Free chapter · Read without an account

Chapter 4

by Queen Jiddah · GAMO MUKA YI

🥹GAMO MUKA YI🥹





Chapter 4





True Life Story😱🙆‍♀️




By Queen Jiddah...✍️



Free page is about to pinish🔔🤓🙋‍♀️


Idan kana bu'katar ka cigaba da karatun Littafin GAMO MUKA YI to ka hanzarta turo da Naira 300 ta wannan bankin👇


0686693377 GT Bank

HAUWA'U MUSA YELDU.



Shedar Biya ta wannan layin👇

***



A Chapter 6 free Page zai kare, idan har na kammala free page baka turo da kudin ka ba, Tofa zasu dawo N400 🤧 saboda haka saiku hanzar ta🤓.



Wanda ya biya ya turomin da screenshot ta numbern dana saka, saina saka sa a paid group💃💃💃









Chapter 4



Haka naga wannan mayyar a mafarki tana biye dani, da wu'ka a hannun ta.



Koda gari ya waye kowa ban gayawa ba naja baki na nayi gum kar kuma ace karya nake😔.


Kuma maman mu taje gidan matar da sassafe ita da officer sai dai lokacin da suka je matar tariga da ta fita, haka mama ta dawo ta bamu labari, nidai bance komai ba, bayan mun karya kumallo haka mama ta shirya ta wuce gidan aikin ta, Nana ma tayi makaranta muka rage nida maryam a gidan.


Duk inda maryam tayi haka nake binta a baya, domin kuwa har yanzu a tsorace nake🤧, ita kuwa sabgar gabanta kawai take yi babu alamun tsoro ko ka'dan a tare da ita.


Bayan mun kammala aikin gida muka 'daura girki, maryam tace zata je ta siyo kayam miya, nace mata muje na rakata saboda bazan iya zama nika'dai ba.



Haka muka tafi tare sai mita take min ni kuma nayi banza da ita, domin Allah ka'dai yasan halin da nake ciki, saboda dama can ni matsoraciya ce abu ka idan ke razana ni.


Dawowar mu gidan siyan kayan miyan kenan muka nufi hanyar gida, ai kuwa muka yi kicibis da wannan mayyar da nayi mafarki jiya🙆‍♀️ domin ganin ta kawai muka yi a gaban mu, ni kuma sai na'ki yarda na kalle ta cikin karfin hali na raku'ba ta gefen ta na shige gida itama Maryam tabiyo ni a baya.



"Malika! Malika!"

Maryam ta kira ainahin suna na tana karasa shigowa cikin gidan namu.


Kallon ta nayi nace.

"Menene Maryam?".


" hmm wai Malika kin kuwa ga Matar nan, wallahi ke take kallo har kika shege gida idonta yana kan ki".


"Hmm na sauke nannauyar ajiyar zuciya sa'annan nace, wallahi Maryam na gani, kuma jiya har mafarkin ta nayi wai ta biyo ni da wu'ka, shiyasa ma yanzu ban yarda na kalleta ba, kinsan bamu ci abinci ba kuma ance maye yana saurin kama mutum musamman idan ya fita bai saka komai a cikin sa ba".


" Hmm Malika kenan, Allah dai ya kare ki daga sharrin ta saboda ni wannan abin ya fara 'daure min kai, ace daga wannan sai wancan".



Nace mata "Maryam kenan, to fisabilillah ita wannan mayyar ta rawa wa zata biyo saini, yo ina ma laifin ta biyo ki tinda ke kinada jikin ki tubarikalla, ni kuwa kamar a busa na fa'di, idan ba jaraba ba me maye zaici a jiki na😩".



Maryam kuwa Ranta baci yayi cikin masifa tacemin.


" Wallahi Malika mugun fatanki ya tsaya akan ki, a hakan dai da nake tu'bul tu'bul 'dina a haka zasu kyale ni, kuje can ku 'karata ai ke suka gani suka ce kinyi musu" a haka dai tayi ta masifa ni kuma na zuba mata idanu, tinda dai ba dakuwa zanyi a wurin ta ba.




Bayan kwana biyu, muna zaune tare da Maman mu da kuma Maryam, sai nake cewa Mama.



"Maman Mu nidai inason mussa( Mage ) dan Allah ki bari na kar'bo ta gidan Aunty Jamila wallahi ta kira ni ta gayamin wai Magen ta ta haihu nazo ta bani 'daya"😁.


Daga Bu'dar bakin ta saita cemin.


" Wai Malika lafiyar ki Kalau kuwa?".


Sai nace "me nayi Maman mu?"🥹.



" ok baki ma san me kika yi ba kenan? To idan baki sani ba bari na gaya miki, kinji na rantse wallahi babu mai kawomin Mage a gidan nan! Sanin kan ki ne sarai Nana tsoron mage take yi, shine saboda tsabagen son kai irin naki zaki ce ki kawo mana mage, to ba'a gidan nan ba, sai dai ko idan zaki je can Tudun Wada sai kije can ki zaune tare da magen". 


Ta fa'da tana huce kamar zata fashe, wai duk akan nace inason mage, harda cewa naje gidan kakar mu ta Tudun Wada, sai nace mata.



"A a maman mu Dan Allah kiyi hakuri, na fasa bazan 'dauko magen ba".


Saita mi'ke tsaye tana cemin " oho idan ma Zaki 'dauko to ba a gidan nan ba" ta 'karashe maganar tana shigewa bedroom din mu.



"Inna lillahi wa'inna ilaihir raji'un!".


Muka jiyo maman mu tana salallami a 'daki, ai kuwa da gudu muka shiga 'dakin nida Maryam.



" Maman mu! Menene?" Muka fa'da nida maryam a tare.


Hannu ta 'daura a ha'ba tana fa'din.


"Amma wallahi 'berayen nan basu da mutunci, yanzu fisabilillah ku duba fa kuga, Kifin nan dana ajiye zanyi wa Jamila miyan cuwaka na Jego, shine dan banzan beran nan ya cinye" ta fa'da cikin takaici tana kallon mu.



Ni kuwa dariya na 'barke da ita ina fa'din.


"To Maman mu ba shine nace miki ki bari na 'dauko Mussa (Mage) a gidan Mama Jamila ba, amma kika 'ki, to aiga ranar Magen nan tazo" na 'karashe Maganar ina sake kecewa da wata dariyar.


Da sauri na ruga aguje ganin Maman mu ta tinkaro ni, kwafa tayi tana cewa.


"Ai da ki tsaya kiga idan jikin ki bai gaya miki ba, kuma mage dai ba a gidan nan ba, Maryam zoki je ki siyomin wani Kifin a kasuwa" ta fa'da tana bu'de jakar ta.


Bayan isha'i ma haka muka shinfi'da yakusasshiyar katifar mu nida maryam muka kwanta, saboda har yanzu tsoro bai sake ni ba shiyasaban fara kwana ni ka'dai ba.



Washe gari kuwa haka naji Maryam tana kwalamin Kira.


"Malika! Malika!".


Na tashi cikin masiba ina tambayar Lafiya Dan ubanki kike kwalamin wannan kiran? Ko bashin ki naci?".


" la'ilaha illalahu muhammadur rasulullahi (s.a.w) Malika aida ni kika zaga tinda ni nace ta tayar dake" Maman mu ta fa'da tana matsar kwalla wai ala dole nayi mata rashin kunya🙄.



Ba yanda na iya haka nace mata" maman mu dan Allah kiyi hakuri wallahi ban zata kece ba".



"Hmm Naji meya kawo Mage a kusa dake?".


" Mage kuma Maman mu?" Na fa'da ina waigen kusa dani.


Kyakkyawar mage ce kuwa Light broun Mai dan girma kwance a kusa dani sai Sharara bacci take.



"Na shiga Uku Malika wai nikam yaushe zaki barni na huta a gidan nan?" Maman mu ta fa'da tana kuka.


Yayin da ni kuma na 'kurawa wannan magen ido ina Murmushi domin harga Allah inson Mage.....✍️




Hmm wata sabuwa inji 'yan caca💁‍♀️ da alama dai Malikan nan ba haka kawai take ba🤔 koya kuka ce?.



Tau kardai ku manta yawan like share da kuma comment yawan page din da zanyi maku💃💃💃




Mu ha'du daku a chapter 5 domin yanzu aka fara🥳🥳🥳




Channel link anan zaku dinga samu daga zarar na 'daura👇





***







Daga Al'kalamin👑 Queen Jiddah....✍️.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol