Free chapter · Read without an account

007

by Fatima Muhammad Gurin · SAFARA A TAƁO

SAFARA A TAƁO 


FATIMA MUHAMMAD GURIN 

*GUREENJOH*


*ADABI WRITERS ASSOCIATION*


*PAID BOOK*


*007*



"Na'am Daddy"

Ta amsa a sanyaye tana komawa zaune.

Momma da take kallonsu sai ta ji zuciyarta ta sake karyewa, ta san irin kaunar da mahaifinta ke mata, ta san irin kusanci da fahimtar juna da suke dashi bata san wani irin ƙaddara bane ya ratsa rayuwar ɗiyarta amma a yanzu tana fata ko ma menene ya tsaya iya hakan.

Ko ma menene tana Adu'a Allah ya sa ta hankalta da darasin da rayuwa ke son koya mata.


"Yaushe za ki koma asibiti checkup?"

Ta ce 

"Ranar monday ne"

"Toh Allah ya kaimu, batun makaranta nake son in miki 'yar uwarki zata koma Litinin ya kamata a ce kema kin koma ɗin"

Da ɗan sauri ta kalleshi don bata taɓa zaton zai bari ta cigaba da fita a gidan da sunan karatu ba ko Momma mamaki ne ya rufeta.

"Kina mamaki ko? Ai ƙaddarar da ta ratsa ba zai sa in katse miki neman iliminki ba Hibbah, ki koma makaranta ki yi karatu ina fata a wannan karo za ki natsu wurin mayar da hankali akan abin da yake daidai. Akwai driver zai na kai ki ya ɗauko ki, wayoyinki kuma zan duba sadda ya dace sai in mayar miki"


"Na gode sossai Daddy"

Ta amsa fuskarta na nuna sakewa alamun ta ji daaɗin zancen komawa makarantar, bayan ta musu sai da safe ta fice Momma ta dube shi.

"kana gani ya kamata ta koma makaranta a yanzu?"

"Me zata zauna ta yi mana a cikin gidan Fatima? Babu abin da zai hanata karatu tunda tana da burin yin abin ta kuma ta fara nisa sai dai zan tabbatar mun saka idanu a kanta ƙwarai da gaske Dukda na san mawuyacin abu ne ta sake maimaita kuskurenta na baya! Fatima na yarda da kaddara ce kawai ta faɗa mata amma ban yi zina ba kema haka na tabbatar Allah ba zai jarrabemu da dattinta cikin zuri'a ba"


Numfashi ta sauke tana furta

"Allah ya tsare mana su gabaɗaya. Ameen"

Shiru suka yi na tsawon mintuna kan ta sake cewa 

"Anya babu abin da yake damunka Daddyn yara?"

Ya sauke gwauron numfashi zuciyarshi babu daaɗi yace 

"Abubuwa suna damuna Fatima, Dukda ɗaya ya fi ɗaya tsayamin a rai fiye da shekaru ashirin da tara zuwa talatin na kasa manta kuskuren da na aikata, na kasa cire abin a raina"

Fuskarta ya nuna damuwa ta san abin da ya faru da Hibbah ne ya tado mishi miƙin abin da ya faru da jimawa wanda ko ita a lokacin da ta aure shi labari ne ta ji kuma ba kasafai yake maganan ba sai in ta ciyo shi a rai ta ce 

"Allah yana sane da wannan lamarin kuma zai yi ikon shi a kai, ka ƙara haƙuri ka san wannan matsalar ne ya janyo maka ciwon zuciya da kake fama da shi ka daure ka danne kar kuma wani abin ya sake faruwa da kai"

Kai ya gyaɗa.


"Ya kuka yi da 'yan jam'iya?"

Murmushi ya ɗan yi marar zurfi 

"Siyasar nan karshe jingine ta zan yi in koma kasuwanci da dama shi na fi wayo, sun fara min wasa da hankali suna kokarin ja na a ƙasa daga partyn masu adawa zuwa namu, gani suke muddin aka zo zaɓe sai an sake tono lamarin Hibbah wanda dole zai rage kima da yawan adadin daraja ta da mutane za su gani har su zaɓe ni a karo na biyu amma ban damu ba. Komai da zai faru Allah ya riga ya kadarta"

Tunda ya ce haka ta san ya gama yardarwa zuciyarshi ne cewa hakan shine tsarin Allah kuma ba zai taɓa bari a fuskarshi a yi wa ƙaddarar yar shi dariya ba. Sun sake taɓa hira kadan kan ya fice masallaci ita kuma ta koma cikin gida.


Hankalin Hibbah ya sake kwanciya ganin iyayenta sun sassauto sossai don cikin kashi ɗari na haushinta da suke ji a yanzu bai wuci kashi talatin ya saura ba don dukkanin su ba gwanayen midiya ba, tunda kuma Daddy Z ya tabbatar an sauke ya kuma kafa tsatsaurar tsaro akan wanda zai ake ɗora videon hankalin duk wani masoyinta ya kwanta, ranar monday bata je school din ba sai da ta shiga asibiti ta yi sa'a babu layi ta samu ganin Dr Najeeb.


Sossai ya dinga janta da hira na musamman yana sakata responding har da murmushi sun dau lokaci a session ɗin kan ta fito kuma ya ji daaɗin ganin improvement a al'amarin ta sossai da sossai kenan ta cire wa kanta tarin damuwar da ya nemi binne ta daga nan school ta ce driver ya kaita.


Ko da ta isa makarantar wayanshi ta karɓa ta kira huda 

"Twinee"

Ihu ne kawai hudah bata saki ba na jin muryarta 

"Twinee ke ce? Kullum na roki Momma ta ba su Fareed waya su kai miki sai ta hau ni da faɗa Aina'u kam ma bata daukar wayana tsantsar yadda na addabe ta, shi kuwa Mumtaz kullum sai ya wani ce baya gida ya kike?"

Murmushi Hibbah ta yi tace

"Ina cikin school kina ta ina?"

"Don Allah? Daddy ya barki?? Alhamdulillah!!"

"Katin driver muke cinyewa faɗa min kina ina?"

"Ina department namu"

"Ok gani zuwa"

Ta katse ta miƙa mishi kan tayi godiya ta fita, kai tsaye hanyar SLT ta ɗauka Dukda ba department ɗinta bane amma saboda Hudah kusan bata shiga school din ta fita bata je department ɗin ba, abin da ya so firgita ta yadda ake ta kallonta har tana tuntunɓe ɗago kan da zata yi ta ga wasu kaman suna yi mata video ko hoto da sauri ta janyo hijabinta ta rufe har rabin fuskarta gabanta na dukan uku-uku.


Ko kan ta isa SLT department ji tayi bata numfashi da kyau, da sauri ta juya don komawa mota sai ta ji ana yi mata magana bata tsaya ba bare ta saurara don kalaman ya fi yanayi da jaje ko kuma tuni akan miƙinta, Meyasa mutane suke haka? Me yasa burin mutanen yanzu su yi mocking ɗinka akan kaddararka? Shiyasa kashe kai ga yaran turawa ya zama ruwan dare, damuwa da depression ya kashe mutanenmu na arewa bila adadin ba tare da an sani ko an farga ba musamman a native wurare irin kauyuka da basu yarda cewa akwai wata cutar ta damuwa ba.


Ko da ta koma mota wani irin kuka take yi tana ja wa Sagir Allah ya isa, tana kuka tana cursing ɗin shi da zuri'arshi gabaɗaya don ta san mutane, wannan tambari ba zai taɓa mantuwa a gare su ba har karshen rayuwarta, driver ya yi kokarin yayi mata magana sai dai duk bata wani sauraronshi ta rikice gabaɗaya, a take tsana da kyamar makarantar ya shige ta, Hudah ce ta kira Layin drivern jinta shiru ya ɗaga a ɗan ruɗe yana gayamata halin da suke ciki, da sauri ta bar department ɗin ta nufi wurin da ya ce mata suke zuciyarta na tsitsinkewa, bata zaci haka Hibbah ta fito ba da ta ce ko facemask ne ta saka don itama sai da ta nemi facemask ta saka Dukda daga an mata magana ta amsa ake gane ba Hibbah bace amma wasu kallon birds of the same feathers suke musu.


Ko da ta zo rungume Hibbah tayi tana rarrashi wasu cikin friends da ake hi/Hello duk sun mammatso jikin motar yayin da wasu suke daga nesa.

"Malam Bala ja motar nan mu tafi daga nan don Allah, duk ba don Allah suka taru ba sai don gulma"

Ta faɗa tsiririn hawaye na bin idanunta ya ja suka bar makarantar, sai da suka yi nisa yayi parking a gefen hanya yana ɗan waigowa don har lokacin kuka Hibbah take yi wanda ke fita daga ƙasan ranta.

"Hajiya Hudah ko asibitin za mu koma?"

"Eh, kaimu asibitin goshinta kaman garwashi aka ajiye don zafi"

Girgiza kai tayi za tayi magana Hudah tace 

"Shhhh ki yi shiru don Allah, ba za ki koma gida ki je ɗaki ki kwanta a wannan yanayin ba. Ki yi haƙuri twinee ki sassauta wannan zubar hawayen."

Bata ce komai ba sai majina da take ja, kanta har kaman zai faɗi haka suka isa asibitin Dr Najeeb suka nema yana ganinta hankalinshi ya tashi 

"Me kuma ya faru? Yanzu fa barinta asibitin nan"

Ya jefawa Hudah tambayar yana nuna mata kan gadon da za ta kwantar da Hibbahn, ba don kayan jikinta ba zai iya rantsuwa ba ita ba ce Hudah ce ba lafiyar don lafiya lau suka rabu tana kuma walwala ba laifi.


"Dr. Makaranta ne ta shiga akan zata koma lectures yau, ka san mutane wasu burin su su nuna sun santa ko suna da alaƙa da ita, wasu burin su ganta kawai bayan ibtila'in da ya afka mata yayin da wasu da basu santa ba ake kiransu ganinta tamkar sabuwar halitta su ne suka rudata har ta shiga wannan hali"

Ranshi bai mishi daaɗi ba don har a fuska bai ɓuya ba, wucewa yayi ya fara kokarin haɗa allurai anan Hudah kuma ta shiga ƙiran Daddy.


Hankalin daddy ma sai da ya tashi jin abin da ya faru nan ya ce gashi zuwa asibitin shi da Daddy Rabi'u.

Kusan mintuna arba'in ya ɗauka kan bacci mai nauyi ya ɗauketa under heavy medications. Dole ta shiryawa hakan dole a yanzu kaɗaici da laying low shi ya fi chanchanta da rayuwarta ko kuma ƙaura zuwa wani garin don samun kwanciyar hankali.

Yana fitowa su Daddy suka tare shi, sossai mutumin ya yi mishi girma a idanu don wani nauyinshi ya ji yana ji, ƙasa miƙa hannunshi ga Daddyn da ke miko mishi na shi yayi sai ɗan rankwafawa tare da gaida Daddyn cikin girmamawa, iso yayi musu har cikin office nashi.

"Likita menene matsalar ne da daga ta shiga ruɗu haka sai jikinta ya nuna? Wani Sabon ciwo ne kuma ya kamata?"


Dr Najeeb ya ce 

"Wato Alhj abin da ya fara faruwa da ita abu ne da za mu ce ya yiwa zuciyarta girma, duba da ta fito cikin gidan mutunci, tana da tarbiya daidai gwargwado, tana da tarin mu'amala kwatsam a ce koina ya ɗume da zancen da har yayi sanadiyar wargaza aurenta bayan gangami da shiri da aka gama, dukan da abin yayi mata a zuciya shi yayi sanadiyar da numfashinta baya ratsa huhunta yadda ya kamata, a gudun kamuwarta da wata cutar ta daban ya sa dole take kan medications ga mental Health ɗinta da is not stable. Wannan dalili ne ya sa daga hankalinta ya tashi numfashin ke gagararta da kuma saukar mata da ciwon kai mai tsanani. Idan har za ta kiyaye dokokin asibiti kuma za ta nesanta ga damuwa komai zai zama daidai amma idan hakan na faruwa akai akai akwai possibilityn kamuwarta da kowani irin cuta ma"


Numfashi mai nauyi Daddy ya sauƙe yana tuna matsalar shi daga haka ya fara, kenan zuciyar Hibbah irin tashi ce, ya san irin wahalhalu da ya shiga a baya saboda wautar shi, har yanzu yana tsanar kanshi ba kuma ya fata a ce mummunar ƙaddarar shi ko ya ɗauka a son zuciya ne ke shirin dawowa kan 'yar shi da tafi soyuwa a ranshi. Wasu kalamai ne ke dawo mishi cikin kunne da sauri ya dafe kunnuwan yana duƙawa, Daddy Rabiu ne ya dafa shi Dr. Najeeb ya miƙe ya kawo mishi ruwa Daddy Rabi'u ya karɓa ya bashi ya sha, sai da ya ɗauki lokaci kan ya ɗan natsu ya miƙe tsaye yana yi wa Dr. Najeeb godiya ba tare da ya mayar da hankali kanshi ba suka fice.


"Hudah ki je Malam bala ya mayar da ke gidanki mamanku na hanya"

Da sauri ta kalleshi sai dai bata iya ta yi magana ba amma Allah ya gani bata so komawa gida ba tare da Hibbah ta tashi ba, ko fa gaisawa basu yi ba. Kaman ta yi kuka haka ta fice.

Daga Daddy har Daddy Rabi'u babu mai magana suna zaune ne kowa da abin da yake saƙawa har Momma da Mumtaz suka shigo ko zama basu kai ga yi ba Ƙiran Hajiya kamila ya shigo wayarshi, har kaman ba zai ɗauka ba sai kuma ya ɗaga da sauri ya miƙe tsaye yana Salati...


***


Hudah na isa gida ta iske Hajiya zaune kan plastic chair a tsakar gidan tana shan iska, kallonta take har ta isa ta duƙa tana miƙa mata gaisuwa.

"Ina shi Mu'azzam din? Ya ce zai je ɗauko ki"

Ta jefo mata maganan ba tare da ta ko amsa gaisuwar ba.


"Toh kila mun yi saɓani dayake ba daga makarantar nake ba, mun je sai Hibbah bata da lafiya na kaita asibiti"

Wani kallo Hajiyar ta watsa mata.

"Shine kika kasa kiran mijin naki ki tambaya?"

Shiru ta yi, har ga Allah bata kuma san me zata ce ba don tana ganin ko me zata faɗa kaman ba yarda hajiyar zata yi ba don tun farko ma bata yarda da maganan ba, kwafa hajiyar tayi tana gyara zama.

"Dole ki min banza! Ba ni da ikon tambayar ki ko? Toh shikenan tashi ki je bari wanda ya ajiyekin zai zo shi dolenshi ya ba ni amsa ko ya ƙi Allah"

Hudah ta miƙe ta nufi kofarta, a kwanakin nan ta juri abubuwan da bata taɓa zato ba daga hajiyar, tun tana ɗauka normal ne har take ganin kaman ba haka ya kamata abubuwa suke tafiya mata ba a matsayin sabuwar amarya da tayi auren soyayya, Adu'a take Allah ya bata juriya don ita bata taɓa bambance tsakanin Mommahnta da Hajiyar ba a ranta shiyasa ko Hibbah bata yi niyyar kaiwa kokenta ba akan hajiyar Dukda kanta a ƙulle yake.

Tana shiga ɗakinta ta tsaya chakk ganin wardrobe ɗinta buɗe kayakinta wasu a kan gado wasu a ƙasa duk ninkakkun an wargaza

"Me wannan??" Maganar ya fito mata ba tare da shiri ba.


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol