Free chapter · Read without an account

Chapter 7

by Asmeetah Writer · MY ENEMY BOOK 1



Ledar jini ne yake ɗiga ɗis! ɗis!! ɗiss!!!  a yayin da ita kuma wacce take kwance a saman gadon hospital take bacci ido a lumshe gwanin burgewa,   a hankali jinin yake shige mata hannun da aka ɗaura mata, 
            haka take fitar da numfashi slowly, 
        jin yanda sanyin A.C yake ratsa jikinta yasa ta ɗan soma mutsil-mutsil tana yatsina fuska still ido a lumshe,  daƙer ta iya fara buɗe eyes ɗinta, a cikin tana ganin dishi-dishi har idon ya washe, haka take bin saman ceilling da kallo ko ƙibta idon bata yi,  jin wani irin la'anannen ƙamshin turaren da yake bugan hancinta yasa ta ɗan juyar da kanta saitin yanda ƙamshin yake tashi, abinda ta fara gani shine zara-zaran yatsun hannu  fari ƙall ga yatsun hannun sun sha zobina da warwaraye na gwal tana ɗauke da wata makekiyar waya wanda a ƙalla zai kai 2millions,   ga wani danƙarariyar Abaya mai bala'in tsada  wanda duk rigar a jere yake da duwatsu masu ƙalƙali da ɗaukar ido, a hankali take bin zazzafar ƙirar jikin matar dake zaune akan chair da kallo har zuwa kan kyakkyawar fuskar ta,  ganin matar yasa ƙirjinta yayi wani irin bugawa  a razane take ƙoƙarin tashi zaune ido a zazzare,  a yayin da ita kuma matar hankalinta duk yana kan wayar hannunta sai daddannawa take alamun chatting take, 
              tasha kitson Attach har gadon bayanta sai gyalen rigar da ta ɗora akanta...
                 
                  Daiden lokacin da Madam Aliya ta shugo cikin room ɗin hannunta riƙe da ledoji guda uku, ganin yanda Baiwar ALLAH take a razane idonta akan Madam Parveen yasa ta ƙaraso da sauri tana faɗin  
          "Lafiya kuwa Baiwar ALLAH? kin tashi ne? ya jikin nakin?...."
      
           haka take jero mata tambayoyi tsabar yanda take jinta a ranta, domin tinda tayi ido huɗu da Baiwar ALLAH taji ta shiga ranta sosai da kuma tausayinta , 
                     tana ƙarasowa ta zauna a bakin gadon da Baiwar ALLAH take still idonta akan Madam Parveen, 
                 Madam Parveen jin shigowar Madam Aliya yasa ta ɗago da kanta tana binsu da kallo daga bisani ta tsayar da idonta akan Baiwar ALLAH yanda taga kallon da take mata kamar wacce ta santa...

                 Madam Aliya tana riƙe da ɗayan hannun Baiwar ALLAH tace        "Baiwar ALLAH shin kin santa ne kike kallon ta?...." 
      
          A hankali ta soma girgiza kai  alamar a'ah!

Madam Aliya ta kuma cewa  "ita ɗin Babbar Aminiyata ce,  tare mukayi primary school to secondary, sunanta Madam Parveen,  jami'ar C.I.D ce wato Agent Madam Parveen, Matar Chief of Defence staff
         General Suraj Mahendra Marka shugaban sojojin ƙasar Australia (U.S).
                    Jiya ta shugo Nigeria domin gudanar da wasu ayyuka na kwana biyu daga nan ta koma can,     ta kawo mun ziyara ne taji labarin ina nan hospital tare da ke shine tazo...."

            Tinda Madam Aliya ta fara kora jawabai Baiwar ALLAH ta sake baki tana kallonta tareda kasa kunne tana sauraron duk abinda take faɗi,     bata ankara ba taji Madam Parveen ta dafa kafaɗarta tareda faɗin   "what's ur name?..."  
              
              Baiwar ALLAH girgiza kai kawai tayi domin ita kanta bata san sunanta ba...

Madam Parveen ganin bata ba ta amsa ba yasa ta mata magana ta Hausa yanda zata gane, a tunaninta bata iya turanci ba ne,
            Ta kuma cewa  "Dota Ya ya sunan ki?..." 

                 Madam Aliya ce ta kwashe da dariya jin har yanzu Madam Parveen bata ƙware a Hausa ba,    
wani irin harara Madam Parveen ta wurgawa Madam Aliya ganin dariyar da take yiwa Hausar ta, 
                 Ta ce "what are you laughing for?...." 
            
           Girgiza kai kawai Madam Aliya tayi ba tareda ta ce komai ba sai  ƙunsar dariya take... 
 
                Madam Parveen sharar da Madam Aliya tayi ta juyo ta cigaba da tambayar Baiwar ALLAH  cewar    " wa ne ne ya sameki kike kwanta a hospital? typhoid or maleria?
              Ga babu jini a body naki  sorry my Dota....."
                  ɗaga mata kai kawai Baiwar ALLAH tayi domin bata san wani amsa ɗaya zata bata ba.... 
                   suna cikin wannan halin saiga Doctor ya shugo da wasu nurses su biyu suna biye da shi, 
            yazo  duba lafiyarta sannan ya cire mata allurar jinin da aka ɗaura mata domin kaɗan ne ya rage,    
ya kalli Madam Parveen yace  "ke ɗin Mamanta ne ko Auntyn ta?...." 
                dasauri Madam Parveen ta girgiza kai tana faɗin "No no noo bani santa ba, I have a Daughter but I lost her since 20 years later.....".  
                 tana kaiwa ƙarshen maganar ta tayi saurin sunkuyar da kanta ƙasi sakamakon hawayen da yake shirin zubo mata....
    
          Doctor ya girgiza kai sannan yace  "sorry Madam  I think you are her mother because naga kuna kama sosai ...." 
          
    yana kaiwa nan yayi ficewarsa tare da nurses dake biye dashi!
                    jin abinda Doctor ya gaya yasa Madam Parveen ta ɗago tana ƙarewa Baiwar ALLAH kallo  tareda share hawayen da yake ƙoƙarin zubo mata, 
                       Ita kuwa Madam Aliya tinda Doctor yayi maganar nan take bin Madam Parveen da Baiwar ALLAH da kallo domin itama ta tabbatar da suna mungun kama sosai kamar wanda suka haɗa jini, bata lura da hakan ba sai yanzu, komai nasu iri ɗaya, har ta buɗe baki zata yi magana   Madam Parveen ta katse ta da cewar  " i known my Daughter she's already died since laters,
                    Omg! inaso zan tafi...."
               ta kai hannu ta shafa sumar kan Baiwar ALLAH tana faɗin  "take care Dota, Quick recovery okay .....".    
             tana kaiwa nan ta tashi ta fice daga cikin room ɗin da sauri domin bata son shiga damuwa,  saboda idan kana son ganin damuwar Madam Parveen shine ka kawo mata maganar Ɗiyarta Amreesha, nan danan zata rikice ta fara kuka ba ƙaƙƙautawa hakan yasa tayi saurin ficewa...

                Ganin haka yasa Madam Aliya itama tabi bayanta da sauri, suka fice a tare.
              Baiwar ALLAH jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba, domin taji wani abu a jikinta  amma har yanzu ta kasa kawo cewar tanada alaƙa da wannan matar Madam Parveen saboda ita ma ta fara tunanin cewar iyayenta mutuwa sukayi,   nan ta shiga dogon tunani tana tambayar kanta  "shin meyasa naji wani abu akan wannan matar? sannan meyasa ake cewa munyi kama alhalin bamu da wata alaƙa, amma kuma tace itama ƴarta ta ɓata tin shekarun baya, to me hakan yake nufi?....."
                     haka zuciyarta take ta magana  amma a zahirance  girgiza kai ta rinƙa yi tana magana a fili cewar   "a'a! a'a!! a'a!!! Bana son kalan dangi, idan iyayena suna a raye nasan wata rana zamu gana da juna amma idan har basa raye to na tabbatar haka zan cigaba da rayuwata cikin ƙasƙanci...." 
            lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka, 
                 ta zura hannunta a cikin rigarta ta ciro ƴar sarƙarta wanda yake ɗaure a wuyanta  mai zanen Jesus Christ,  tana murza sarƙar tana hawaye  kanta na kallon ceilling, tana cikin wannan halin saiga Madam Aliya ta shugo tana ta surutu tin kafin ta shugo  
             "Daman ai nasan bazata tsaya ta saurareni  ba, ita idan aka kawo zancen Amreesh shikenam an rasa hankalinta, Allah dai ya bayyanar mana da ita idan kuma ta mutu Allah ya jiƙanta....."
                       da haka ta zauna a bakin gado tana wannan surutun daga bisani tayi tagumi tareda sunkuyar da kanta ƙasi tana hura iskar bakinta,   itama damuwarta ya isheta  na rashin haihuwa tsawon shekara da shekaru amma haka take danne zuciyarta babu yanda ta iya....

                  Jin shishshitun kukan Baiwar ALLAH yasa ta ɗago da sauri tana faɗin  "lafiya kuwa Baiwar ALLAH meya faru dake?...."
   Cikin kuka Baiwar ALLAH take faɗin  "Mamanaaa! Abbanaaa!! Ina son ganinsu, Mommy and Daddy  suna inaaaa? Kowa yana tareda iyayensa amma banda nii, wannan wata iriyar ƙaddara ce haka....." 
             nan ta ƙara fashewa da kuka sosai mai cin rai, 
            
          Daƙer Madam Aliya take rarrashinta cikin kulawa, tana bata haƙuri,      
              Baiwar ALLAH ce ta rirriƙe hannayen Madam Aliya tana cewa  "dan ALLAH ki temaka mun naga iyayena, dan ALLAH Aunty..."
               Ita kuwa Madam Aliya ta ƙafar da ƙwayar idonta akan sarƙar wuyan Baiwar ALLAH, cike da mamaki take bin baiwar Allah da kallo tareda sarƙar wuyan,  tanaso tayi magana amma ta kasa lips ɗinta har rawa yake,   domin tasan a yanda taga irin wannan sarƙar,
                    Wannan sarƙar kaf Nigeria babu mai irinsa kuma Designer ɗin sarƙar a iya mutum ɗaya kawai akayi shi, 
Domin Madam Aliya bazata taɓa mantawa ba,    ita da Madam Parveen suka je har ƙasar Maleshiya aka ƙero wannan sarƙar wa Amreesh,  dake Madam Parveen su ɗin christal ne hakan yasa aka yi musu mai design ɗin zanen Jesus  kuma ba ƙaramin kuɗi aka kashe wa sarƙan nan ba,  
                   Madam Aliya hannu na kakkarwa ta miƙar da hannunta saitin wuyan Baiwar ALLAH tana jujjuyar da sarƙar   ata gefe da gefen sarƙar akwai yanda aka rubuta sunanta da ƙananun baƙi wato amreesh,  
                  A razane Madam Aliya tace "Amreesh...." tana bin fuskar Baiwar ALLAH da kallo sai a yanzu kamannun Amreesh lokacinda take ƙarama yake bayyanowa akan fuskar Baiwar ALLAH, 
                 A lokacin ba ƙaramin ruɗewa Madam Aliya tayi ba,  muryarta har harɗewa yake gurin faɗin  "Please juyo naga bayanki akwai abinda nake son gani...."
               
           Baiwar ALLAH cikin rashin fahimta take bin Madam Aliya da kallo kamar wata zautacciya, 
         Haka Madam Aliya ta kwantar da Baiwar ALLAH kan cinyarta ta ɗage mata rigar jikinta  saiga drowing photon bindiga ya bayyano,  Madam Aliya bata san lokacin da ta fara washe baki ba tsabar farin ciki  domin ta tabbata Baiwar ALLAH ɗiyar Madam Parveen ce, domin duk ƴaƴan Madam Parveen sunada wannan tambarin zanen bindiga a gadon bayansu,  Yayun Amreesh su biyu  Mohandas da Rakesh sai Amreesh  hatta ita kanta Madam Parveen tanada wannan tambarin da Daddynsu shima,  ba ƙaramin farin ciki Madam Aliya ta tsinci kanta a ciki ba,  a zabure ta miƙe tsaye tana faɗin  "bari nabi bayan Madam Parveen yau zatayi kwanan farin ciki...." tana kaiwa nan ta fice daga room ɗin da gudu...

           Ita dai Baiwar ALLAH sam bata fahimci komai ba sai sake baki datayi tana bin bakin ƙofa da kallo yanda Madam Aliya ta fice, abun ya ɗaure mata kai sosai.....

              Ita kuma Madam Aliya tana  zuwa ta shige motarta a ɗari ta fice daga cikin hospital  kai tsaye airport ta nufa domin  Madam Parveen ta sanar da cewar ita komawa ƙasar U.S zatayi baza ta iya aikin da tazo yi ba saboda ɗiyarta Amreesha,  kwata-kwata ta tsani nan ƙasar Nigeria.....




Please help me and share dis book 🙏🏼🙏🏼🙏🏼








Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol