Free chapter · Read without an account
Page 3
by ZAINAB LAMINU · ROMON BAKA
Romom baka
PAGE___ 3
Dawowar yara ce ta dawo dani daga duniyar tunanin dana afka tun zamana. Bayan wasu kwanaki a tsahon kwanakin nan da suka biyo baya babu wani sauyi a zamantakewa ta da Zayyan, sai ma ƙara kwaɓewa da al-amura suka sakeyi, dan yanzu har takai ta kawo in har Zayyan ya bar gidan nan tun asuba baya dawowa sai can tsakiyar dare, dan ni wani sa'in sai nayi barci na farka nake jin dawowarsa, wannan alamarin ya sake dugunzuma raina matuƙa.
A yau ne na kasa jurewa nayi zaman jiransa ya dawo gidan, duk da yadda gabana yake faɗuwa sanda naji tsaiwar motarsa a harabar gidan, amma haka nayi ta maza na tsaya ina jiran shigowarsa, koda ya shigo ya ganni a tsaye amma sai ya nuna kamar bai san ma da wata halitta a falon ba, ya nufi hanyar ɗakin shi, cikin dakiyar da ban san ina da ita ba na ambaci sunan shi sanda yazo zai giftani, "Zayyan".
Cak kuwa ya tsaya jin wani baƙon al-amarin da bai taɓa cin karo da shi ba tun zaman shi da ita, juyowa yayi yace, "Aminatu yau ni kika kira da sunana kai tsaye babu ko sakayawa?".
"Kayi ha...". "Dalla! can dakata min". Ya katseni tun kan na ƙarasa abinda zan faɗi ɗin, sannan ya ɗora da cewa, "Ni zaki rai nawa wayo matse bakinki a kayi kenan kokoya?". Yayi maganar kamar zai kai mata duka, saurin ja baya tayi tana girgiza mai kai". "Mtsssss". Ya ja wani dogon tsaki yana wuceta zuwa ɗakin shi, ya barta a nan kamar wanda a ka dasa, ta jima a nan yadda ya barta bata ko motsa ba, jin ƙafafuwanta suna neman zubar da ita ƙasa ne ya sa badan taso ba ko dan ta gaji da tsaiwar ba ne yasa da lalube ta kama hannun kujera ta kai zaune ƙasan aka cafet ɗin dake falon, tana mai da nunfashi a gwagwgwame.
Dan sai faman fizgo shi take kamar mai asma, koda yake marabarta da me asma kaɗan ne, dan na tabbata yau da tana da amsa babu abinda zai hana ba tayi ajalinta ba, saboda yadda nake jin nunfashina ya dunƙule a maƙoshina, kamar wani gingimemen dutse, ya hana iskar dake isar da saƙo zuwa ga gangarji jiki damar yin aikinta yadda ya kamata.
SHEKARAR ALIF 1996
A ƘARAMAR HUKUMAR DUKKU DAKE JAHAR GOMBE.
"Yanzu Muhammadu kana ganin wannan abun ba matsala?". "In sha Allahu Baba ba wata matsala amincewarka kawai na keso, kuma Baba wannan abun kamar jahadine". "To ai shi kenan tunda kace kaji ka gani Allah ya taimaka". "Amin Baba na gode".Ya miƙe cike da farinciki mara misaltuwa, bai zame ko ina ba sai gidan Liman, in da ya barota.
Da sallama ya shiga gidan, da ita idon shi ya fara yin tozali tana zaune a ƙarƙashin bishiyar darbejiyar dake gidan ta haɗa kai da gwiwa, har ya ƙaraso in da take bata motsa ba, saboda zurfin da tayi a tunani, sai da ya ɗan kaɗa hannun shi a saitin fuskarta kafin ta kawo nannauyan nunfashi.
Kallon shi tayi da manyan idanuwanta waɗan da suke farare tasss, lallausan murmushi ta sakar masa wanda ya ƙara ƙawata kyakykyawar fuskarta, martanin murmushin ya mai da mata, kafin yace komai, sai ga Liman ya fito, ɗan duƙawa yayi yana gaida shi, amsa mai Liman ɗin yayi yana tambayarsa yadda suka yi da mahaifin nasa, muryarsa cike da farinciki yace,"Ya amince". "Ma sha Allah hakan yayi kyau, kaga ana fitowa daga sallar zuhur kawai sai a ɗaura auren kada a tsaya jinkiri har wata matsalar ta ɓullo ko ya kagani?". Liman ɗin yayi magana yana kallon Muhammadun, da sauri yace, "Ehh hakan ma yayi". Dan baya fatan mahaifiyarsa tasan da wannan batun kafin a ɗaura auren, dan yasan ba zata taɓa barin ya auri Rumana ba, kasancewarta sabuwar musulunta, shiyasa gara kawai a ɗaura yanzu kawai yadda koda taji babu yadda zatayi, dan yasan mahaifin shi bazai bari ya saki Rumana ba, sai dai tayi masifarta ta bari.
"Karka damu abinda ya dace ne nayi". Fita sukayi tare da Liman ɗin zuwa masallaci, bayan idar da salla ne a kayi sanarwar ɗaurin aure, cike damamaki mutane suke tambayar ɗaurin aure kuma tun da dai sun san babu wani ɗaurin aure da za'ayi yau a garin, amma ace wai gani ya kori ji, dan haka kowa ya zauna dan kashe kwarkwatar idon shi, da a baka labari gara kai ka bayar ai, haka kowa ya zauna ana jiran aji wanda za'a ɗaurawa auren, Liman ne ya miƙe wanda ya kasance shine waliyin amarya kasan cewar babu wani nata a nan ɗin, shiyasa ya zama waliyinta, sanarwar ɗaurin aure yayi kamar haka;
"A yau ne aka ɗaura auren Muhammadu Ɗan Yaro da Rumanatu, a kan sadaki naira dubu goma sha biyar, lakadan ba a jalan ba".
Wannan ɗaurin aure ya daki zukatan kowanne mutum dake masallacin nan saboda jin wanda ba'a taɓa tsammani ba, kafin kace me magana ta gama waɗe garin nan dama sauran garuruwan dake kusa da su, dan da nan kuwa aka shiga ƙananan maganganu a kan cewa Muhammadu ya auri arniya, abinka da magana a bakin mutane masu jiran ƙiris haka aka rinƙa ƙarawa barno da waki, dan harda masu cewa dama can karuwarsa ce a can inda yake neman kuɗin, haka maganganu marasa daɗi suka dinga fitowa babu ko daɗin ji.
Dan babu wanda yasan ta musulunta idan kacire mutane ukun nan wato Liman da shi Muhammad ɗin sai kuma mahaifin shi da ya sanarwa, amma idan banda su babu wanda ya san ta musulunta, jin waɗannan maganganun da suke tashi ne yasa Liman ɗin tara mutane ya sanar da su musuluntarta, wasu sun fahimta wasu kuwa sun dai ji Liman ɗin ne kawai ba dan sun yarda da abinda ya faɗa ɗin ba, sanda labari ya isa kunnen Anaa wato mahaifiyar Muhammad, jin maganar tayi kamar a mafarki ko kuma tatsuniya, amma sai taga ina ba haka abin yake ba da dai taga maganar da gaske ce ba kawai mafarki ko tatsuniyar da tayi tsammani ba, ai sai tashiga neman Muhamnadun ruwa a jarlo dan jin ta bakin shi.
Da gaske ne koya abin yake, dan tasan dai bata isa tunkarar mijin nata da wannan batun ba, in dai bashi yayi ra'ayi ya sanar mata da yadda a kayi ba.
BY
ABIDAH