Free chapter · Read without an account
11
by Mahma Lamido · INAYATU
Kallon aunty Halima tayi tana ajiye kamannun ta kana ta sake kallon fuskar da ke jikin screen din tabbas wannan fuskar yaya Em ce, sai dai bata ga ta ina Aunty ta ke kamanceceniya da yan gidan baba Dr ba bare har kanen ta ya biyo yaya Em sak.
Mafarki ta ke ko bacci ta kasa gasgata shin daya daga cikin mafarkan da ta saba a kan shi ne ko kuwa idon ta biyu.
Idan har idon ta biyu tabbas Emran yayi katutu a zuciyar ta, da har ta ke ganin kamannun sa a fuskar sauran maza.
Muryar ta na rawa da kyar ta furta "Aunty ya sunan kanen nan na ki"
"EMRAN, EMRAN ALIYU BELDO shine cikakken sunan" Aunty ta amsa
Ta faru ta kare inaya ta raya a kanta, tabbas ta gama zaucewa tunda har gashi mafarkan Emran basu tsaya a iya bacci ba kawai har a ido biyu ma basu raga mata ba.
"Inaya Inaya, kina ji na" Halima ta fada tana girgiza ta, kamar wacce ta tashi daga barci ta zabura
"Aunty Yayan Em, yaya Em din baba Dr ne" ta furta
Halima tace "Tabbas yaya Em din da kika sani ne na baba Dr da maamah kuma Kane na da nake yiwa campaign"
Tsalle zata yi a kan murna ko sujudu shukur zata yi ta gode Allah, tabbas Allah sami'u du'a ne, ta roke sa ya kawo mata mafita akan lamarin Emran, ya kuma kawo mata ba tare da dubara ko Iyawar ta ba
Amma ta ya yaya Em ya zama kanen Aunty Halima don tana da tabbacin ya girme ta nesa kuwa, ko da yake Kane ya ke a gurin mijin ta tunda yah Murtala ya girmi yaya Em
Hannun ta ta ji Aunty Halima ta kama a tausashe "Abba zai kira ki gobe a kan zancen, daddyn su Farid ne yace in tuntube ki da zancen a yau kar a zo miki bagatatan, saboda haka kiyi tunani a kai kafin gobe, kiyi tunanin mai kyau inaya kafin ki amsa amincewa ko rashin amincewar ki"
Aunty Halima ta fada tace da daukar wayar ta da ke kan cinyar inaya ta nufi kofa
"Matar sa fa" inaya ta fada kan ta a kasa, Halima tayi tsaye bakin kofar tare da waiwayowa tana karantar yanayin inayar sosai "Emran saurayi ne, duk wanda ya gaya miki yana da mata toh bai gaya miki dai dai ba" ta ja kofa ta bar mata dakin wani abu na tsaya mata a rai, bata ga murna a fuskar inaya ba, amma tabbas yanayin ta ya nuna acceptance na lamarin kai tsaye, hakanan ta ga rudani sosai da mamaki a fuskar ta a lokacin da ta ci karon da hoton Emran, toh hakanan na nufin inayar na son Emean tun dama can ko yaya.
Yaya em ba shi da mata, ita ce bata ji da kyau ba ko kuwa bata fahimci Amal ba, tabbas Amal ta gaya mata suna gidan yaya Em har take cewa matar sa na cikin aiki, me hakan ke nufi, ko dai sun rabu da matar sa ne.
Sai dai kuma iya tunanin ta tayi, zata tuna auren yah Amadu duk da bata da wayo a lokacin amma ba zata iya tuna auren yaya em ba wanda ta ke da tabbacin Komi lalacin sa dole dai ya dawo gida a lamarin auren sa. abinda ta sani dai aunty ba zata yi mata karya ba hakanan zata iya zama da shi ko da cikin mata uku ne itace cikon ta hudu