Free chapter · Read without an account

5

by Mahma Lamido · INAYATU

Kamar wacce allura ta mintsina ta zabura kadan tana dawowa ainahin duniyar mu, da fada yayi maganar hakanan fuskar sa ta nuna a fusace yake, amma akwai wani sanyi a cikin muryar sa kamar mai lallashin mutum.


    Sunkuyar da kan ta tayi tana wasa da yan yatsun ta kana ta dago kan ta tana sake sauke idanu kan sa, daddadan Amber scent da ya cika dakin gabakidaya ya cika ta wanda take da tabbacin yana fitowa ne da ga jikin sa wato turaren da yayi amfani da shi .

      

      Zuwa lokacin har ya zauna yana kokarin kunna tv domin some part of him na bashi wannan yarinyar na da alaka da shi, yanayin da take da yan uwan sa ya Saba hankali, hakanan a kab fadin duniyar nan bai ga wadanda ke kama da yaran gidan su irin ya yan uncle ubaidu ba. Saboda haka duk yanda akayi wannan jinin sa ce kuma kanwar sa.


     Juyawa tayi ba tare da sake bata lokaci ba ta fice daga falon cikin sassarfa, a nan harabar gurin ta tsaya tana mayar da numfashi tare da dafe zuciyar ta da ke doka mata kamar wacce ta ga abin tsoro


    Sai da ta nutsu kana ta koma cikin gida, zuwa lokacin Ana ta kokarin fitowa da amarya.

        

      Tun da aka gama lunch dazu bata sake sanya sakina ko Sa'ada a ido ba sai yanzu tana chan cikin kawayen amarya hanifa kasancewar sa'anin juna ne su. sa'ada ta karba daga hannun sakina, motar da aka bawa su Amna musamman domin zuwa kai amarya suka bi, daya daga cikin motocin baba Dr ne Katuwar Range Rover Velar ce da mahmaah ta basu su je da ita.


     Daga yan biyun sai ita da wata kawar su Amnan da ta jira kai amarya sai Rabia da ta nace sai ta bisu.


    Gidan hanifa yana sharada phase one , katon gida ne da yaji komai na more rayuwa, kama daga tsarin gidan har izuwa kayan da aka narka naira aka zuba, a nan zasu taba zama da mijin ta kafin su koma Abuja  bakin aikin sa.

    A gajiya likis suka dawo gidan, daga gidan amarya suka rabu da su Dede yayin da ita kuma suka dawo Nasarawa GRA da su Amal.


    Gurin kwanciya kowa ke nema domin dai hidima kam an sha ta a yan kwanakin, har goggoriyon shiga bathroom su ke domin watsawa jikin su ruwa ko zasu ji sanyi.

    Tana jin su suna cin abinci amma ta kasa tashi ta iya ci, saboda wata irin kasala da take ji wacce bata San mafarin ta ba.

   Tana fashin sallah shiyasa ko da asuba bata tashi ba, sai zuwa 8:30 da wata irin yunwa ta tayar da ita, tun jiya bata wani ci abincin kirki ba, ko a gurin event din dan Tsakura kawai tayi ta ajiye, hakanan a Daren jiya ma bata yi dinner ba ta kwanta, shortbread din Amna ne da ta gani kan bedside ta cinye a jiyan.


     Mikewa tayi da kayan bacci jikin ta, ta Saba saka kayan su Amna duk da kuwa yawa da suke yi mata sosai, domin zasu fi ta jiki, pajamas ne masu taushi sai kawai ta Dora gyalen ta na jiya ta fice kitchen domin yunwar da ke cikin ta idan bata yi quenching din ta ba zata iya halaka ta.


    Gidan shiru ba hayaniya sabanin jiya, da alama gajiyar jiya ce ta boye kowa, kitchen ta nufa kai tsaye ta yi tsaye tunanin abinda zata samawa cikin ta, 

fridge ta bude akwai raguwar abinci da yawa daga jiya da aka sanya fridge, spaghetti bolognese ce with meat balls, ta zuba a plate ta saka a microwave tana jira yayi zafi.


     Jinginawa tayi da kitchen cabinet idon ta a kasa tana kidayar tiles din kitchen din.


    Da hanzari aka turo kofar kitchen din, dawowar sa kenan daga morning strolling din da ya zame mishi jiki, a irin wannan lokacin ya Saba har ya shigo ya dauki abinda zai dauka a kitchen din bai ga walgawar kowa ba, except may be sometimes yan aiki.

    Shiyasa wannan Karon yayi mamaki sosai ganin mutum tsaye a kitchen din, kallo daya yayi wa sashen da ta ke ya dauke kai tare da nufar fridge

       A bangaren inaya kuwa bugun zuciyar ta ne ya da da tsanan ta wanda kuma ta rasa dalilin sa, ko bata dago ba kamshin sa da ya cika mata ciki ya tabbatar mata da shi ne a kitchen din, wannan amber scent da ta shaka jiya da kwarjinin sa tun bata dago ba suka shaida mata wanzuwar yayan su Amna a kitchen din.

     

  Bata iya dago da kan ta ba don bata ji zata iya hada ido da shi, har ya buda fridge tare da daukar ruwan swan masu sanyin gaske ya kwankwadawa cikin sa.

   

    A lokacin da yake kokarin daukar kettle din da ke kusa da ita har numfashin ta ta ji yana neman daukewa na wucin gadi

     wannan wane sabon al'amari ne ke faruwa da ita da bata taba ji ba? Inaya ta tambayi kan ta da kanta wasu kwallah na taruwa idon ta.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol