Free chapter · Read without an account
28
SHIN SO DAYA NE?
Hafnancy...
Zazzafar soyayya, Cin amana, mugunta da kuma Sadaukarwa
#Free Book#
28.
"Agaskiya 'yar Kareematu wannan Mubarak din ya kwanta min arai,na yaba da hankalinsa ba kadan ba,fatarmu dai Allah yasa yadda azahiri yake da halin kirkin nan yasa haka ma zuciyarsa mai k'yau ne...... "
Cike da farin ciki nace"Amin Ummu Fadima,agaskia naji dadi sosai da kika yi na'am da Mubarak..... yanzu sauran mana Abba.... "Tace"Ga shawara idan zaki Karba.... Abbanku na dawowa ki tunkareshi da batun Mubarak din tun kafin lokaci ya k'ure miki...... "
Da sauri nace"No Umma am very scared....ban san ko taya Abba zai karbi zancen ba sabida yadda naga yake sona sosai tare da Haidar.... Ummu Fadima pls ki tayani yi masa magana yadda zai fahimta..... "
Girgiza kanta naga tayi tace"Not again my darling,har sai yaushe zan daina shige muku gaba ina tayaku fighting kan abubuwan daya shafi rayuwarku?har sai yaushe ne zan soma nannade hannuwa na zuba muku ido kuma na kyaleku ku kwaci 'yancin kanku? Ko baki san su kansu 'ya'ya suma suna da hakki akan iyayensu ba?" Ahankali nace"Eh! Suna dashi Umma."
Ta cigaba"Good.... Toh ina son ki san cewar yadda mahaifinki keda hakki akanki haka zalika kema kina da hakki akansa.... yana daga cikin hakkin uba ya zabawa 'ya'yansa abokan rayuwa na gari,ku ya'yan zamanin nan ma ku godewa Allah yadda ake kyaleku kuke tsula tsiyarku son ranku,azamaninmu wallahi uba yake zabawa dansa ko 'yarsa abokin rayuwa don idan baki manta ba ni da mahaifinki ma auren hadi aka mana,amma azamanin nan sai kiga iyaye sun baiwa 'ya'yansu damar kawo duk wanda suke so sai ah aura musu zabinsu...... My daughter what am trying to figure out to you is that, karki sake kiyi wasa da wannan damar da mahaifinki ya baki na ki kawo zabinki,Mubarak kika ce kikeso kuma nima nayi na'am dashi,don haka Abbanki na dawowa ki tareshi da batunsa,ina son ki cire duk wani tsoro aranki,mahaifinki ne wanda ya tsugunna ya haifeki ba wani dodo ba,u don't hav to fear ur father at all... Ni kaina nasan yadda suka shaku da Alhaji Ahmad mahaifin Haidar,kuma nasan bazai so yaki baiwa dansa aurenki ba... Amma abinda nakeso ki gane shine,mahaifinki mai saukin kaine da kuma fahimta don haka nasan bazai miki dole ba,insha Allahu zaiyi na'am da zabinki idan har yayi bincike ya tabbatar da Lallai Mubarak nada halayen kirki.... Is dat taken 'yar Kareema?"
Cike da jin wani gwarin gwiwa nace"Insha Allah Umma na fahimceki kuma zan tuntubeshi da maganar Mubarak din da zarar ya dawo.... "
"'Yata kar kiyi tunanin kamar bana son tunkarensa da maganar ne da kaina,a'ah,bana son ne yaga kamar ni nake daure muku gindin yin abubuwa,misali,zuwanku kano kwanakin baya ai nice na shigar da maganar wajensa tare da nemar muku izini,ko alokacin ma sai da yayi dan korafi akan meyasa bana kyaleku kuna tambayar abu agunsa sai dai kuta aikoni kamar wata 'yar aiki? Toh kinga abinda ya sanya nake son ke da kanki ki tunkareshi da maganar kenan,kuma ki hanzarta kada yazo ya bullo mana ta bayan gida..... "
"Umma wai meh kike nufi ne da bayan gidan nan da kullum kike fada? "Cike da rashin fahimta nayi mata wannan tambayar.
Murmushi tayi kafin tace"Ina nufin kada ya aurar dake ga wani can wanda ba zab'inki ba.... "
Da sauri na dafe kirji nace"A'zubillahi!!! Insha Allah hakan ma bazata faru ba,babu wanda zai min auran dole sai wanda nakeso ko ummata? "
"Ni wacece da zanki idan har wanda ya fini iko dake ya zartar da hukuncin hakan? "
"No Ummu Fadima kar ku min hakan don Allah" na fadi hakan ina girgiza kaina kamar wacce aka fada mata cewar ai tuni ya riga da ya zartar da hukuncin hakan.
***
Washegari,5:45pm*
"Abba oyoyo! Abba oyoyo!! "
Abinda naji kannena nata fada suka dad'a nanatawa kenan wanda hakan ya bani tabbacin lallai mahaifin namu ya dawo kenan.
"Fadima! Suhaima!!.... Kuna ina? Maza duk ku fito nan...... "
Hakan naji Abba ya fadi wanda tuni zuciyata ta hau dukan chalugude.Toh meh kuma mukayi wa Abba?daga dawowarsa ko hutawa beyi ba sai kwalla mana k'ira cikin b'acin rai abinda bai taba yi ba? Innalillahi kar dai ace Lee ya fallasa asirin? Because da Dad dinsa Abba yayi wannan tafiyar,so definitely idan har ya gayawa dad din nasa toh babu yadda za'ayi Alhaji Ahmad yaki tadantawa da mahaifin namu akan zancen.... Wayyo! Idan kuwa haka ne Leedar ko kadan be k'yauta min ba..... Am juz in trouble because my dad don't accept such shits,yana matukar daukar zafi ga duk wanda yayi masa k'arya ko kuma yai masa wasa da hankali.
"Wai baku ji abinda na fada bane?Fadima! Suhaima!! ko kuwa so kuke ni na biyoku da kaina?...... "
Haka naji ya Kara maimaitawa wanda tuni jikina ya hau rawar mazari,banko kofar dakina naji anyi wanda saura kiris! gabana ya tsinke sabida faduwar gaba.Ajiyar zuciya na saukar ganin Suhaima ce not Abba as I thought.Itama jikinta naga yana shaking wanda yafi nawa kuma ga dukkan alamu ihun Abban ne ya tasota daga bacci.
"Yaya Fadima kinji yadda Abba ke kiranmu kuwa muryarsa cike da b'acin rai? Am scared Allah dai yasa Haidar ba tona mana asiri yayi ba...... " cike da rawar murya take wannan maganar wanda bana jin zan iya amsata ahalin yanzu.
Da k'yar dai na daure nace"Kije kada yaji shirun yayi yawa yace mun rainashi.... Yanzu na fito wanka,bari na hanzarta saka kaya na biyo sahunki,pls Suhaima hurry up kada ya biyomu da kansa kin san abin bazai mana k'yau ba..... "
Da sauri ta juya ta fice wanda har zuwa wannan lokacin jikin nata be bar shaking ba.Gaban sif dina na tsaya,na hau hargitsa kaya ina nemar simple gown da zan sanya,abin mamaki ko doguwar riga daya banci karo da ita ba,kun san haka abin yake idan mutum yana sauri sai kaki ganin wasu abubuwa da kake nema alokacin don hankali ba kwance yake ba.Yanke shawarar saka rigar dake rike ahannuna nayi wanda nayi tunanin skirt & blouse ce.To my outmost suprise ashe wata gown ce.Da gudu na zura wanda ban lura ba ashe baya na sanya agaba,gaba kuma abaya.Ban damu ba nayi saurin zura hijab akai na fice,hijab din mah be zauna daidai akaina ba,kan hijabin ya karkace gefe wanda ya sanya nayi looking like a baby,shima din I don't care,burina kawai naje amsa kiran mahaifina,mutum mai muhimmanci arayuwata.
Zuciyata ce ta tsananta faduwar gaba ah sa'ilin da idanuwana suka sauka kan fuskar Abba wanda b'acin rai ne k'arara ya bayyana saman fuskar.wani irin mugun kallo naga yana aika min dashi tun kan na karaso inda suke tsaye dashi da Umma,sai kuma Suhaima wacce take durkushe agabansu jikin nan nata sai aikin kyarma yake tayi.Umma ce naga ta umarci su Lubna da Su tafi dakinsu sannan ta juya tana duban Abba.
Tace"Wai Abba lafiya kuwa? dawowarka kenan daga doguwar tafiya ko hutawa baka yi ba ka hau kwalawa yara k'ira cikin tsananin b'acin rai? ai ko wani laifi dai suka maka yaci ace ka bari ka huta tukun before anything....don Allah ina rokanka ko menene pls ka sasauta zuciyarka kabi ahankali..... "
Inaaa! wanda yayi nisa baya jin kira,ga dukkan alamu karatun da Umma ta karanto masa ko daya be shiga kwakwalwar Abba ba don daga mata hannu yayi alamun ta meh shiru sannan ya juyo zuwa gareni yana nuna ni da 'yar yatsa.
"Fadima kinci amanar yardan dana dauka na baki, na yadda dake fiye da tsammaninki ashe ke raina min hankali kike tayi babu wata batun soyayya tsakaninki da Haidar,all diz while yawo kuke ta mana da hankali....Toh ayau asirinku ya tonu,shi Haidar din da kansa ya sanarwa mahaifinsa ayayin da shi kuma mahaifin nashi ya sameni da maganar,I was so much surprised don har naso na k'aryata hakan akan cewa ni 'yata bazata taba min hakan ba sai kuma nayi tunanin Alhaji Ahmad babban mutum ne,toh meh zai amfana dashi idan yai min k'arya? Sai kuma nayi tunanin cewa 'ya'yan zamanin nan ka haifesu ne amma baka haifi halinsu ba.....yanzu so nake ki fada min tsakaninki da Allah da gaske din ne wai game kuke ta playing akan Suhaima? "
Gabana ne ya hau bugawa da sauri da sauri,kallona nakai ga Suhaima wacce naci sa'a itama ni din take kallo.
"Wai bake nake tambaya ba kin min shiru? Iyyeh?"
mukut!! kakeji na hadiyi wani miyau wanda har wani daci-daci nake jinsa ah mak'ogorona,da rawar murya nace"Eh.....ha..kane Ab..ba don Allah kayi hakuri...... "
Kallon Umma yayi ya kwashe labarin komai ya fada mata na soyayyar dake tsakanin Leedar da Suhaima da kuma shiga tsakaninsu da Rukky tayi har kawo nemar gafarar da suka zo nema da kuma bayyana mana gaskiyar al'amari da sukayi,sai dai banji yayi batun wata aljanu ba wanda hakan na nufin Leedar bai fada musu wannan ba kenan.
Umma kuwa sai tafa hannaye take tana fadin"Ikon Allah kenan!... "
Abba ya watsawa Suhaima wani mugun kallo kana yace"Ke kuma na dawo gareki... Kin bani mamaki sosai da aka fada min cewar tun SS1 dinki kika soma soyayya abinda nayi muku hani dashi na kuma gindaya muku sharad'in har sai kun kammala secondary level dinku kafin ku soma tsayawa sauraren wani saurayi da sunan wata soyayya... Ke kuma kika take wannan umarnin nawa kika nuna min halinku ta 'ya'yan zamani kika bi son ranki... Koda yake ni naki be wani zafeni sosai ba kamar na 'yar'uwarki da suka raina mana hankali,suka maida mu kananan yara irinsu,suka maida mu sa'anninsu na wasa ta hanyar sakamu akwana sunata yawo mana da hankali son ransu abinda ni Sa'adu na tsana arayuwata kenan amai dani shashasha.... "
Maida kallonsa gareni yayi,da sauri na saddar da kai kasa ayayin da nake jin yadda zuciyata ke mugun dukan chalugude.
"Toh! ku bud'e kunnuwanku da k'yau ku saurari hukuncin da zan yanke koma nace hukuncin dana riga na yanke...... Yanzu ku saurari yadda tawa wasar zata kasance....."
Da sauri na dago kai na kalleshi cike da fargabar jin kalaman da suka fito daga bakinsa.
Ya cigaba"Ke! Fadima atunaninki kinyi nasarar gyara k'yakk'yawar alak'ar dake tsakanin 'yar'uwarki da Haidar ko?.... Toh! Ina son ki san cewar su sunyi winning ayayin da ke kuma kinyi failing..... "
"Abba failing kuma? How? " Na fadi hakan cike da mamaki.
Murmushi naga ya saki wanda nake tunanin kila na takaici ne,kana yace"Yes! I repeat,Fadima Sa'ad kinyi failing.... Adalilin yawo da hankalina da kikayi shiyasa na yanke hukuncin ita Suhaimar zata auri Haidar din,ayayin da ke kuma na riga nayi miki miji don haka bazan bari ki auri zab'inki ba duk da cewar ban sani ba ko kina wanda kikeso or not wannan be dameni ba,amma ki sani nan da sati biyu za'a kawo gaisuwanku duka,gaisuwa da sadaki atake arana daya, ke infact! na tsayar da lokacin auranku nan da wata daya cur! babu ragi babu kuma k'ari................. "
Ihu na sanya iya k'arfina ina fadin"Wayyyo! Abbbbbbbbbbaaaaanaaa! don Allah kayi hakuri wannan hukuncin yayi min tsauri da yawa,wlh Abba na tuba bazan sake ba.. Allah Abba ina da wanda nakeso pls kada ka aura min wanda ko saninshi banyi ba,wlh bana sonsa gobe insha Allah zan turo maka Mubarak shi nakeso please......... " kuka nake sosai kamar raina zai fita ina zuba sambatun nan.Da sauri naja kaina zuwa inda Umma ke tsaye duk jinkinta ya mace da jin hukuncin da Abba ya yanke.
Kama kafafuwanta nayi nace"Mahaifiyata please ki saka baki acikin wannan maganar don Allah ki roka min Abba daya taimaka ya min rangwame wlhy bazan sake raina masa hankali ba..... "
Kallon Abba Umma tayi,cike da tausayin yarta da take ji tace"Abbaa.......... "
Da sauri ya daga mata hannu"Karma kice komai,kinji nace wallahi don babu wanda ke bina bashi rantsuwa na riga na zartar da wannan hukuncin,idan kuwa har kika ga Fadima bata auri wannan yaron ba,toh sai idan har shi yace ya fasa auranta ko kuma idan bana raye.........sai dai kuma idan guduwa tayi wanda aranar da kuwa ta sanya kafafuwanta tabar gidan nan da sunan guduwar,toh ta sani aranar na cireta daga cikin list din 'ya'yana......"
Jin abinda ya fada ya sanya na sake sakin wata sabuwar shafin kukan ina rok'ansa,amma abin mamaki sai naga kawai ya kada kansa yayi waje wanda nake tunanin kila masallaci zashi don har an soma k'iraye-k'irayen sallar magrib.Suhaima mah kuka take sosai sai naji kamar na kwasheta da wawan mari don duk ta sanadiyyarta hakan ta faru,amma ai kuma bata aikeni taimaka matan ba.
Zaman 'yan bori nayi ak'asa tare da sanya hannu aka kamar mai shirin zaucewa,toh kila na zaucen ne ban sani ba.Wani tunani naji ya fad'o min arai,ai kuwa da azama na mik'e nayi dakina ina jin Umma na k'irana amma ko tankata banyi ba don sosai itama taban haushi da taki tabuk'a komai.Zaro wayata dake chargy nayi,da rawar hannu na nemo lambar Mubeen nayi dialing,cikin rashin sa'a akace min switched off.Ji nayi kamar na sanya hannu aka na kurma wawan ihu da zai iya fasa gidan da muke ciki.
Engr.Mahmood ne ya fad'o min arai,da sauri na binciko lambarsa,cikin sa'a kuwa naji k'iran ta shiga,can sai kuma naji tune din 'number busy' alamun ya yanke call din.Dama nasan ah rina,don so da yawa hakan yake min idan na kirashi sai kaga ya yanke call din sai shi ya k'ira,acewarsa baya son ya cinye min kati.
Dakatawa nayi ina jiran call dinsa,ai kuwa babu wani b'ata lokaci naga k'iran ya shigo.Da sauri na danna 'receive'.
Ina jinsa yace"Hello! my dear sister inlaw........ " kamar jira nake naji muryarsa na fashe da kuka.Kuka sosai nake mai daga hankali.
Cike da tashin hankali naji yace"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...mamana lafiya kike kuwa?meya faru?meh aka miki?... Pls stop crying & talk to me wallahi har cikin zuciyata nake jin kukan nan,Zahra dear please speak out..... "
Alokaci d'aya na sami kaina da yin yadda yace,wato tsayar da kukan.
Nace"Abba ne wai shi zai aurar dani ga wani ba Mubarak ba,kuma wai nan da sati biyu za'a kawo gaisuwata,sannan wata d'aya cur! ya tsaida lokacin bikin..... " fashewa da kuka na sakeyi nace"Sir! I don't know wat to do na rokeshi yace wallahi his decision is final,gashi inata trying layin Mubeen yaki shiga,pls brother help me out kasan duk yadda zakayi kuyi get intouch da juna ka fad'a masa halin da ake ciki ayanzu................. "
"Miko min wayar nan........ " hakan naji an fad'a da k'arfin gaske wanda kiris! ya rage na kurma uban ihu don tsananin firgitar da nayi.Juyawa nayi da sauri ina kallon Abba daya shigo dakina,yanayinsa kamar wani Zakin da yaga abokin gabansa yana shirin kai masa farmaki.Beyi wata-wata ba ya iso inda nake ya warce wayar,ina ji ina gani Abba ya zare sim-cards dina,ya babballasu gutsi-gutsi kana ya watsar akasa.Hawaye sai bulbulowa suke asaman kumatuna amma na kasa furta komai agareshi don lamarin mahaifin nawa ya soma bani tsoro,ban taba tunanin Abba nada mugun zuciya haka ba,koda yake ance ka guji b'acin ran shiru-shirun mutum.
Nuno ni yayi da 'yar yatsa yana fadin"As from today,I have restricted ur movement,ba shiga ba fita,God's so kind mah kuna cikin hutu don haka baza kice zaki fita zuwa makaranta ba,in that case,idan har kika ga kin saka kafa kin fita cikin gidan nan toh sai ranar da zan sallameki ki tafi d'akin mijinki,idan har kuwa kika kuskura kika tsallake wannan umarnin nawa kika fita da gangan,toh karki kuskura ki dawo cikin gidan nan don daga ranar zan cireki ah list d'in 'ya'yana..... Kuma koda gangan karki kuskura ki ari wayar wani acikin gidan nan ki kira wani,ko Kuma wani yazo nemanki ki fita ki sameshi,wallahi kinji dai na fad'a miki bada yawuna ba......... "
Sai ayanzu na sami damar magana nace"Haba Abba! meh yayi zafi haka? meyasa kake nemar tarwatsa min zuciya ne?meyasa kake k'ok'arin jefa 'yarka cikin kogin damuwa ne? Why are trying to make things hard for me? Abba ka tuna fa Allah madaukakin sarki yace acikin al'qur'aninsa mai girma................. "
Da sauri naga ya daga min hannu yace"Malama dakata ba wa'azi nazo ki min ba,ina san ki sani,ni mahaifinki ne mai sonki Kuma bazan so na ganki cikin damuwa ko Kuma nayi k'ok'arin cutar dake ba,am juz trying to punish you for wat you did don abinda kuka mana rashin k'unya ce don be kamata ace kun saka iyaye acikin shirmeku ba wanda ko kadan banji dadin hakan ba don ni sam na tsani mara gaskiya da kuma kawo wasa cikin al'amari mai k'arfi... Ko kuwa kin manta sunana ne? 'Adalin alk'ali' ko Kuma ace'Alk'ali mai gaskiya ko mai nasara', don haka nakeson Kuma kuyi koyi dani ba wai kuyi koyi da shirme ba............ "
Yana kawo nan da jawabinsa naga ya juya ya fice daga d'akin.Hawayen idanuwana sun kafe sunki zuba,nabi karyayyun sim-cards dina dake watse akasa da kallo ina tunanin yadda za'ayi na sake ganawa da Mubeen d'ina kafin nan da sati biyun da za'a kawo so called gaisuwata,gaskia I really nid to speak to him don mu nemi mafitar wannan al'amarin,kai infact! ko guduwa ne sai muyi idan muka ga abin bana wasa bane,da sauri na soma istigfari ganin ina nemar b'ace hanya.
*(gareku 'yan mata masu tunanin guduwa idan akayi kakorin lika musu wanda basa so,sam ba shawara ce mai k'yau ba Kuma alamace ta rashin ilimi,don idan da'ace mutum nada wadatacciyar ilimi toh bazai yi tunanin yin hakan ba,ku sani idan har kuka amince da wannan zabin tabbas kunyi biyayya Kuma zaku ga wannan auren tana iya yiwa wani alheri ne agareku duka.... Allah yasa mu dace).*
Suhaima ce naga ta shigo dakin sum-sum kamar wata mara gaskia,yo! ai kusan kamar mara gaskiyar ce.Zata soma magana nace"Suhaima pls juz get out,allow me to be alone with my thoughts and sorrows.... Don Allah ki tafi kawai bazaki iya magance min komai ba.... Ina tayaki farin cikin samun masoyinki amatsayin mijin da zaki aura,Hak'ika burinku ya kusan cika,congrats..... " Araina nace"Ni Kuma meh zancewa kaina?Ina jajantawa kaina or wat? "
Da k'yar na iya jan kafafuwana zuwa bandaki don d'auro alwala.Ina nan kan sallaya har aka soma k'iraye-kirayen sallar isha'i,na tashi na sauketa sannan na d'ora da shafa'i da wutiri.Addu'o'i sosai na shiga zubawa babu gaggautawa ina yi ina hadawa da kuka cikin k'aramin sauti.Ina jin sanda aka shigo d'akina aka zauna saman gado,amma ko ajikina ban damu nace nabar kwararo addu'o'in da nake afili ba,illa k'ara bada himma da nayi.
Sai da nayi mai isata sannan na mike ina nannad'e sallaya,na juyo ina fuskantar Umma wacce itace ta shigo ta zauna tana jiran iddarwata.
"'Yata zo ki zauna muyi magana" Da sauri na isa gareta,instead na zauna kamar yadda ta umarta,a'ah sai kawai na fada jikinta tare da rushewa da kuka.
"Fadimaaaa!! "Kiran Sunana naji tayi wanda kusan zan iya cewa tunda nake da ita ban taba jin ta k'irawo ainihin sunana ba sai 'yar Kareematu (kun san fulani da kunyar dan fari).
Tsagaita kukan nawa nayi,na mike daga jikinta na zauna saman gado tare da ruk'o hannayenta,cike da tausayin kaina nace"Ummu Fadima ji hirar da mukayi jiya yana neman rikid'ewa ya zamo gaskia.....Ko dai Umma kin san da batun bada ni ga wani da Abba ke kokarin yi ne shiyasa kika yi min wannan hirar jiya?kawai fada min gaskiyar lamari ne kika kasa? "
Da sauri naga ta girgiza kanta tana fadin"A'ah 'yata ko kadan bani da masaniya akan wannan zance kuma har ga Allah ni ban ma san yaron ba haka kuma ban ban ko dan gidan wanene ba... Ke infact! nima sai yau din nan nake jin wannan kudirin na mahaifinku akanku duka.......... "
"Fadima hakik'a kunyi wauta ba kadan ba,kunyi wawancin saka iyaye acikin shirmen wasanku alhalin kin san mahaifinki baya k'arbar irin rainin nan don aganinshi rashin kunyace kuka musu.....dole abin yai masa zafi sosai sabida tun farko keda kanki kika mana introducing Haidar amatsayin wanda kikeso kuma wanda kike son ki aura har aka turashi Adamawa dangi suka ganshi,sai yanzu rana tsaka kuce mana ba soyayyar aure atsakaninku kawai game kuge bugawa?mu sa'annin wasanku ne?Nifa banga laifin mahaifin naku da hukuncin daya yanke ba sabida tabbas kun maishe su kananan mutane masu karamin kwakwalwa..........kuma ni nasan wannan haushin naki da yake ji da biyu ne,ya baki lokaci ki fito masa da wanda kikeso sai kika share baki sake tada batun ba,duk kuma ire-iren ababen nan duk rainin hankali da rashin kunya yake d'aukarsu,shiyasa nake ta fad'a miki ki hanzarta sanar masa da batun Mubarak amma kika k'i,toh gashi nan ya bullo miki ta bayan gidan da nake ta gudun miki faruwarsa...... Shawarata anan itace,yanzu nasan yana cikin fushi dake sosai,ki bari idan ya sakko sai Kije ki nemi gafararsa amma dakyar idan har zai fasa baiwa wannan yaron aurenki tunda har naji yayi rantsuwa......... "
Kuka sosai na sake fashewa dashi jin abinda ta fada.Rana ta farko dana soma dana sanin wannan game din da muka shirya nida Leedar wanda dama can nice na kawo wannan shawarar gashi ayau nina fad'a ciki ayayin da su kuma sunci nasara,ina neman bankwana da farin cikina ah sanadin hakan.I juz hav to blame myself for all sabida nina jawa kaina faruwar komai...
**
sosai Engr. ya shiga cikin tashin hankali sanda yaji muryar mahaifin Fadimar tasa na mata ihu har yaji ya warce wayar ahannunta,yana kallo har call din ya tsinke.Yau da safe ya dawo daga Kaduna har yake tunanin kila yau da daddare yakai mata ziyara sai gashi wannan al'amarin ya kunno kai. Ya tabbatar Fadimar tasa tana cikin damuwa sosai wanda ko kadan baya k'aunar ganin b'acin ranta balle ace tana cikin damuwar.Zuciyarsa ne yaji ta hau tafasa kamar zata fasa k'irjinsa ta fad'o waje daya tuna yadda hirar tasu ta kasance before her Dad interrupted.
Yanzu burin Fadima ta auri Mubarak shiyasa ta shiga cikin wannan tashin hankalin don ance wani zata aura ba shi ba?Dat means har yanzu shi bata fara sonsa ba kenan?Kuma ai cikin kwanakin nan yaga alamun kamar ta soma sonsa amma kodai ita bata ma san cewar ta soma sonsa bane?
Wani bangaren zuciyarsa yace"Kai man karka dauki k'yautatawa da kuma shakuwar dake tsakaninku azuwan sonka take,sam u are wrong if dats ur thinking!!"
Wani Shu'umin murmushi naga ya saki tare da furta"Yah Allah! ka mallaka min Fadima Zahra don ina sonta sosai.!!"
***
Bangaren Mubeen kuwa,wuraren karfe biyar na yamma suka shiga dakin theater don gudanar da CS ga wata mata wacce ta kasa haihuwa da kanta.Koda zai shiga sai da ya kashe wayoyinsa kamar yadda ya saba yi.Sai bayan kusan awa biyu suka fito.Alokacin kuwa har an soma kiraye-kirayen sallar isha'i,masallacin asibitin ya nufa ya sauke farali sannan ya kama hanyar gida don sosai ya gaji da yawa,tun safe yake asibitin yake ta ayyuka sai yanzu ya sami kansa,ya gode Allah mah yau baya cikin 'yan night duty,don haka zai more baccinsa sosai.
Sai daya kusa da kofar gidansu sannan ya tuna cewar wayarsa har yanzu akashe take kuma tun safe da suka yi waya da Zahransa be sake jin duriyarta ba,kila mah ta nemeshi bata sameshi ba.Akofar gidan yayi parking motar,kana ya lalubo k'aramar wayarsa ya kunnata,ya latso layin Fadima,cikin rashin sa'a akace masa switched off,latso dayar layinta yayi shima still haka akace masa.
Karamin tsaki ya saki yace"Kila bata da chargy ne... "
Ya sake cewa"Baby Zahra am badly missing you,ji nake kamar idan banji muryarki yanzu ba toh dakyar zan iya kai safiyar gobe.... " ya fadi hakan kamar zai saki kuka.Da k'yar ya iya fitowa yaje ya bud'e gate sannan ya shigar da motarsa.Ya dawo ya rufe gidan gabaki daya,kana ya nufi ciki duk jikinsa amace na rashin ji daga tauraruwar tasa.Ga wani zancen haushi da ogansa ya sameshi dashi ah office dinsa yau da safe,wai an matso da tafiyar tasu nan kusa sabida wasu dalilai,wai nan da Jibi zasu wuce Indiar.Ji yayi kamar ya shak'oshi ya hallakashi har lahira sanda yake fad'a masa wannan zancen haushin,shi da yayi planning cewar kafin ya tafi zeyi kokari yaga ya kai gaisuwa gidansu Fadima amma yanzu ogan nasu ya b'ata masa shiri.Gashi sam duka layin Zahran sam basa shiga.Ya yanke shawarar gobe idan har Allah ya kaimu still layin be shiga ba,toh insha Allah zeyi wa Zaria dirar milkiya.
*
"Abba magana nazo muyi... " Umma ce ta cimma Abba ah daki,alokacin har ya soma shirin kwanciya bacci.
Kada baki yayi yace"Haba Kareema toh karaso mana kin tsaya daga kofa kina kame-kame... "
Dan muskutawa tayi jin abinda ya fada,kana ta k'arasa bakin gado ta zauna kusa dashi.
"Ina sauraronki. " ya fada tare da tsareta da idanuwansa don yasan kan batun 'ya'yan nata ne ya kawota. "Karime da son 'ya'yanta abin sai ahankali... " ya aiyana acikin zuciyarsa.
Ahankali ta soma magana"Abba an san tabbas yara basu k'yauta da abin da suka aikata ba,Hakika sunyi kuskuren saka iyaye cikin shirmensu, shiyasa nazo don in tayasu neman afuwarka, Abban yara ka gafarta musu sannan kuma kayiwa Fadima sassauci ka aura mata zab'inta..... "
Shiru yayi na tsawon dakik'u hamsin,kana ya kamo hannayenta yace"Kareema hakik'a Fadima ta b'ata min rai sosai da maidani sa'arta da tayi,and again ya za'ayi ina mahaifinta na bata umarnin kawo min wanda takeso amatsayin wanda take burin aura,sannan yarinyar nan ta watsar da batun akwandon shara don ta raina ni? Ki duba fa kusan wata daya kenan dayi mata maganar amma shiru kakeji,kuma nasan bazata rasa wanda take son ba,don raini sai data ji nace nayi mata miji shine zata bud'i baki tace ai tana da wanda take so?.... "
Da sauri Umma tace"Kayi hakuri Abba nasan kunyar fada maka take ji,jira kawai take kai ka sake mata magana da kanka.... "
Daga mata hannu yayi"Ai dama na fad'a,kece ke d'aure musu gindi suna aikata abubuwan da ransu keso,toh bari kiji ni dai na riga nayi rantsuwa idan har kika ga Fadima bata auri wannan yaron ba toh kuwa sai idan bayan raina ko kuma idan shi yaron yace ya fasa.amma kuwa muddin ina raye sai Fadima ta auri d'an gidan Alhaji Mu'azzam nasan kin gane Alhaji Mu'azzam din da nake nufi,wannan abokina din nan wanda ta dalilinsa har na kai kan matsayin da nake ayau.Na yaba da hankalin d'an nasa duk da cewar ya sanar min wai yaron d'an wani kaninsa ne amma ya tabbatar min da yaron bashi da matsala ko kadan....... "
"Abba Fadima tana da wanda takeso fah... "
"Kareema don Allah tashi ki fitar min adaki tunda kin kasa gane abinda nakeson fahimtar dake..... "
"Allah ya huci zuciyarka. " Umma ta mik'e tabar dakin don tasan tunda Abba ya riga yayi rantsuwa tofa ba zeyi kaffara ba sai ya aiwatar da abinda yayi niyya.Tabbas tasan Alhaji Mu'azzam abokinsa ne sosai wanda tare da taimakonsa Abba yakai matsayin da yake kai ayau.Yanzu ta gano nufinsa,wato so yake shima ya saka masa ta hanyar aurar da Fadima ga d'an kanin Alhaji Mu'azzam din.
Ghen! Ghen!! Ghen!!! wata sabuwa inji 'yan caca...waye kuma ake shirin aura mah Fadima bayan Mubeen da Engr. Kamar yadda muke ta saka rai?
Anya kuna ganin Fadima zata yadda ayi wannan auran kuwa?
wani kalar action kuke ganin Mubeen zai dauka idan yaji wai Fadima zata auri waninsa ba shi ba?
Laaah! nama manta da Engr. Mahmood.... Hmmm! Kawai zan iya cewa
To be contined…
#’Yar Mutan Naija#
***.