Free chapter · Read without an account
12
by Mahma Lamido · INAYATU
Ta jima ita kadai a dakin tana ta juye juye, kana daga bisani ta mike ta nufi toilet, wanka tayo ta fito daure da towel tana shiri.
Shirin ta ba wani mai wahala ba ne ta kimtsa ta fito falo kai tsaye inda mutanen gidan ke zazzaune ana raha, Dede ce da yan jikokin ta, zama tayi gefen mahaifiyar ta tare da dora kan ta a kafadun Dede.
"Amma dai 'yar nan baki da kunya, ya zaki zo ki tattaushe ni haka, ke kiyi, 'ya'yan ki suyi ai sai ku kakkarya ni"
Murmushi tayi Tana fadin "kai Dede har wani nauyi ne da ni, na wuce ki saba ni a baya kiyi yawo da ni" Inaya ta fada cikin tsokana
"Ba yawo zan yi da ke ba, saba ki zanyi a baya in arta na kare" Dede ta fada Tana ture kan ta, Fareed da ke gefe da iPad din sa yana latsa ya Mike kafafun sa yana fadin "zo ki kwanta nan Aunty inaya"
"Dadin haihuwa kenan" inaya ta fada lokacin da take dora kan ta kan kafafun Fareed wanda ya shiga sanya dariya kamar ya ga wani comedy.
Gabakidaya duk wata damuwa ta inaya ji tayi kamar an yaye mata ita, haka take jin kanta kamar iska yana daukar ta saboda wani irin relief da ta ke ji.
Haka take kwana ta tashi cikin walwala har zuwa Washegarin da Abba yayi kiran ta falon sa "Assalamu Alaikum" tattausar muryar inaya tayi sallama falon Abban, mutum
Uku ne falon, Abba da ke zaune kan daya daga cikin leather seats din da ke falon kan three seater,Dede ke gefen sa, sai babban yaya Murtala da ke hakimce kan 2 seater.
Dukan su suka amsa sallamar ta kusan a tare, kusa da yayan ta ta nufa kai tsaye tana zama kan carpet, fuskokin su na nuna alamar seriousness din da ke falon.
"Ina yini Abba, Dede ina yini" inaya ta fada Tana yin kasa da kan ta, Abba ya amsa cikin sakin fuska yana gyara zaman sa.
"INAYA ya karatu da fatar a nan ana ta kokari""
Dago da kan ta tayi kadan ta kalli Abban kana ta saki dan murmushi "Alhamdulillah abba"
"Masha Allah ana aji biyu yanzu ko" Abban ya sake tambaya, wannan Karon ta amsa sa ta hanyar gyada kan ta alama eh.
"Allah ya taimaka" abba ya furta
"Inaya zamu yi magana, wata magana mai muhimmanci" ya nisa
"Allah ya sani kema na so kiyi zurfi da karatun ki kamar yar uwar ki, kafin zuwan wannan ranar, sai dai na mu tsarin daban na Allah daban"
"kin san yayan ki IMRAN" ya tambaya kai tsaye
Daga kasan da kan ta yake bata dago va ta amsa Abban ta da "eh Abba"
"Yawwa toh baban ki ya zo min da wani zance kwanaki, na kuma yi tunani na tattauna da mahaifiyar ki, a matsayi na kuma na uba, mahaifi, mai ikon zaba miki mijin aure na amince da zancen kai tsaye ba tare da tuntubar ki ba, toh dai Ina fatar zakiyimin biyayya, ki amince da zabin da nayi miki da dan uwan ki IMRAN a matsayin mijin aure, ni a gani na mun isa da ke mun kuma isa mu zaba miki mijin aure kai tsaye, sai dai baban ki ya matsa a tuntube ki kan zancen da amincewar ki kafin magana duk tayi nisa, Ina fatar babu wata matsala Inaya"
Tun da abba ya soma zancen sai lokacin ta iya dago da kan ta daga kallon carpet da take, ta kalli mahaifiyar ta da ta kafe ta da ido domin jin ta bakin ta, ita din bata da wani zabi da ya wuce na iyayen ta, ko da bata son Yaya Em, ko da bata san shi ba bata taba ganin shi ba ita mai biyayya ce ga dukkanin abinda iyayen ta suka zaba mata, Baba Dr ya isa da ita, ya isa yace tayi ta kuma yi din, bare uwa uba Abban ta, Inaya ta samu kan ta da gyada kai cikin amincewa ba tare da wani dogon nazari ba
"Duk hukuncin da kuka yanke dai dai ne Abba, ni mai yin biyayya ce a gare ka" inaya ta furta
"Na sani inaya, na sani ba zan samu matsala daga gare ki ba, Allah yayi miki albarka, yanda kika faranta min Allah ya baki 'ya'yan da zasu yi miki fiye da haka" ya waiwaya gefen Dede ya waiwaya gefen yaya Murtala kana yace
"Idan da wanda zai ce wani abu zai iya fadar ra'ayin sa"
Dede tace "ba abinda zance sai Allah ya tabbatar da alkhairin sa a cikin wannan abin, ya sa ayi damu"
Yaya Murtala ma sai lokacin ya magantu "we are proud of you Inaya"
Daga haka tayi sum sum ta mike tana bar musu falon inda suka cigaba da tattaunawa akan al'amarin"
A daki kuwa juye juye inaya ta rika yi tsakiyar gado ta rasa tunani daya takamaimai da zata yi, sai lokacin take jin lamarin a wani banbarakwai, sai lokacin take ji kamar komai yana zuwa da sauri, kamar akwai gaggawa a cikin lamarin, yayan ta Em ne ya ganta yana so har yayi wa iyayen su zancen ko kuwa iyayen na su ne suka yi wannan hadin don ganin dacewar hakan.
Wannan amsar bata da mai bata ita face uban gayyar da kansa wanda bata san a wace duniya ko hali yake ciki ba.