Free chapter · Read without an account

PAGE _______25 & 26

by SultyWrites · BLOOD CROWN (THE HEIRS APPARENT)




"You are a big liar Nazbeer, sure I will fire you".......Jikin Nazbeer ɗin ne ya fara rawa ya shiga rantse rantse kan maganar daya faɗa gsky ce, Bai saurare shi ba yai picking call ɗin yana faɗin, "hello My Ninie........"

"Salamu alaikum".......... Muryar wani namiji ta doki dodon kunnen sa .

" Wa alaikum Salam, Ina m......"...........Katseshi akayi ta hanyar faɗin, "Amjad?".

"Yeah"..........Ya amsa cikin ƙarfin hali tare da fargabar jin abinda zai biyo baya.

"Da ALLAH muna san ganin ka yanzu a general hospital, saboda me wayar tayi hatsari Kuma ta bamu number ka ta buqaci a kira mata kai ".

"Tana Ina yanzu ?"..........."Sai kazo dai".

"Ina kofar emergency ɗin "..........Ya bashi amsa.

"Okay bari nazo na shigo dakai"............ Mutumin ya faɗa tare da kashe wayar , kallon Nazbeer da yayi tsuru tsuru yayi sai Kuma ya ɗauke Kai ba tare da yace komai ba. Fitowan da wani Dr yayi ya sanya jami'an tsaron da suka zo tare da ambulance ɗin tasowa suna tambayar, "Ya ake ciki Dr?".

" Da sauki muna kan aiki ne".......... Ya ƙarashe Yana kallon Amjad da mamaki ya ce, "Ranka ya dade dama Kai ne"............Kai ya ɗaga masa kawai alamar eh.

Nasan Kuna cike da mamakin yadda ake girmama Amjad a ko Ina ko? To bashi kaɗai ba dukkan ya'yan Hashim Darwin girman da ake basu daban ne a faɗin duniya ba ma a ƙasar Nifaz kaɗai ba, Amma kuma girmamawar da ake bawa Amjad tafi ta sauran saboda Alhaji Hashim yafi nuna shi a idon duniya, kowa kuma ya shaida cewa ya fi kusanci dashi, Dan akwai inda in su Awais suka shiga ba a san fuskarsu ba matsayin ya'yan Hashim Darwin, Amma Amjad ko yaro ƙaramin ya san sunansa da kuma fuskarsa.

"Bismillah muje"........... Dr ya faɗa yana komawa ciki, bin bayansa Amjad yayi suka wuce ciki har zuwa ɗakin da Nayrah ɗin take, tun daga bakin Ƙofar da ya hango ta yaji jijiyoyin jikinsa sun mimmiqe, Nayrah ɗinsa ce ta dawo haka a ƙasa da hour ɗaya, lalle ALLAH me yadda ya so da bawan sa ne, daidai da taku ɗaya in ALLAH bai nufa ba baza kayi shi ba whl. 

Cikin dakiya ya Ƙarasa gaban gadon, idanunta biyu sai binsa take da wani irin kallo me taɓa zuciya hawaye ne ya cika idanun nata, da sauri ya girgiza mata Kai tare da riqo hannunta ba tare da ya ma sani ba, ya ce "Ninie......!"

Tare shi tayi da muryar dake nuna mai ita na cikin tsananin yanayi na rashin lpy ta ce, "Amour ashe zakazo gareni, Amour please let me die with my dream come true........" Shuru tayi tare da jan numfashi daƙyar ta ce, "I want to be your wife even if it means it's the last thing I do in this world, Amour wlh duk abinda na faɗa ƙarya ne ba daga zuciyata yake ba, ji nake kamar mutuw........." Saurin rufe mata baki yayi yana mai girgiza mata Kai, Wanda hakan yasa ta lumshe idanun ta har hakan ya bawa hawayen da ya taru a kwarmin idanun nata damar sauqowa. Dariyar ƙarfin hali yayi dan kana kallo kasan iya fatar baki ta tsaya saboda yadda idanunsa suka sauya, jijiyoyin kansa sun fito sunyi rada rada. " Nayrah!"...........Slowly ta buɗe idanunta ta sauke a kansa .

"Kin amince da aure na a duk yadda nake da Kuma yadda zaki sameni a gaba?"........... lumshe idanunta tayi ta buɗe alamar eh.

"Kin shirya fuskantar duk qalubalen dake tattare da kasancewa tare dani?"............ Nan ma da confidence ɗinta ta ɗaga masa Kai.

"Zaki iya zama dani ko da kuwa baki sameni a yadda kike tunani ba?".

"Zan iya kasancewa dakai a duk yadda kake Amour, ko da duk duniya kuwa zasu juya ma baya ni Ina tare dakai har iya karshen rayuwata"............ta faɗa dakyar muryanta na seizing, wasu doctors ne suka iso wurin gadon tare da Dr ɗin farko wanda ya shigo dashi, matsawa Amjad ɗin yayi ya basu wuri amma still hannunta na cikin nasa, examining ɗinta sukayi kafin su janyo cylinder oxygen suka saita suka maqala mata saboda ganin numfashinta yana sake yin qasa. Idanunta a Kansa hannun ta cikin nasa har Drs' ɗin suka gama abinda yankamata sannan suka matsa gadon dake gaba.

Wani zazzafan numfashi ya furzar kafin ya ce, "Ninie na miki alqawarin gobe za'a ɗauramin aure dake in sha ALLAH, I'm ready na fuskanci kowacce irin matsala ce in dai hakan zai faranta Miki".......... murmushin karfin hali ta masa yayinda shi kuma ya sanya hannu ya goge mata hawayen dake gefe da gefen idanunta ya juya da niyyar fita, Mumu da Dad ne suka sawo kai a rikice, ganin Amjad a wurin ya sake hassala Dad. "Touu ai sai kace min Kai ne ummal kabaisin ɗin da ke son kashemin ya', Wai bama nace Maka karka Ƙara zuwa inda ya'ta take ba. Okay Bama wannan ba wato bayan ta shaida ma gobe za'a ɗaura mata aure shi ne kabi ta ƙarƙashin ƙasa ka sa aka kashe yaron mutane ko? Kana tunanin baza a gano ka bane?"...........Kallon dad yake kawai kamar ya samu wani TV yayinda ita Kuma Nayrah idonta yana kansa ne, addu'ar ta ALLAH yasa Kar Amjad ya buɗi baki yace wani Abu, dan tasan tabbas ba dan Dad bane da babu wanda ya isa ya matso inda yake ballatana har ya tsaya gaban sa ya gaya masa magana haka ba taunawa.

Saida yayi namijin ƙoƙari wurin saita kansa, ba tare da yabi ta kan Maganar Dad ɗin ba ya ce, "Dad Ina roqon alfarma wurinka, Ina so gobe a ɗauramin aure da Nayrah".

"Wanna alfarma kake nema ko Kuma sanar dani kakeyi ubana, to bana aurawa ya'ta wanted criminal Kuma dan iska me lalata ya'yan mutane, Abu na karshe shi ne ka fita harkar ya'ta na shaida ma na ƙara"........... Sauke ido ƙasa Amjad yayi zuciyar sa na wani irin ƙuna kamar zata kama da wuta, ɗagowa yayi da niyyar maida masa wanna martanin idon sa ya sauka cikin na Nayrah dake kuka Marar sauti, ga majinyata duk hankalinsu ya dawo kan su da sauri ya juya ya fita yana taku cikin butsuwa kamar ba abinda ya dameshi.

"Duk inda zakaje hukuma saita kamoka, In kuna ji da kuɗi da matsayi shi ma ubansa wani ne ai kuma bazai Barka ba". 

"Alhaji ka rage murya Dan ALLAH, ka fara duba halin da yarka take ciki mana haba".

" Rabu dani kinji, ku in aka biya taku baza ku kwaci yancin kanku ba"........... Dr ne ya dawo wurin su yana fadin, "Haba ranka ya daɗe kai fa babba ne hakan bai kamata ba, ko ba komai ai ka bari in kunje gida ku tattauna saboda nan ɗin wuri ne na jinya a dinga ɗan rage murya". Shuru Dad yayi tare da jan kwafa.

_____________Ko da ya fita wurin motar sa ya wuce su Kamal zasu bishi yace ba tafiya zaiyi ba su jira anan. Wayar sa ya dauko yayi wasu yan latse latse sannan ya kashe, idon sa akan harabar asibitin, ba'a fi 2 minutes ba wayar ta fara ringing, ɗagawa yayi da tambayar, "Kaga saqon?"............ Bansan me akace a ɗaya bangaren ba ya sake faɗin, "Ina son nan da hour uku a gama komai"......... Shuru yayi Yana sauraran me maganar can Kuma ya ce, "Eh ka faɗa mata, zuwa anjima ma ai zan shiga wurin nasu"............Shuru ya sake yi kafin ya ce, "in kaje ka kirani zan haɗasu"...........daga haka ya kashe wayar tare da juyawa da niyyar komawa ciki yaga giftawar mutum ta bayan motar tasa, tsayawa yayi jim kamar me tunani ganin kamar laɓe aka masa, can Kuma ya ɗaga ƙafa ya wuce cikin asibitin.



-------------------------√




Bayan ta kai Shazen waje tayi fitsari suka koma cikin asibitin, dube dube ta fara amma bata hango Sahnish ba, wucewa tayi wurin da ta bar Sahnish ɗin zaune inda ta ga wani mutum a maimakon sa, "Salamu alaikum bawan ALLAH da ALLAH ko kaga inda saurayin dake zaune a wurin nan yayi?"........... "Kamar yabi bayan ku ai". Mutumin ya faɗa yana miqewa ya wuce ciki.

"Okay" .......... Ta faɗa tare da juyawa da sauri, Dad dake tsaye a daf dasu yana waya sai surfa ruwan masifa yake ko shi da waye oho ya juyo tare da bin bayan Hushaima da kallo yana me kashe kiran ya zura wayar a aljihu. 

Waje ta nufa kamar wadda hankalin ta baya jikinta, saboda bata san inda Sahnish ya tafi Neman su ba, ga shi bashi da lpy Kuma, ko lura batayi ba da Amjad ta bigi kafaɗar sa zata wuce juyowa tayi shima ya ɗago, kallo ɗaya ya mata ya wucewar sa kamar ba abinda ya faru, ganin ya wuce yasa itama jan hannun Shazeen sukayi waje da sauri, a nan ta samu Sahnish ɗin tsaye yana kalle kalle da alama neman ta inda zasu fito yake. "Har ka tsorata ni whl Kai da baka da lpy Kuma ka fito nan ka tsaya bayan na barka a ciki, ko so kake sauron asibitin ya sake tara ma gajiya".

"To ai naga daga cewa bari ki rakata fitsari kinje kun zauna, ni Kuma na gaji da zaman ne whl tun 4 fa muke nan".

"To ya za'ayi Sahnish babu ce tasa, muje kawai Ina ledar magungunan"?".

"Gasu a hannu na"........... Ya faɗa yana ɗaga mata su, Har sun fara tafiya taja ta tsaya kamar wadda tayi mantuwa tare da juyawa da sauri ta sake kallon ƙofar shiga asibitin saboda fuskar Amjad ɗin da tayi flashing a ƙwaƙwalwarta sai taga ya mata kama da wani wanda ta sani amma kuma ta kasa tuna a ina. "Lpy?". Sahnish ya tambaya shima yana bin inda take kallo ɗin . Girgiza Kai tayi alamar ba komai taja hannun Shazeen sukayi gaba, ba wanda ya ƙara cewa komai har suka tari Abun hawa suka hau, shi dai Sahnish binta kawai yake dan yasan duk kuɗin hannun su ya Kare.

A kofar gidan ya sauke su, sauka sukayi Hushaima ta ce, " Barin shiga in ɗauko ma kudin".......... Da " To". ya amsa sannan suka wuce ciki. " A ina zamu ɗauko kudin?".

"Kaga ka wuce ka kwanta kawai karka Ƙara tambayata inda zan samo, ka barni da zafin da kaina keyi Dan ALLAH".

" ALLAH ya baki hakuri , Saida safe ".......... Ya faɗa yana wucewa ɗakin sa, itama ta wuce nasu ta rufo ƙofarta kamar bata ajje me tuktuk a waje ba .

Mai tuk tuk kuwa Jin shuru ya sashi kutsawa cikin gidan, "Gafaran ku dai". Ya faɗa saboda ganin yanayin mutanan gidan yasan irin wannan sallamar ce daidai dasu dake shi ma ɗin ɗan kwalta ne.

"Ya akayi ne malam zaka shigowa mutane gida kai tsaye?"............Yar Charas ta faɗa tana aika masa da saqon harara ganin kayan dake jikinsa da kuma takalmin ƙafarsa.

" Eh wata mata nake jira, tace na jirata ta kawomin kuɗi na kuma naji shuru".

"Kaga ƙofar ɗakin ta can, matsa daga can dan ALLAH Karka gurɓata mana iskar muhalli"............. Faɗin Shamsy dan daudu dake zaune tsakiyar yam matan gidan yana kwalliya kamar wata mace. Me tuktuk bai ce dashi komai ba ya wuce zuwa ƙofar ɗakin Hushaima da suka nuna masa tare da ƙwanƙwasawa . "Malam ka saki jiki ka buga sosai, yanzu saita iya manna ma hauka tace bacci take".......... Wata dattijuwa dake barar gyada ta faɗa.

Jin bugu kamar zaya ɓalle mata ƙofar ɗaka ya sata tattare sauran kuɗaɗen su data haɗa ta ɗaga ƙasan katifa ta sa sannan ta tashi ta fito tana shan mur ta ce, " Ya akayi?".

"Bangane ya akayi ba, kuɗi na malama"..........Ya Ƙarashe yana miqa mata hannu.

"Ka bani ajiya ne da zaka zo karba"..........Ta faɗa tana watsa masa wani wulakantaccen kallo.

"Ke da ALLAH karki nemi raina min hankali mana, ki fito min da kuɗi na kawai ".

Wani dan iskan murmushin gefen baki tayi tana wani abu da haƙori qiii qiii ta ce, " Ai kudi ya ciwu, da hannu na kuma bana baka kuɗi, to wai ma tsaya su wanda kakewa aikin a banza kake musu ne da har kake miqe jijiyoyin wuya akan kuɗin da bai wuce dubu ɗaya ba".

"Ahhh kamar yaya? Ke bar ganin fa kina taƙama da bariki nima ita ta raine ni whl zan zabga Miki rashin mutunci ban kuɗina dan durun uwarki" ......... Ya faɗa a fusace.

Kallon sa tayi cikin ido sannan ta ɗaga kai ta dubi mutanan dake tsakar gidan cikin ɗaga murya ta ce, "ku rufe ƙofofin gidan nan kuzo kuyi aikin ALLAH". 

Dan ja baya yayi da faɗin, "Kamar ya a rufe ƙofar gida, me kike nufi ne?".

"kamar ya a rufe Miki ƙofa, ki Bashi kuɗinsa in zaki bashi ya wuce kawai".......... Aunty Barma ta faɗa tana watsa mata kallon ƙasan ido.

Ba tare da tabi ta kan maganar aunty Barma ba ta ce, "Tun ban tona ma asiri ba kaja tsumman ƙafafuwanka ka fice a gidan nan dan whl Ni dai nafi karfin duk wani me sharri da qulunboto"..........Ƙwafa yaja ba tare da wani tunani ba ya ce, "Zanje amma kuma zan dawo, kuma saikin bada kuɗin nan, dan baza ki cinye min kuɗi ba kuma ki ce zaki nunamin isa da gadara"........... Ya faɗa yana juyawa ya fice, girgiza kanta kawai tayi tana binsa da wani irin kallo da ita kaɗai tasan ma'anar sa kafin ta juya ta shige ɗaki zuciyarta cike da saƙe saƙe.

 Nan fa aka juye hirar zuwa kan Hushaima dan dama duk gidan haushin ta suke ji in ka cire baba ilerika, kawu garba da Kuma Jey da dama shi Babu ruwan sa da sabgar kowa.

Ba'a rufa minti talatin ba sai ga me tuk tuk ɗin nan ya dawo da gangin yan daba kamar wanda zasu je fada da wasu group ɗin, wai nan duk mutum ɗaya aka ɗaibowa, kana ganin su kasan ba'a cikin nutsuwar su suke ba, duk sunsha sunyi makil, kowannen su daga me sanda sai me adda sai haɗa hanya suke kamar igiyar Lipton. Da gudu mutanan gidan dake waje suka shigo ciki, suma na cikin basu tsaya tambayar ba'asi ba suka ara ana kare sai ɗaki har suna gware da juna , Jey da ya kawo Kai da niyyar leqowa yaga meke faruwa jin Ife Ife da kuma ƙarar guje guje amma tozali da yayi da gangin yan daban da suka danno Kai ya sashi komawa da baya, kafin kace me tsakar gidan kamar an share shi, daga masu leqe ta window sai ta ramin ƙofa. 

Ba ƙaramin tashi hankalin Sahnish ya tsinci kansa a ciki ba ganin abinda ke shirin faruwa, buɗe ƙofa yayi ya fito tare da tare me tuk tuk ɗin nan ya shiga bashi haƙuri, "Malam dan ALLAH kayi hakuri, whl za'a biyaka kuɗin ka, kuɗin ne babu a hannun mu amma ko wani abu ne za'a Saida a biyaka ".

"Shi ne?"......... Ɗaya daga cikin yan daban dake karkace kamar bishiyar kuka ya tambaya yana kallon Sahnish.

"Bashi bane ƙanwar sa ce, itace fitsararriyar........" Bai gama magana ba Hushaima ta buɗe ƙofa ta fito tana hamma, "Uban waye yake son hana mutane bacci cikin daren nan....... Au ashe Kai ne, su ne masu karɓa ma kuɗin kenan?"..........Ta faɗa tana nuna su da yatsun hannun ta biyu, ta riqe kugu tana musu kallon tara saura kwata.

"Hushaima da ALLAH ki koma ciki, wai miye haka kikeyi ne, kaga malam muje na samo kuɗin ka na baka".

A tsawace ta ce, "Kai da ALLAH dakata Ina zakaje kake wani firirita, tukunna ma uban wa ya baka damar fitowa daga ɗakin".

"Gsky Hushaima abinda kike bakya kyatawa ki basu hakuri m........" Bai karasa magana ba ta dallah masa wani mari, "Yaushe har kayi wayon da kasan me duniya take ciki da har zaka faɗamin abinda ya kamata inyi. Kai na dawo kanka, ka rantse dai bakasan rayuwarka ko? Kuma a dole dole sai kun amfana da jini na". 

"Ahhhh kai ba wata whl"...........Ɗaya daga ciki su ya faɗa yana daga addar sa ya kai mata sara, wani irin cafa tayi wa addar, runtse ido Sahnish yayi saboda yasan dole ta gifce hannu. Warto Addar tasa tayi tare da gyara mata riqo ta ce , "Haka ake riqe Adda malamai ashe dabar taku ma baku shirya ba kuka shigo, kallon kallo sukayi. Da addar ta nunasu tana faɗin, "Whl duk wanda baibar ƙofar ɗakin nan ba da wanna addar zan zubda jinin sa".

Baya baya ɗayan yayi yana shaqar wani abu a hanci rabinsa a duniyar mu rabin sa a duniyar bacci ya ce, "Karfa gwada mataaaa...kwarewar mu"......... Gorar dake hannun Wanda aka Kira da Karfa ya ɗaga da niyyar buga mata Sahnish yayi saurin shiga tsakiya suka kuwa sauke masa ita a gadon baya, wani irin ihu ya fasa Wanda ya tunzira Hushaima ji kake shafff ta tafi da naman hannun Wanda ya bugawa Sahnish gorar, ganin haka yasa suma suka rufar mata, rufe ido tayi tare da fara wasa da Addar hannunta ta kan me uwa da wabi cikin ƙasa da minti biyar ta zubar dasu gabaɗaya a ƙasa sai jini kake gani kawai yana tsartuwa . 

Da jan ƙafa kowannen su ya kwashi jiki ya fice, mai tuktuk ne na ƙarshe yana kokarin fita ta haɗa masa wani harbi da ƙafarta sai gashi ya koma ya zube, gabansa ta Ƙarasa tare da faɗin, " Su wa kakewa aiki kai kuma?"..........jikinsa ne ya ɗau rawa ya shiga roqon ta kan tayi hakuri ta barshi ya tafi.

"Ai ka riga ka makara, na baka dama kayi wasa da ita, dan haka ko ka faɗamin su wa kakewa aiki ko ka faɗawa hukuma, tukunna ma fara fito da abubuwan dake jikinka"........... Ta faɗa hannunta ɗaya riqe da kugu ta kafa bakin Addar a ƙasa, tabbas duk wanda ya kalla Hushaima a wannan lokacin sai ta bashi tsoro saboda yadda ta rikiɗe a lokaci guda .

Sai a lokacin Jey ya dawo duniyar mu kifta idanun sa yake kamar wanda yayi ƙarya girgiza kansa yayi tare da ƙarfin halin fitowa dan duk mutanan gidan sun qame a inda suke, ƙarasawa yayi wurinsu tare da taimakawa Sahnish ya miqe kallon Hushaima da har lokacin bata motsa ba ta tisa mai tuktuk a gaba, ya ce, "Ya fa ji ciwo".

Ba tare data dauke idonta akan me tuktuk ba a  fusace ta ce, " Ya mutu ma kowa ya huta, nagaji nace masa ya koma ɗaki yaqi, ba ruwan sa a wannan abun yaqi ji duk abinda ya sameshi shi ya juyo ba abinda ya shefe ni".

Da mamaki yace, "Eh?" . Saboda ganin ai duk abinda tayi saboda dukan da ya same sa ne amma take cewa ya mutu kowa ya huta.

"Eh din"......... Ta amsa still ba sassauci a tare da ita.

Baba ilerika ne ya shigo da sauri har yana ƙoƙarin kifawa ,jinin dake wurin yabi da kallo kafin ya maida kallon sa kan addar dake kafe a ƙasa da Kuma hannunta dake zubar da jini, ga me tuktuk jikinsa sai faman kerma yake daga inda yake tsugunne. "Subahanallahi Hushaima me ya faru? Ina Majalisa aka kirani anga gangin baqin yan daba sun shigo gidan Nan".

Kanta a sama take kallon sa, a daƙile ta ce, "To da kazo me zaka iya yi, loma ɗaya zasuyi dakai ko birbidi baza su bari ba".........maida Kallonta tayi kan me tuktuk, "Kai Karka ɓatamin lokaci ka fito da abinda ke jikinsa ko na raba kanka da gangar jikinka na rage mugun iri"..........Ta faɗa tana ɗaga Addar ta ɗaurata gefen wuyansa, da sauri Jey ya saki Sahnish ya matsa gabanta tare da sanya hannu ya fisge Addar daga hannunta, a fusace ta ɗago idonta ya sauka cikin na Jey sai kuma tayi da nata tana haɗiyar wani yawu. "Kai fito da abinda ke jikinka"..........Shi ma ya faɗa kamar yadda yaji tans faɗa ɗin.

"Ni na gaya muku bakomai a jikina, Dan ALLAH ku barni in tafi ".......... Wani kallon banza ya watsa masa kafin ya zaro wayarsa ya kira yan sanda, yana kashe kiran ya matsa ya sanya hannu a aljihun me tuktuk ɗin ya shiga caje shi, da sauri ya zaro hannun, mai ya tuna kuma sai ya maida tare da ɗauko wata leda cikin hanzari ya kunce ta in da tozali da wani farin kyalle, wani irin tashi tsikar jikinsa keyi tun ma kafin yaga abinda ke ciki saboda yadda kyallen ke jiqe da jini, yana budewa idonsa ya sauka kan kwayar idanu da kuma harshen Mutum, Runtse idanunsa yayi da ƙarfi yayin da Hushaima kuwa ta nufi mutumin nan gadan gadan cikin wani irin fusata, ba tare da ya buɗe ido ba ya sanya hannunsa ɗaya ya riqo tsintsiyar nata hannun. 

Salatin Baba ilerika yasa mutanan gidan suka fara leqowa har suka fito gabaɗaya ai suna gama sanin Meke faruwa suka rufarwa me tuktuk ɗin nan, duk ƙoƙarin Jey na ganin ya kwace shi ya ƙasa ga Hushaima da take neman kwacewa daga riqon ɗaya mata ga Sahnish kuma a zube a ƙasa.

Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da yaji jiniyar yan sanda, suna shigowa sukayi kan me tuktuk da mutanan gidan sukawa raga raga kamar kura taga nama, miqawa dan sanda ɗaya wannan kyallen jey yayi sannan ya sake musu bayanin abinda ya faru daga nan suka ɗauki me tuktuk sukayi waje dashi, sakin hannunta Jey yayi yabi bayan yan sandan, ita kuwa Hushaima ko kallon inda Sahnish yake batayi ba ta wuce ɗakinta tare da gabzo ƙofar.

Bai fi minti huɗu ba ya dawo cikin gidan inda ya samu mutanan gidan ana ta maida zance, wurin Sahnish ya wuce direct yana faɗin, "Baba ka taimaka min mu kai yaron nan asibiti Dan inaga kamar sun ji masa ciwo a shoulder ɗinsa " .

Baba ilerika da hankalinsa bai yi wurin Sahnish ba sam, ya nufo wurin da hanzari yana faɗin, "Subahanallahi Sahnish, ashsha ashe Kai tsautsayin ya faɗawa kuma, taimaka masa muje, kai rayuwar nan ta zama Abun tsoro"........... Da taimakon baba ilerika Jey ya kai Sahnish asibitin kusa dasu, ALLAH ya taƙaita babu karaya kawai buguwa ne, nan suka basu magungunan suka masa allurar pain reliever Sannan suka taho, a hanya Jey ya ce, "i think itama taji ciwo a hannu ku ƙarasa kawai, ni zan tsaya chemist na taho da Nurse da zaiyi treating hannun nata".

"To ba damuwa Jawaad ALLAH yayi albarka kaji, ai kayi taimako whl ba kaɗan ba".

"Ka kula dashi baba bari naje"...........Ya faɗa Yana wucewa ya barsu.

Ko da ta shige ɗaki wuri ta nema ta zauna tare da zubawa hannayen ta ido, ji take kamar ba lpy take ba, kamar akwai abinda ke juya rayuwarta, komai na neman rikita mata tunani, wani abun bata sanin tayi sai bayan ta gama. Cikin wanna yanayin taji knocking a hankali ta ce, "Waye?"..........Mai makon ya amsa sai kawai ya shigo ciki, gyara zaman ta tayi tana kallon sa dan bata taɓa zaton gani sa ba, daga ƙofar ɗakin ya tsaya tare da karewa ɗakin kallo a ƙasa da second 60, idonsa ya tsayar a kanta kamar wanda aka tilasta ya ce, "Na zo da Nurse zai Miki dressing hannun ki fito waje". 

Kallon hannun tayi har lokacin yana fitar da jini kaɗan kaɗan ga wasu har sun daskare, miqewa tayi dankwalin kanta ya zame sunkuyawa tayi da niyyar ɗauka gashin kanta ya kunce, warwarewa ya dingayi daga daurewar data masa in a sleek bun style har ya baje a gadon bayanta gabaɗaya, harta ɗauki gyalen Kuma ta fasa ta ɗauko hijab ta zura, har tazo zata fice sai ta ɗan ɗago da niyyar satar kallon sa ganin bai motsa ba, karaf idonta ya shige cikin nasa, kallon ta yake kawai irin kallon nan me cike da tarin tambayoyi da sauri ta ƙarasa ficewa, ya rufa mata baya yana tunanin yanayin gashin kanta da ya gani sai kace aljana.

Tana fita ta samu baba ilerika da wani me lab coat zaune sai first aid box a gabansa Wanda tafi tunanin shine nurse ɗin da Jey ya faɗa mata, kujerar tsugunno data gani ta ja ta zauna tare da miqa masa hannun. "Sannu Hushaima ALLAH ya tsare gaba".........Baba ilerika ya faɗa.

Akan labban ta ta amsa da Ameen Dan gabaɗaya bata jin ƙarfin jikinta .

Spirit ya dangwalo a audugar ya fara goga mata. " Sorry"......... Ɗagowa tayi ta kalle shi tsaye yake a wurin kanta hannayen sa zube a aljihu dukda fuskarsa a hade take ta nuna alamun tausayawa, murmushi ta masa kawai ba tare da tace komai ba. Har aka gama aka naɗe hannun da bandage bata motsa ba, miqewa tayi bayan an gama ta ce, "Nagode baba ALLAH ya Kara girma".........Juyawa tayi bangaren sa inda idanunsa ke yawo a kanta kamar me nazari, kallo ɗaya ta masa ta ɗauke Kai a zuciyar ta kuwa faɗi take shi sai yace baya son kallo shi Kuma yaita ƙarewa mutane kallo, "Nagode". Ta faɗa cikin sanyin murya .

"Kije ki duba shi"............ Shine abinda ya faɗa yana nufar hanyar fita daga gidan tare da nurse ɗin, bayan sa ta bi da kallo tanajin wani abu na taso mata a rai kafin ta juya ta kalla ƙofar ɗakin Sahnish ɗin a hankali taja ƙafarta zuwa ɗakin.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.