Free chapter · Read without an account

Page-33

by 🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚 🖋️ · “SANADIN ƘADDARATA”

*FASAHA WRITER'S ASSOCIATION*
     (*F.W.A)*©✍️
     ⭐⭐⭐

Ƙungiya masu aiki cikin salon hikima da fasaha gurin juya tunanin al-umma, kaifin alƙalumansu ya zarta takobi ©✍
___________________________________________________



بسم الله الرحمن الرحيم.
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد. 




❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁ 




Free book📓



By


*Aisha G Umar*
_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_




Page3️⃣3️⃣





INNA JUMMAI.

Yanzu da wannan dubu biyar ɗin ta lallaɓa ta fara sana'ar suyar ƙosai a ƙofar gida, duk da jarin kaɗan ne amma haka ta ke lallaɓashi, mutanen unguwa sun yi mamaki da ganin wannan al'amari, amma ba wanda ya tinkareta da maganar, sun riga da sun san halinta ba ta ganin darajar kowa, kuma ba komai ba ne yasa sai saboda 'yarta Halima, shiyasa duk wanda su ke ganin Halima à wuraren banza, ba sa zuwa sanar mata domin suna ganin ta sani ita ce ma ta bar Halimar dama.

Haka dai Inna ta cigaba da gara rayuwarta cikin wahala, ƙunci da baƙin ciki, ta bi ta rame, ga ƙosan ma wata rana haka za ta soyeshi amma ta yi kwante, ɗan jarin dubu biyar da ya fara tashi sai ga shi ya fara komawa, tunani kaɗai ya ishi Inna, na Halimar ma kawai bare na abun da ta yi mata. 

HALIMA.

Ko da ta bar gidan à wannan daren da S man, a wani guri su ka kwana washe gari kuma su ka ɗaga daga garin Adamawa zuwa garin Abuja, wani gida ya kaita mai shegen kyau, da zummar gidan da ya siya mata da kuɗaɗen da ya ke tara mata ne, ta yi farin ciki sosai, har tana jin sonsa ya ƙara shiga cikin zuciyarsa.

Tana kwance a gefensa bayan sun gama aikata alfashansu, ta ce, "my S man ya ake ciki ne? Yaushe za mu yi auren? Na ga tun da mu ka zo ba ka ce da ni komai ba" ya saki wani fara'a wanda bai kai zuciya ba, ya ce, "kar ki wani damu my Hali, kema kin san ke ce wanda na ke so kuma na ke son aura, don haka wani ƙaramin shiri na ke yi, kuma da zarar na gama cikin 'yan kwanakin nan za mu yi aure".

Sake shigewa jinkinsa ta yi, domin kuwa maganarsa ya faranta mata rai, ta kuma faɗin, "shikenan ina jiran wannan lokacin, ranar farin ciki a gareni, akwai wani surprise ɗin da na ke son faɗa maka, wanda hakan ne yasa na ke son ka da aurenmu ya ja lokaci" "wani surprise ne haka? Ina jinki faɗa min" à hankali ta tashi ta zauna sannan ta ce cikin murna, "kasan jiya na je asibiti saboda tun da na zo garin nan ban ganewa jikina".

Gyara zama ya yi sosai yana sauraronta, ta cigaba da cewa, "toh bayan na je, shine likita ya ke sanar da ina ɗauke da ciki", shiru ya ratsa ɗakin S man bai ce komai ba, Halima kuma na jiran ganin murna. Kafin ta sake magana kamar wanda aka tsakura, S man ya yi wani irin tashi daga kan gado ya dire ƙafafunsa à ƙasan tayis, da ƙarfi ya ce, "kee! Kin san me ki ke cewa kuwa? Kina cikin hankalinki kuwa!?".

"Kamar ya S man? Ina cikin hankalina mana". Cewar Halima tana binsa da kallo, "Wannan abun ba zai taɓa yuwa ba, taya bayan aurenki da zan yi kuma ya zama harda ɗa? A ah abun ya yi yawa ai kuma, toh ma na waye cikin wai?".

Da mamaki itama ta sauka ƙasa, a iya saninta daɗi S man zai ji da kuma yin murna idan labarin ya riske shi, amma ya ta ga ya wani ta da hankalinsa? Wato halin 'yan bariki zai nuna mata kenan? Lallai aikuwa ba da ita ba. Cikin nuna masa ya yi kaɗan ya wulaƙanta ta ta fara cewa.

"Me nufinka to S man? Ciki na waye zan yi idan ba na ka ba? Ai ko wani ya yi min wannan bayar kana da amsa bare a ce kai da kanka zaka furta min, to wallahi ka yi kaɗan, ni ba irin matan nan marasa sanin kimarsu ba ce, bare ka ce za ka yaudareni, wallahi ba ka isa ka wulaƙantani ba, aurena ne dole ka yi idan ba haka ba kuma nuna maka cikakkiyar ko ni wacece, ka san cewa na fika iya bariki! To kuwa gwara ka shiga taitayinka ehe!". Ta faɗi har da ɗaura hannaye biyu a kwankwaso.

Jan numfashi S man ya yi ya ijje, kamar ba shi ya yi maganar ba, ya matso kusa da ita yana kallonta cikin ido, ga yadda ta mayar da fiskarta à ɓace, da sanyin murya ya fara controlling fushinta, "yanzu my Hali taya ki ke tunanin ni S man zan gujeki? Ko me ya sameki à rayuwa ni ina tare da ke bare wani ciki, cikin da nawa ne ba na wani ba". "To taya ba zan yarda ba bayan kai ka yi maganar da kanka?" Faɗin Halima.

Murmushi ya sakar mata ya kuma cewa, "gwaji ne na yi sai kuma na ga kin yarda, kenan da a ce wani ya sanar da ke zan gujeki za ki amince?" Ya faɗi yana ɓata rai wai shi ba ta kyauta masa ba. Hannunsa ta kama sannan ta ce, "kai ka san na yarda da kai fiye da kowa a duniyar nan, wanda dalilin hakan ne yasa na mallaka maka kaina, ka yi haƙuri da abun da ya faru yanzu to".

Nan dai su ka yi maslaha S man har da nuna mata ya ji daɗi sosai kasancewar tana da ciki. Babu wani tunani ta miƙa masa wannan akwatin ƙarfen kuɗin Innar nan ya ɗauka ya fita da shi akan zai je ya yi abun da ya kamata da su. 

Bayan fitarsa ɓalle akwatin ya yi, ya kwashe kuɗin gaba ɗaya ya sauya musu jaka, da mamaki ya ga kamar wani abu maƙale a gefen akwatin, hannu ya sa ya zaro shi, ashe hoto ne, saboda tsabar daɗewa da kuma kasancewarsa cikin akwati mai tsatsa, hakan yasa hoton gefensa ya yi fara ɓaci sosai, sai dai bai rufe fiskar yarinyar da ke jikin ba.

Da sauri S man ya miƙe tsaye yana zurawa hoton ido da mamaki sosai, "wannan kamar ita ce, domin marabar kaɗan ne da fiskarta n'a yanzu, kawai dai wannan lokacin yarintarta ne, to amma me ya haɗa Hali da ita?" Ya faɗi yana sa ke share hoton don ya tabbatar da ita ɗin ce ba wai idonsa ba ne ke yi masa gizo. 

Ijje hoton ya yi awurinsa, don yana son ya tambayi Halima ya ji me alaƙarta da ita?. Kusan magriba ya koma gida. Bayan ya isa falon samun Halima ya yi tana zaune a falo tana kallon indian film a tashar Tauraruwa, bai zauna ba ya wuce kitchen, buɗe fridge ya yi ya ɗauki lemo mai sanyi, sannan ya ɗauki kofi guda biyu, ya buɗe ya tsiyaya lemon a cikin kofin sannan ya ijje ragowar a gefe bayan ya kulle. Hannunsa yasa à aljihu ya fiddo da wani ƙwayar magani.

Ɗagasu sama ya yi yana kallo sannan ya saki murmushin mugunta, idanuwansa su ka cika da annuri amma mai haɗari yana cewa, "Halima ba ni da buƙatar ki haifa min jini na, domin kuwa ba na sonsa, to idan na barshi har ya fito duniya ban yi masa adalci ba. Don haka za ki sha wannan maganin, kuma shi wannan maganin, zaɓi biyu ne garesa, na ɗaya! Ko cikin ya zube, na biyu! Ko kuma cikin ya dawo mai son illataki!". Ya faɗi sannan ya sauke, ya juya don ganin ba ta taho ba, sannan ya ɓare ya jefa guda biyu a ciki.

Sai da ya jira maganin ya narke a ciki, sannan ya ɗau cokali ya gauraya, bayan ya ijje cokalin ya ɗaga kofunan guda biyu, na sa a hannun hagu, wanda ya sa magani kuma a hannun dama. Da murmushi akan fiskarsa ya iso falon haɗi da ijje kofin a gabanta, ya zauna a gefe yana faɗin, "my Hali ga lemo nan ki sha, yadda na ga kin zauna haka kina buƙatar abu mai sanyi don kallon ya yi miki daɗi.

Halima ta ji daɗin abun da ya yi mata sosai, don haka ta sa hannu ta ɗauka tana kashe masa ido da cewa, "nagode mijina", murmusawa ya yi mai cike da manufa da mugunta, tare da ɗaga na sa kofin ya sa a baki yana kurɓa, cikin zuciyarsa ya ce, "asha lemo laafiya my Hali!".....

SADIYA.

Ta yi farin ciki sosai ko da ta ji labarin sa ranar auren ƙannenta da kuma yayanta, sai dai har yanzu babu wanda ta faɗawa abun da ya ke faruwa da ita, hatta maganar auren da mijinta zai ƙara ba ta faɗa ba, su Baaba sai hidima ake yi buri ya cika Faruq zai auri wanda ta ke so. Faruq ko sau ɗaya bai nuna jin daɗinsa ga auren ba, su Baaba su ke kiɗansu kuma su ke rawansu abunsu. Yayin da a wurin Mairo kuwa tuni shiri ya kammala da zarar 'yarta Nusaiba ta shiga gidan to komai zai tafin musu daidai.

Malam bai ce komai akan lamarin ba, domin kuwa ya kira Faruq kuma ya ce masa ya amince da batun ba tare sa sanar da Malam dalili ba. Haka dai kamar yadda Baaba ta ce aure ko sati ɗaya bai kai ba aka ɗaura auren Faruq da Nusaiba, inda aka ijjeta à ɗakin baƙi wanda ya ke ciki ɗaya. Sadiya kuwa ta sha kuka ita kaɗai a gefe duk da ta san cewa Faruq yana sonta, sannan kuma dama ba wai son auren ta ke ba.

Amma fa sai abu ya sanja, Faruq ya shallake mata tunani baki ɗaya, tun ranar da aka kawo Nusaiba gidan, Faruq ya kwana a ɗakinta, shikenan ya sauya gaba ɗaya, ko kallon inda Sadiya ta ke ba ya yi bare ya kulata. Abu ya sake yiwa Sadiya yawa, amma kuma sai ta fawwalawa Allah lamarinta, ta cigaba da yin addu'a domin zuwa ɗaya zuciyarta ta ba ta ba lafiya ya sanya Faruq yi mata haka ba. 

Sadiya na ɗaki tana kwance akan gado, waya ta ke yi da Momy, "ya mijin na ki da sauran 'yan uwansa?" Cewar Momy, Sadiya ta ba ta amsa da, "duk suna lafiya Momy" "to masha Allah, ina fatan komai lafiya a can ko? Babu wata matsala?" Lumshe ido ta yi wanda hakan yasa ƙwallan da ya tarun mata a ido ya sauko, 'akwai matsala, ina cikin matsala Momy' ta faɗi a zuciyarta.

Sake tambayar da Momy ta yi nne yasa Sadiya saurin tashi ta zauna haɗi da share hawayen, murmushi ta ke son kawowa kan fiskarta amma hakan ya gaza yiwuwwa, ta daure dai ta ce, "ba komai, ba wata matsala Momy" , "toh Allah ya miki albarka 'yata, ki gaishe min da mijin na ki", da ameen Sadiya ta amsa sannan ta ijje wayar.

A hankali ta fara cewa. "SANADIN ƘADDARATA shine kalaman da Momy ta faɗa min, amma na san zan ci ribar rayuwa a nan gaba, komai zai sauya min insha Allah. Momy na riƙe maganarki, ban san me yasa ba, amma wannan maganar ta ki ta kamu sosai a zuciyata Momy. Kuma na san da yardar Allah haƙuri zai min rana kamar yadda ki ka ce, sannan addu'ata za ta amsu".

Tana faɗi ta kwanta tana kuka, saboda rashin kulatan da Faruq ba ya yi shine babbar jarrabawarta a yanzu. Tana a haka ta ji sallamar Badiyya da Fatima, tana jinsu suna yada mata zance, da ƙarfi su ke maganar don ta ji. Ba ta tashi daga inda ta ke ba, sai ma kukan da ta sa ko ranta zai samu salama.

Su kuwa ko da su ka isa ƙofar ɗakin Nusaiba da sallama su ka shiga, ba su sameta à cikin ɗakin ba tana toilet à waje. Gefen gado Badiyya da Fatima su ka zauna akai. Bayan Nusaiba ta fito daga banɗaki ta tarar da su akan gadonta, "anty Nusaiba ina wuni?" Suka haɗa baki gurin faɗi suna washe baki, domin ita suna sonta har da Anty su ke ce mata.

Kamar kashi haka Nusaiba ta ke binsu da kallo, "me haka!?" Ta faɗi da ƙarfi tana ƙarasowa inda su ke, juyawa su ka yi suna kallon juna da mamaki, sai Fatima ta juyo ta dubeta ta ce, "Anty Nusaiba me ki ka gani?" "Ba ku da hankali ne kuna ganin na share ɗakina tas za ku shigo min da ruɓaɓɓun ƙafafuwanku cikin ɗaki? Hakan ma bai isheku ba saboda renin wayo za ku zo ku zaune min akan gado, salon ku karye min shi?", cewar Nusaiba da masifa.

Tsabar mamaki bushewa Badiyya da Fatima su ka yi suna kallonta, ganin ba wanda ya motsa a cikinsu yasa ta sake cewa, "tsayawa ku ka yi kuna kallona? Ku fice min a ɗaki don Allah! Sai ka ce na gayyace ku", da sanyin guiwa su ka baro ɗakin suna ta kallon juna, ita kuwa ko da su ka fita zuwa ta yi tana karkaɗe inda su ka zauna tana jan tsaki, wato yaran nan sai ta yi maganinsu.

Juyawa su ka gun Sadiya da ta fito daga ɗaki, harara su ka jefa mata sannan su ka wuce sashinsu, ko da su ka isa su ke sanar da Baaba da Lantana abun da ya faru, Baaba sai cewa ta yi, "to ku dama me ya kaiku zama mata akan gado, ai kun san abun babu daɗi" Shiru su ka yi su ka kasa cewa komai....

DARE.

Kamar yadda mahaifiyarta Mairo ta sanar da ita, à daren bayan sun kammala cin abinci ta dubi Faruq ta ce, "Faruq dama akwai wata buƙata da na ke nema a wurinka, kuma nasan ko shakka babu zan samu masoyina" ɗagowa Faruq ya yi ya kalleta da nishaɗi ya ce, "faɗi duk buƙatarki zan yi miki shi". 

"To ka ga ɗakin nan guda daya ne, bai da wani girma mai kyau, sannan akwai wasu 'yan uwana da za su zo dubani, ba su zo biki ba kasancewar da gaggawa aka yi komai, shine na ke son idan ba damuwa Sadiya ta dawo ɗakin nan da zama, ni kuma na koma na ta sabida ya fi girma da kuma kyau, toilet yana cikin ɗakin amma nan sai na fita kafin nan, sannan idan 'yan uwan nawa su ka zo za su min dariya ba idan su ka ganni a nan".

Ba tare da wani musu ba Faruq ya miƙe, "ina za ka je?" Ta faɗi ganin yana shirin fita, sai ya ce mata zai je ya faɗawa Sadiya ta fitar da kayanta a ɗakin ne, cikin jin daɗi da ganin gaskiyar maganar Mairo, magani yana aiki, sai ta ce, "a ah kar ka ce mata yau, ka ce mata zuwa gobe, sannan ina son ka sanar da ita ta rinƙa yi mana girki domin yau ma da ƙyar na yi wannan ma, ka ji?" Murmushin da na fitar hayyaci ne ba shi da kansa ba ya yi mata, sannan giɗa mata kai ya bar ɗakin.

Sadiya na zaune ta yi tagumi akan kujrarta kawai ta ji mutum ya faɗo cikin ɗakin ba sallama, zumbur ta miƙe tana kallonsa, mai makon ta ji wani abu saboda yadda ya shigo, sai kawai ta fara sakin murmushi idanuwanta su ka cika da hawaye, tun ranar da aka ɗaura masa aure su ka yi hira da shi, bai sake zuwa inda ta ke ba, ko ta ganshi a waje baya kallonta bare ya amsa maganar na ta, amma sai gashi yau yazo.

"Dama na san za ka dawo my dear, na san ba za ka wulaƙantani ba, na sani" ta faɗi tana fitar da hawayen farin ciki har ta isa dap da shi, za ta rungumeshi kenan ta ga ya ha da baya. Sai à lokacin ta lura da wani irin kallon da ya ke jefe mata. Tsayawa ta yi kawai ba tare da ta kuma cewa komai. "Wacece ke da ki ke son raɓar jikina?!" Ya faɗi cikin dakewa fiskarsa na yi mata kallon da ta kasa fassarawa, wani irin ƙara ya ziyarci zuciyarta saboda yadda maganar ya ratsa majiyarta.


Last page
___________________________________________________ 

Hmm kun ga dai yadda rayuwa ta sake yiwa Inna, shin ya zai kasance a ɗan lokaci gaba?.

Shin hoton waye S man ya gani? Sannan kuma ya santa? Wacece kuma ya aka yi ya santa? Ga shi yana son zubar mata da ciki, da kuma magani mai haɗari, shin kuna ganin Halima za ta qha maganin?.

Ga Sadiya baiwar Allah, da alama dai Nusaiba da shiri ta shigo gidan nan, ga shi za ta fara ci wa Sadiya mutunci. Hmmm. Ga dai yadda Nusaiba ta yiwa su Fatim😃 me ku ke tunani?




_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol