Free chapter · Read without an account

3

by Hauwa A Usman · DA KAMAR WUYA...!

'''DA KAMAR WUYA...!'''

*HAUWA A USMAN*
~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''

*ArewaBooks:- Hauwaausmanjiddarh*

#500 Only
Hauwa Auwal Usman
Gt Bank
0153259310
***, katin MTN banda VTU saboda WhatsApp kawai nake yi da Number, so idan kikayi transfer kati kai tsaye cikin layin ko kikayi VTU kinyi asara domin ba Jiddarh kika turawa ba, ki siyi katin MTN ki turo min numbobinshi ko hotonshi

3️⃣

A hankali Nadeer ya d'agawa Papa kai ba dan ya so ba, dan harga Allah yana son yaron, baya son rabuwa dashi, cikin ranshi ya soma addu'ar Allah yasa kar'a samu iyayenshi, Allah ya bar mishi shi su zauna tare ya samu d'an uwan daya rasa....

"Ina zamu nufa Alhaji...?

"Maitama! Papa ya fad'a a tak'aice batare daya d'ago ya kalli driver ba, gaba d'aya hankalin Papa yana kan yaron yana kallan yaron da Nadeer ya rad'awa suna Nadeem, 
bacci yaron yake yi amma da gani baccin dole ne sai zabura yake yi yana sauke ajiyar zuciya, da remote control Driver ya bud'e get d'in katafaren gidan ya danna kan motar ciki,
yadda kasan anan su Papa ke zaune mutane ma'aikata birjik kowa na sabgar gabanshi yadda kasan gidan sarauta, gidan a gyare tsaf komai tsaf, kamar a hotels d'in turai, 
Papa d'auke da Nadeem while Nadeer na rik'e da hannun Papa d'aya, gaisuwa mutanen gidan suka fara mik'owa, yana tafiya yana amsawa....

"Ranka ya dad'e kawo yaron...

"A'a barshi zan iya....

Ya fad'a still yana cigaba da tafiya, har ya basu 'yar tazara ya tsaya cak tare da juyowa yana kallan Isma'il...

"Isma'il mena ce muku?

Shiru Isma'il yayi kanshi k'asa yana duk'e bisa gwiyoyinshi...

"Bana ce kar wanda ya sake durk'usa min ba?

"Kamar bance muku Allah kad'ai ake yiwa gurfa ne ba?

"Idan ba mantawa nayi ba na fad'a muku ku daina durk'usa min ya fi sau dari?

"Ubangijin sammai da kassai kad'ai ya halatta a rink'a yiwa irin wannan durk'ushen ba ni bawanshi ba, bana so, I said it, and I mean it, 
duk wanda yake so ranshi yayi mugun b'aci, ya cigaba kar ya fasa, yayi maganar cike da kashedi da gardad'i yana bin gaba d'ayansu da kallo, kansu k'asa suka amsa mishi, bai sake cewa komai ba ya wuce danshi ba mutum bane me yawan magana da nanata magana d'aya ba, 
kwata-kwata bashi da mita idan yayi magana ya barta, ta wuce kenan har abada a wajenshi....

Harya shige ciki Isma'il na durk'ushe inda ya barshi yana tunanin tayaya zai iya gaida Alhaji a tsaye?

Ta ina zai soma iya yiwa Alhaji magana a tsaye k'erere?

Ya rasa Alhaji wanne irin mutum ne, da baya san duk irin wad'annan abubuwa, shi mutum ne na daban wanda sai an tara dubu kafin a samu d'aya irinshi, 
in wani ne yadda kake da wannan tarin arzikin da na k'asa dashi sun shiga uku da girman kai da k'i fad'i, amma dayake shi d'an na gada ne ba haye yayiwa arziki ba, 
shiyasa ba ruwanshi da zumudin dukiya dayake a cikinta aka taso an saba da ita tuni...

A katafaren gadon Nadeer kirar Italian, mai d'auke da American Foam, ya kwantar da yaron, 
sassanyar ajiyar zuciya yaron ya sauke had'i da gyara kwanciyarshi ya takure waje d'aya hakan yasa Papa fahimtar sanyin da yaron yake ji,
American doubled bedsheets dake shinfid'e a saman gadon yaja blanket ya rufe yaron ruf dashi.....

"Ka shiga ka d'auro alwala ka same ni a House Masjid muyi sallah, kabi a hankali banda sound mai k'arfi karka tashe shi kaga allurar bacci akayi mishi....

Papa yayi magana yana kallan Nadeer.

"Ok Papa I will! Nadeer yace cike da girmamawa, Papa ya fita, a nutse Nadeer ya shiga katon bathroom d'inshi dayayi girman wani d'an k'aramin gidan ya d'auro alwala,
saida ya cire kayan jikinshi ya sanya sky blue Arabian Jallabiya, ya zura farar k'afarshi a Puma Luxury slippers, takalmin very soft, a harabar gidan suka had'u da Papa shima ya fito sanye da Jallabiya me kyau da tsada sai shek'e take yi, suka jera suka shiga masalcin abin sha'awa,
Nadeer ne yajasu sallar bayan sun idar suka dawo keb'antaccen falon Papa, Mima na sauke tana jiransu, hannunta rik'e da jarbi while jikinta sanye da hijabi...

A hankali ta mik'e tana fad'in " kuzo mu ci abinci ko?

Dinning d'in shak'are da kala-kalar abinci, Nadeer ya zauna kusa da Papa, masu aiki biyar ne tsaye kansu suna jiran umarni, da hannu Nadeer yayi musu nuni dasu soma aikinsu, 
a nutse suka soma zuba abincin bayan kowa ya fad'i abinda zaici, bayan sun gama zubawa Papa yayi musu nuni dasu tafi...

Duk yadda Nadeer yaso yayi magana da Papa akan yaron Papa yaki bashi dama, daya dame shi ma Papan cewa yayi " please leave me alone ina san na huta gobe mayi magana,
dole Nadeer ya hak'ura badan yaso ba, dan yasan idan ya matsa rayuka ne zasu b'aci dan Papa ba wasa...

Hasken d'akin ta rage musu kafin ta hawo gadon ta zauna kusa da Papa, daya tattara gaba d'aya hankalinshi kan system d'in dake gabanshi, 
yayinda Black tea ke aje saman bedside, a nutse ta kira sunanshi " Alhaji..

Bai d'ago ba ya amsa while yana cigaba da aikin da yake yi, bata wani damu ba danta riga da saba, hakan d'abi'arshi ce dan ya wuce ace halinshi ne....

Cikin sanyinta tace " magana nake son muyi dakai idan ba damuwa, kuma idan kana da lokaci a yanzu...

Sai a lokacin ya d'ago kanshi ya kalle ta yana fad'in " uhummm ina jinki.

"Ban takura maka ba dai ko?

"Ah Gimbiya guda tace tana son magana ace ba haka ba, wane mutum ai kin wuce nan ranki ya dad'e, yayi maganar cike da zolaya yana murmushi gami da zare farin glass d'in dake manne da idonshi....

Kyakkyawan murmushi tayi had'i da kwantar da kanta saman kafad'arshi yayinda hannunta d'aya ke cikin sumar kanshi...

"Ina godiya da wannan karamcin, da kuma babban gurbin da aka bani...

System d'in dake saman cinyarshi ya rufe ya aje saman bedside kana ya d'ago kanta dake kafad'arshi ya kwantar a saman cinyarshi yana shafa kanta yace " El-Yaqoub naki ne Halimatu sai yadda kike so za'ayi...

Murmushi ta sake yi a karo na biyu tana jin kalamanshi na ratsa k'irjinta suna lumewa cikin zuciyarta, duk da ta saba da jinsu, danshi mutum ne bai kod'a ta akoda yaushe kuma a gaban kowa....

"Idan haka ne abarwa Nadeer yaron nan Alhaji..

D'an jummm yayi kana ya fitar da nannuyan namfashi yace " na d'auka zaki fi kowa fahimtar abinda nake nufi da abinda nake so nayi, saboda kinfi kowa sanin waye ni,
kinfi kowa sanin halaye da d'abi'una, ke kanki kin san idan muka rik'e yaron nan a haka komai yana iya faruwa, babu abinda bazai iya biyo baya a gaba ba,
na sani ni mutum ne mai tarin mak'iyan da akoyaushe suke jiran suga aibuna ko gazawata akan wani abun amma har yanzu Ubangiji bai basu wannan akai na ba,
dole idan Allah yayi maka wata ni'ima saika samu k'alubale ta fannoni daban-daban, ni ban san wani fitaccen mak'iyi na ba,
saboda har yanzu babu wanda ya fito ga da ga ya nuna k'iyayyarshi a gare ni, so zan iya cewa bani dasu tunda akoyaushe ina kansu, Ubangiji na yana kare ni daga tuggunsu da makircinsu,
na yarda ina dasu me dan ta haka me kawai zan zauna lafiya...

"Sanin kanki ne idan muka rik'e yaron nan a haka bamuyiwa iyayenshi dashi kanshi yaron adalci ba, ban sanki da son kanki ba Halimatu, 
ina da yak'ini akanki please karki ruguza yak'ini na akanki, karki zama me san kanki a wannan karon, idan mukayi haka mu kanmu bamuyiwa kanmu adalci ba, 
kuma hakan da zamuyi yana iya farautar mu a gaba, ko Ubangiji yayi mana Jarabawa akan hakan, ke ya kamata ki tayani fahimtar da Nadeer wannan...

Jikinta ya gama mutuwa murus, cikin sanyin jiki ta d'ago kanta ta zuba mishi fararen idanuwanta masu d'aukar hankali ta dad'e tana kallanshi deep down tana mamakin tarin baiwar da Ubangiji yayi mishi wanda saika zauna dashi zaka fahimci hakan, hikimar zance tana cikin baiwar da Ubangiji yayi mishi,
kiss tayiwa goshinshi tana murmushi tace " Alhamdulillah a kullum ina yiwa Allah godiya daya bani kai matsayin miji, 
ina fatan Allah yasa har a Aljanna mu rayu tare, dan nasan muddin ina tare dakai in sha Allah Aljanna bazata yi min wahalar shiga ba,
duk yadda nakai da d'aurewar kai sannu a hankali zaka warware min komai, nagode sosai mijina in sha Allah zanyi yadda kake so, har k'arshe rayuwarmu zan kasance mayyi maka biyayya...

Kanta ya shafa yana murmushi had'i da cewa " Allah yayi miki albarka 'yar Aljanna, ta amsa da Amin ya Allah, daga nan salon ya canja zuwa na raya sunnah...

Nadeer kam gam ya rungume yaron a jikinshi had'e daja musu blanket daddad'an bacci mai cike sanyin ruhi yayi awon gaba dashi, koda ya tashi sallar asuba da sand'a ya sauka daga kan gadon ya shiga bathroom ya d'auro alwala ya fita a hankali batare dayayi kwakkwaran motsin da zai fitar da sauti ba.....

K'arfe goma na safe yaron ya soma motsi yana juye-juye akan gadon, cikin sanyin muryarshi da bata fita sosai ya furta " Abba...!

Dai-dai Nadeer ya d'ora hannunshi akan handle d'in k'ofar zai fita breakfast, saurin juyowa yayi tare da zubawa yaron ido yana san gaskata abinda kunnuwanshi suka ji....

"Amma....

"Yayah...

Yaron ya sake fad'a lokaci d'aya, jikin Nadeer na kerrrrma ya k'arasa kan gadon, ko takalmin k'afarshi bai cire ba,
ya d'ago yaron ya tallafe shi yana girgiza shi tare da fad'in " Nadeem! ka tashi?

A hankali yaron ya bud'e idanuwanshi ya sauke su akan Nadeer had'i da sakar mishi murmushi, shima Nadeer murmushin yayi mishi yana sake shigar da yaron jikinshi...

Bakin Papa da Mima d'auke da sallama suka shigo d'akin, ganinsu a haka ba k'aramin tausayi ya bawa Papa ba, take yaji matsanancin tausayin d'an nashi ya kama shi, duk da dama yana mugun tausayin Nadeer,
Mima kam burgeta sukayi, abun ya bata sha'awa, cikin ranta tace inama dukkaninsu 'ya'yanta ne na cikinta,
fuskokinsu d'auke da yalwataccen murmushi suka k'arasa bakin gadon tare da zama kusa dasu...

"Ya tashi kenan?

Papa yayi maganar yana kallansu cike da tausayawa dukkansu...

"Eh ya tashi Papa, yanzu ma ya tashi ba dad'ewa, zame jikinshi yaron yayi daga na Nadeer ya koma jikin Mima yana fad'in " Ammah!, 
wani irin abu Mima taji ya ratsa zuciyarta da k'arfi, lokaci d'aya taji tsananin so da k'aunar yaron sun shigeta,
sake matse shi tayi a jikinta had'i da k'ok'arin mayar da hawayen dake k'ok'arin zubawa saman kuncinta, Papa ya kula da yanayinta sarai amma ya basar yayi kamar ma bai san tana yi ba...

"Ka kaishi yayi wanka yayi brush, Papa ya fad'a yana kallan Nadeer...

Mik'ewa Nadeer yayi gami da rok'o hannun yaron yana fad'in "zo muje kayi wanka...

Hannunshi dake cikin na Nadeer ya zame tare da mak'ale kafad'a yace " a'a nidai Amma zatayi min...

Yayi maganar yana sake shigewa jikin Mima, ai ji tayi kamar ta tsaga k'irjinta ta cusa yaron...

Kallan Mima Nadeer yayi da sigar rok'o, ta mik'e d'auke dashi tana murmushi tace " ai ba kai kad'ai ne ka samu d'an uwa ba, har damu ma mun samu d'a....

"Thank you best Mom, I love you.., ya fad'a yana yi mata kiss a kumatu, tana dariya ta ture tana fad'in " ka nemar mishi kayan sawa...

"Tab! ai tuni na tanadar mishi komai, jiya banyi bacci da daddare ba, saida na gama yi mishi order duk abinda zai buk'ata, yau da safe aka kawo harna jera mishi komai a wardrobe...

Batare da Mima tayi magana ba ta shige bathroom d'auke da yaron, tanayi mishi wankan yana zuba mata surutu tana biyeshi, da alama yaron yana da shegen surutu wai a haka ma dan bashi da lafiya ne,
tass ta wanke shi, ta gashe mishi jiki da ruwan zafi tayi mishi brush ta nad'o shi a lallausan towel, sosai mamaki ya kamata ganin kayan da Nadeer ya saiwa Nadeem,
dan batayi tunanin yawonsu yakai haka ba, takalma ma kad'ai abin kallo ne, kayan bacci da kayan sawa kam ba'a magana sai dai ayi shiru,
yana mak'ale da Mima harta gama shiryashi,
ta rik'e hannunshi suka jera zuwa dinning yin breakfast, a wajen cin abincin ma mak'alewa yayi sai Mima ta bashi, da hannunta ta rink'a bashi har ya k'oshi while yana zuba mata d'an banzan surutu, Mima da Nadeer sai dariya suke yi,
yayinda Papa ya zuba musu ido yana kallansu cike da tausayawa, yasan halin matarshi sarai, yasan wacece Halimatu, yana sane da duk wani motsinta, yasan daurewa kawai take yi akan yaron bata san ta sake kawo mishi buk'atar tana son ya bar mata yaron saboda maganar da sukayi, 
amma tuni ya garo tarin soyayyar da take yiwa yaron ta cikin idanuwanta...

Ya sani ita mutum ce mai son yara musamman yara irin Nadeem masu shiga rai, ga surutu da shigewa jikin mutum, 
ba Mima dake so mutum irin Nadeem me shiga jiki ba koma waye zai so Nadeem, abinda basu sani ba shima yana jin abinda suke ji akan yaro, koma yace ya fi su, shi mutum ne babba da shekarunshi suka soma ja,
yana da harkoki sosai babu abinda ya kamace shi irin idan ya dawo gida ya samu k'ananan yara suyi wasa da dariya gami da hira, su d'ebe mishi kewa, 
sai yanzu yasan dalilin dayasa manyan mutane ke san yara k'anana, jikokinsu ko kuma 'ya'yansu, so da dama zakaga babban mutum ya k'ara aure yawancinsu badan macen bane sai dan ta haifa musu yara k'anana ababan d'ebe kewa,
amma yasan duk yadda zai yiwa Mima da Nadeer bayanin halin da yake ciki bazasu fahimta ba, kansu kawai suka sani, amma shima yana matuk'ar buk'atar yaron a kusa dashi...

A hankali ya mik'e yana duba agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunshi yace " Nadeer d'auko yaron nan muje Police Station ko?

"Alhaji dashi kuma za'a tafi?

Kallan eh mana yayi mata batare dayayi magana ba...

"Gaskiya bai kamata a tafi dashi ba, bai kamata ayi komai a gaban idanuwanshi ba, tunda bamu san me Allah zayyi a gaba ba, watakilla muna da rabon rik'e shi, 
kaga idan yaji komai bazai tab'a sakewa damu ya zauna damu matsayin asalin iyayenshi ba,
ni kuma wannan ne bana so da tuni nayi adopting yara, nafi son wanda zai d'auke ni matsayin uwa mahaifiya...

Baya san ya sake sakata cikin k'unci da damuwa yasashi amince dole badan yaso ba, ya rik'e hannun Nadeer suka fita, itama kuma ta d'auki d'anta suka bar dinning room d'in....

JIDDARH....✍🏻

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol