FreeArewaPen original
MY ENEMY BOOK 1
- 1views
- 25chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
I'm Asmeetah Writer
Sample · Chapter 1
꧁꧂ (C.D.S) Chief of Defence staff Chief Suraj Mahendra Marka shugaban sojoji na ƙasar U.S wanda a baya ya zauna anan ƙasar Nigeria dake garin Babban Birnin F.C.T Abuja, yana da mata ɗaya wato Agent Madam Parveen jami'ar C.I.D da ƴaƴansu uku! Babban Ɗansa shine Marshal. Mohandas Suraj Mahendra, Sai kuma Ɗansa na biyu shine Commander. Rakesh Suraj Mahendra, Sai kuma Autarsa Amreesha Suraj Mahendra, C.D.S Suraj ya rasa Ɗiyarsa Amreesha tin tana ƴar shekara biyu a duniya ta hanyar hatsarin mota da sukayi ita da mahaifiyarta Madam Parveen a hanyarsu ta dawowa daga garin Kaduna zuwa Abuja, wacce Madam Parveen ita take driving ɗinsu Anan suka samu babban hatsari anyi nasarar ceton rayuwar Madam Parveen amma saidai ita Amreesha yarinya ƴar shekara biyu ba'a sameta a cikin motar ba, an dudduba ko ina a wajen da sukayi hatsarin amma an gaza samun koda ƙyallenta ne balle gawarta, iyayenta sun shiga damuwa mai tsanani na rashin ɗiyarsu Amreesha, yanzu shekara goma sha takwas da faruwar wannan Al'amarin, shin Amreesha tana raye ne ko dai ta mutu? ALLAHU a'alamu....Sai dai wannan family christal ne, gaba ɗayansu jami'ai ne hakan yasa suke da wani tambari na zanen catoon ɗin bindiga a gadon bayansu daga iyayen har ƴaƴan, kuma itama wacce aka rasa wato Amreesha tanada wannan tambarin, babban burin C.D.S Suraj shine idan Amreesha ta girma zata zamo jami'a ta musamman acikin sojoji amma kash lokaci guda ya rasata... Amreesha wasu masu farauta ne suka tsince ta acikin jeji a yashe, saida tayi wajen shekara guda a hannunsu tukun suka yanke shawarar kaita gidan marayu ko za'a samu iyayenta tinda su har yanzu sun kasa samun iyayenta, a wannan lokacin kuwa iyayen Amreesha har sun bar Nigeria sun koma ƙasar U.S gaba ɗayansu domin sun saddaƙar da cewa ɗiyarsu Amreesha ta mutu....꧁꧂Chief of Army's staff Chief Muhammadu Zaiduddeen Bature. yana zaune a nan ƙasar Nigeria dake garin Abuja G.R.A. su uku iyayensu suka haifa daga shi sai ɗan uwansa Sarki Abubakar Zaiduddeen Bature, mai martaba sarkin ƙasar Jidda, sai ta ukun su Aunty Yolash tana aiki a ministry of education dake garin Bauchi.. Chief Muhammad Bature Matarsa ta farko itace Hajia Fateema wacce ALLAH yayi mata rasuwa tin shekarun baya sakamakon haihuwar ƴan biyunta wato the twins, MAJOR GENERAL RAZHDEEN (M.G.R) da kuma SURGEON DOCTOR ROSHAN (S.D.R).. daga baya Chief Muhammad Bature ya Auri Matarsa ta biyu Hajia Kilishi wacce yanzu take zaune dashi da yaranta Biyar duk Mata, ta farko itace Meenat sai ta biyu kuma Pinky sai Ruky da Ummy sai Autar ɗakinsu wato Tiny itace ƙaramar cikin su, Hajia Kilishi taso ta samu ɗa namiji amma ALLAH bai bata ba, tin akan ƴarta Tiny aka cire mata mahaifa sakama...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.