Free chapter · Read without an account

Chapter Three: (A.A MAI HULA CONSTR.COMP.)

by The Healer's Pen · NI DA KANNENA

                    

Misalin 8:45am Nuratu ta ƙaraso ƙofar shiga wani katafaren Company mai matuƙar kyawun gaske wanda gaba ɗaya ginin an ƙawata shi ne da glass, a ƙalla ginin yana da hawa 8-9.


Wajen da aka tanada domin parking ɗin motoci ta nufa tayi parking ɗin sabuwar motar ta a dai dai ƙasan rumfar da aka rubuta 'Managing Director.'


Maza aƙalla guda uku ne suka nufo in da motar tata take da kuma mace guda ɗaya, gaba ɗayan su cike da ladabi suna gaisheta, wannan mace ta saka hannu ta buɗe ɗaya ɓangaren motar inda ta ɗakko jakar Nuratu da kuma Lunch bag ta nufi wata katafariyar ƙofar glass wadda a samanta aka rubuta 'A.A MAI HULA CONSTRUCTION COMPANY OF NIGERIA.'


Cikin nutsuwa ta fito daga motar, sanye take da suite riga da siket baƙaƙe, kan ta tayi rolling da wani magenta purple na jersey Veil kalar suiter ta ta ciki wadda ta rufe har wuyan ta, ƙafar ta wani dogon takal mi ne baƙi shima ya amshi ƙafar ta sosai, fuskarta cike da annuri ba yabo ba fallasa. 


Bayan ta gama fitowa daga motar ɗaya daga cikin ma'aikatan ya buɗe booth ɗin motar ya ɗako 'car upholstery' ya lulluɓe motar.


Ta juyo ta kalli wani kyakkyawan saurayi da yake gefen ta yana yi mata murnar sabuwar mota tace:


"Ameen Nagode Al'ameen." 


Sannan ta fara tafiya cikin sauri sauri yana bin bayan ta tare da ƙara tunatar da ita akan Annual meeting ɗin da zasu yi a yau.


Duk in da suka ratsa mutane sai gaisheta ake yi tare da yi mata sannu da zuwa. Gaskiya tsarin Company yayi kyau sosai kamar a Turai, sannan ko ina tsaf tsaf kamar ba'a takawa ita kanta Nuratu yau Company ya ƙara yi mata kyau. 


Gyara muryarta tayi da ta dashe dai dai lokacin da suke ƙoƙarin shiga elavator domin sada ta da office ɗin ta, sannan tace da Al'ameen:


"Ashraf ya ƙaraso?" 


Girgiza mata kai yayi tare da faɗin:


"A'a bai ƙaraso ba har yanzu." 


Cike da mamaki ta kalli Al'ameen tace:


"Ka tabbata kuma ka tura masa da text message ɗin da nace maka jiya?"


Cike da kwarin gwiwa yace:


"Wallahi Ukhty na tura masa, kuma naga delivery report." 


Jinjina kai tayi tare da faɗin:


 "Ok!"


Ta kalli Al'ameen tace:


 "Ayi shifting meeting ɗin zuwa 11:00am." 


Ta faɗa dai dai lokacin da ta iso ƙofar wani katafaren office wanda wani bangaren nasa duk na glass ne kana iya hango ƙayatuwar sa daga waje.


Cike da mamaki Al'ameen yace:


"Ayi shifting kuma Ukhty? Kusan kowa fa yazo, kuma it's unusual a wannan company a saka meeting kuma a canja lokaci."


Kallon sa kawai tayi cike da takaici tare buɗe ƙofar shiga office ɗin nata ta shiga cikin sauri Al'ameen ya sake bin bayanta.


Addu'a ta fara yi sannan ta zauna akan kujerar, babu ƙarya office dai ya haɗu iya haɗuwa, duk wani abu na ƙawatashi an zuba kuma masu tsada na gaske, ta ɗago kanta fuskata cike da takaici tace:


"Dole sai Ashraf ya ƙaraso zamu fara meeting, kayi abin da nace kawai Al'ameen, ai gaba ɗaya staff ɗin mu ne ba baƙi bane, kawai dai kowa a tabbatar da an tura masa da text message na shifting ɗin meeting ɗin, sannan ka kawo min mukullin office ɗin da nace a gyarawa Ashraf idan ya tambaya kace yana wajena sannan in ka fita ka turomin A'isha." 


Cike da ladabi Al'ameen ya amsa tare ficewa daga office ɗin.


Ita kuwa Nuratu shirye shiryen zuwa meeting ɗin ta fara ta hanyar fara daddanna laptop ɗin ta da already A'isha ta ɗora mata akan table ɗin, ba'a fi mintuna 2 da fitar Al'ameen ba A'isha ta ƙwanƙwasa ƙofar shiga office ɗin da Nuratu take.


"Yes" Nuratu tace sannan ta samu damar buɗe ƙofar tare da yin sallama, Nuratu ta amsa ba tare da ta kalleta ba sannan tace:


"Miƙo min kayan tea, nayi breakfast banaso na wuni da yunwa, duk wanda yazo kuma ya jira ni a waje."


Cikin ladabi A'isha ta amsa tare da aiwatar da abinda aka umarce ta.


 Bayan Nuratu ta kammala breakfast ɗin ta tana shirin miƙewa ta shiga toilet wayar ta ta fara ringing, sunan Daddy ta gani a jiki saboda haka ba shiri ta ɗaya wayar.


Bayan sun gaisa ya buƙaci da ta bawa Ashraf wayar zasuyi magana.


"Cikin rashin kulawa tace:


"Bai shigo nan ba." 


Cike da mamaki Daddy yace:


 "Na ce masa idan ya ƙaraso direct yazo office ɗin ki kafin na karaso ya akai haka kuma?"


Murmushin takaici Nuratu tayi sannan tace:


"Bana jin ma ya iso Company, saboda haka ma nayi shifting meeting ɗin zuwa 11:00am."


Cike da muryar faɗa Daddy ya ci gaba da magana:


"Akan me zakiyi shifting saboda shi kaɗai bayan an tura masa da text din duk wani schedule na meeting, ni da kaina da asuba na tambaye shi yace ya gani me zai saka ki daga meeting ba sai a fara babu shi ba..." 


Bai ƙarasa maganar ba Nuratu ta mai da hankalin ta kan ƙofar shigowa in da taga Ashraf ɗin sun shigo tare da Al'ameen yana bin bayan a.


Tayi ajiyar zuciya tare da cewa Daddy:


"Gashi nan ya shigo ma."


Cikin muryar faɗa Daddy yace:


"Bashi wayar"


Miƙa masa wayar kawai tayi tana kallon sa, don gaskiya babu hassada Ashraf yayi kyau sosai, suite ɗin daya saka ta karɓi jikin sa sosai, da sauri ta ɗauke kanta daga kansa don shi ma kallonta kawai yake yi don shima har ga Allah shigar tata ta birgeshi matuƙa.


Banda faɗa babu abinda Daddy ya dinga yi masa a wayar, saboda Daddy mutum ne ɗan ka'ida wanda yake respecting ɗin lokaci sosai, duk da Ashraf yaji haushi amma haƙuri kawai ya dinga bashi sannan daga bisani ya kashe wayar ya miƙa mata tare da neman wajen zama a ɗaya daga kujerun da suke gefen table ɗin ta. 


Shima Al'ameen zama yayi ,sannan Nuratu ta fara basu summary na abubuwan da meeting ɗin ya ƙunsa tare da yadda zai kasance.


Yanayin yadda take bayanin ya matuƙar bawa Ashraf mamaki yadda akai take da working experience haka, duk da yasan halin Daddy shima hardworker ne amma tabbas Nuratu ta bashi mamaki. 


Ta lura da yadda ya sauya lokaci guda, da yadda ya bata duk wani attention nasa hakan ya ƙara mata ƙwarin gwiwa wajen yi musa bayani tare da taimakon Al'ameen wanda daga ƙarshe tace idan akwai abubuwan da yake buƙata direct ya neme ta ko Al'ameen. 


Hakan yayi masa daɗi kasancewar shi daman yana da sauƙin hali wani lokacin mahaifiyar sa ce take sashi yayi wasu abubuwan.


Nuratu ta jingina bayanta da kujerar da take zaune ta kalli Al'ameen tace:


"Ka tabbatar da ka samar masa da duk wani abun buƙata a office ɗin nasa?" 


Cike da ƙwarin gwiwa yace:


"Yes! Everything is intact, sai dai idan ya shiga yana buƙatar wasu abubuwan sai yai min magana."


Jinjina kai tayi sannan tace:


"To ka kaishi ka nuna masa komai da komai." 


Amsawa Al'ameen yayi tare da miƙewa shima Ashraf yabi bayan sa.


Cike da mamaki Nuratu ta bisu da kallo, saboda yana yin da Ashraf yau yazo dashi ya bata mamaki, gaba ɗaya yayi sanyi kamar bashi ba, kuma ta lura da hakan har cikin ransa ne duba da yadda ta gani a ƙwayar idon sa da kuma yadda yake bin al'amura a sannu. 


Tabbas da Ashraf zai ci gaba a hakan da zasu samu daidaito a tsakanin su domin hakan ba ƙaramin faranta ran daddy zai yi ba, domin zasu haɗa hannu ne don su kawo ci gaba a kasuwancin su. 


Sai dai amma tana tsoron makircin Mummy ko ba komai ita ta haifi Ashraf dole tana da tasiri a rayuwar sa kasancewar bata ƙaunar ta ko kaɗan, duk da bata cika nuna hakan a zahiri ba amma bin diddiginta da take yi ta ƙarƙashin ƙasa da bincike kala kala ya nuna duk duniya bata da maƙiya irin ita da junior.


Misalin 10:50 na safe kowa ya hallara a wani keɓeɓɓen meeting room kuma ƙawatacce, wani dogon table ne a tsakiya sannan gefen dama da hagu an jera kujeru da microphone da sunan kowa da rank dinsa akai da kuma ruwa da lemo a ƙalla kowanne ɓangare akwai kujeru goma.


Sannan daga ɓangaren tsinin table ɗin akwai kujeru guda biyu ɗaya a gabas ɗaya a yamma, daga na yamma aka rubuta sunan NURATU da rank ɗin ta a jiki, ta ɓangaren gabas kuma sunan ASHRAF ne, wanda saɓanin shekarun baya Nuratu ce a bangaren gabas Daddy a mazaunın ta na yanzu. 


Hakan na nufin duk wani role na Daddy ya ɗauke shi cancas ya ɗorawa Nuratu tsawon shekara guda kenan. Wannan shine karo na biyu da zata jagoranci Annual meeting ɗin.


A yadda tsarin meeting ɗin yake, ba iya na ma'aikatan Company ne kawai ba, a'a har da sauran ma'aikatan kamfanonin Daddy da basu ma da alaƙa da wannan company.


Kasancewar Daddy ya mallaki a ƙalla manyan Company guda biyar, wanda ake sarrafa fata, kamfanin sarrafa timber zuwa katako, kamfanin robobi, kamfanin shinkafa, kamfanin sarrafa man gyaɗa da kuma kamfanin kwangilar gine gine wanda Nuratu take jagoranta a halin yanzu. 


Sannan bayan wadannnan akwai ƙananun kamfanoni da branches na buga bulo da abinda ya shafi ɓangaren dutse, furnitures da sauransu. 


Basu tsaya iya nan ba, duk abinda suke samarwa suna da manya da ƙananun shaguna a ciki da wajen Kano wanda ake siyar da abubuwan nasu a farashin ɗai ɗai ko sari.


Shi wannan taro suna yin sa duk shekara, sam bana ƙananun ma'aikata bane, na manajoji ne na kowanne Company,  da project managers ta ɓangarorin kamfanoni guda biyar ɗinnan kawai.


Kowanne ma'aikaci a cikin su zai kawo details da analysis na dukkan abinda ya faru tun daga farkon shekara zuwa ƙarshen ta, ta yadda zaiyi bayanin komai ribar da aka samu, ta hakan za'a tantace jarin da aka zuba a shekarar da kuma ribar da aka ci.


A wannan taron za'a yi taza da tsifa domin tabbatar da gaskiyar kowa da amanar sa. Kusan kowa daka kalla a wajen zuciyar sa fal take da saƙe saƙe saboda dayawa waɗanda akayi taron dasu bara basu bane a bana, kasancewar wasu su da yawa an kama su da laifin al'mundahana, sata da zambo cikin aminci. 


Duk yadda mutum yake da Daddy sallamar sa kawai yakeyi tare da kawo wasu, sai dai Daddy bazai bari mutum ya tagayyara ba musanman idan tsautsayi ne ya faru da mutum ko rashin ƙwarewar aiki zai ɗakko jari ya bashi yadda zai iya riƙe kan sa. 


Duk Shekara a wannan company ake gudanar da wannan taron kasancewar shine Company Daddy mafi girma.


Ɗakin taron ya cika da duk waɗanda suke da ruwa da tsaki, kowa yayi shiru zuciyarsa tana saƙa masa abubuwa da dama. Wannan shine lokaci mafi haɗari ga duk wani jijjige na waɗannan kamfanonin na Daddy, saboda yau za'a yi taza da tsifa a warware komai, kowa jikin sa a sanyaye yake Nuratu ta lura da hakan ta tausayawa wasu daga ciki wasu kuma tana kallon su ne kawai saboda tasan wannan shine karon su na ƙarshe a wannan tafiya. 


A hankali ta numfasa ta kalli kowa dake gurin daya bayan ɗaya fuskar ta sam babu alamar wasa, ta mai da hankalinta kan wani babban mutum mai kamala da siffar malamai, a ƙalla shekarunsa zasu kai 50 don duk yafi kowa shekaru a wajen. tace: 


"Bismillah malam Nuhu a buɗe mana taro da addu'a" 


Ya amsa tare da buƙatar kowa yaiwa Annabi salati.


Bayan kammala addu'o'in Nuratu ta fara bawa kowanne ɓangare dama domin gabatar da abinda ya dace. 


Cikin salo da tsarin kimiya da fasahar zamani kowa ya fayyace dukkan abubuwan da suka shafi ɓangaren aikin sa na wannan shekara tare da fitar da ribar da aka samu, manyan hanyoyin da aka bi domin samun wadannan ribar, cigaban da kowane bangare ya samu, yadda aka samu cigaban, ƙalubale asarori da aka samu da sauransu.


Sannan a ƙarshe kowa zai bada shawarwari ta ɓangaren sa ta yadda za'a magance kowacce matsala kokuma inganta kowanne ɓangare. 


Ba ƙaramin daɗi Nuratu taji ba ganin yadda ake samun sauyi me kyau a kowacce shekara, sannan da haɓakar riba da samun ci gaba ta kowanne ɓangare tun da ta fara jagoranci a wannan ɓangaren. 


Ta yaba sosai da ƙwazon kowa, ƙwarewa da jajircewar su matuƙa acikin ranta duk da bata fito da hakan a zuciyar ta ba, ta lura kuma da ɓarnar da wasu tsirari sukayi kuma suka binne ta ta yadda ba kowa ne zai fahimta ba. 


Duk da ɓata garin basu da yawa aciki, amma hakan bazai bari ta rabu dasu ba kowa sai ya fuskanci hukunci daidai da abinda ya aikata .


Ba iya Nuratu kaɗai ba, har Daddy da yake kallon tattaunawar daga office ɗin sa ta fasahar zoom yayi farinciki matuka tare da jinjinawa Nuratu wajen tsayawa kai da fata domin yaƙar al'mundahana da kuma almubazzaranci da dukiyar sa. Shikuwa Ashraf shiru kawai yayi yana nazarin wadannan ƙwarewa ta ma'aika tare da mamakin dabarun da kowa yake bi ta ɓangaren aikin sa.


Shiru ɗakin taron yayi, idanuwa gaba ɗaya suna kan Nuratu wanda itace committee zartarwa, ta lura da halin da kowa yake ciki amma sam ko a jikin ta hankalin ta na na kan laptop ɗin ta tana danne danne. 


Bayan wani ƙankanin lokaci ta ɗago ta kalli kowa taiwa Allah godiya ta jinjina musu, sannan ta bawa kowanne ɓangare shawarwari tare da yi musu takaitaccen wa'azi akan gaskiya da riƙon amana sannan daga bisani ta miƙe domin gabatar da nata report ɗin kasancewarta wadda take jagorantar '.   'A.A MAI HULA CONSTRUCTION COMPANY'


Ba ƙaramin mamaki kowa yayi ba da jin bayaninta, musamman yadda tasan dabarun  kasuwanci, wayo da siyasa, sannan kuma uwa uba ribar da akayi generating a shekara guda, sannan da manyan ayyukansa da suka gabatar kama daga kan manyan tituna, gadoji da manyan gine-ginen gwamnati.


Tabbas Nuratu ba karamin bawa kowa mamaki tayi ba, ciki har da Ashraf wanda kawai tsayawa yayi yana kallonta can cikin zuciyar sa tana raya masa abubuwa da dama amma, magana ta gaskiya ta birgeshi duk da yasan ita ɗin rainon Daddy ce amma ita ma tana da tata baiwar.


Misalin 2:15 na rana Nuratu ta kammala nata bayanin, abun gwanin sha'awa kuma tayi shine cike da koyawa kowa darasi don kowa yaci gaba da gudanar da nasa aikin cikin kwarewa. 


Bayan ta kammala ta buƙaci kowa yaje yayi Sallah ayi Lunch zuwa 5:00 na yamma za'a dawo domin a ɗora daga inda ka tsaya.


Sannan ta buƙaci duk waɗanda akayiwa text message da su kasance a office ɗin daddy misalin ƙarfe 3:00 na rana domin amsa wasu tambayoyi. 


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol