Free chapter · Read without an account

Page-43

by 🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚 🖋️ · “SANADIN ƘADDARATA”

*FASAHA WRITER'S ASSOCIATION*
     (*F.W.A)*©✍️
     ⭐⭐⭐

Ƙungiya masu aiki cikin salon hikima da fasaha gurin juya tunanin al-umma, kaifin alƙalumansu ya zarta takobi ©✍
___________________________________________________



بسم الله الرحمن الرحيم.
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد. 




❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁ 




Free book📓



By: _*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_




Page4️⃣3️⃣





Nusaiba kallon Sadiya ta ke ita kuma ta sauke hannun Nusaiba da ƙarfi sannan ta kifa mata mari fiskarta a haɗe ba tsoro.

Sake dafe kuncinta ta yi karo na biyu, ta ɗago idanuwanta da su ka cika da matsanancin fushi tana kallon Sadiya. Buɗe baki su ka yi ganin abun da Sadiya ta aikata cike da mamaki, sai kallonta su ke yi musamman Baaba ko ƙyafta ido ba ta yi akanta, inda Sadiya kuwa ta buɗi baki da zafin rai ta ce da Nusaiba, "duk rashin kunyarki ya kamata ki jawa kanki kunne idan ta yi tunanin aikatawa Baaba haka!"

"Ni za ki mara don na mari wannan abar?" Faɗin Nusaiba tana nuna Baaba da hannu, "ba wannan abar ba ita tamkar mahaifiya ta ke a gareni, kula idan ki ka sake kiranta da wannan suna sai na kuma kifa miki mari mai shiga jiki!" Sai da hawayen da su ka taru a idon Baaba su ka sauko da jin kalaman Sadiya, Nusaiba kuwa yunƙurawa ta yi tana shirin yin kokuwa da Sadiya har da cewa, "yau sai kin gane ni ki ka mar...".

Ba ta kai ƙarshe ba sakamakon hankaɗar da Sadiya ta mata ta faɗi, ta bugu da ƙasa sosai har da sakin ƙara, ba ta saduda ba ta kuma ɗagowa tana sake shirin kokuwa da ita, Sadiyar ta kuma turatada ƙarfi, Nusaiba ta yi ƙoƙarin tashi, amma gwiwoyinta suka kasa ɗaukar nauyinta. Ta ɗago ido, a karon farko tsoro ya ratsa zuciyarta game da Sadiya.

Su Baaba kuwa tsaye su ke kamar an tsaida taɓarya, suna ganin ikon Allah. "Abun da ki ka aikatawa Baaba ba zan iya barinki ba, duk abubuwan da ki ke min ina shiru Nusaiba ba wai don ina tsoronki ba ne, kawai haƙuri na ke yi ina shanye duk abun da ake min saboda wani dalili! Da ba don haka ko kusa ba ki isa ki nunani da yatsa ba wallahi!" Faɗin Sadiya babu dana sani.

a sa hannu ta ɗago ta ta kuma kifa mata wani zazzafan marin.

Ja baya kaɗan Nusaiba ta yi tana sauke numfashi, ta juya tana kallon su Aisha da ke yin dariya ƙasa-ƙasa, ban da Baaba da ko motsi ba ta yi, Nusaiba ta ce, "wai waye ki ke karewa Sadiya? Wacche ta tsaneki kuma ta wulaƙanta ki? Wa'yan da ko kusa ba su taɓa ƙaunarki ba matsiyata?" Ɗago da ita Sadiyata yi a karo na uku ta kuma kifa mata zazzafan mari tana cewa, "ina sake gargaɗarki Nusaiba, kada ki sake kiran Baaba da mummunar kalma, tamkar mahaifiya ta ke a gurina, kin ga kuwa ko me za ta min ba zai rage darajarta à gareni ba".  

Rufe ido Baaba ta yi tana jin wani abu mai zafi mai kama da dana sani ya daki ranta. Nusaiba kuwa da gudu ta nufi ɗakinta ta kulle. Sai da Sadiya ta ja numfashi zuciyarta na harbawa, ta dawo da idonta gunsu Baaba, su Fatima haɗiye nyawu su ka yi ashe dama Sadiya ba kanwar lasa ba ce? Har Lantana sai da ta yi wannan tunanin, don yadda aka yiwa Nusaiba ko su Sadiya za ta iya musu hakan, amma tsawon lokacin nan ko yatsa ba ta taɓa gwada musu ba.

Ba tare da magana ya gifta a wurin ba Lantana ta kama hannun Baaba su ka bar gidan dukkansu jiki a sanyaye. Sauke numfashi Sadiya ta yi, yau ta karya maganar Momy ta kasa haƙuri, amma koma me tana darajta Baaba sosai, ko rashin kunyar da Nusaiba ta yi mata rannan ma ba ta ji daɗinsa ba, amma ba za ta bari a mareta a gabanta ba, kamar yadda ba za ta haƙura tana gani à ɗagawa Momy ko da murya ba. Sai dai tana jin wani fargaba a ranta kan kada Nusaiba ta sa Faruq ya yi mata wani abun ko ya saketa.....

Ta zauna a kujera sai sauke ajiyar numfashi ta ke ba ƙaƙƙautawa, yayin da ta ke jin ranta na tafarfasa kan abun da Sadiya ta aikata mata, ba za ta taɓa haƙura ba, wai ita za'a yi wa haka? Ita Sadiya za ta wulaƙanta kuma a gabansu Baaba harsu Fatima na yi mata dariya? Ita za ta mara? Don ta yi mata alfarma ta barta cikin gidan nan da zama? Wato yau ta nuna mata tana da ƙarfi kenan, to wallahi ba zai taɓa saɓuwa ba wai bindiga a ruwa, ta fi ƙarfin Sadiya ta mareta, alwashi ne sai ta rama fiye da abun da aka yi mata yau, idan ta bar komai ya wuce to ba Nusaiba ta ke ba.

"Ni Nusaiba na yi alƙawari! Sai na yi maganinki na san kin yi da kin sanin ɗaura hannunki ga fiskata, domin kuwa ba ki mari banza ba Sadiya!" Ta faɗi tana shafa ko wani gefe na kumatunta da tasha maruka, ta miƙe zuwa gurin window, fiskarta babu annuri a ciki sai tsantsar baƙin zuciya ta kuma faɗin, "tun da na zo gidan nan ban nunawa kowa asalin gaskiyar halina ba, to yanzu Sadiya ki shirya don amsan sakamakonki a hannuna! Idan na sa Faruq ya sake ki ai kamar kin ci banza ne, don haka za ki ɗanɗani kuɗarki cikin azaba!".

WASHE GARI.

Nusaiba ba ta sanar da Faruq komai ba, sai dai ita akwai abun da ta shirya, musamman ma da ta ƙara ƙuluwa Sadiya ba ta kawo mata abincin dare ba.

Ita dai Sadiya abun da ya hanata yin hakan jiya da zazzaɓi mai zafi ta kwana har zuwa yanzu, da ƙyar ta samu damar kammala dafa gandar ma, ta zuba a kula kawai ta koma ɗakinta ba tare da ta kaiwa Nusaiban ba, tana kwance sai sauke numfashi a hankali, domin kuwa yadda yau cikinta ya ke juya mata ba ta san ko me dalili ba, ko kuma ƙila ta yu ko saboda wannan karon watanta ya yi mata wasa ne, domin kuwa wata na biyu kenan bai zo ba, ta rasa dalilin da zai sa ya yi mata haka.

Tana à wannan halin ta ji sallamar Faruq, sai da zuciyarta ya tsinke domin kuwa tun ranar da ya zo ya sanar da ita su canza ɗaki, bai ƙara zuwa gurinta ba, amma me yasa ya zo yau? Tabbas akwai dalili, to ko abun da ya faru jiya ne yasa shi yazo?.

Tashi ta yi ta zauna tana kallonsa da fargaba, "me yasa ba ki dafawa Nusaiba gandan ba?" Ya jefa mata tambayar fiskarsa ba wasa, baki na rawa ta ce, "zan kai mata" "to ki je yanzu ta ke son cinsa" ya faɗi zai fice, da ƙyar Sadiya ta yi dauriyar tsaida shi ta ce, "dear" turus ya tsaya cak ba tare da ya juyo ba, sai dai kalmar ta shiga zuciyarsa, "don Allah ina son ka bani kuɗi zan je asibiti, ba na da lafiya".

"Zan tambayi Nusaiba" abun da kawai ya iya furtawa, sannan ya wuce, Sadiya ta ja numfashi mai ƙarfi, ta rasa ma abun yi, a ƙarshe dai ta sauka daga kan gadon tana tafiya a sanyaye saboda yadda jikin na ta ke yi mata, bayan ta shiga kitchen kawai ta ji ƙofar ya kulle, da sauri ta waigo tana duban wurin da tsananin mamaki, ya aka yi ƙofar ya rufu da kansa haka? Bayan kuma ba ya rufuwa sai an turasa?.

Sai kuma ta yi burus da wannan tunanin kasancewar dama akwai hasken fitulu a ciki, wani irin wari ta fara ji na shiga hancinta, amma ba ta lura ba, ta isa gurin kula da ta zubawa Nusaiba ferfesun a ciki, ta ɗauka ta nufi ƙofa, sai dai abun al'ajabi sai ta ji ƙofar ya ƙi buɗewa, ta tura da ƙarfi amma da alamu a datse ya ke ta baya....

_Nusaiba da dama tana tsaye, bayan Faruq ya fito daga ɗakin Sadiya ya ke sanar da ita ana kawo mata yanzu, sannan ya ce, "Sadiya ta ce tana son kuɗi za ta je asibiti, in ba ta?" Nusaiba ta haɗe fiska tana hararsa ta ce, "ƙarya ta ke yi babu wani rashin lafiya da ta ke yi, rabu da ita jeka kawai" ba musu ya amshi jakar aikinsa da ke hannunta ya fice, cikin wani yanayin rashin natsuwa da ke shigarsa. Yana fita Nusaiba ta nufi kitchen dama abun da ta shirya kenan, Sadiya na shiga ta tura ƙofar a hankali ta datse da sakatar da ke waje_

Faruq motarsa ya shiga sannan ya ja yana tafiya amma zuciyarsa ba adaidai ba, yau dai zuciyarsa ta ɗan karkata akan Sadiya, yana so ya ba ta kuɗin amma ba zai iya ba sai Nusaiba ta ba shi dama.

Nusaiba bayan ta rufe ƙofar ta jingina da bangon wurin, a zuciyarta ta ke cewa, "Sadiya Sadiya, yau sai kin gane kiɗa da karatu, ƙila ki rigamu gidan gaskiya yau ɗin nan! Allah ya ji ƙanki Sadi baby" ta faɗi tana murmushin da da ka ganshi ka san mugunta ce ziryan, sannan ta juya ta wuce falonta, ta fito da MP mai ɗan girma ta ijje a ƙofar ɗakin ta kunna kiɗa tare da sa volum.

Domin ko da Sadiya tana ihun neman a gaji ba wanda zai ji, idan ta mutu za a ɗauki hakan da sunan tsautsayi wanda ba sa masa rana. Dariya ta sheƙe da shi sannan ta ɗaura kanta a kan kujera tana lumshe ido cikin natsuwa sosai, alwashi ya rufe mata ido komai za ta yi.....

Ijje kular da ke hannunta ta yi a kan desk ɗin kitchen, sannan ta sa ƙarfinta sosai tana tura ƙofar ko za ta buɗe, "warin gass!?" Sadiya ta furta cikin tsoro da ta dafe ƙirjinta da ke matsanancin bugu, domin kuwa warin fita ya ke sosai ta gane na gass ne.

A daidai lokacin majiyarta ya jiye mata tashin kiɗa mai ƙara, da gudu ta ruga gurin tukunyar sinadarin gass don ta rufeshi, amma sai dai ya ƙi rufuwa hasalima kamar ƙara buɗesa ta yi. Numfashinta ya tsaya cak, wani irin jiri ya ratsa kanta, ta sake shakar iskar warin ya ƙaru, ta koma ga ƙofa cikin matsanancin tashin hankali.

Take ta fara bubbuga ƙofa tana kururuwa, "waye kusa?! Ku taimakeni ku buɗe ƙofar nan, gass yana buɗe, Faruuuuq! Nusaiba kina ina? Nusaibaaaa, Faruq ku taimakeni, ina cikin kitchen,Nusaiba kina ji naa? Taimakoooooo, Aishaaaa, Baabaaa! Faruuuq wani ya taimaka miin!" amma muryarta na fita kunnuwanta su ka kasa jinta da kyau bare wanda ya ke waje, sakamakon sautin da ke tashi,.

NURIYYAH. 

_Har Ayusha ta juya za ta fita, sai kuma Asma'u ta dakatar da ita, tsayawa ta yi tana jin Allah yasa amincewa ta yi, ita ko Asma'u ba komai ba ne ya sa ta yin hakan sai ganin bai kamata ta yi mata magana haka ba, domin ta tuna da maganar Nuriyyah na rannan, "shi kenan mu je" ta faɗi tana sauka daga kan gadon ta ɗauki mayafita. Suna cikin tafiya Ayusha ta ɗaga wayarta à fakaice ta turawa Sunusi saƙo kamar yadda suka shirya. Suna shan kwana Asma'u ta ganni tsaye da Sunusi, sai dai ni na bata baya, shi kuma Sunusi ya yi kamar bai ganta ba, Asma'u na shirin yin magana kawai ta ji kalaman Sunusi da su ka gigita mata tunani, wai duk Nuriyyah ce tai mata duk wannan abubuwan? Tana ganin Sunusi ya ƙare zancen ya juya sai ta tsaidashi_

"Babu inda za ka je!!" Muryar Asma'u ya ratsa kunnuwana, wani irin bugu zuciyata ya yi jin yadda ta furta maganar. Shi kuwa Sunusi ya washe baki yana ɗan zaro idonsa kaɗan na makirci.

Da sauri na juya idona ya sauka kan Asma'u da Ayusha da tun ɗazu su ke sauraron duk abun da Sunusi ya faɗa, nufan gurinta na yi ba da wani zato ba, sai dai kan na ƙarasa na ji ta kuma cewa, "babu inda za ka je Sunusi, kuma aure ni da kai kamar anyi ne insha Allah yadda aka tsara!" Sunusi ya waigo fiskarsa ya bayyanar da murna, sai Ayusha da ta murmusa na ƙasan baki.

Ni kam mamaki ne ya cika ni sosai da sosai, ban san lokacin da na ƙarasa kusa da ita ba ina cewa, "me ki ka yi haka? Kin san me ki ka ce kuwa Asmee? Ko kin manta abun da na ce da ke ya yi ne? Haba 'yar uwata ka da ki..." "ni ba 'yar uwarki ba ce!" Asma'u ta katseni da wannan furucin da ya girgiza ni, na dakata ina kallonta.

Idonta ya yi ja da kawo ruwa saboda ɓacin rai, ta ɗaura da cewa, "Nuriyyah me na yi miki? Me na aikata miki da na cancanci wannan daga gareki? Kina cewa ni 'yar uwarki ce ashe ba haka ya ke a zuciyarki ba, me yasa Nuriyyah? Ban taɓa tunanin kina da wannan halin ba, kenan kina da hali ɓoyayye kuma gurɓatacce ba mu sani ba?".

Girgiza mata kai na yi idona ya kawo ƙwallah wato ta ji kalaman Sunusi, na juya ina kallonsa, kenan ya riga da ya ga Asma'u tun farko shiyasa ya sauya kalamai, ba tare da na lura ba na afka cikin raminsa, gashi Asma'u ta amince. Da zantukansa.

Na juyo ina kallonta zan yi magana amma ta ɗaura da faɗin, "wallahi da ba don da idona na ga komai ba da ba zan taɓa yarda ba, ko à tunani ban kawo za ki yi min wannan abun ba, sai ga shi da gaske ne, wai ke ce ke bin namiji aikata mummunar zunubi Nuriyyah?" Ta ƙarashe tana zubar da hawaye cike da jin zafi.

Girgiza mata kai na cigaba da yi a karo na biyu nima ina hawaye na ce, "ba gaskiya ba ne, Asmee kada ki yarda da wannan mugun mutumin, duk abun da ya faɗa ƙarya ce, wallahi ni ban san wani komai daga cikin labarin da ya bayar yanzu ba, ni ban taɓa waya da Sunusi ba ko sau ɗaya, in banda gaisuwa da ya ke haɗani da shi ba bu..." "Nuriyyah me yasa ki ke son juyar da komai a kai na? Wace irin zuciya ki ke da shi ne?" Sunusi ya katseni da wannan maganar yana matsowa kusa.

Cike da zafin rai na nufi inda ya ke, na ɗaga hannuna na wanke shi da mari, sannan na ce, "kai ko kunya ba ka ji? Wani irin..." ban ƙarasa ba saboda juyo da ni da Asma'u ta yi ta gaura min mari, take hawaye su ka fara tsere kan kuncina babu jira, hatta cikin zuciyata ma hawayen ta ke yi, na ɗago ina dubanta idanuwana sun fara ja. 

"Ke kin isa kisa hannu akan fiskar wanda zai zama mijina Nuriyyah!? Kin yi ƙarya da Ayusha akan za ki je siyo magani, kawai don ki haɗu da shi ki samu hankalinsa? To ki saurareni da kyau! ke ce burinki da ki ke da shi cikin ahalinmu ba zai taɓa cika ba!" Faɗin Asma'u, muryata ya fara fita da kuka ina cewa, "no, no Asmee, da gaske ne abun da na fito yi kenan" na faɗi ina komawa gurin Ayusha na ce, "ki faɗa mata ba abun da ya faru ba kenan? Ayusha ki faɗa mata don Allah".....


Last page
___________________________________________________


Waiii!! Ga Sadiya cikin komar Nusaiba, ashe muguntarta ya wuce tsammani. Me zai samu Sadiya? Za ta tsira?🥺

Tom ga Nuriyyah, Asma'u dai ta yarda da batun Sunusi, me ku ke tunani gaba, su Ayusha sun kulla mana tsiya.🥺



_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol