Free chapter · Read without an account
6
by Mahma Lamido · INAYATU
THE SECOND ENCOUNTER
Wani iri take ji, yanayi na rashin kyautuwa ga kin gaishe shi da ta yi, duk da kuwa shi ya kamata yayi mata sallama kamar yanda addini ya tanada amma ai itace kasa da shi, saboda haka ta samu kanta da iya furta
"Good morning Yaya Em" ba tare da ta dago kan ta ba
Sai lokacin ya sake sauke manyan idanun sa a kan ta, masu saka mutum nutsuwa nan ta ke ko shi waye kuwa, shi mutum ne da ya san hakkin dan Adam.
Ya Saba idan ya shigo for his morning coffee one of the workers available ke hada masa, idan ya shigo bai gan su ba, alamar basu tashi ba kenan, shi ba zai tashe su ba saboda kawai su hada mishi coffee after all they are humans su ma.
Da kai ya amsa ta yana kokarin balla murfin bottle water da ke hannun sa alamar a kettle din zai juye.
Samun kan ta tayi da iya karfin halin dago kan ta a hankali tare da sauke masa kallo, sanye yake cikin Track suit din Nike grey in color, zip din rigar a bude yana bayyanar da fara kal din vest din sa da ke ciki, hakan na da da fito da faffadan kirjin sa da ya budu da daga karfe.
Takowa tayi gaban sink din da yake tsaye tana Mika hannun ta "zan hada maka yaya em" ta furta a sanyaye.
Siraran faratan ta ya zurawa ido da suka sha jan lallen da ya haskaka farar fatar ta, yana da da jin kamshin wannan turaren da ta bar masa a falon sa a Daren jiya.
For some seconds da basu Gaza goma ba ya zurawa yatsun ido kana ya sakar mata kettle din ba gardama, karba tayi tana isa gaban sink ta dauraye cikin kettle din kana ta juye ruwan ta kunna heater.
Jinginawa yayi da jikin fridge ba tare da ya sake cewa komai ba yana folding hannayen sa a kirji, tsaye tayi ta kasa Juyowa tana jiran ruwan suyi zafi
Ba tare da ta waiwayo ba tace "tea or coffee"
"Coffee" ya bata ansa kai tsaye, da yake gidan ba bakon ta bane, mug ta dauko, nan da nan ta hada mishi simple coffee mai madara a ciki.
Karbar coffee sa yayi ya juya, yayin da ita kuma ta samu kan ta da bin bayan sa da kallo, har ya kai bakin kofar ya waiwayo kadan
Sakina right? Ya tambaya.
Dan zabura tayi tana dawowa daga shagalar da tayi.
Saukar da kanta kasa tayi kana tace "yaya ta ce sakina, i am INAYA" ta karasa a kasalance, jinjina Kansa yayi tare da dan taba baki kadan ya bar kitchen din yana furta "thank you INAYA"
Tunda ta tashi tayi wayo ta ji ana kiran ta da INAYA, ta sani sunan na ta is Rare and unique in some ways, sai dai bata taba sanin sunan na ta na da dadi har haka ba sai a yau, sai a yau da ta ji shi a bakin wanda ya fi kowa iya furta shi, sai da taji shi a bakin yayan ta, yayan ta mai tarin al'amura masu ban mamaki.
Numfashi mai zafi ta sauke, wadannan new feelings din da ta ke ji, ita kam inaya bata san ma'anar su ba.
Ta dan jima kafin ta samu nutsuwar ta, microwave din yayi aiki har ya kashe kan sa tuntuni, abincin ta ta dauka da chilled Guava juice ta koma dakin su.
Har garin Allah yayi haske fau tana zaune ita kadai kamar mayya, ta rasa tunanin me take yi amma dai tabbas tunanin na ta ba ya dakin.
Sai 12pm su Amna suka tashi, wanka suka yi suka shirya, cikin bakar abayar Amna ta shirya kasancewar bata zo da kaya ba, tsab suka fito tayi wa mutanen gidan sallama, mahma ta bata tarkace souvenirs hakama su Amna sun bata daga cikin na su da suka yi, daga gidan amarya zata wuce gida saboda gobe zata shiga school.
Tunda suka fito ta ke waiwayen tsakar gidan ko da zata hango sa ko daga nesa ne, zuciyar ta ta daina mintsinin da ta ke mata, har suka fice daga gate din gidan idanun ta basu yi tozali da abinda su ke marari ba.