Free chapter · Read without an account
Chapter 8
꧁꧂
Madam Aliya hanyar airport ta nufa tana gudu tana ƙoƙarin ƙiran wayan Madam Parveen akan ta dakatar da ita daga tafiyar da zatayi, dan zai iya yuwa tana zuwa ta samu jirgin da zai tashi, ƙira akan ƙira amma Madam Parveen taƙi yi picking hakan yasa Madam Aliya ta ƙarawa motarta gudu....
Ita kuwa Baiwar ALLAH tana zaune abun duniya duk yabi ya isheta ga bala'in yunwar da take ji bata ci komai ba, idonta ne ya sauƙa akan ledojin da Madam Aliya ta shugo dasu, da sauri ta sauƙa akan gadon ta bubbuɗesu cikin sa'a ledar farko banƙararrun kaji ne a ciki sun sha eggs, sai leda na biyu soyayyun dankali ne da eggs sai shawarma ga lemukan gora da farro na ruwa, haka ta zauna ta fara tura su kamar wanda wani zai ƙwace, taci abinda zataci tabar sauran domin ba ƙaramin ƙoshi tayi ba, ta buɗe murfin gorar lemo tass saida ta shanye su, sannan ta miƙe ta nufi toilet tayi wanka tare da ɗauro Alwala tazo ta shimfiɗa sallaya ta tsaida sallah...
꧁꧂
꧁꧂
꧁꧂
Ɓangaren Ƴar Amana!
tana zaune a bakin gado ta haɗe kai da gwiwa sai sumar gashinta da ya rufe mata kanta gaba ɗaya,
tana jin buɗar ƙofar ɗakin tayi saurin ɗagowa domin ganin ko wanene ya shugo idonta duk yayi jawur tsabar kukan da take sha kullum, ganin wanda yake shugo mata kullum ne yasa ta ƙara fashewa da kuka saboda tasan bazai taɓa jin tausayinta ba balle yayi ƙoƙarin fitar da ita, mutumin koda yaushe fuskarsa a rufe take da baƙar hula, yauma kamar yanda ya saba haka ya shugo da wata ƴar leda wanda ba komai ne a ciki ba sai abinci jallof rice, yana zuwa gabanta ya wurga mata ledar abincin sai pure water da ya kuma jefa mata, da sauri ta rarumi ledar abincin ta buɗe a gaggauce ta wangame ɗan ƙaramin bakinta ta fara turawa ba ƙaƙƙautawa domin ba ƙaramin yunwa take ji ba, abinci ne a rana sau ɗaya ake bata, idan aka bata yanzu sai kuma gobe shiyasa bata wasa waran cin abincin nan danan har ta lashe ta ɗauki ruwan shima ta gwangwaɗe,
Shi kuwa Guest yana zaune ya kafa idonsa a kanta yana jiran ta kammala yayi mata abinda ya saba yi kullum domin bazai iya ganin Nama a gida ya barta ba dole zai ɗan rage zafi,
tana kammalawa yasa hannu a cikin rigar sanyinsa ya ciro wata ƴar ƙaramar allura yana jujjuyata idonsa zuru-zuru acikin hular fuskar yana ƙareta da kallo,
Ƴar Amana ganin allurar yasa ta fara ja da baya domin tasan allurar kullum sai yayi mata daga nan bata sanin abinda yake faruwa da ita saboda hankalinta fita yake daga jikinta sai bayan 24 hours take farfaɗowa,
tana cikin karkaɗa masa kai da hannu bibbiyu tana roƙonsa domin babu bakin magana, bata san lokacin da ya yo sufa ya janyota jikinsa ya caka mata wannan allurar ba, daga nan bata ƙara motsi ba sai kanta da yake kan faffaɗar ƙirjinsa, yafi minti 30 yana kallon kyakykyawar fuskarta, sannan ya kwantar da ita kan gadon yasa hannu yana shafa sumar kanta da gefen fuskarta, yana jin wani abu sosai a ransa wanda shima kansa bai san dalilin hakan ba, yana mamakin kansa sosai abinda yayi niyar yi baya taɓa aikatawa, yana son kasancewa tare da yarinyar amma yana matuƙar jin tausayinta especially idan ya hasasho yawan shekarunta wanda bazata wuce 15yrs ba, sannan gata Kurmiya..
A razane ya miƙe daga kan gadon ya sauƙa kullum acikin haka yake bai taɓa aikata abinda yayi niyya ba saidai kawai yayi mata allurar, kuma daya kasance daman ba manemin mata bane, sam baya shiga harƙar mata wannan ma abinda yasa yake jin hakan a ransa saboda a fake suke kuma yarinyar tana matuƙar burge shi, bai taɓa jin wani abu akan wata yarinya ba sai akan Ƴar Amana, abun yana matuƙar ɗaure masa kai gata yarinya ce bata gama cika cikakkiyar mace ba,
Wannan mutumin shi ake ƙira da GUEST mungu ne na asali akan abinda aka umarce shi, shima yana aiki ne a ƙarƙashin wani mai ƙarfin iko, baya taɓa bayyanar da fuskarsa kuma sannan baya shiga cikin gari sai cikin dare, ya kasance rayuwarsa a cikin daji ne da mutanensa manya-manyan ƴan daba masu kayan yaƙi,
Itama ƴar Amana sashi akayi ya ɗaukota ya cigaba da riƙeta a gurinsa kafin a aiwatar da aiki akanta, shima kansa Guest bai san dalilin da yasa aka ce ya ɗaukota ba, sannan bai san mai za'a mata ba sai dai idan lokaci yayi a sanar masa idan har shine zaiyi aikin akanta,
GUEST baya neman mata sannan baya shaye-shaye, idan kuwa aka bashi aiki akan kisa bayayi saidai shima yasa wani yayi, bashida tsoro sam sannan baya fargaban komai, baya aiwatar da abu da kansa saidai idan an bashi umarni.....
꧁꧂
꧁꧂
Baiwar ALLAH tana zaune akan sallaya kusan awa uku sai faman addu'o'i take tana jiran shigowar Madam Aliya shuru-shuru har yanzu gashi ana shirin ƙiran sallar mangarib, tana zaune taji an turo ƙofar ɗaki, ɗagowar da zatayi taga Nurse tayi tunanin Madam Aliya ce domin ta gaji da zaman asibitin nan,
Nurse tana shugowa tace "am kece wacce Madam Aliya ta kawo?..."
Dasauri Baiwar ALLAH ta ɗaga mata kai tareda faɗin "eh Ni ce..."
Nurse taja dogon numfashi tare da girgiza kai tace "sorry for what am going to say...."
Baiwar ALLAH idonta akan Nurse domin tana son jin abinda zata gaya ita har ranta so take taji Nurse tace an sallame su domin ba ƙaramin gajiya tayi ba,
Nurse tace "Doctor ya ce kada na sanar miki amma naga babu amfanin ɓoye miki tinda naga kinada tawakkali da sanin ƙaddara mai kyau ko akasin haka, kiyi haƙuri dan ALLAH,
ALLAH yayiwa Madam Aliya Rasuwa sakamakon hatsarin mota akan hanyarta na zuwa airport....."
Kafin Nurse ta ƙarasa maganar Baiwar ALLAH ta miƙe tsaye da sauri ido a zazzare tana bin Nurse da kallo kamar wata zararriya,
Nurse ta ƙarasa maganar ta da cewar "motarta ce ta shige cikin traller, yanzu haka tana nan mutuware zaki iya zuwa ki ganta...."
tana zuwa ƙarshe ta juya ta fice tabar Baiwar ALLAH a sanƙare a wurin...
Mutuwar Madam Aliya ba ƙaramin girgiza mutane yayi ba, domin babu wanda bai santa ba saboda ba ƙaramar mata bace ta sanu sosai, anji mutuwarta sosai especially mijinta,
Innalillahi wa inna ilaihi raju'un,
Sai bayan isar Madam Parveen ƙasar U.S sannan ta biyo ƙiran wayan Madam Aliya ganin yawan miss call ɗin da tayi mata waran 30 missed call, abun ya bata tsoro sosai, kuma bawai taƙi ɗaukar ƙiranta bane wayar ce a silent, bayan ta ƙira jin muryar Namiji yasa ƙirjinta bugawa, a hankali ta furta cewar "where is madam Aliya?..."
Mutumin yace "sorry Madam Parveen baki ganeni ba koh? Ni mijinta ne wayar tana hannuna sakamakon hatsarin motar da Hajia Aliya tayi, yanzu haka bata raye ta riga mu gidan gaskiya, har mun ɗaukota a mutuware tana gida za'a sallaceta...."
duk wannan maganar ta turanci yayi mata,
yana kaiwa ƙarshe ya katse ƙiran,
Madam Parveen kamar a mafarki taji wannan maganganun, jin kanta tayi yana juyawa, a ruɗe ta fara girgiza kai tana faɗin "kai kai Kaiii i can't believe, Madam Aliya she never die, dis is a lie...."
haka ta ƙara dialing number Madam Aliya tana ƙira amma ba'a picking daga ƙarshe akayi switch ɗin wayar, jin hakan yasa ta hau Social media a ruɗe domin ta ƙara tabbatarwa ai kuwa tana hawa abinda ta fara gani shine photon Madam Aliya ana sanar da labarin mutuwarta ta ko ina!...
bata san lokacin data jefar da wayar gefe ba, haka ta ɗora hannu akai ta fara rausa ihu tana faɗin "Jesus! Jesus!! Jesus!!! Oh my God my Best friend...." ihu take kamar ta nitse ƙasi, ga bata samu kowa a gida ba balle a samu mai rarrashinta.....
Baiwar ALLAH tinda taji labarin mutuwar Madam Aliya tasa ƙafa tabar hospital bata tsinci kanta a ko inaba sai akan titi, tafiya kawai take tana kuka ita kanta bata san ina zata je ba, rabonta data taka saman kwalta tin tana ƴar yarinya,
tana tafiya har dare yayi mata a hanya,
Ganin bata san ina zataje ba yasa ta samu guri a bakin wani ShopRite ta zauna, ta zuba uban tagumi hawaye yaƙi tsayuwa, tana cikin wannan halin saiga wasu maka-makan motoci kusan guda 15 a jere sun zo sun wuce, a razane ta miƙe tsaye tana ɗaga musu hannu tare da ɗaga murya tana faɗin "Dan ALLAH temako! temako!! temako!!!...."
haka tabi bayan motocin da gudu saboda taga basuda niyyar tsayuwa kuma ba lalle su jiyota ba, tana cikin binsu da gudu taga sun sha wata kwana duk da tayi mungun gajiya amma haka ta daure itama tasha kwanan da sukabi tana haki numfashinta har ƙoƙarin ɗagewa yake tsabar gudun data sha, ita kanta tayi mamakin yanda ta iya bin motocin nan da gudu, tana shan kwanan da motocin suka bi ta fara ganin wani irin haske mai kashe ido sai walwali hasken yake yana bada haske kala-kala, ga wasu maka-makan gidaje wanda daƙer zaka iya ganin tsayin gidajen, unguwar yanda kasan a wani country yake, ko wane gida da kalar haskensa wannan yana bada hasken red wannan gidan hasken blue wannan green wannan white wannan purple wannan yellow kala-kala gasunan,
babu alamar duhu a unguwar haske ta ko ina, wannan unguwar shi ake ƙira da Aljannar duniya, domin duk wanda ya shugo unguwar nan bazai so fita ba saboda tsaruwar da yayi, unguwa ne na manya-manyan masu kuɗi na gaske, gidajen ministoci ne da govrnoni, da Generori gasu nan dai,
Baiwar ALLAH ta kasa tsayar da gudun sannan kanta na kallon sama sai kallace-kallacen gidaje da ta tsaya yi still bata dena gudun ba, ita har ta manta mai take bi da gudun, gaba ɗaya ta shagaltu, bata tashi ankara ba saida taji an girbe mata ƙafa da ƙarfi wanda saida tayi sama kafin ta doku a ƙasin floor wanda duk unguwar a zagaye yake da floor babu ƙasa ko ɗaya,
Goshinta ne ya bugu da ƙasi bata san lokacin da ta sau ƙara mai ƙarfi ba,
lokaci guda tayi shuru saida ta ɗau kusan minti 30 kanta a kife kafin ta soma motsawa a hankali tsabar buguwar da tayi hatta jikinta saida yaji,
A hankali ta fara ɗago kanta ga goshi har ya fashe sai jinin da yake zuba, lumshe idonta ta fara yi saboda tsananin hasken da yake shirin kashe mata ido, ba hasken komai bane illa hasken unguwar da kuma layin gidan data biyo wanda layin gidan yake cike da manya-manyan security sojoji masu jajayen handkerchief a ɗaure saman goshinsu,
Baiwar ALLAH ganin sawun takalmin sangamemen soja a gabanta yasa ta fara bin ƙafar da kallo tana binsa da kallo har saida ta ɗage kanta sama sosai kafin ta iya ganin fuskar mutumin yana ɗaure da jan ƙyalle akan goshi sai huci yake, mai ƙirar samudawa jikinsa sai zaƙami yake yana sanye da kakin sojoji,
Ganin wannan soja yasa ta ƙara kifar da kanta alamar suma tayi...........