Free chapter · Read without an account
Chapter 5
by Queen Jiddah · GAMO MUKA YI
🥹GAMO MUKA YI 🥹
Chapter 05
True Life Story 🙆♀️😱
By Queen Jiddah...✍️
Free page is about to finish🧏
Saboda haka ku hanzarta ku biya kudin ku Naira 300 kacal🤌 Domin cigaba da Karatun Littafin🤓
Akwai group na musamman, ga masu bukatar littafin GAMO MUKA YI na karatu🤓.
0686693377 GT Bank
Hauwa'u Musa Yeldu
Shedar biya ta wannan layin👇
***.
Wannan shine YouTube channel Dina, ana zaku dinga samun Na saurare insha Allah.
***
Akwai VIP group
N700
Normal group N400
Na tanadesa ne domin wa'yanda ba zasu iya zuwa YouTube su 'dauko na saurare ba, acan zan dinga Saka maku dashi, amma fa Littafin GAMO MUKA YI kawai🤓👌
A VIP group zan dinga Saka litattafaina na saurare duka💃💃
0686693377 GT Bank
Hauwa'u Musa Yeldu
Shedar biya ta wannan layin 👇
***
Allah ya Baku iKon biya🤓🤲.
Chapter 05
Ni Kuma ban furta komai ba, face cigaba da kallon Magen da nayi Ina murmushi, domin harga Allah inason Mage, shiyasa nayi farat Daya ta shigemin arai.
Jikin Maman mu a matukar sanyaye ta 'dau hijabinta ta Saka domin wucewa gidan aikinta, domin harga Allah itadai hankalinta Bai kwanta da Magen nan ba.
Maryam kuwa ko a jikinta, domin sabgogin gabanta kawai take yi, Daman ita ba Mai shiga abinda Bai shafe ta bace.
Ni kuwa a wannan ranar cikin farin ciki na fara aikace aikacen gidan, Kai harda na Maryam na ha'da duk nayi, Mage ta kuwa duk inda nayi haka take bina a baya, tana ma'kal'kaleni, farin ciki duk ya isheni, yau Gani ga Mage.
Bayan kammala aikin gidan MUKA zo MUKA zauna nida Maryam domin karya kumallo, itama magen tawa haka tazo a kusa Dani ta zauna tana kallon mu, abinda ya 'kara burger ni da ita shine , ita ko iron yanda Mage keyi idan suka ga abinci suzo suna shinshinar sa sam bata YI, kawai lafewa tayi a jiki na, ni Kuma na dinga shafa jikin ta.
"Malika gaskiya sai dai ki Nemo waje ki 'debi naki abinci, domin ba zai yiyu ki shafa mana gashin mage a abinci ba" Maryam ta fa'da tana wani kumbura fuska.
Murmushi nayi nace "Haba Maryam, yanzu fisabilillah ita magen I tace abin kyama? Karfa ki manta acikin sahabban manzon Allah (s.a.w) akwai Wanda har Abu Huraira ake ce masa, saboda yanda yake tsananin son Mage "na fa'da Ina sake shafa jikin Magen, murmushi 'dauke a fuska ta.
"To naji, aike ba Kya cikin sahabban nasa, saboda haka koki daina ko wallahi a raba abincin " ta fa'da cikin tijara tana kallona.
Daina shafa magen nayi na Sanya hannu na a cikin kwanon abincin, na joloup din Taliya wace taji kayan ha'di sai kamshi take yi, na 'debi kadan na sanyawa Mage ta, ai kuwa ta fara cin abincin cikin kwanciyar hankali, nayi shiru Ina kallon ta, can dai nayi Bismillah sa'annan na Sanya hannu tare da fara cin abincin nima.
GABA 'Daya yinin ranar a haka MUKA wuni, lokacin da Nana ta dawo daga makaranta, bata wani tsorata ba da taga magen, saboda magen ko Ina bata zuwa, idan har kaga taje wani wurin , to nice naje ita Kuma ta bini abaya.
Da daddare ma bayan Mama ta dawo bata sake magana akan magen ba, Gani da tayi nana bata tsorata ba kamar yanda ta saba.
Da muka zo kwanciya, daga ni sai Mage ta kadai muka kwanta a katifa, saboda Maryam cewa tayi ita wallahi ba Zata kwanta da mage ba wai saboda yanda mage keda son jiki, nace mata kanta ake ji, haka ta tattara inata da nata ta koma wajen Nana suka kwanta a tare, ni Kuma na kwanta a kusa da mage ta muka rungume juna.
Da misalin karfe 2:30 na dare na dinga Jin Mage ta tanata yakushi na, idan na tashi saita daina idan Kuma na koma na kwanta saita cigaba.
Da naga ba Zata daina ba, haka yasa dole na tashi na fita waje ita Kuma tamin rakiya, ban'daki na shiga na fito madaidaicin tsakar gidan mu nayi alwala kana na koma 'daki na shimfi'da dadduma na tayar da sallah, ita Kuma magen tawa tayi kwanciyar ta akan dadduma kusa Dani.
Raka'a biyu nayi, tare da tasbihi sa'annan na shafe addu'a na lankafe sallayar ka na nakoma saman yakusasshiyar katifa ta na kwanta, Mage na biye Dani abaya, itama ta kwanta nan take bacci yayi awon gaba damu.
Washe gari ma haka MUKA sake tashi, Ina lure da maman mu tana fushi dani amma nayi kamar ban Gani ba, zamu karya kumallo Maryam ta 'debi fatefaten Kanzon da muka yi Wanda yasha alayyahu a cikin sa, ta sanyawa Mage ta a gaban ta, amma ko ka'dan magen bata Kalli wannan abincin ba ballantana taci.
Maryam tace "Malika anya kuwa magen nan taki lafiya kalau take?".
Nace "Me kika Gani halan?".
Tace "duba fa kiga na Saka MATA abinci, amma ko kallon sa ba tayi ba".
Nace "iKon Allah, to bari na gwada Saka mata muga ko zata ci" na sanya hannu tare da 'dibar kadan na Saka mata, ai kuwa ta matso da sauri ta fara ci.
Nayi murmushi nace "to Kinga dai ni dana Saka mata taci, Ina tinanin bata son abincin hannun kowa saina Mai ita" na fa'da Ina murmushi.
Maryam kuwa cewa tayi" Amma fa wallahi Magen nan taki munafuka ce, aikuwa zanga wanda zai bata abinci a gidan nan idan bakya nan" ta fa'da tana kumbura fuska wai ita ala dole ranta ya baci.
Maman mu dai komai bata ce ba, saima murmushi da tayi tana Mai jinjina kanta, wanda ita kadai tasan manufar hakan.
Tun daga wannan lokacin Koda ace fita nayi, tofa mage ta ba zata ci abinci ba harsai na dawo, idan na dawo haka za kuga ta she'ko a guje ta tarbeni tana min oyoyo, idan Kuma naje wani wajen nayi kwana 'daya ko biyu, tofa idan na dawo bata kulani, Kuma a haka zata zauna bataci komai ba, wai ita ala dole fushi take yi.
Dana lura da hakan saina dinga fita tare da ita, domin ko bakin shago zani, Bina take a baya, idan Maman mu ta aikeni, ma tare da ita nake zuwa shiyasa na dena cewa Maryam tamin rakiya kwata kwata saboda daman, idan na nemi rakiyarta ta dinga min mita kenan, yanzu kuwa na samu 'yar rakiya wace bata gajiya Dani.
Har a unguwar mu ma cemin ake YI Malika Mai Mage, ni kuwa sam hakan baya damu na, saima dadin hakan dana keji.
Ranar wata Juma'ah, a haka na shirya nacewa Maman mu zanje Tudun Wada, gidan kakarmu, so nake nayi kwana biyu a can, saboda akwai shakuwa sosai tsakani na da ita. Tace min saina dawo, na shirya cikin farin ciki, itama Magena na shirya mata.
Domin har Karamar jaka na saya mata, wace nake saka mata madarar ta da kuma sauran abubuwan ta.
Shukrah! Shukrah!
Na ambata Ina kallon kofar falon mu, saiga mage ta, ta she'ko aguje ta tsaya kusa Dani, na rataya jakata na sunkuya na 'dauki Mage ta shukrah, nacewa Maman mu.
"Maman mu mun tafi sai mun dawo".
"Allah ya tsare " tace min ta cigaba da sabgar gaban ta.
Ni Kuma nayi murmushi Ina yiwa Maryam da Nana bye bye na wuce nida Shukrah zuwa waje.
Ina fita na tari adaidaita na hau, kasancewar gidan mu akan titi yake.
Bai tsaya Dani ko Ina ba sai Tudun Wada gidan kakarmu, na sauko tare da Daukar jakata na rataya, ka na na'dauki shukrah na runguma a jiki na, shi Kuna na biyasa ha'kkinsa.....✍️
Hmm masu karatu, ku biyo ni a Kashi na gaba din ganin irin rawar da shukrah Mage zata taka a gidan kaka tare da Malika, karku bari a Baku labari🤓.
Kuyi sharing like da Kuma comment domin samun update da wuri👌.
DAGA AL'KALAMIN👑 QUEEN JIDDAH.....✍️