Free chapter · Read without an account
Page-31
*FASAHA WRITER'S ASSOCIATION*
(*F.W.A)*©✍️
⭐⭐⭐
Ƙungiya masu aiki cikin salon hikima da fasaha gurin juya tunanin al-umma, kaifin alƙalumansu ya zarta takobi ©✍
___________________________________________________
بسم الله الرحمن الرحيم.
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد.
❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁
Free book📓
By
*Aisha G Umar*
_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_
Page3️⃣1️⃣
A sannu na dawo da idona kansa ganin yadda ya damu sosai a ɗan ƙaramin ciwon nan da na ji, ga yadda ya ke min aiki cikin kulawa, kallonsa kawai na ke yi sosai, har da lumshe ido ina buɗewa, iska mai sanyi na ji yana shigata na shauƙi.
Ni dai ban san lokacin da Abba ya gama yi min tritment ba saboda hankalina na kansa, ɗagowa ya yi yana min sannu amma kuma sai ya ga ina kallonsa, bai yi wata-wata ba shima ya cigaba da tayani, nan fa jarabawar kallon-kallo ya cigaba da wakana tsakani na da Abba. Asma'u kuwa dariya dukkansu su ka ba ta, har da tuna lokacin da su ka yi cecekuce, inda Abba ya ce ba zai yiwa Nuriyyah gwaji ba, sai ga shi yau kuma har da tritment ya yi mata.
Ba ta san lokacin da ta sheƙe da dariya ba, wanda hakan ya dawo da hankalinmu kanta, kallon ƙafata na yi ashe har ya gama, "ke lafiyarki kuwa?" Faɗin Abba wa Asma'u bayan ya miƙe, zama ta yi a kusa da ni ta dafa kafaɗata sannan ta ce, "ba komai yaya Abba kawai dai dariya kuka ban ne" "dariyar me ke fa ba na son iskanci" cewar Abba yana murmushi. Kan ta ba shi amsa Momy ta shigo falon bayan ta yi sallama.
"Too me ya ke faruwa anan haka?" Cewar Momy, Abba ya gaisheta yana faɗin, "Momy 'yarki Nuriyyah ce ta ji ciwo a yatsan ƙafa, da sauri Momy ta iso guna tana tambayata ya na ke ji? Haɗi da duba ƙafar ta wa. "Momy kar ki wani damu fa, yaya Abba ya ba ta kulawa ta musamman, don na lura ma kamar ba ta san yaushe ya kammala ba" da sauri na juya ina kallon Asma'u da ta yi maganar tana dariya, na harareta a hankli na ce, "ke Asmee me ki ke cewa ne?" Ta ce, "eh mana ko kin san yaushe ya gama ɗin?" Ta faɗi tana ɗaga min gira.
Abba dai juyawa ya yi ya wuce ɗakinsa, ita kuwa Momy ta ce, "sorry Nur, amma ki rinƙa kula sosai" da to na amsa mata sannan ta wuce ɗakin Hajiya Kaka. Gyara zama Asma'u ta yi tana cewa, "keh wai kin san me Sunusi ya ke faɗa min yanzu da mu ka yi waya?" "A ah ina dai fatan lafiya ko?" "Hmm cewa ya yi in faɗawa su Dady gobe iyayensa za su zo maganar aure".
Da murna na ce, "alhamdulillahi, amma na yi farin ciki sosai my Asmee, wow! Allah alhamdulillah". Taɓoni ta yi ta ce, "sai murna ki ke yi kamar auren aka yi" "hmm ai wannan abun farin ciki ne a wurina, tun da har ya ce zai turo da magabatansa kuma ai shikenan, na san dai da ƙyar à sa lokaci sosai, wayyo daɗi zamu sha biki, my Asmeeta za ta yi aure, oh my God! Kin sanarwa su Momy?" Murmushi Asma'u ta yi domin kuwa ta ji daɗin yadda na yi farin ciki da wannan lamari ta ce, "eh na faɗawa Momyta ce ba komai Allahya kaimugoben, za ta sanarwa Dady".......
Kamar yadda Sunusi ya faɗi, washe gari iyayensa su ka zo maza biyu, bayan sun gaisa da Dady su ka gabatar da manufarsu, akan suna nemawa ɗansu Sunusi auren Asma'u, su Dady sun yi farin ciki, amma sai Dady ya ce yana buƙatar su ba shi nan da sati ɗaya kafin za su ji shawaran da su ka yanke akai. Daga nan zama ya tashi cikin mutunta juna.......
Momy ce zaune a falon Hajiya Kaka suna hira, Hajiya Kaka ta ce, "yanzu ya kenan zamu yi akan lamarin nan?" Momy ta ce, "nima shi na ke tunani Hajiya, yanzu ban san me zamu yi ba, gashi ita Nur ko sau ɗaya ban taɓa jin ta kawo maganar saurayi ba bare ayi tunanin tana da, ko da na tambayi Asma'u ce min ta yi Nur ba ta saurayi, ba ta ba samari dama ko kaɗan. Gashi kuma Dadyn Abba ya ce so ya ke ya aurar da su lokaci ɗaya, domin ya sauke haƙƙin Nur akansa itama, duk da na ji daɗin nufin na sa, amma ba na son a aurawa Nur wanda bai da ce da ita ba".
Sai da Hajiya Kaka ta ijje numfashi ka na ta ce, "akwai wani hanzari ba gudu ba, akwai wani tunani da na ke yi, ni fa ina ganin kamar akwai wani abu a tsakanin yaran nan Abba da Nuriyyah". Cike da murna da farin ciki Momy ta ce, "Hajiya Kaka na ji daɗin maganar nan, kuma nima zan so hakan, shi Abban ya faɗa miki?.." "A ah Rahama, ba wai shi ya faɗa ba, kawai dai lura da fiskanta na yi, amma ba wanda ya faɗa min, sai dai na kasa gasgata abun".
Momy ta ce, "toh yanzu Hajiya Kaka wace hanya ki ke ganin ya dace mu bi donmu fahimci gaskiyar? Saboda abun farin ciki ne aguna Nur ta auri Abba, na san zai kula da ita sosai. Wallahi tuntuni na ke da wannan burin, amma ganin yadda ba su cika shiri ba shine ya sakar min da guiwa", murmushi Hajiya Kaka ta yi sannan ta ce, "to mu bari zuwa anjima sai mu shirya wani abun, amma ni dai ina ganin alamu. Abba bai cika zama cikin mutane ya yi ta surutu ba, kin san shi ko a cikinmu ne sai ya yi shiru, amma inkin lura yana zagewa ya yi ta tsokanar yarinyar nan". Da farin ciki Momy ta ce, "haka ne kuma, to shikenan Allah ya sa hasashenki gaskiya ne Hajiya Kaka".......
BAYAN LA'ASAR.
Muna zaune a falon Momy muna hira. "Asma'u me yasa Dady zai ce sai nan da sati sannan zai ba da amsa, kin fahimci wani abu ne?" Cewar Wasila tana kallon Asma'u da fiskarta ke ɗauke da damuwa, domin babu wanda ya san abun da yasa Dadyn ya yi haka. Asma'u tana son Sunusi sosai da sosai, domin yadda ya ke kasheta da kalaman soyayya, da kuma yadda yake nuna mata ita ce rayuwarsa. Ɗago kai ta yi ta ce, "nima ban san me yasa ba".
Ɗauke kaina na yi da kallon gefe na dawo da shi kansu, sannan na dafa Asma'u ina cewa, "kada ki sa damu à ranki Asmee, na san ba wani matsala ba ne yasa Dady ya buƙaci lokaci, ta yu kuma bincike ya ke son yi akan Sunusin, don ya tabbatar da ya zamo uba na gari a gareki" giɗa kai ta yi, Wasila kuma ta ce, "maganarki zai iya zama gaskiya" nan mu ka cigaba da hira abunmu.
"Ina Momy ta ke?" Faɗin Abba da ya shigo yanzu yana kallonmu, kayan da ke sanye a jikinsa sunvyi masa kyau sosai, ko sallamarsa ma ba mu ji ba bare mu san yaushe ya shigo, da sauri na ja ɗankwalina na rufe kaina cikin jin kunya, ya min kyau sosai yau fiye da kullum. Shi kuwa ta cikin ransa ya yi murmushi, amma à fili ya kuma maimaita maganar, "Momy kaman tana sashin Hajiya Kaka fa yaya Abba, saboda ba ta daɗe da shigowa ba ta kuma komawa can" cewar Wasila.
Ya ce, "ok bari na je na sameta" ya faɗi ya juya yana fita, da sauri na miƙe ina bin bayansa, suna tambayana ina zani na dai ce musu ina zuwa. Taka ƙafata na ke à hankali duk da har yanzu ina jin zafinsa, "yaya Abba, yaya Abba!" Na ƙwala masa kira sau biyu sai a sannan ya jini, dakatawa ya yi ya juyo, kallon yadda na ke taka ƙafar ya yi, hakan yasa bai bari na iso garesa ba shi ya zo kusa da ni, da mamaki ya ke kallona don jin dlilin kiran.
"Ya dai Gajera?" Ya yi maganar yana ɗage min gira, ƙasa na yi da kaina, ban ma san me zan ce masa ba, so na ke na yi masa godiya akan abun da ya faru jiya, amma na rasa ta ina zan fara, "ya ki ka yi shiru? Ko dai bakinki na miki ciwo? Ko kuma dai saboda jin daɗi ki ka tsaidani? you are wasting my time".
Ɗagowa na yi ina kallonsa yayin da ya ke maganar, kafin ya ƙarasa na ce, "na gode" hakan yasa ya dakata yana kallona, ni kuma na sakar masa murmushi zuciyata na motsawa ahankali, domin jiya na ji daɗin yadda ya bani kulawa, sai ya mantar da ni wani ɓata min ran da ya yi a baya, "what did you say?" Ya furta a hankali ba tare da ya ɗauke daga kallona ba, "thank you so much yaya Abbah" lumshe ido ya yi ya buɗe ba tare da ya ce komai ba.
Ni kuma sake sakin murmushi na yi ina juyawa. Zan wuce kenan sai kuma ƙafar da na ji ciwon ya min zafi sakamakon harɗewa da na yi, kamar zan faɗi cikin hanzari yazo zai taroni, sai ban faɗin ba, na dafe ginin da ke kusa da ni. Ajiyar zuciya Abba ya sauke ni kuma na juyo ina dubansa, "ki bi à hankali" ya faɗi yana kallona, a hankali na janye idona daga cikin na sa, na wuce sai faman murmushin dai na ke yi. Shima Abba à haka ya wuce yana jin kansa duniya sabuwa......
"Ke ki dai bi à hankali, inba haka ba wani ciwon za ki kuma ji" cewar Asma'u ita da Wasila suna kallona da dariya, ni kuwa da na shigo ɗakin Momy ina ta murmushi kamar ba a cikin hankalina na ke ba, na lura da inda na nufa a she ba tsakiyar falon na ke zuwa ba. Mamakin kaina ne ya kamani, ya aka yi daga jiya zuwa yau na sauya akan yaya Abba, na bar jin haushinsa, ya dawo burgeni, anya lau na ke ni Nuriyyah?.
Shima mutumin na ku, ko da ya isa falon Hajiya Kaka, kamar ba a cikin hankalinsa ya ke ba, tafiya ya ke yi kawai amma ƙwaƙwalwarsa na kawo masa murmushin da Nuriyyah ta yi masa shafi-shafi. "Kai Abba ina za ka kamar ba ka samu kowa a nan ba?" Da sauri ya juyo gun Momy da Hajiya Kaka da ke zaune, ya ma manta dama gurin Momyn zai je.
Dariyar ya ƙe ya fara saki yana sosa ƙeya, ya iso gabansu yana gaishe da su, haɗi da zama à gefen Momy, su ka amsa suna tambayarsa ya aikin asibitin komai na tafiya daidai? "Eh komai alhamdulillah, mutane na samun kulawa ba wata matsala" ya fadi sannan ya ɗaura musu da cewa, ya yi magana da Sayyid abokinsa, nan da ɗan lokaci zai dawo su yi aiki tare, kuma zai zauna tare da su, yana ƙare maganar ya ɗau goran ruwan da ya gani akan center table, ya buɗe ya fara sha da bismillah.
Cikin farin ciki Hajiya Kaka ta ce, "to masha Allah haka akeso ai, Sayyid yaron kirki ne idan ma ka yi masa fiye da haka ya cancanta, ba komai" sai ta juya gun Momy ta ce. "Yauwa ni kam Rahama kin tabbata wanda ya dace da Nuriyyahn ne yaron? Ya kamata ya zama yaro mai hankali, wanda zai so ta tsakani da Allah".
Wani irin bugawa zuciyar Abba ya yi, bai san lokacin da ya furzo da ruwan da ya ke sha ba, ta ke ya fara tari ba ƙaƙƙautawa, saboda jin maganar da Hajiya Kaka ta yi akan Nuriyyah, to wai wace Nuriyyah ma ake magana? Sannu su ke ta jera mishi Momy a amshi goran ta ijje, bayan tarin ya lafa ya fara sauke numfashi, bai haƙura ba sai da ya yi tambayar, "Momy wai wace Nuriyyahr ku ke magana akai?".
Haɗa ido Momy da Hajiya Kaka su ka yi, su ka sakarwa junansu dariya mara sauti, yanzu sun fahimci dalilin ƙwarewar ta shi, sai Momy ta dawo da dubansa gun Abba ta ce, "Wace Nuriyyah kuwa inba ta gidan nan ba? Ita dai na samar mata miji mai hankali, don Dadynku ya ce zai haɗa aurenta da Asma'u, kuma nan da sati ɗaya ne zamu tabbatar da mijin da za ta aura".
"Amma Momy me yasa Dady ya ke gaggawa haka? Nan da sati ɗaya kuma? Ita Nuriyyar ce ta fito da wanda ta ke so?" Ya faɗi zuciyarsa na rawa da tsumayin abun da Momy za ta ce, gaba ɗaya hankalinsa da ya tashi ya maida kanta. Murmushi Hajiya Kaka ta yi, Momyn ma haka, domin kuwa shirin da su ka yi kenan, su ga ya zai yi.
Haɗe fiska Momy ta yi saboda ya gasgata maganarta ta ce, "ko ma dai menene nan da sati ɗaya za'asawa Nuriyyah ranar aure, tun da dai mu a familynmu babu wanda ya ke sonta, idan ma ba ta da shi ba sai mu neman mata ba? Ko Hajiya Kaka?" Itama Hajiya Kaka ta ce, "ƙwarai kuwa, ni dama akwai wani yaro da na yarda da tarbiyyarsa, kin ga zuwa nan...".
"Haba Hajiya Kaka, haba Momy, kuna nufin talla za ku yi da Nuriyyahr ko me? A ah don Allah kar ku yi haka" "to inba hakan ba me za mu yi? Ko kana da wani zaɓi ne? Tun yaushe kai mu ke binka akan ka fitar da wacche za ka aura, daga ƙarsheka ce mana kai ba ma ka da budurwar, to yanzu kuma za mu yiwa Nuriyyah zaɓin miji ka ce mana kar mu yi hakan?" Cewar Hajiya Kaka suna ƙura masa ido don gano wani abu a tattare da shi.
Sosa ƙeya ya fara yi, yana son faɗa musu shi zai auri Nuriyyah, don dai wallahi shi ba zai iya bari a aurar da ita ga wani ba. Momy ta ce, "muna jinka kai kuma ka yi shiru? Imm Hajiya Kaka rabu da shi kawai a haɗa Nur da..." "a ah Momy please karki min haka", ya faɗi da hanzari, sai kuma ya sake sunkuyar da kai, Momy da Hajiya Kaka su ka kuma haɗa ido, Hajiya Kaka ta ce, "eh, faɗa mana ya zamu yi maka?".
Zuciyarsa na harbawa ya ɗago kai yana kallonsu, a hankali ya buɗe baki zai yi magana, amma kamar mai jin kunya kamar wanda ake ja ya samu dai ya ce, "imm ah Momy......
Last page
___________________________________________________
Kuna ganin Abba zai furta ko kokuwa? Ita fa Nuriyyah ba ma ta san da maganar ba. Ku ba ta amsar tambayarta na me ya ke damunta ne wai😂
_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_