Free chapter · Read without an account

PAGE 07

by Nanameera · WATA AL'UMMA

*WATA AL'UMMA🌹*


Wattpad_@Nanameera08
Arewapen_@Nanameera08. 



PAGE 07. 



Jabeer ya tsaya cak. A hankali kuma ya juyo yana kallon mai martaba, Fuskarsa a haɗe take babu wani alamar annuri. Ya ɗan yi gyaran murya kafin ya ce“Idan na koma gida ka zo akwai aikin da zan saka ka.” Sai da ya ɗan risina sannan ya ce“In sha Allah mai martaba. A tashi lafiya” Daga haka ya juya ya buɗe ƙofar ɗakin ya fice. Anna ta yi saurin bin bayansa da sauri, A ƙofar ICU ɗin ya tsaya sakamakon takunta da ya ji. Ya juya yana kallonta da idanunsa waɗanda suka rine, A sanyaye ya ce


“Ki koma ciki”


Girgiza kanta ta yi ta ce“A'a zan bika ne. Na fasa zama” 



“Ki koma ciki na ce!!” 


Ya yi maganar a tsawace. Sai da ta runtse idanunta, Ta ɗago ta kanta ta kalleshi. Huci kawai yake, Ya juya ya ci gaba da tafiya kamar zai tashi sama. Shiru ta yi ta zubawa bayansa idanu, Tana hango sanda ya shige mota ya bar asibitin. Sai a sannan ta sauke numfashi ta juya ta kalli cikin ICU ɗin, Kamar ba zata je ba. Sai kuma ta nufi ciki, Amma sam fadawan suka hanata shiga. A cewar su; Har sai sanda Sarki ya fito, Ganin bata da wani zaɓi ya sanyata neman waje ta tsaya kawai. Tana nan tsaye har bayan mintina biyar sannan Sarkin ya fito da matarsa, Sai Ameema da kuma Farooq, Fadawa sai kirari suke masa, Ita dai ta dinga bin su da idanu har suka shige mota suka bar asibitin. Sai a sannan ta nufi ciki. Ta buɗe ƙofar ɗakin ta shiga tana kallon sa, Zaune yake akan gadon, Hannunsa riƙe da kofin shayin ɗazu har sannan bai kai shi bakinsa ba. Yanayin yanda ya yi shiru zai tabbatar da baya cikin hali na jin daɗi. Amma jin ƙarar bude ƙofa ya sanya shi ɗagowa, Idanunsa ya sauka akanta. Tana tsaye ta zuba masa idanu, Murmushin ƙarfin hali ya yi cikin son ɓoye damuwarsa ya ce


“ƙaraso mana” 


Jiki a sanyaye Anna ta ƙarasa ciki, Ya nuna mata gefen gadon ta zauna har sannan shi take kallo. Ajiye kofin ya yi akan drawer, Ya kalleta yana mai faɗaɗa fuskarsa ya ce


“Kina lafiya?” 


Ɗan murmushi ita ma ta yi kafin ta ce“Eh. Ya jikin naka?” dafa saitin inda ta caka masa wuƙar ya yi yana murmushi ya ce“Da sauƙi sosai. Ina jin kamar zan iya kamowa gida” Girgiza kai Anna ta yi ta ce“A'a baka warke ba, Pore ya ce min zai ɗauki lokaci mai ɗan tsawo kafin ka warke. A ƙalla sati biyu, Yau kwana biyar taya zaka ce ka warke?” Ta ƙare maganar tana marairaice fuska. Ɗan murmushi kawai Fa'ik ya yi ya ce“Kin ga ai ni soja ne, Shi ya sa na warke” Jinjina kanta ta yi ta ce“Eh na gani.” Daga haka ta yi shiru, Kallonta kawai ya yi amma bai ce komai ba. Sai bayan wasu mintuna sannan ya sauke numfashi ya ce


“Ya sunanki?” 


Ta ɗan buɗe idanunta ta ce“Ba ka san sunana ba?" gyaɗa mata kai ya yi, Ta taɓe baki sai kuma ta ce“Sunana Anna Ƴar Golma ɗan Zukpá jikan warka. Mai tsafin Kara” Jinjina kai Fa'ik ya yi, Ya ce“Wow nice name” Anna ta ce“kaifa?” Numfasawa Fa'ik ya yi sai kuma ya ce


“Sunana Fa'ik Muhammad Arɗo. Ɗa a wajen Sarki Lamiɗo Muhammad Arɗo, Ni ne ɗa na uku a wajen sarkin. Ina da Yayyi da ƙanne, Ni soja ne. Anan barack ɗin da ke kusa da garin ku” 


Anna ta ɗan yi shiru, Kafin ta ce“Kai ma ɗan sarki ne?” Gyaɗa mata kai Fa'ik ya yi, Ta ce“To shi wanda ya bar nan shi ne sarkin?” Gyaɗa mata kai ya yi nan ma. Ta numfasa bata ce komai ba, Fa'ik ya ce“Look ki tambayi duk abin da ki ke son sani. Zan faɗa miki” Kamar jira take ta ce“Wanda ya kawoni nan ya sunansa? A ina yake?” Shiru Fa'ik ya yi, Lokaci ɗaya jikinsa ya yi sanyi. Anna ta ɗago kansa ta yi masa alamar mene ne da hannunta. Girgiza kai kawai ya yi, Ya sauke zazzafan numfashi sai kuma ya fara cewa


“Sunansa Jabeer Muhammad Arɗo. Shi ɗin Yayana ne, Babban ɗa a wajen Sarki Lamiɗo Muhammad Arɗo.” Da ɗan mamaki Anna ta ce“Shi ma ɗan Sarkin ne?” Gyaɗa mata kai ya yi. Ta ɗan tura baki ta ce“Amma me ya sa na ga ya mare shi? Ko laifi ya yi masa? Dama daga ganinsa ba ya ji.” Ta ƙare maganar tana zumɓura baki. Ɗan murmushin yaƙe Fa'ik ya yi sai kuma ya ce


“A'a yana ji sosai. Yaya Jabeer yana da kirki fiye da tunanin ki, Kawai dai shi baya son wasa ne. Kuma yana da faɗa” taɓe baki Anna ta yi ba tace komai ba, Don ita sam bata yarda da abin da Fa'ik ɗin ya ce ba. Shi ma bai sake yi mata wannan maganar ba ya shiga tambayarta akan rayuwarta, Ai ko babu abin da ta ɓoye masa. Har abin da bai tambaya ba ma sai da ta faɗa masa, Sosai Fa'ik ya yi mamaki. Dan da gaske bai yi tunanin akwai mutanen da ke irin wannan rayuwar ba, Ashe har yanzu ba su ƙare ba. Ganin bai ce komai ya sanyata cewa 



“Tsoro ka ji ko?” 


Ɗan murmushi kawai ya yi bai bata amsa ba. Ta ɗauke kanta tana kallon tvn da ke maƙale a bango ta ce“Nima na ji tsoron ku. Amma fa ba sosai ba, Saboda Golmanya ta taɓa bani labarin irin ku” Da sauri ya kalleta, Ya ce“Da gaske? Ita ta san akwai irin al'ummar mu? Ta san da wata al'ummar bayan taku?” Jinjina kai Anna ta yi, Ta ɗan kalle shi sai kuma ta sake ɗauke Idanunta ta ce“Ta sani mana. Ta sha bani labarin irin ku, Ko kuma idan na sakko daga kan tsaunin mu ina ganin Fulani. Na san su sosai” Murmushi kawai Fa'ik ya yi, Yana kallon yanda take da fuska. Kallon sheƙeke Anna ta yi masa sai kuma ta ce“Me ya sa ka ke min dariya?” girgiza kansa ya yi, Ya ce“Ba komai” Ta yi shiru kamar ba zata ce komai ba sai kuma ta ce 


“Ina so na koma gida.” 


“Baki son zama anan?” Fa'ik ya tambayeta da sauri. Anna ta ce“Ina so. Amma na fi son na koma gida, Na san Golma yana can yana nemana. Zaka kai ni gida?” Murmushi Fa'ik ya yi ganin yanda ta yi da fuska kamar ƙaramar yarinya. Ya jinjina mata kai kana ya ce


“E zan kai ki. Amma sai na warke” 


Dariya Anna ta fara yi, Ta ja kumatunsa ta ce“kana da kirki Zurma. Ba kamar wancan ba” ta ƙare maganar tana murmushi. Bai ce komai ba, Sai kallonta kawai yake. Yana kallon zallar kyawun da ke kan fuskarta, Anna asalin kyakkyawa ce. Musamman idan ta yi dariya ko kuwa ta buɗe dara-daran ruwan zuman ƙwayar idonta. Duk da ya saba ganin kyawawan mata, amma bai taɓa ganin mai kyau irin nata ba. 


“Me ya sa ka ke kallona?” 

Muryarta ta dawo dashi daga tunanin da yake. Saurin girgiza kai ya yi cikin ƙinƙinar da ta zo masa ya ce


“A... a'a ba komai” Ya ƙare maganar yana girgiza hannayensa. Karkace baki ta yi ta ce“ka san hukuncin wanda ya kalleni a garinmu? Golma kashe shi yake yi!” Ta ƙare maganar tana murmushi. Kallonta kawai ya yi, A ransa kuwa tausayinta yake ji. Sam rashin addini bai dace da ita ba, A don haka ya ɗauki aniyar sai ya musuluntar da ita ta kowane irin hali.” Anna ta kai masa duka tana cewa “Baka ji ina maka magana?” Da sauri Fa'ik ya ce“Yi haƙuri ban ji ba ne. Me ki ka ce?” Ta harareshi sannan ta ce“cewa na yi ka ce yi haƙuri gimbiya Anna. Abar bauta Kara ta sanyaya zuciyar ki” ɗan murmushi kawai Fa'ik ya yi yana girgiza kansa, Ta haɗe rai ta ce“ko ba zaka ce ba?” 



“Ki yi hakuri gimbiya Anna. Ba zan sake ba” 


Ya faɗa yana murmushi. Sake haɗe fuska ta yi ta ce“Haka na ce maka?” Fa'ik ya ce


“Ki yi haƙuri gimbiya Anna. Allah ya sanyaya zuciyar ki” 


“wane Allah?” 

Ya ji ta tambaye shi. Cike da nutsuwa ya ce“kina so na faɗa miki wane ne shi?” gyaɗa masa kai ta yi, Fa'ik ya kamo hannayenta ya riƙe cikin nasa sannan ya fara cewa“Allah shi ne abun bautar mu. Mu anan ba ma bautawa gunki, Addinin gaskiya muke bi. Wato addinin musulunci, Wanda ya shi ne addinin gaskiya. Mabiyansa ne kaɗai zasu shiga aljanna a ranar gobe ƙiyama. Allah kuma shi ne ubangijin mu, wanda ya halicci mutane da aljanu. Duk wanda ya bi shi ya tsira, wanda kuwa ya saɓa masa wuta ce makomarsa.” Yayi shiru yana kallonta. Anna ta ɗaga masa gira ta ce“me ya sa ka yi shiru?” cikin sakin fuska ya ce“kina so na ci gaba?” Anna ta janye hannayenta daga nasa sannan ta ce“barshi kawai.” Fa'ik bai sake cewa komai ba, Don baya son ya takurata. Ta zubawa tv idanu tana kallon wani film da ake haskawa, Duk da ba fahimta take ba....




****Misalin ƙarfe 5:00 na yamma ya yi parking a harabar gidan. Ya ɗaga idanunsa yana kallon doguwar katangar gidan, Gida mafi kyawu a idanun al'umma. Gidan da jama'a da yawa ke mararin a ce a nasu ya zo, sai dai sam ba haka abun yake ba a gurinsa. Gida ne wanda yake tamkar kurkuku, Gidan da ya tsani ya buɗi ido ya gan shi ciki. Gidan da rayuwar dabbobi ta fi tashi daraja a cikinsa, Wato gidan Sarki Lamiɗo Muhammad Arɗo. Sarkin da ke mulkar jama'ar garin Adamawa, Ɗan sarki Arɗo AbdulRahman. Yana da shekaru 65 a duniya, Ya'yansa biyar. Babban cikin su shi ne Jabeer Muhammad Arɗo, Sai A'isha Muhammad Arɗo, Fa'ik Muhammad Arɗo, Umar Muhammad Arɗo, Surayyah Muhammad Arɗo(Ameema). Matansa uku, Gimbiya Ramlah ita ce uwar gida, Kuma mahaifiya a wajen Jabeer. Sai Gimbiya Bilkisu mahaifiyar sauran ya'yan ban da Ameema, Ita mahaifiyarta ƙwarƙwarar Sarki ce. Wadda ta rasu yayin haihuwarta, Inda Gimbiya Ramlah ke riƙe da ita. Mai martaba na da ƙanne guda biyu mace da namiji, Kilishi Zainab, Sai kuma Galadima Kabir. Sarki Lamiɗo Muhammad mutum ne mai halin kirki, Mutum mai tarin ilimi da sanin yakamata. Wannan ya sanya soyayyarsa a zuciyar duk wani ɗan garin Adamawa. A gurin kowa shi mutumin kirki ne, Yana da son ya'yansa, Duk da kasancewarsa Sarki hakan bai hana shi jan yayansa a jiki ba. Ya'yansa su ne abokan shawararsa, Komai nasa sai ya saka su. Don haka ya sanya suke son mahaifinsu fiye da komai, Sai dai shi sam Jabeer ba haka ba ne a wajensa. Babu wanda Sarki ya tsana sama dashi, Baya taɓa yi masa uzuri. Kullum cikin kyararsa yake da hantararsa, ko sunansa bai isa ya kira ba, Sai dai ya dinga kiransa da sunan dabbobi, Haka kuma ya haramta masa shi ma ya kira sunansa yanda Yan uwansa ke yi, Sai dai ya ce masa mai martaba kamar sauran mutanen gari. Wannan kuma ya samo asali ne tun yana ƙaramin yaro. A sanda mahaifin Sarki Lamiɗo wato Arɗo AbdulRahman ya rasu, A cewarsa Jabeer shi ne wanda yake da alhakin rasuwarsa kasantuwar wani abu da ya faru a sannan. Tun daga wannan lokacin Jabeer bai sake samun kulawa ta mahaifi ba. Koda yaushe cikin aibata shi yake, A gaban kowa yake nuna zallar ƙiyayyar da yake masa. Sai dai duk da waɗannan abubuwan bai sa Jabeer ya gagara yi masa biyayya ba, Koda yaushe cikin son faranta masa yake. A tunaninsa wata rana sarkin zai sauya, Duk da yanzu an ɗauki a ƙalla shekaru 30 a haka..


       Jabeer ya sauke hannunsa daga kan steering motar, Ya ɗauki wayarsa ya sauka daga motar. Pcap ɗin dake kansa ya sake ja ta zo har goshinsa, Sannan ya rufe motar ya nufi cikin gidan yana tafe ciki da izza. Kai tsaye ɓangaren Fadar Sarkin ya nufa kamar yanda ya bashi umarni, Yana zuwa ya same shi zaune tare da fadawansa. Suna ganinsa suka shiga gaishe shi ana masa kirari, Shi dai bai tankasu ba ya nemi waje ya zauna a ƙasa. Ganin haka ya sanya su fita suka bar shi daga shi sai Sarkin, Cike da girmamawa ya ce


“Barka da Yamma Mai martaba.” 


Bai bashi amsa ba, Sai kallonsa da yake. Ganin haka ya sanya shi sunkuyar da kansa, Sai da wasu mintuna suka shuɗe sannan mai martaba ya ce


“Da farko ina son na yi maka gargaɗi, Duk ranar da aka sanar da kai wani abun akan ƴaƴana ka ɓoye min sai na yi maka abin da har abada ba zaka mance ni ba!” Jabeer ya sunkuyar da kansa ya ce“tuba nake. A gafarce ni” Mai martaba ya sake cewa“Zuwa an jima ina so ka je barack ɗin su Fa'ik ka samo bayanin yanda aka kai masa harin” Cikin sanyin murya ya ce“In sha Allah mai martaba.” Bai sake cewa komai ba ya jingina da bayan kujerarsa yana kallonsa, Ganin haka ya sanya Jabeer cewa“Idan mai martaba ya gama magana ina son tafiya” Ya ƙare maganar yana kallon sa. Shiru ya yi, Can kuma ya ce“Na gama amma ban baka ikon tafiya ba” Jabeer wanda har ya yunƙura ya koma ya zauna bai ce komai ba. Mai martaba ya ci gaba da kallonsa yana jijjiga ƙafafunsa, Bai bari Jabeer ya bar fadar ba sai da aka fara kiraye kirayen sallar magriba. Ko da ya fito sashin Gimbiya Ramlah ya nufa, Yana shiga ya samu ta tada Sallah, Sai hadimarta Zulai a tsaye, Tana ganinsa ta gaishe shi cike da girmamawa sannan ta juya ta fice daga parlourn. Gimbiya na idar da sallah ta juyo tana kallon sa ko addu'a bata tsaya yi ba, Fara ce, Tana da uku-uku irin na Fulanin Katsina. Tana da kyau sai dai kana ganinta ka san ta manyata, Cikin sanyin murya ta ce



“Yarimana” 


Kallonta kawai ya yi, Ya taso ya dawo inda take ya zauna ya ɗora kansa akan cinyarta. Zare hular kansa ta yi ta fara shafa gashin kansa, Ya saki ajiyar zuciya sannan ya ɗago ya ce


“Ina yini Mammi?”


Bata amsa ba, Ta shafa fuskarsa ta ce“Kana cin abinci kuwa Yarima?” Gyaɗa mata kai kawai ya yi. Ta ƙura masa idanu, Can ta ce“mene ne ya samu fuskar ka?” Saurin riƙe hannunta ya yi ya ce“No... Babu komai fa, Me ki ke gani?” Ya ƙare maganar yana murmushi. Girgiza kai kawai Mammi ta yi, Sai kuma ta ɗago ta kalle shi. Hawaye ya gani kwance cikin idanunta, Ya yi saurin riƙe hannunta ya ce


“Mammiii! Babu komai fa.” 


Cikin rawar murya ta ce“me ya sa ka ke ɓoye laifin mahaifinka? Me ya sa Jabeer? Ameema ta sanar dani komai. Me ya sa?” 



Shiru Jabeer ya yi, Dama abin da yake gudu kenan. Ashe an faɗa mata, Ya ɗan faɗaɗa fuskarsa ya ce“Ai babu komai Mammi. Mai martaba fa mahaifina ne, Kuma laifi na yi masa. Shi ne ya sa ya hukuntani, Mahaifin da ke son ɗansa shi ne yake hukunta shi idan ya yi laifi, So I'm so proud of him.” Ya yi murmushi har sai da beauty point ɗinsa suka lotsa. Mammi ta ɗan kalleshi kafin ta ce


“Amma duk da haka kai ba ƙaramin yaro bane Jabeer. Da ace ka yi aure da wuri da yanzu ka ajiye Ya'ya, Akan me zai dinga yi maka haka? Kuma ma a gaban yara na ga...” 



“Mammi.... It's normal fa, Yanzu ma daga wajensa nake ya aikeni. Abb... Au mai martaba bashi da wani laifi” 


Shiru ta yi, Ba don ta gamsu da abin da ya faɗa ba. Domin ta san ya faɗi ne kawai don ya kare mahaifinsa kamar yanda ya saba a koda yaushe, Ta goge hawayenta tana jin tausayin tilon ɗan nata. Ganin yanda ya yi da fuska ne ya sanyata cewa 


“mene ne? Ka ci abinci?” 

Ya gyaɗa kansa kawai duk da bai cin ba, Mammi bata yarda dashi ba, Don haka ta ce“Ka zauna anan bari na saka Jakadiya ta kawo maka abinci ka ci.” Jabeer ya girgiza kansa yana murmushi ya ce“A'a Mammi, kin ga ko sallah ban yi ba. Kuma mai martaba ya aikeni, Idan na dawo zan biyo sai na karɓi abincin” Da fari ƙin yarda ta yi, Daga baya kuma ta ce“Shikenan. But make sure you come back” Ya gyaɗa mata kai ya ce“In sha Allah Mammina” Murmushi ta yi, Ta ce“Allah ya tsare” Da Amin ya amsa sannan ya juya zai fita. Sai kuma ya dawo ya ce“au na mance, Na tawo miki da abu amma yana mota. Idan na dawo zan biyo na kawo miki” 



“Jabeer yaushe zaka dawo gida? Bana son kana kwana a wani wajen kai kaɗai” Shiru ya yi, Don bai ɗauka zata yi masa wannan tambayar ba. Ya ce“Mai martaba ne ya ce na tafi Mammi, Kin ga ai ba zai yiwu na dawo ba.” Mammi da ranta ya soma ɓaci ta ce


“Idan haka ne zan je wajen Inna na faɗa mata. Na gaji Jabeer!” saurin girgiza mata kai ya yi, Ya riƙe hannayenta ya ce“don Allah ka da ki yi haka Mammi. Ka da ki bari ta ji, Idan ya ce na dawo na miki alƙawarin zan dawo” Numfasawa ta yi ta ce“shikenan na ji je ka, amma ka tabbata ka dawo” To ya ce sannan ya fice daga ɗakin da sauri. Mammi ta bi shi da kallo sai kuma ta sunkuyar da kanta... 



****Bayan sallar magriba Anna na zaune kan farar kujera sai hira take yiwa Fa'ik wanda yake zaune gefen gado bayan ya idar da sallah. Sai dariya suke abin su, Turo ƙofar ɗakin aka yi, Suka kalli wajen a tare, Jabeer ne ya shigo. Hannunsa zube a cikin aljihun wandonsa, Tsayawa suka yi da dariyar. Fa'ik ya ce


“Sannu da zuwa Yaya” 


Ƙarasowa ciki ya yi, Ya tsaya a jikin gadon yana ci gaba da kallon su. 

“Ya jikin naka?” 


“Da sauƙi” Cewar Fa'ik. Jinjina kansa ya yi sai kuma ya kalli Anna ya ce“ke taso” kallonsa ta yi, Sai kuma ta nuna kanta da hannunta ta ce


“Ni?” wani banzan kallo ya watsa mata, Sai kuma ya ce“A'a ni.” Anna ta miƙe tana tura baki, Bai sake cewa komai ba ya juya ya fice daga ɗakin. Ta kalli Fa'ik ya ɗan yi murmushi ya ce


“Gobe ma za ki dawo?” Gyaɗa masa kai ta yi, ta ce“Eh mana. Zan dawo mu ƙarasa” Ya jinjina kansa ya ce“Okay Allah ya tashe mu lafiya” Bata ce komai ba ta juya ta fice daga ɗakin ita ma. Sanda ta fita har ya yi nisa, Don haka ta bi bayansa da sauri da sauri. A bakin motarsa ya tsaya, Ya kalleta ya ce


“Shiga muje” 


Anna bata ce komai ba ta shiga front seat ɗin da taga ya buɗe mata. Ya rufe sannan ya zagaya ɗaya side ɗin ya shiga, Sai da suka ɗan yi nisa sannan ta kalle shi, Hankalinsa na kan tuƙin da yake. Gashi ya kunna karatun Alqur'ani yana bi a hankali, Anna ta ɗan tura baki sannan ta ce


“Kai ma ɗan sarki ne dama?” 


Juyowa ya yi ya kalleta, Sai kuma ya ɗauke kansa. Ta ɗan yi jim sai kuma ta sake cewa “Fa'ik ya faɗa min ya ce kai ma ɗan sarki ne. To amma me ya sa ya mareka? Kai baka ji ko?” Sake kallonta ya yi, Wannan karon bakinsa buɗe. Ya yi kwafa sai kuma ya ɗauke idonsa. Anna ta harareshi ta ce“Kai sai ka dinga share mutane, Nima na iya wulaƙancin” 



“To uban wane ya ce ki shiga harkata?” 


Ta tsinkayi muryarsa. Kallonsa ta yi, Ba ita yake kallo ba, Ta taɓe baki ta ce“Kar dai ka zage ni” Wani irin wawan birki Jabeer ya ja. Ji ka ke "ƙuuuuu!" Anna ta ɗan rufe idanunta saboda tsoron da ta ji. Ɗago kanta ta yi ta kalle shi, Ya juyo a fusace ya ce



“Idan na zage kin me zai faru?” 


Ganin yanda ya haɗe fuska ya sanyata haɗiye ragowar maganar da ke bakinta. Ta ɗauke kanta kawai, Jabeer ya dinga kallonta kafin ya ci gaba da tafiya. Ɗan nesa da Barrack ɗin ya yi parking motar ya buɗe ya fita ba tare da ya kalleta ba. Ita ko ta bi shi da idanu, Sai da ta ga ya shige cikin barrack ɗin sannan ta ce


“Masifaffe kawai!” 

Ta yi maganar tana murguɗa baki. Ta jima sosai a motar kafin ya dawo, Bai kalleta ba ya sake yiwa motar key ya bar wajen. Tafiya mai yawa suka yi, Ita dai kallon hanya kawai take. Duk da babu haske inda suke bin sai na motar da ya kunna, Ciyayi ne duk a wajen. Anna ta juyo ta kalle shi jin ya tsayar da motar, Kafin ta yi magana ta ji ya ce



“Can shi ne tsaunin dana ɗakko ki. Gashi na dawo da ke, Ki sauka ki tafi gida” Kamar a mafarki haka ta ji kalaman nasa. Cike da rashin fahimta ta ce


“Ban gane ba. Gida ka dawo da ni?” 


Juyowa ya yi ya zuba mata manyan idanunsa, Ta sunkuyar da nata ƙasa. Can ta ji ya ce“Ba kin yi alƙawarin ni zan dawo da ke gida ba? To na cika miki alƙawari, Sauka ki tafi” Bata iya cewa komai ba, Ta dai kalleshi. Fuskarta ta sauya sosai, Ita ba me farin ciki ba kuma ita ba mai damuwa ba. Ya lumshe idanunsa ya sake buɗe su akanta. 



“Sauka mana” 


Ya ce yana nuna mata murfin motar. Jinjina kai kawai Anna ta yi, Ta buɗe motar. Juyowa ta yi ta kalle shi, Ta ga ba ita yake kallo ba. Don haka ta sauka ta rufe motar, Tafiya ta fara yi a sanyaye tana waiwayensa. Ya kunna hasken motar sosai yanda zai bata damar ganin inda take bi, Yana nan zaune har ta fara hawa matattakalar tsauninsu. Ta sake juyowa ta kalli motarsa, Idanunta ya sauka akansa, Numfasawa kawai ta yi. Sai kuma ta juya ta ci gaba da tafiya, Sai a sannan ya sauke numfashi shima. Ya juya ya bar wajen....



***
Nanameera. 



Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol