Free chapter · Read without an account
Shafi Na Bakwai
by SaNaz deeyah · A CIKIN IDO...
*A CIKIN IDO...*
_Ake tsawurya_
_Wattpad @SaNaz_deeyah_
*_Heart touching love story🥰_*
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_
_*Sadaukarwa ga BEEBAH LUV(Writer), Allah ya jaddada rahama a gareta*_
_Free Page_
_Shafi Na Bakwai_
_________________Kallon Rahina tayi tana murmushi ta ce "Na É—an samu farin ciki da naji ya ce ana warkewa."
"Nima wallahi naji daÉ—i, yanzu sai ki shawarce shi É—in kiji"
"Bara zuwa anjima na kirashi dan na san ba lallai ya tashi daga bacci ba.
***
Kallonta yake itama tana kallonshi. "Maheer yanzu saboda Allah ace ko kaÉ—an baka runtsa ba"
"Nutsuwa take sakawa ayi bacci, ni kuma Mommy bani da ita a yanzu"
"Maheer...." Ta furta sannan ta zauna gefen gadon.
"ÆŠan uwanka ayyukansa da matarsa sun fini muhimmanci a gurinsa, baya zuwa gurina sosai, kai kuma da nake saka rai da kai shine kake son sakani a damuwa?"
"Mommy ina tausayin Amal, ni sai nake ganin kamar Amal tana sona, Mommy ina jin tausayinta har cikin raina"
"Maheer idan Amal tana sonka ba zata ce a haÉ—aka da wata ba, in kace dai ta damu da kai da halin da kake ciki na yarda, amma batun soyayya ta aure bata yi maka ita"
Ajiyar zuciya kawai ya sauke, tare da janyo wayarshi"
"Wa zaka kira da sassafen nan?"
"Amal zan kira naji lafiyarta"
"Allah ya kyauta, idan ka gama wayar dai ka daure ka fito ka karya ko a kawo maka nan?"
"Eh da yafi, dan bana jin daÉ—in jikina"
"To shikenan, ka daure kasha magani dai in ka gama break fast É—in" Kai kawai ya gyaÉ—a. Tana fita ya kira Amal.
"Hello!"
"Ya kake?"
"Ina lafiya fatan kema haka?" "Hmmm! Idan babu damuwa ina son magana da kai"
"A ina zamu haÉ—u?"
"Gida mana, kazo gida sai muyi magana"
"Amma ya naji muryarki wani iri?"
"Daga bacci na tashi" Bata jira me zai ce ba ta katse.
Da sauri ya tashi, ya fitar da kaya sannan ya shiga toilet.
_KANO STATE_
Jin ana bugunsa ya É—an buÉ—e idanunsa a hankali. Dariya tayi tare da hayewa kansa, shi kuma ya rungumeta jikinshi, tare da shafa gashin kanta.
Buɗe ƙofar da akayi aka shigo, ya ɗago ido a hankali ya kalleta.
A fusace ta janye yarinyar daga jikinsa tare da faɗin "Kada ka ƙara raɓarta." Murmushi kawai yayi sannan ya miƙe zaune. Yana kallo yarinyar na fuzgewa amma haka a fitar da ita.
Taɓe baki ya yi sannan ya sake kwanciya abinsa.
_Ilham ina kika shiga ina son na ganki, ina son naji É—uminki, ina so na san halin da kike ciki a yanzu._ Pillow yaja ya rungume tare da lumshe idanunsa.
_Few Minutes Later_
Yana tsaye jikin mirror yana feshe jikinsa da turare.
Yana gamawa ya É—auki brief case ya fita.
A parlour ya tarar da Mommy, ya zauna kusa da ita da sauri ta tashi tana mai jan yarinyar zuwa jikinta.
"Mommy why?"
"Ja'afar ka fita daga rayuwarmu dan Allah"
"Idan na tafi na barku dawa zanyi rayuwa Mommy?"
"Da ƴan uwanka masu shan jini" Sai kuma ta fashe da kuka tare da cewa "Tunda har ka iya kai mahaifinka, matarka da kuma ƙannenka na san yanzu saura ni da Afnan"
Jikinsa gaba ɗaya ya yi sanyi, ya ɗauki hanky ya goge fuska sannan ya ce "Mommy ki daina danganta ni da secret society, wallahi masu yi ma ba zan taɓa son in raɓesu ba, an aikata abu an liƙa min saboda kawai ina da haƙuri?"
"Ka rufa min baki, ka sani darajar haihuwa ce ta saka na barka a gidan nan, amma nima gab muke da tashi ni da Afnan, kuma Allah ya isa idan har ka zaluncemu"
Miƙewa ya yi tsaye tare da faɗin "Zan wuce office"
Tsaki taja. Shi kuma a sanyaye ya fita, Afnan na ta miƙo hannu tana son ya ɗauketa.
_KADUNA STATE_
Ajiyar zuciya Maheer ya sauke tare da faÉ—in "Yanzu yaushe zanje Niger É—in?"
"Zan baka number shi duk abinda ta kama zai faÉ—a maka"
"To shikenan babu damuwa."
"Yauwa kuma dan Allah ka ɗaukar min alƙawarin ko nawa ne zaka kashe domin lafiyarka"
"Karki damu Beautyn-Beauty, na miki alƙawari tun daga nan Kaduna har zuwa ko birnin sin ne zanje domin lafiya ta"
"Ina maka fatan samun ingantacciyar lafiya. Yauwa ɗazu kafin na fito Noor ta kirani ta sanar dani cewa an saka bikinku tun a daren jiya, Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba" Tana gama faɗa ta buɗe murfin mota zata fita ya riƙo gyalenta.
Juyowa tayi ta kalli gyalen sannan ta kalleshi, sai kuma ya saki "Idan har baki murna da hakan ba zan yi abinda ba zaɓinki ba" Ya furta a sanyaye.
Kallonshi take yana kallonta, kusan seconds 20 suka É—auka a haka kafin ta lumshe ido, wasu hawaye masu zafi suka fito daga cikinsu.
"Ba farin cikina kaɗai ya kamata kaso ba, har dana Mommy, ka manta nina faɗa mata Noor, ai na san Noor zata ƙaunaceta kuma zata kula da kai"
Leda ya É—auko a baya tare da É—ora mata akan cinya "Wayarki ce wannan"
"Bana buƙatar waya a yanzu"
"Kiyi haƙuri, wannan kyauta ce daga Mommy"
"Kayi haƙuri Maheer am..."
"Dan Allah karki ƙi amsa" Yayi saurin katseta.
"Nagode sosai"
"Zama bai sameki ba domin kuwa dake za a haÉ—o lefe kuma komai dake za ayi domin kece best friend na groom"
Murmushi tayi ta ƙara ƙura masa manyan idanunsa masu kama dana mage _Ka yafeni Maheer na san da sonka za a binneni, daga yau ba zaka sake ganina ba sai nan da shekara ɗaya, idan da rabo, ina fatan dawowa na sameka da rai, idan kuwa har ka rasu kafin na dawo sai na fi kowa baƙin ciki, Maheer ba zan taɓa daina sakaka cikin addu'ata fatan lafiya a gareka, ka gafarceni zan tafi ne domin Mama._
Jin ya dafa kafaÉ—arta ya saka ta É—an zabura.
"Tunanin me kike?"
ÆŠan lumshe ido tayi a hankali ta furta "Dan Allah ka yi amfani da ko wane irin magani da za a baka komin rashin daÉ—insa"
"Na miki alƙawari"
Kallon hannunsa tayi sannan ta ce "Ka bani wannan zoben" Tana faÉ—a ta ciro ta babban yatsanta lokacin shima ya ciro tashi.
Miƙa masa tayi ya saka a ƙaramar yatsarsa, sannan ya kama hannunta ya saka mata a babban yatsa, sai kuma yaƙi sakin hannun nata.
Kallonshi tayi har za tayi magana ya yi saurin cewa "Kamar akwai abinda kike ɓoyewa ko?"
Murmushin dole ta ƙaƙalo sannan ta ce "Ba komai, so nake kawai naga kun samu lafiya da kai da Mama"
"Zamu samu lafiya da yarda Allah"
"Allah yasa."
Hannun take ƙoƙarin zamewa, yaƙi saki, sai ma waya daya janyo ya ɗora hannunta akan giyar mota sannan ya saka yatsunsa cikin nata ya fara ma hannayensu video. Sai da yayi da yawa yayi saving sannan ya saki.
"Zan tafi gida" Ta furta a sanyaye. "Kin gaji da gani na ko?"
"Ba haka bane"
"To ya yane?"
Shiru kawai tayi. "Shikenan jeki tunda kin gaji da ganina"
"Nifa ba haka nake nufi ba"
Ɗan murmushi yayi sannan ya maimaita abinda ta ce da salon shagwaɓarta da tayi.
"Beautyna gaskiya Kamal ya more zai sha shagwaɓa" Ɗan ɓata rai tayi.
"Wai mene ya faru ne?"
"Babu"
"Shagwabar ce dai ta motsa ko?
Har ta bar motar bata ƙara cewa komai ba, har taje ƙofar gida zata shiga sai kuma ta juyo ta dawo ta buɗe motar ta kalleshi, shima ita yake kallo. "Bana so na tafi bamu yi sallama ba, kuma ban son mu rabu cikin fushi" Murmushi ya yi tare da cewa "Ai ni bana fushi dake, karki damu ki shiga ciki, ki duba Mama. Rufe motar tayi sannan ta tafi. Sai da har yaga shigarta gida sannan ya juya kan motarsa zuwa gida.
Tun daga parlour yake kwaÉ—awa Mommy kira, a firgice ta fito dan tayi tunanin wani abu ne ya faru.
"Lafiya Maheer?" Ta faÉ—a tana kallonshi cike da firgici.
"Mommy ni gaskiya na gaji da ɓoye yadda nake ji, kuma ta riga ta san ina da blood cancer dan haka ni Mommy babu wata Noor da zan aura Amal nake so na gaji da ɓoye sirrin raina dan haka zan bayyana mata."
"Amal...!
"Ƙwarai Mommy ko ba za ta aure ni ba kuma ba za ta so ni ba at least ta gane irin son da nake mata, Mommy Amal ba ita tayi kanta ba in kowa ke halittar kansa Amal ba za ta yi kanta a marar uba ba, Mommy wannan shi ne aibun Amal, abin da ba ita ta aikata ba dan haka ni indai ba Amal ba babu wadda zan aura ina son Amal kum...." Marin data sauke masa a fuska ne ya dakatar da shi daga maganar da yake.
"To ba zaka auri Amal ɗin ba, ita da bakinta ta ce a baka Noor, tsabar rashin mutunci, maimakon ta ce ita za ta aure ka, koma ba dan haka ba, wallahi ba zan bari ka auri ƴar da ba ta sunnah ba, a yanzun ma bana son tarayyarku, dan dai kafi ƙarfina ne"
Juyawa tayi ta bar parlour shi kuma da ido kawai ya bita yana mai jin ƙunar zuciya.
*Bayan kwana biyu*
Yana kwance a kan gadonsa yana waya, Mommy ta turo ƙofa ta shigo.
"Eh na gane duk bayanan naka Baffa, kuma insha Allah yanzu dana fita zan saka a tura kuÉ—in, ban sani ba ni ne zanzo ko kuma aiko min za ayi?"
Ɗan kallon Mommy yayi wadda ta zauna a side drawer sannan ya cigaba da wayar "Eh to jikina yana yin zafi lokuta da dama, sai kuma haɓo da nake yawan yi, amma dai har yanzu ina da suma"
"To shikenan Allah ya tabbatar da alkhairi ya kuma kawoka lafiya, nagode sosai. Sai ka ji ni" Katse wayar yayi ba tare daya kalli Mommy ba ya gaidata.
"Mun yi waya da Noor tace min tana ta kiranka bata samu"
"Layin da aka sanni dashi na suke shi a wayata"
"Amma wanda ka saka yanzu ai Amal tana dashi ko?"
"Ita ce ma ta bani"
"Har kana kallon idona kana faÉ—in ita ce ta baka?"
"Mommy dan Allah kiyi haƙuri yanda nake ji a jikina babu wanda zan iya magana dashi a waya shiyasa na sauke wancan layin, ita kuma Amal da take da wannan number bata nemeni ba nima haka, saboda ina buƙatar hutu Mommy."
"Oh saboda nayi maka magana a kanta shiyasa kake fushi har dani? Ina ankare da kai ko abinci sai dai a kawo maka nan, wato ka fifita Amal a kaina"
"Ni ban ce haka ba Mommy, amma na faɗa miki gaskiyar zuciyata ne ina son Amal, kuma haƙurina ya ƙare, tun lokacin dana haɗata soyayya da abokina na ƙarajin cewa ina sonta kuma ina matuƙar kishi a kanta" Hannu ya saka ya goge ƙwallar data zubo.
"Maheer kuka akan mace?" Ta faÉ—a cike da mamaki.
Shiru ya yi bai ce komai ba, ta miƙe tsaye tare da cewa "Kamal yana parlour yana jiranka, ya ce kwana biyu baka je office ba kuma yana kiran numberka bata shiga"
Da ƙyar ya iya cewa "Mommy ya shigo nan"
"Break fast É—inka ma a kawo nan kenan?"
"Eh..." Ya faɗa a taƙaice.
Yana kishingiɗe daga jikin fuskar gado. Kamal ya turo ƙofa ya shigo bakin sa ɗauke da sallama.
"Kamal..." Maheer ya faÉ—a a sanyaye.
Sai da har Kamal ya samu guri ya zauna sannan ya ce "Allah dai yasa lafiya naga kwana biyu baka zuwa office?"
"Wallahi bani jindaÉ—i amma dai zuwa gobe insha Allah zan je"
"Allah ya ƙara sauƙi, ko dai abinda ya faru da Amal ne ya sa ka kwanta ciwo?"
A ɗan tsorace Maheer ke kallonsa "Mene ya sameta?" "Kana nufin baka da masaniya" Kai ya girgiza tare da cewa "Dan Allah Kamal ka faɗa min" "Ina ta kiran numberta bana samu so sai nayi deciding zuwa gidansu tunda already kayi min kwatance, so ina zuwa kuma ban sameta ba, ƙanwarta ta fito kuma ta tabbatar min da tun daren jiya Amal ta gudu kuma basu san ina ta nufa ba. Nayi ta ƙoƙarin samun numberka amma ina... So yanzu haka dai daga gidan nasu nake, ƙanwar ta ta ta nemi in bata numberka domin akwai saƙon da Amal ta bayar a baka, shine nace zanzo in faɗa maka domin numberka bata shiga"
Tun kafin Kamal ya ƙarasa magana, Maheer ya miƙe tsaye yana jero salati.
₦300 Regular Group
₦500 V.I.P
*Regular group zasu riƙa samun page 1 a ko wace rana, while V.I.P zasu riƙa samun pages 3 a ko wace rana*
*0088814969, Adamu Halima Salahu, Access Bank.*
*Zaku tura shaidar biya ga wannan number ****
*Sai kuma katin waya ko Vtu kuyima wannan number *** sai ku tura shaidar biya ta wannan number ****
_Zaku iya turo kuÉ—aÉ—enku a saka ku group kafin a gama free pages_
Idan ya zama complete 1k za a biya.