Free chapter · Read without an account
Chapter Eight
Misalin karfe biyar na yamma suna zaune a wani kayataccen garden da yake nesa da harabar gidan. Sauban yana ta iya bakin ƙoƙarin sa akan Sultan ya saurare shi domin su tattauna akan wata mahimmiyar magana amma yaki sauraron sa.
Sai tsokanar sa yake yi saboda tsananin farin ciki da yake ciki tsakanin jiya da yau, wanda kowa sai da ya fahimci hakan. Sai da Sauban ya ɓata fuska sannan Sultan yayi gyaran murya yace: "Sorry bloody go ahead."
Ƙwafa kawai yayi tare da hararar sa, sannan yace:
"Tun jiya nake cewa ka duba mails din ka kaki. What's wrong with you? This is serious."
"Okay!" Kawai Sultan ya faɗa yana kokarin danne dariyar sa. Saboda ya rasa dalilin da yasa duk lokacin da Sauban ya haɗe rai dariya yake bashi.
Baiyi aune ba ya sake jin wata dariyar ta sake kufce masa, a daidai lokacin da Sauban yake kokarin nuna masa wani sako a laptop ɗin sa.
Kasaƙe Sauban yayi yana kallon sa. Sannan ya ya haɗe ransa ya sake cewa:
"You need to be professional Sultan."
Yanayin da ya gani a fuskar Sauban da kuma sunan sa da yaji ya ambata ƙarara, dole ya saka ya haƙura da tsokanar da yake masa. Ya jawo laptop ɗin sa ya fara duba sakon da Sauban ya tura masa tun jiya.
Direct ta kan bayanan lafiyar Radiya ya fara. Ganin hakan ya saka Sauban ya kalle shi yace:
"Yakamata ka fara ganin fuskar baby Maman ka before."
"No need." Abinda Sultan ya furta kenan yana cigaba da bin bayanan.
Murmushi Sauban yayi. Sannan ya kalle shi yace:
"Are you serious?"
Da mamakin sa Sultan ya ɗago ya kalle shi. Saboda sam bai gane me yake nufi ba. Sannan yace:
" I don't understand I'm serious or not?"
Dariya Sauban yayi sannan ya sake kallon sa yace:
"Sultan, are you interested in her physical appearance or not?"
"Hold on!" Abinda Sultan yace tare da daga masa hannu.
Sannan ya sake bin sa da wani kallon mamaki yace:
"You asked me to be professional, Right?
So why are you asking me such rhetorical questions?
Na faɗa maka ina da Interest ne akan ta?
See, I'm searching for my genetic match, and nothing more."
Murmushi Sauban ya sake yi tare da juyo da fuskar laptop ɗin sa ta fuskanci Sultan. Sannan ya fara magana yana kallon cikin idon sa:
"This is your black gorgeous beauty. Her name is Radiya Hamza Gaya, she's 25. She was raised in Kano metropolis."
Wata sanyayyiyar dariya Sauban ya saki a dai dai lokacin da yaga Sultan ya ƙame ƙam, ya ƙura wa hoton Radiya ido.
Gabaɗaya imanin sa da hankalin sa ya tafi kan screen din computer. Bai san lokacin da ya sauke ƙafar sa daga ɗora ta da yayi akan dayar.
Ya dauki laptop ɗin ya ɗora a cinyar sa yana kallon hoton ta, fuskar sa cike da mamaki. Babban abinda ya fara jan hankalin sa shine; kalar fatar ta.
Sannan daga bisani ya ɗago ya kalli fuskar Sauban da yake dariya kasa kasa harshen sa yana sarkewa yace:
"Are you trying to find my genetic match, or you're matchmaking for marriage? I don't understand." Ya faɗa fuskar sa cike da mamaki.
Anan ne Sauban ya saki dariya, saboda yadda yaga Sultan ya rikice lokaci guda, kuma yana nema ya wayance. Saboda ya san halin dan uwan sa sarai tabbas Radiya itace kalar macen da ya daɗe yana nema.
Kasaƙe Sultan yayi yana kallon sa, a hankali kuma yana satar kallon hoton Radiya. Sannan shima ya kwashe da dariya saboda ya sani dole Sauban ya gano shi. Sannan daga bisani ya kalli Sauban yace:
"To be honest Sauban, wannan itace genetic match ɗi na?"
A nutse Sauban ya ɗaga masa kai. Sannan ya fara danne danne a laptop ɗin, sannan daga bisani ya kalle shi ya ga duk ya rikice yace:
"The more interesting part is that; she's fearless, courageous and stubborn."
Ya faɗa yana kallon fuskar Sultan. Shi kuwa jingina kan sa yayi da jikin kujerar da yake kai ya ɗora ƙafar sa daya kan daya ya lalubo hoton ta a laptop ɗin sa yana daɗa kare mata kallo yana kurbar juice din da yake hannun sa.
Sannan ya kalli Sauban yace:
"Yes, is possible, skin complexion din ta ya nuna tana da ra'ayin kan ta. But how did you know all this?"
"Okay!" Sauban ya faɗa sannan ya fara laluben wasu videos a laptop ɗin. Ya ɗago ya kalli Sultan yace:
"like I told you earlier, a kano take, also she attended Queen College of Nursing wanda mata ne zallah a makarantar. So last two years an samu increase na registration da hostel fee. So itace ta shirya protest akan wannan matakin..."
"Ta shirya protest ko ta shige gaba aka yi protest da ita Sauban?" Sultan ya katse shi cike da mamaki.
Juyo masa da laptop ɗin nasa ya sake yi a karo na biyu. Video Radiya ne da take magana da ƴan jarida a wancan lokacin fuskar ta sam babu alamar tsoro. Sannan Sauban ya kalle shi yacigaba da bayani:
"Kamar yadda kaji ita ta shirya zanga zanga acikin makarantar na kwana uku. Ba shiga class, ba shiga ba fita a makarantar.
Babban abinda zai baka mamaki shine; suddenly protest din yaje viral don tayi trending sosai a wancan lokacin.
Also hukumar makarantar sun kira ta a sirrince sunyi mata tayin kudi masu yawa domin ta janye, but she refused. Becouse she's not materialistic, she mentioned this a wani interview da akayi da ita wani TV channel.
Wannan measures din nata ya saka alot of NGOs suka yi participating a makarantar financially da wasu wealthy individuals.
To cut off, yanzu saboda ita duk yarinyar da ta fito daga poor background in dai she's eligible zata biya half na school fees.
But, before all this, sunyi suspending din ta suka hana ta results. So case din nata was publicized, mutanen gari da hukumomi suka shigo ciki dole suka haƙura ta ƙarasa karatun ta anan."
Duk bayanin nan da Sauban yake yi hankalin Sultan yana kan videos din Radiya. Kama daga na zanga zangar da interviews din da tayi da kafafen yaɗa labarai.
Duk wani motsi da take yi da yanayin yadda take magana cike da ƙwarin gwiwa birge shi take yi, sai murmushi kawai yake yi shi kaɗai ya rasa me zai ce.
Shi kuwa Sauban ya ƙura masa ido kawai yana kallon sa. Shi kansa yana cikin farin ciki mara misaltuwa. Saboda ya manta yaushe rabon da yaga Sultan acikin wannan yanayin.
Gyaran murya yayi sannan ya kalli Sultan cike da tsokana yace:
"It seems like you're interested with your baby mama?"
Murmushi yayi ya ɗago ya sake jingina jikin sa da kujerar ya ɗora ƙafar sa akan dayar yana sake kurwa screen din laptop din kallo yana kurbar lemo ba tare da yace komai ba.
Sauban ya sake yin murmushi yace:
"The preliminary medical report shows she's normal, but further test are needed to confirm her biological health."
"Interesting."
Abinda Sultan ya faɗa kenan. Har yanzu idon sa yana kan hoton Radiya ya kasa dauke kan sa.
Haka Sauban ya dage yana bashi bayanai sosai akan Radiya, shi kuwa kallon hoton ta kawai yake yi yana murmushi, shi kan sa ya rasa murmushin me yake yi, har sai da lokacin sallar magariba yayi suka miƙe domin gabatar da sallar.
••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
Misalin karfe 10 na daren ranar Sultan yana ta kaikawo a katafaren bedroom ɗin sa. Sam bacci ya gaza daukar sa. Zirya kawai yake yi da kofin coffee a hannun sa, lokaci zuwa lokaci yana duba hoton Radiya.
Duk irin jan kunnen da yake yi wa zuciyar sa amma taki bashi hadin kai a wannan lokacin. Ya rasa me yasa lokaci guda ya kamu da son ta.
Tabbas ba zai yaudari kan sa ba, saboda shi ba bako bane a soyayya ya sani sarai ya fara son Radiya. Amma babbar matsalar itace ta yaya hakan zata kasance?
Kusan sama da shekaru goma ya riga ya gindaya wa zuciyar sa sharadi akan ba zai sake saka wata ƴa mace a ran sa ba, saboda wasu dalilai nasa na kan sa. Amma me ya saka ya kamu da son Radiya?
Ko don ta kasance mahaɗin halittar sa tana da damar haifa masa yaya?
A'a ko don ta dace da kalar macen da yake so?
Wannan tambayoyin ne suke zarya acikin ƙwaƙwalwarsa.
Zama yayi a gefen gadon sa. Take ya miƙe zumbur ya dauki wayar sa ya fara laluben number Sauban. Bayan ya dauka Sultan ya sassauta muryar sa yace:
"Bloody, we need to talk. Seriously, na fara zargin akwai wani abu a ƙasa. Anya ba wani abu kuke shirya min ba kai da Ammey akan yarinyar nan? like yadda kuka yi shekarun baya?"
Dariya ce ta kwacewa Sauban sosai har sai da ya kasa magana. Cikin takaici Sultan tace:
"Smart, you set me up. Ba matsala. Nagode, amma kace da Ammey tayi nasara a kaina wannan karon, I salute you all." Ya kashe wayar.
Ransa a bace yana huci ya sake daukar wayar tasa cikin zafin nama ta fice ya nufi ɓangaren Ammey. A zaune ya same ta a bedroom ɗin ta tana lazimi. Sai da ya jira ta idar sannan ya kalle ta yace:
"Ammey meyasa zakuyi min haka? Kunyi wasa da rauni na, ba sai kin biyo min ta haka ba zan yi aure. Please Ammey kar ku sake, you know this is my weakness."
Ya ƙarasa maganar a wa ta murya mai cike da abun tausayi.
A nutse ta kare masa kallo, sannan ta tambaye shi mai ya faru. A hankali ta fuskanci in da ya dosa. Kamo hannun sa tayi duk biyun ta riƙe, sannan ta kalli cikin idon sa tace:
"Daman ɗan uwan ka yana yarda wani yayi wasa da wannan al'amarin? Ballanta kuma shi da kansa?"
Girgiza mata kai yayi alamar a'a. Sannan tacigaba:
"Menene ya rufe maka ido Sultan baka lura da farin cikin da ɗan uwan ka ya shiga ba? Kana tunanin zai yaudare ka ne?"
"A'a Ammey" Abinda ya furta kenan muryar sa tana rawa alamar kuka ya zai kufce masa.
"Me yasa ka kasa gane duk wannan?" Ta fada tana kallon yadda yake kokarin rike kukan sa amma hakan ya gagare shi.
"Ammey gani nake yi kamar a mafarki, gani nake yi kamar kawai kin shirya hakan ne don nayi aure ba don ta kasance mahaɗin na ba.
Ina mamakin na samu genetic match ɗina, and she's complete full package, yadda nake son mace. Ammey gani nake yi kamar ba'a gaske ba."
Murmushi ta yi sannan ta sake kallon sa tace:
"Kana wasa da hukuncin Ubangiji? Ka manta hakurin da kayi da tawakkali? Ka manta da addu'ar da ni da duk wani masoyin ka suke yi maka?
Sultan, haka Ubangiji yake ikon sa, matuƙar ka miƙa komai naka gare shi, da sannu zai amsa maka bayan ya gama jarraba ka.
Saboda haka wannan ba komai bane a wajen Ubangiji, kai dai ka cigaba da bin umarnin sa, da sannu zaka ga abinda yafi haka."
Jinjina kan sa yayi yana share kwallar da take fuskar sa. Sannan ya zamo kasa ya kwanta akan kafafun ta ta fara shafa sumar kan sa tana yi masa nasiha mai ratsa jiki.
A haka har ya samu nutsuwa, amma zuciyar sa tuni tayi nisa da azalzalar sa akan tunanin Radiya.
Shuru tayi na ɗan lokaci, sannan ta ɗago fuskar sa tace:
"Meya ja hankalin ka akan ta?"
"I don't know....But, I like her....I can feel it."
Jinjina kan ta kawai tayi tacigaba da shafa gashin kan sa. A haka har bacci ya ɗauke shi. Da dabara ta janye jikin ta ta saka masa pillow tare da lulluɓeshi da bargo ta zauna ta kura masa ido tana share kwalla.
BAYAN KWAN BIYAR
Radiya tana zaune a ɗaya daga cikin kujerun da aka ƙawata office ɗin dasu. A hankali take ƙarewa office ɗin kallo saboda kyawun sa da kayatuwar sa sun birge ta.
Daga gefe kuma, trolley din ta ne a ajiye saboda tasha alwashin daga nan sai gida, don bazata sake kwana a Abuja ba, saboda ta gaji da garin.
A hankali aka bude ƙofar office ɗin. Dr. Cara ta shigo cikin nutsuwa, ta rufe ƙofar, sannan ta zauna a kujerar da take fuskantar ta tace:
"You've been very patient, I'm sorry."
Radiya daga kanta kawai tayi, sannan tace:
"I was told to wait for a one week, yanzu sati guda ya cika ina so kuyi min bayani, what job did I apply for?"
Dr. Cara ta ɗan yi murmushi sannan tace:
"Before we discuss about placement, we need to complete your medical evaluation."
Radiya ta kalli fuskar ta cike da mamaki sannan tace:
Want the next chapter?
ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol