Free chapter · Read without an account

Chapter 15

by @Mrs Alkali · ƘAUNA DA KADDARAH

💫 ƘAUNA DA KADDARA 💫 

✍️Mrs Alkali 

Page 1️⃣5️⃣
Misalin qarfe 5:30pm na yanma motar Alhaji Turaki ne ke shigowa harabar gidan, tare da ta AA Turaki, a yau bai dauko bodyguard din sa ba daga Motar su Hajja sai motar shi da driver ke jan shi a baya. 
Alhaji Musa da Mami suna zaune a falo, yayin da Ramlart take gefen Mami da hijab a jikinta, amma fuskarta cike da shakku da jin nauyin su don sun titsiyeta a gaba sai ta fad'a musu dalilin zuwan ta gidan.
Jin an bud'e gate d'in gidan ne, ga kuma karan motoci alamar sun shigo harabar gidan ne ya sa baba ya daka ta da tambayar ramlart.

Ba a jima ba suka ji an yi nocking din kafar falon, ramlart ce ta tashi da sauri ta nufi k'ofar falon dama tana Allah Allah tasa mu dama ta zullewa su baba sai gashi dama ta samu, bud'e k'ofar tayi batare da tayi tsammanin ganin sa ba ta ganshi tsaye a bakin k'ofar.
Yayi shigar alfarma; yau babban riga fara wacce ta sha  ɗinki na zamani, a jikin shi ,ga agogon Rolex mai uban tsada a hannun shi, wasu takalma half cover shoes black in colour masu tsada ne sanye a kafafun sa, ga wani sassanyan kamshin turare mai daɗin ƙamshi, da yaci ka wajen, a hankali ya tako , cikin nutsuwa da izza, fuskarsa cike da kwanciyar hankali da tsantsar kamewa. Kamar wani saraki, haka ya shigo cikin falon bakin sa dauke da sallama kasa kasa.

 Ramlart ce ta zuba masa ido, kamar yau ta fara ganin sa.
Idanunta suna ƙara gaskata mata cewa babu wani da'namijin da ya kaisa kyau. zuciyarta ce  ta buga da karfi, kamar ana buga gangar yaki. Har ya wuce ta bata sani ba Ta zuba masa idanu tanabin sa  da  kallo ba tare da ta iya ɗauke idanunta ba. tayi matuƙar rikicewa. A zuciyarta tana jin Wani irin ciwon son sa yana kara tasowa a cikin zuciyar ta.
Jin sallama ne ya katse mata tunanin ta ganin Baffah da Hajja ne yasa ta sunkuyar da kanta kasa , zuciyar ta na dukan uku uku, shikenan tata ta kare, dan batayi zaton cewa yana tare da su Hajja ba.

Cikin wani juyin zuciya, Ramlart ta daure ta sunkuyar da kai amma zuciyarta na mata kuna  .

Shi kam AA Turaki yana shiga cikin falon , ya gaishe da su Mami cikin mutunci da ladabi, suka gaisa da su baba. Sai dai  ko  ɗaya bai  kalla inda Ramlart ta ke tsaye ba, da alama bai san ma da wanzuwar ta a wajen ba.

 hakan da yayi ya kara sosa ran Ramlart – a hankali ta dafe ƙirjin ta dake mata barazanar tarwatsewa,  tana kokarin boye hawayen ta. A cikin zuciyarta, ta tabbatar da abu guda: soyayyar ta ga AA Turaki har yanzu ba ta mutu ba… kuma bazata iya rayuwa ba tare da shi ba.
A lokacin da Hajja da Baffah suka ƙaraso cikin falon, Alhaji Musa, ne ya mike tsaye cikin murnar ganin su ,ya tarbe su da fara’a, ya rungume abokinsa Alhaji Abdullahi cike da farincikin ganin aminin nasa,Mami cikin murna da farin ciki ta gaida Hajja da fara’a. Aunty Hauwa ma tana falon tare da ‘ya’yanta haka suka gaisa da su Hajja cikin sakin fiska .

Alhaji Musa yana murmushi yace:
"Wallahi wannan ziyara da kuka kawo mana, ta faranta mana rai sosai. Mun ji daɗin ganinku."

Cikin nitsuwa Hajja tace:
"Mu ma muna godiya da irin karamcin ku. Mun zo ne saboda zumunci, da kuma wata muhimmiyar magana."

AA Turaki yana zaune cikin nutsuwa, kai kace baya cikin falon yanda ya kame yana danna wayar sa kamar ma baya wajen, ga Hajiya ramlart dake rakube a gefe tana aikin kallon sa.

Alhaji Abdullahi Turaki ne ya gyara zaman sa tare da cewa:  
"Alhaji Musa, Hajiya Rakiya… akwai wani al’amari mai nauyi da ya shafi ‘yar mu wato Ramlartu .
Wani irin bugawa ƙirjin ramlart yayi ,har wani jiri jiri take ji yana kok'arin ibanta, da kyar ta iya seta kanta, duk wani addu'a da yazo bakin ta karantashi kawai takeyi, jin Baffah yaci gaba da cewa"Mun tabbatar da cewa ita ce ta sakawa Hajja wani sinadari a abinci, wanda hakan yayi sanadiyar kwanciyan Hajja a asibiti…"
Kuma Likitocin sun gano hakan ne ta hanyar gwaji inda board na asibitin suka had'a meeting naganin cewa sun tsanan ta bincike angano mai laifin, ganin hakan ne yasa Aliyu ya nemi alfarma yadakatar da su inda ya tabbatar musu dacewa zai dauki mataki da kan sa, bayan bincike da aka gudanar ansamu ganin hoton Ramlartu ta cikin CC camera in da aka tabbatar da cewa ita ce ta aikata hakan ,hakan ne ma yasa mijin ta ya umarce ta da ta dawo gida, toh kaji wannan ne dalilin zuwan mu .

Ai a lokacin baba ji yake kamar lokacin ya tsaya masa baya tafiya, kowa dake dakin yayi shiru har Aunty hauwa da ta cika musu gaban su da abubuwan motsa baki cike da mamaki suke kallon ramlart dake rakube a gefe kamar muna fuka. Ramlart na rakube a gefe, ta sunkuyar da kai kasa.

Cikin fishi  Alhaji Musa ya kalle ta fiskar nan babu alamar rahama a tattare da ita cikin tsawa yace.
"Ramlart! Wannan ai ba laifi bane kawai, wannan keta mutunci ne da rashin hankali! Abinda kika aikata ya wuce a yafe miki da cikin sauki, kisan kai fa kike kok'arin yi innalillahi wa'inna ilaihirraji'un baba ya kara maganar cike da rauni."

Cikin kuka Mami tace"Na yarda da tarbiyyar da muka baki ba haka take ba. Me ya rinjaye ki har kika aikata hakan?"

Cikin bacin rai Aunty Hauwa ta matso tare da zabga mata wani lafiyayyan mari, wan da yasa jinta ya d'auke na wucen gadi, ta sake dağa hannun ta zata sake zabga mata taji Baffah yace kull kull hauwa'u barta haka, ai shi duka baya gyara sai dai ma ya sake lalatawa dan haka addu'a zaki mata, Wani irin kallon zamu had'u Aunty hauwa ta mata tare da cewa.
"Na rasa dalilin da zai sa ki hallaka kanki da hannunki. Wannan kuskure ne babba!, kuma ina mai tabbatar miki da sai kin girbi abunda kika shuka."

Cikin miryan kuka Ramlart  tace  "Na tuba… na yarda da kuskurena. Don Allah ku yafe mini…wlh sharrin shaidan ne bazan karaba wlh na tuba."

Cike da ta kaicin ta Alhaji Musa ya juya zuwa ga Alhaji Abdullahi Turaki yace  ."Wallahi in har wannan abun ramlart ta aikata , to sai dai ta zauna a nan gidan. Ina son Ka umarci Aliyu da ya sauwake mata ta dawo nan ta zauna … tunda ta zubar da mutuncin ta."

Cike da jin nauyin shi Alhaji Abdullahi Turaki yace "Alhaji, ba karamin nauyi na ji ba, dana kawo maganar gaban ku sai dai kuwa ba yadda zanyi ne ya zama dole kusan da maganar a matsayin ku na iyayeh a gare ta. Amma ina rokon ku daku dubi girman zumunci, da girman mutuncin mu, ku yafe mata. Mu ma muna bakin cikin faruwar hakan. Amma in ba damuwa, a bata dama ta biyu ta gyara. Allah yana yafe wa bawansa, mu ma mu yafe mata, hakan zai sata ta gyara kura kuran ta na baya."

Hajja ce ta sauke ajiyar zuciya, ta kalli AA Turaki wanda bai ce komai ba, kamar ma wanda baiya wajen.

Cikin nitsuwa Hajja tace   "To… kamar dai yadda Alhaji ya fad'a Allah ma muna masa laifi ya yafe mana bare kuma ace mu bayin sa , dan haka nima na yafewa ramlartu  ,Amma fa wannan kuskuren ba ƙarami bane, sabi da haka saita kiyaye gaba duddah har yanzu bamu san dalilin ta na aikata hakan ba."

Shi dai AA Turaki bai ce komai ba, sai ma wayar sa da ya ci gaba da dannawa, amma a chan cikin kasan zuciyar sa bakaramin haushi yake ji ba, a zaton sa Hajja zata sa ya rabu da ramlart amma sai gashi sun buge da yafe mata, duddah iyayen ramlart sun chanchan ci fiye da haka a wajen su dan ba karamin girmama su yake ba sabi da karamci irin nasu, sai dai duddah haka albasa batai halin ruwa ba.

Cike da borin kunya Ramlart ta taso ta  durƙushe a gaban iyayenta da iyayen mijinta, fuskarta cike da hawaye. cikin rawar murya tace"Na gode… Na gode da wannan dama da kuka bani. Nasan Ban cancanta ba, amma duddah haka kun yafe mini. Allah ya saka da alheri, zan gyara halayena, wallahi zan gyara..."

Hajja ta tab'e baki tace"ai kuwa kam gara Ki gyara Ramlart, kada ki sake kuskuren da zai sa mu zubar da hawaye saboda ke anan gaba."

Cike da tsantsar girmama wa Alhaji Musa kalle su yace "To amma ina da wani sharadi. Ramlart ba zata koma gidan mijinta yanzu ba. Zata zauna a nan gidan tare da mu na wani lokaci... har sai Aliyu ya sami wata matar da zai aura. Na yi alkawari , zan nema masa auren mace ta gari. Sai ya auri wata, sannan sai Ramlart ta koma d'akin ta Wannan shine hukuncina a gare ta."

A hankali AA Turaki ya d'ago ido ya kalli iyayen nashi a karo na farko tunda ya  zauna a falon cikin shiru, zuciyarsa cike da rudani da nauyi, jin hukuncin da Baba ya sake yankewa, Hajja ta kalleshi da damuwa dauke a saman fiskan ta sabi da tasan an sake jefa rayuwar d'an ta a cikin tsaka mai wuya, tana tuna auren Ramlartu ma da yaya ya amince bare kuma wani auren a karo na biyu.

Cikin hikima Hajja tace"Alhaji Musa, wannan hukunci mai nauyi ne, amma ka nuna mana karamci da adalci. Allah ya saka da alheri."

Alhaji Abdullahi Turaki ya gyara zama kafin yace"Mun amince da hukuncin ka, kuma muna godiya da fahimta da muma karɓan uzurin mu da kayi."
Baffah ne ya Kalli Aliyu ya ce"ina ce kaji hukuncin da mahaifin ku ya yanke, ina fatan ka fito da matar auren ba da jimawa ba".
AA Turaki ne ya ɗago ido ya na kallon kowa, dake cikin falon ba tare da furta kalma ba, ya sauke kan sa kasa,  A zuciyarsa kuwa, ya kudirta cewa kasar ma zai bari gaba daya… ba auren da yake so, kuma zuciyarsa har yanzu cike take rauni da kuma dacin abun da yafaru da shi a shekarun baya, sabi da haka bazai yadda ya sake wani auren ba.


Ita kam ramlart duddah hukuncin da Baba ya yanke bai mata dad'i ba amma a hakan ta daure zuciyar ta dan tasan taci darajar su Baffah ne da yanzu ba wannan maganar ake ba , duddah tana tunanin cewa su baba basu hakura ba, ga Mami dake gefe guda tana ta kuka tun d'azu da taji abunda ramlart d'in ta aikata, Aunty hauwa ma tana zaune a gefe tana hararan ramlart d'in, da ba don idon su Hajja ba da sai jikin ta ya gaya mata a hannun ta yanzu ma bata tsira ba jira take su Hajja su tafi .
Bayan Wani lokaci su Baffah suka musu sallama, haka su rabu cikin mutunci da girmama juna.

Bayan tafiyan su Hajja ne Mami tasa Aunty hauwa ta jarawa ramlart zama dan acewar dama jira take su Hajja su tafi, babu bata lokaci Aunty hauwa dake jin haushin ta tafara sauk'e mata gajiya ,duk abunda ake yi baba bai hana ba hasali ma yaji dad'in hakan, bayan Aunty hauwa ta gama kumburawa ramlart jiki ne , Baba ya sake kafa mata sharrudan shi, yace duk wani aiyukan gidan daga yau itace maiyin su, hatta da sharan tsakar gidan nasu, haka ramlart ta ja jikin ta ta wuce d'akin ta jikin ta duk ya mata tsami.


🔚 ƘARSHEN  FREE PAGES!

_Ahamdulillah, a nan nakawo ƙarshen Free pages... Amma tambayar ita ce:_

Shin ƙauna zata iya shawo kan kaddara? 
Ko kuwa kaddara ce zata wargaza ƙauna? 😢💔

Wane mataki AA Turaki zai ɗauka bayan sake ganinta?

Shin wace yarinya ne AA turaki yake yawan mafarkin ta ?

Shin zai sake had'uwa da ita shin wace kaddarah ce ya ke gudu?

Ramlart zata iya samun yafiya daga zuciyar AA Turaki?

Shine da gaske ramlart tayi nadama?

Shin Ya alak'ar ramlar da  majeed İbrahim jatau?

Shin sabuwar soyayya zata iya dinke tsohuwar rauni?  

Ko kuwa sabon masoyi zai bayyana daga inda bamu zata ba?

Shin AA turaki zai sake aure a karo na biyu?

Shin wacece Dr Farida?

Mene yake kunshe a cikin rayuwar shin da gaske Ameer dan ta ne?

Shin zata auri Dr İmam?

Shin  wani sirri ne su Hajja su ka boye shekaru 21 baya?

Mene musabbabin ciwon zuciyar AA turaki?

Shin wannan ƙaddarar soyayya ce ko hukunci?

Shin da zuciya Daya zuly take son ramlart?

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol