ya zuba wa fuskarta da take ta zubar da hawaye idanu cikin salon dakiya da magananshi ya furta 

"Hibbatullah...!"

Bata ko motsa ba bare ta nuna alamun ta ji ƙiran da yayi mata, his gaze are still fixed on her ya ce

"Kashe kan ki kike son yi ne kam? Baki san komai na bawa rubutacce ne ba kuma karɓar kaddara na daga cikin imani ba? Kuka babu abin da zai janyo miki sai wani wahalan Look at this..."

Ya ɗaga file ɗinta yana nuna mata 

"Numfashi ba ya isa huhunki yadda ya kamata, zuciyarki tana nan a kumbure kika ci gaba a wannan hali mutuwa za ki y..."


"Da sai na fi kowa farin ciki, da hakan ya fiye min wannan rayuwar marar future... Ni da fanko duk ɗaya muke saboda ko na rayu zuciya da ruhina sun jima da mutuwa don haka ka kyaleni in mutun kawai ko zan huta..!"

Ta ƙarasa da fashewa da kuka, iska ya furzar yana kallonta zai yi magana sai aka turo ƙofa Hudah ce bayanta mu'azzam ganinsu bai sa Hibbah ta daina kuka ba sai ma kifewa da tayi ta ɓoye fuskarta tana sake fashewa da sabon kuka.. Wani irin abin kunya ne wannan wani irin kuskure giyar soyayya ya sa ta aikata? Taya za ta fara haɗa idanu da mijin 'yar uwarta? Ba za ta iya ba ta tabbatar likitan nan ma da ke nuna tausayawarshi gareta bai san me ta aikata ba ne ko kuma hotunan tsiraicinta da ta tabbatar miliyoyin mutane zuwa yanzu sun gani bai riske shi ba ne.


Ficewa ya yi da ga ɗakin ganin Hudah ma ta fara nata kukan sam baya son kukan mace shi mutum ne mai rauni da tsananin tausayi, ya je wuce Nurse station ya ji wata Nurse tana faɗa wa wata

"ke wallahi yarinyar nan ce a amenity room 8 duba da kyau ita ce wacce gabaɗaya media ya ɗau dumi a kanta sabon update nata ya bayyana, ai ita ce wacce aka fasa aurenta a jiya an ma ce mahaifinta har tsine mata yayi..."

Runtse idanu yayi yana jin ba daaɗi har ranshi a hankali ya wuce su zuwa office ɗin shi, wayanshi ya zara ya shiga Facebook ko scrolling uku bai yi ba ya gamu da hotunan da sauri ya kife kan wayan yana ambaton sunan Allah.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol