Free chapter · Read without an account
chapter nine
Dr. Tariq Asalin shi Bahaushe ne amma yanayin sa da launin shi da Allah ya yi masa da tsari mutane dama su kanyi tunanin half caste ne. Fatar jikinsa light brown with a natural glow, ba irin wadda ake fakewa da filters ba. Fuskar sa cike take da kwarjini— duk da ba yawan murmushi ne dashi ba, Idanunsa masu zurfi ne, kaman suna gaya maka “I know what I’m talking about.”
Gashinsa? soft, well-kept, irin wanda zaka rantse bature ne amma har yanzu zaka gane jinin Hausa yana jikinsa. Yana gyara kansa ba don ya burge mutane ba, amma don discipline. Jikinsa kuwa—lean, athletic, well-trained. irin jikin da ke nuna healthy lifestyle, consistency, da self-control.
Dr. Tariq certified Nutritionist ne—ba na magana kawai ba, qualified and grounded. Amma bai tsaya a certificate ba. Shi content creator ne mai tasiri sosai. A Instagram, TikTok, da YouTube, yana da miliyoyin mutane da ke sauraron sa—mata, maza, matasa, manya—duk suna koya, suna gyara rayuwarsu daga abubuwan da yake koya musu.
Yana da kudi. Very very rich. He is not flaunting, ba unnecessary show-off. Komai nasa clean, calm, expensive in a quiet way. Gym dinsa private ne. Yana daukar online private classes, kuma wasu clients dinsa yana haduwa da su a gym for workouts—but strictly professional. No flirting. No crossing lines.
Har yau, nobody has ever seen him with anyone.
No scandals.
No rumors.
No late-night club stories.
Babu wanda ya san who he loves, where he goes, how he relaxes. Outside his content? Blank space. Mystery. Discipline. Boundaries. Wannan shi ne Dr. Tariq.
—
Samha ta sauke wayar a hankali bayan video din ya kare. Zuciyarta na bugawa—not fast, but deep. Ta dan lumshe ido, ta ja numfashi, sannan ta shiga DMs dinsa.
Hannunta na dan rawa kadan yayin da take typing:
“Hello Dr. Tariq. I’m Samha. I run a talk show, and a lot of my followers have been asking to see you beyond health talks. I’d love to invite you to my studio for a sit-down conversation, if you’re open to it.”
Ta danna send.
Nan take, ta dora wayar a kirjinta, ta dago kanta sama.
“Allah,” ta rada a hankali,
“ka sa ya amsa invitation dina this time around.”
Domin ba sirri ba ne—everybody knows.
Dr. Tariq is her crush
*****
Dr. Tariq yana gym dinsa—wurin da komai ke tafiya cikin tsari, tsafta, da natsuwa. Haske mai kyau na ratsawa ta manyan gilashi, soft instrumental workout music na tashi a baya, yana bada wani irin sanyi ga zuciya duk da gumin da ake sha.
Yana tsaye a gaban yoga mat, sanye da black sleeveless top da grey joggers, jikinsa na nuna class da discipline. A gabansa akwai wata client dinsa—mace wacce suke work out da shi akan growing hips.
Dr. Tariq yana koya mata moves din a hankali, ba da gaggawa ba, muryarsa calm kamar kullum.
“Focus on your posture,” in ji shi, yana nuna mata yadda zata daidaita bayanta.
“Breathe in… breathe out. Don’t rush the movement.”
Se dai ita kam—mind dinta baya nan. Maimakon ta maida hankali kan exercise da suke yi, idonta na binsa, murmushinta ya wuce misali, jikinta na kokarin matsowa kusa da nashi fiye da kima. Ta fara lanƙwasawa ba yadda ya Ke koya mata ba, tana neman attention dinshi by seduction.