Free chapter · Read without an account

Page-44

by 🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚 🖋️ · “SANADIN ƘADDARATA”

*FASAHA WRITER'S ASSOCIATION*
     (*F.W.A)*©✍️
     ⭐⭐⭐

Ƙungiya masu aiki cikin salon hikima da fasaha gurin juya tunanin al-umma, kaifin alƙalumansu ya zarta takobi ©✍
___________________________________________________



بسم الله الرحمن الرحيم.
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد. 




❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁ 




Free book📓



By: _*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_




Page4️⃣4️⃣






Muryata ya fara fita da kuka ina cewa, "no, no Asmee, da gaske ne abun da na fito yi kenan" na faɗi ina komawa gurin Ayusha na ce, "ki faɗa mata ba abun da ya faru ba kenan? Ayusha ki faɗa mata don Allah".

Ba ta amsa min ba, sai shiru da ta yi haɗi da yun ƙasa da kai, ita kuwa Asma'u kallonta ta maida kan Sunusi, ta ce, "ka yi haƙuri da ƙin ɗaga wayarka da na yi, yanzu na gane komai" ta yi maganar tana share hawaye, murmushi kawai ya yi mata sannan ta wuce ko kallon inda na ke ba tai ba, da sauri na bi bayanta ina kiran sunanta da faɗin ta tsaya ta saurareni.

Ganin mun yi nisa Ayusha ta sheƙe da dariya Sunusi ya matso kusa da ita shima yana yi, su ka juya kallon juna. "Good job, man, ka yi shi fiye da yadda muka ka tsara, acting ya yi kyau!" Faɗin Ayusha cike da murna, Sunusi ya dara yana faɗin, "zan iya fiye da haka, indai akan abun da na ke muradi ne, musamman ma da ya zamana riba biyu na ke da shi, faɗa min yanzu Ayusha, yaushe ne zan ji alert 'yan mata?".

"Angaya maka ni wawuya ce da zan ba ka kuɗi bayan kaima akwai ribarka a cikin harkar?" Ta yi maganar daga zuciyarta, sai kuma ta yi murmushi ta ce a fili, "Don't worry, zan tura maka kuɗinka, but now ya kamata na je a ƙarashe toya wainar akan idona, za mu yi waya" ta faɗi tana wucewa, shima Sunusi juyawa ya yi ransa fal farin ciki.....

Kama hannun Asma'u na samu damar yi ina faɗin, "my sister, don't do that, ki tsaya ki saurareni in sanar da ke cikakken abun da ya faru, ba yadda ki ka fahimta ba ne Asmee, taya ni zan aikata haka? Ba zai taɓa yiuwa ba", fincike hannunta ta yi da karfi ta juyo tana yi min kallon da ban taɓa ganin ta yiwa wani ba bare ni, "wani abu ne ya rage ban gani ba Nuriyyah? Me za ki sanar da ni bayan wanda kunnuwana su ka jiye min?".

Ta faɗi tana share ƙwallan kan fiskarta, ta cigaba da cewa, "na yi mamaki, na yi matuƙar mamaki Nuriyyah, kawai abun da na ke buƙatar ji daga gareki bai wuce sanin, me yasa ki ka shigo cikin familynmu ba, Menene nufinki à cikinta? Na yarda da Mama, sannan na yarda da su Anty Rumaisa, duk zantukan da su ke faɗa akanki gaskiya ne! Me yasa ni da su Momy duk ba mu ankara ba?".

Hawayen da su ka cika à idona fal su ka kuma gangarowa a karo na babu adadi, kalaman Asma'u kamar garwashi su ke saukar min cikin ƙirji, "ki sanar da ni gaskiyar me yasa ki ke son auren yayana Abba? Ko shima so ki ke kawai ki mori gangar jikinsa ba zuciyarsa ba?" Rintse idona na yi da ƙarfi na 'yan seconds, ka na buɗesu sun ja sosai, ba su daina aikin fitar ruwan da su ke ba.

Wannan kalmar ta taɓa min zuciyata sosai, cikin murya raunanne da kuma sake son nusar da Asma'u gaskiya, na ce, "Asmee kin san ba halina ba ne, ni ba zan taɓa aikatawa ba, tun da mu ke da ke na taɓa kwatanta makamancin hakan? Kada ki manta tsawon lokacin da mu ka yi a tare, shaƙuwar da mu ka yi da ke kaɗai, ya isa yasa ki yi shaidana ako ina, don Allah kar 'yan kalaman Sunusi su sauya miki tunani akaina Asmee, kada kiyi min mummunar fahimta rana ɗaya ba tare da bincike ba".

"Da ba ni na ji komai ba, tabbas ba zan taɓa yarda da Nuriyyah wacche iyayena su ka ɗauka a matsayin 'ya, tana da wa'yan nan halayyar ba, babu abun da Momy ba ta yi miki ba, ta canza miki rayuwa, da yanzu ba ki san ina kanki ya ke ba, iyayena sun tufatar da ke, sun ciyar da ke, sun baki rayuwa kamar kina gidanku, sun miki gatar da ba wanda ya miki, amma à ƙarshe ashe kina da abubuwan da ki ke son sa ka musu da shi, kin nuna cewa, maganar hausawa na tsintacciyar mage ba ta mage gaskiya ce, kin zama butulu mai rama sharri da alkhairi, me yasa ma na yarda da ke? Na yi dana sani Nuriyyah!!"

Tana kaiwa ƙarshe ta shige cikin gidan, ƙafafuna sun yi min nauyi, na saki jiki na yi ƙasa, kalamanta na min yawo a saman kaina, kuka matsananci na fara rerawa babu ƙaƙƙautawa, Sunusi ya jefani cikin makircinsa da fitar da kaina zai yi wuya a wannan lokacin, ya zan yi in fahimtar da kowa ƙarya ya ke min? Wa zai yarda da ni?.

Na haɗe ƙafafuna na sa kai na a ciki ina cigaba da kuka, Asma'u 'yar uwata ita ce ta faɗa min kalaman nan masu kama da zafin wuta?. Ina a haka sai ga Ayusha ta iso gurin, ban san da zuwanta ba kasancewar kaina ba a ɗage ya ke ba, ita kuwa dariya ne ya so kufce mata saboda murna, 'farko kenan, ki jira hukunci na gaba' ta faɗi cikin ranta.

Asma'u na shiga ɗaki ta rufo ƙofa, ta isa kan gado ta faɗa kai tana kuka sosai. "Me yasa za ki saka mana da haka? Me mu ka yi miki?" Ta ke tambayar kanta da kuma fashewa da kuka sosai, "Asma'u a wannan lokacin ba kuka ba ne abin yi, ya kamata ki je ki sanarwa da kowa a gidan nan ya san waye ita, ya kamata kowa ya gane mayafin sharrin da ta ke da shi" cewar Ayusha da ta shigo har da dafata, fiskarta na nuna ta damu da Asma'u. Sassauta kukan ta yi ta ce, "don Allah ki fita a ɗakin nan Ayusha, ba na buƙatar kowa yanzu".

Ayusha na shirin magana Asma'u ta sake cewa, "don Allah ki fita!" Ba musu ta juya, fiskarta ya cika da haushi, ita yanzu ta so ƙwan ya fashe, amma wai har Asma'u na ce mata ta fice daga ɗakinsu cikin ɗagun murya? Ta juya ta dubeta sai kuka ta ke yi ta manne da filo, Ayusha ta yi murmushin mugunta tana cewa a hankali ta yadda Asma'u ba za ta ji ta ba, "cry as much as you want, ni dai kawai ki biya min buƙata, zan barki yau amma gobe tabbas sai na saki kin sanar da kowa!". Sannan ta fice a ɗakin.

Na ɗau lokaci a haka ba wanda ya ganni daga cikin gida, a ƙarshe dai na miƙe ina jan hanci, har yanzu ƙullutun da ya ke cikin zuciyata yana nan tamkar yanzu komai ya faru, sai da na share hawayena sannan na doshi cikin gidan.

Da Wasila na ci karo, tsayawa ta yi tana dubana da kyau, ita ba ta gane min ni da Asma'u ba tun jiya, ga shi ba wanda ya sanar da ita me ya faru, kafin ta ce komai na sakar mata da murmushin dole kawai na wuce. Da kallo ta bini haɗi da mamaki ta ga alamar kuka a tattare da ni, ba ta bini ba don ta lura ba ma son ta san komai.

A hankali na tura ƙofa na shiga cikin ɗakin, kasancewar yau asabar ba makaranta, sai zuwa monday kuma za mu fara semester exams na shekara ta uku. Daga ƙofa na tsaya ina kallon Asma'u da ke kwance kan gado, kauda kaina na yi na nufi toilet na shiga, a ƙasa na zube wasu sabbin hawaye na fitowa daga cikin idanuwana, na ɗau lokaci a ciki daga bisani na fito.

Ranar gaba ɗaya Asma'u ba ta ce min ko kici kanki ba, ko da na yi mata magana ba ta tanka min, sai dai ta yi kamar ba ta ji ni ba, ina jinta lokacin da ta ke waya da Sunusi ko a jikinta. Domin magan-ganuna ta riga da ta koresu shara. Iya ƙoƙari na yi don kada Momy ta fiskanci wani abun, amma ta lura, domin ganin rashin walwala daga ni har Asma'un, ta tambayeni me ya ke faruwa, amma na ce mata kawai tunanin exam ne mu ke yi, shiyasa ko wannenmu ya ke a haka, ba don ta yarda ba ta yi shiru....

SADIYA. 

Tun tana ƙoƙarin yin ihu har muryarta ya dusashe, ga warin gass da ya gama cika ko ina a ciki, har numfashinta ta ke jin yana neman rabuwa da gangar jikinta, dama ba lafiya ta ke da shi ba, ai sai abu ya haɗe mata goma da ashirin. Takawa ta yi ta nufi gefen window da ƙyar tana ƙoƙarin rufe hancinta, kuka ta ke yi marar ƙara don ba muryar kukan ma. 

Hannu ta sa ta fara buɗe window, ba ta kaiga buɗesa sosai ba, sanadiyyar kanta da ya sara mata, ta fara ganin kitchen ɗin na juye mata. Ƙarshe zubewa ta yi kan tayis tana fitar da numfashi da ƙyar idanuwanta na juyawa, sai hawayen da su ke ta gudun fitowa......

Nusaiba na zaune babu abun da ya yi mata zafi, hansakalinta ya kai kan wayarta da ke ƙara kasancewar sautin da ke tashi ba ta ji ba, ɗaga wayar ta yi bayan ta shiga uwaɗɗaka ta toshe kunnenta ɗaya, Iya da ta kira a wayar ta ke sanar da ita ta aiko mata da magani, ta faɗi mata inda za ta je ta amsa.

Ta sauke wayar tun kafin Iya ta gama tambayarta sautin da ke tashi, ta ja mayafinta da jakarta ta fice, tana murmushin jin daɗi ƙila dawowarta sai dai ta tadda gawar Sadiya, yanzun ma kamar za ta je ta leƙa sai kuma ta fasa......

Da fitar Nusaiba ba à jima ba sai ga Faruq ya yi parking a ƙofar gidan ya dawo, bayan ya sauka daga motar ya shigo gidan da sallama, dama wasu takardun da zai tafi da su ya manta ya zo ɗauka. A company har an fara lura da canjin yanayinsa, baya maida hankali akan aikinsa, ga shi da ya zauna sai tagumi da tunani, ko antambayeshi sai ya ce ba komai, sai ga shi yau ya tafi ya manta wasu files masu mahimmanci, kafin ya dawo ɗauka sai da ogansa ya yi masa faɗa sosai, har ya ke ce masa idan ya daina son aikin ne yanzu ya bar company mana. 

Ƙarar kiɗan da ya fara ji daga waje ne ya shigo ya tarar ashe a cikin gidansa ne, da sauri ya nufi gurin MP ya kashesa, sai kuma ya tuna kar dai Nusaiba ce ta kunna don tana so, shi kuma ya kashe mata. Shiga ɗakin ya yi yana kiran sunanta, "Nusaiba, Nusaiba" sai dai shiru ba ma ta ciki, sauke nannauyar numfashi ya yi har da zama kan kujera yana ajiyar zuci, sai dai ya rasa me yasa zuciyarsa ya ke tsananta bugu a halin yanzu.

Gaba ɗaya ransa ba daɗi, miƙewa ya yi ya nufi inda ya ijje takardun, don ba ya son Nusaiba ta dawo ta same shi, ƙila ta sashi yin wani abun ya kuma sake samun matsala a gurin company, gashi ana jiransa daman. Ƙishin ruwa ya ji hakan yasa ya nufi fridge, sai dai bai tadda komai a ciki ba, ya yi mamaki da komai da ke ciki ya ƙare, ko ruwa babu à ciki.

Ya fito zai je kitchen ya san ba za a rasa ba a ciki, inyaso ko na fanfo sai ya sha. Sadiya na kwance ta gama sallamar da yau ce ranar tafiyarta zuwa ga mahaliccinta, sai ambatan kalmar shahada ta ke yi a cikin ranta, idanuwanta a rufe, ƙwaƙwalwarta sai juyi ya ke mata. Faruq ya kusa dap ƙofar kitchen aka kirawo wayarsa, ya dakata haɗi da ciro wayar daga aljihu ya amsa.

Daga can ogansa ya ke yi masa masifa, mutanen hallara takardun kaɗai ake jira. Haƙuri Faruq ya bada da cewa yanzun nan yana kan kawo musu insha Allah, da haka ya kashe wayar ya bar zuwa kitchen ya juya zai koma.

Da ƙyar ta samu damar buɗe bakinta da ya yi mata nauyi, jin kamar muryar mijinta a kusa, ta ce, "Faruq! Faa... Faruq! A... taimaka...min". Cak Faruq da ya juya bai kai ga wani taku ba ya tsaya, sakamakon jin da ya yi kamar wani sauti ya fito daga wani guri, wanda bai gama gane wani sauti ba ne. Da sauri ya juyo yana zagaye gurin da kallo. Sadiya dai tun da ta samu damar wannan furucin komai ya ɗauke mata gaba ɗaya, kunnuwanta su ka yi dum.

Yana kan kallon gurin nan sai kuma ya fara jin wani irin wari mai kama da na gass cikin hancinsa, zare ido ya yi ya fara kiran sunan Sadiya, a tunaninsa tana cikin ɗaki kuma ta bar gass a buɗe, zai je ɗakinta ya kirata amma ya yi tunanin gwara ya yi saurin kulle gass ɗin nan don babban hatsari ne sosai.

Da mamaki ya ke bin ƙofar kitchen ɗin da kallo ganin anrufeshi ta waje, tunanin inda key ɗin ya ke ya yi, ya juya ya nufi ɗakin Sadiya tun da ita ce ke amfani da kitchen ɗin, amma bai ganta ba, a ɗakin na ta ya ijje takardun sannan ya fito, domin ba zai tsaya wani ɓata lokaci ba don ya ji warin sosai bayan ya isa wurin.

Ƙarfinsa ya sa gaba ɗaya yana bangaje ƙofar, ya ja da baya sannan ya dawo da ƙarfi, sai da ya yi kusan sau bakwai sannan ya samu ƙofar ya buɗe, don ya ji jiki sosai, amma kasancewar ba zai iya haƙura da bari haka ba yasa ya dage, ƙofar na buɗewa sai da ya yi saurin rintse ido haɗi da toshe hanci, saboda yadda warin ya daki hancinsa sosai, a hankali ya buɗe idanuwansa, ya nufi gurin gass da dauriya, jin sa ya yi ya ƙi rufuwa, ya dai yi dabara ya samu ya rufe.

Miƙewa ya yi ya juya zai wuce domin ba zai yu ya tsaya a wannan wurin ba. Kwatsam idanuwansa su ka sauka kan Sadiya da ke kwance kamar gawa. Wani irin sautin rugugi ya sauka kan zuciyarsa, ya fiddo idanu sosai......

SU BAABA.

Bayan sun koma sashinsu, suna zaune dukkansu a ɗakin Baabar, Aisha ce ta fara cewa, "kun gani ko Baaba? Wallahi Anty Sadiya mace ce mai hankali da tarbiya, sannan da sanin ya kamata, Baaba maganar Malam gaskiya ne, yanzu ku ga yadda Anty Nusaiba ta mareki kamar ke ba babba ba ce akanta, ta tozartaki, ta kuma nuna miki asalin kammaninta, amma me anry Sadiya ta yi? Ta kareki, ta nuna ke tamkar uwa ki ke a gareta, Baaba tun da na zauna da Anty Sadiya ko sau ɗaya ban ga wani abun kushewa daga gareta ba, kun ma san me? Ita che wacche ta tilasta yaya Faruq ya dawo kusa da mu".

Dukkansu su ka juya suna kallon Aisha cikin mamaki, girgiza musu kai ta yi ta kuma cewa, "eh ƙwarai yaya Faruq da kansa ya faɗa min wani lokaci, duk da baya so amma ta nuna masa ku ne mafi mahimmaci a rayuwarsa, Anty Sadiya tana ɗaya daga cikin matan da ke kallon ahalin mijinta tamkar na ta, ita ce wacche ta ke nuna wa mijinta darajar ahalainsa fiye da komai a rayuwarsa, amma Baaba ko da yaushe ku tsanarta shine abun da ya rufe muku ido".

Kalaman Aishaba wanda bai shegewa jiki ba,, hawayen da ya gangarowa Baaba ta share, cikin muryar da na sani ta ce, "gaba ɗaya kalamanki gaskiya ne Aisha, yau na ƙara tabbatar da hakan, Sadiya mace ta gari ce sannan 'ya ta gari, wallahi na yi dana senin duk abubuwan da na yi mata, Nusaiba da na ke ganin ita che alkhairi a rayuwar ɗana, wacche na ke ganin ta fi dacewa da shi, yau ita che ta ɗaga hannunta babu kunya babu tsoron Allah ta kifa min mari, ta ke kallona marar daraja a idonta. Amma ga Sadiya duk abun da na yi mata ba ta taɓa tsanata ba".

Baaba na kaiwa ƙarshe ta fashe da kuka, suma gaba ɗaya su Lantana kukan su ka sa sosai, Lantana ta ce, "na yiwa Sadiya abubuwa da dama amma ba ta taɓa ce min komai ba, ko kallon banza Sadiya ba ta taɓa yi min ba" Fatima ta ce, "a matsayinmu na ƙannen mijinta mun faɗa mata kalamai munana, ko Anty ba ma ce mata saboda ba mu ɗauketa hakan ba, amma ko sau ɗaya ba ta taɓa tanka mana ba, duk da kuwa za ta iya ta ka mana birki, hasalima sai dai ko da yaya Faruq ya so faɗa mana magana, ko kuma yunƙurin duka, ta ke tausansa da roƙan ya ƙyalemu, mun kirata da suna juya ga shi mu har yanzu ko saurayi ba mu da shi, duk samarinmu sun tafi kamar korasu mu ka yi".

Tana kaiwa ƙarshe su ka sake fashewa da kuka, hatta Aisha abun da ta ke yi kenan. "Yafiyarta ya kamata ku nema ba wai ku tsaya kuna yin wannan kukan ba" su ka ji muryar Malam da ya shigo yana kallonsu, ya kuma cewa, "kamar yadda ku ka san ita yarinyar kirki ce, tabbas na san idan kuka nemi yafiyarta za ta yafe muku, saboda haka kada ku ɓata lokaci, ku je yanzu ku roƙeta".

Baaba ta miƙe ta ce, "haka ne, za mu je dukkanmu mu nemi yafiyarta, Sadiya 'yar albarka mun cutar da ke da yawa" Badiyya ta ce, "Allah yasa ta yafe mana" nan su ka kama hanya gaba ɗayansu zuwa sashin Sadiya......

Bakin Faruq ya fara girgiza ya buɗe da ƙarfi ya furta, "Sadiyaaaaa!!!" Da wani irin sauri ya isa gareta haɗi da ɗaga kanta zuwa cinyarsa, ya fara jijjigata cikin tashin hankalin da bai taɓa shiga ba, ambatan sunanta ya ke yi da ƙarfi.

Take hawaye ya fara rige-rige akan fiskarsa. Cikin ruɗewa ya ke faɗin, "my dear! My dear ki buɗe idonki, me ya sameki? Matata ki buɗe ki ce min wani abu don Allah", sai dai Sadiya ko motsi ba ta yi sai ma jikinta da ya saki. Ɗagata ya yi ya fito da ita daga cikin kitchen yana nufar ƙofar gida, don ya kaita asibiti da hanzari, gaba ɗaya jikinsa har rawa ya ke yi.

Nusaiba na shirin shiga kenan ta ga Faruq ya yo ƙofar gida hannunsa riƙe da Sadiya, dimm diim! Ƙarar da ya shiga zuciyarta, ta saki ledar maganin da ta riƙo à hannu ya faɗi ƙasa, ta zare ido tana kallonsa har da sakin baki. 


Last page
___________________________________________________


Hmmm ni yau har bakina ya maƙale, kuna ganin Asma'u za ta faɗi abun ya faru wa su Momy? To Ayusha dai ta ce za ta sa ta.

Ga Sadiya kuma, me ku ka yi tunani akanta? Baaba sun gane gaskiya, anya lokaci bai ƙure musu ba? Ga Faruq fa kamar hankalin ya ɗan waro, tun da yau ya kirata da dear.

Ya Halima ne kam? Shin ta samu damar isa gida ko ƙa ƙa?

Mu kasance a next page don jin yadda za ta kaya.




 _*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol