Free chapter · Read without an account
Chapter Four (Mafari)
Misalin ƙarfe 9:30 na dare likita ya fito daga ɗakin daya duba Auwal, miƙewa gaba ɗayan su sukayi suka nufo inda yake.
Fuskar likitan babu yabo ba fallasa yace dasu:
"Ku kwantar da hankalin ku, ya samu raunuka ne a cikin sa amma inshaAllahu mun samo kan sa, amma yana bukatar ya huta sosai na kwanaki"
Ajiyar zuciya gaba ɗayan su sukayi, sai sannan Nuratu ta dawo cikin hankalin ta, ta mai da hankalinta kan wayar ta taga missedcall ɗin Anuwar da Ameera rututu sai sannan ta tuna dasu, cikin sauri ta fara laluben layin Anuwar.
Bugu ɗaya Anuwar ya ɗauka tare da faɗin:
" Ukhty lafiya ina kuka shiga ne duk hankalin mu ya tashi gashi kin ƙi ɗaga waya?"
Numfasawa tayi ta kalli Mummy wadda tun ɗazu ta tsira mata ido cike da tsana sannan ta ɗauke kan ta tace:
"Ɗaya daga cikin staff ɗin mu ne ya gamu da tsautsayi, infact yanzu haka muna asibiti saboda haka ku tafi gida kawai ina jin anan zan kwana.."
Wani irin ɗagowa Ashraf yayi ya kalleta cike da tashin hankali, duk da yana cikin tarkon kallon banzar da Mummy take musu shi da Nuratu amma hakan bai saka ya kasa ƙurawa Nuratu ido ba cike da tashin hankali, wani irin baƙin kishi yaji yana addabar sa kamar ya mutu, bazai taɓa iya jurewa ba hakan yasa ya fice ya bar asibitin.
Ita kuwa Nuratu lallashin su Anuwar taci gaba dayi a waya har suka haƙura suka tafi, duk da tasan baza su ji daɗi ba saboda ba wani sabawa suka yi da rashin ta ba, amma dole su haƙura saboda tasan Auwal ba ɗan garinnan bane.
Auwal ɗan Kaduna ne, aiki ne ya kawo shi Kano, duk da akwai ma'aikatan lafiya da zasu kula dashi sosai a asibitin amma yana da kyau ace yana ganin wani a kusa dashi, duk da bata san dalilin da ya saka Ashraf yai masa wannan irin dukan ba, amma jikin ta yana bata kamar itace sila.
Katse mata tunanin ta Daddy yayi a lokacin da ya dawo in da suke, kasancewar ya matsa domin ya amsa waya, kallo ɗaya yayi mata sannan yace:
"Nuratu yakamata ki tafi ko?"
Sunkuyar da kanta tayi sannan tace:
"Nayi musu waya nace su tafi akwai key din mota na a hannun Anuwar zan kwana anan zuwa da safe"
Girgiza kai kawai yayi ya jinjina irin tausayin da Nuratu take dashi da kuma kulawa, duk da zuciyar sa bata so hakan ba amma dole ya daure saboda rage zargin da ake musu yace:
"Bakomai Allah ya tashe mu lafiya"
Ya juya ya nufi hanyar fita Mummy ta bi bayan sa tana watsa mata harara.
Murɗa ƙofar shiga ɗakin da Auwal yake tayi tare da yin sallama ƙasa ƙasa, duk da bata ji ya amsa ba ga dukkan alama bacci yake yi, ta ajiye wayar ta ta nufi toilet, a nutse duk ta wanke make-up ɗin da take fuskar ta, sannan ta ɗauro alwala ta dauki dadduma (kasancewar asibitin akwai komai na buƙata) ta rama sallar magrib sannan ta ɗora da Ishaa.
Tana zaune tana istigfarin jinkirta sallar da tayi ta fara jin alamar motsi, cikin sauri ta juyo taga Auwal yana motsa hannun sa, da hanzarin ta ta miƙe ta nufi in da yake ta tsaya dai dai kan sa, ya buɗe idon sa yayi arba da ita ya saki wata ajiyar zuciya, sannan ya buɗi bakin sa a hankali yace:
"Thank you so much I'm really love you!"
Murmushin ƙarfin hali kawai tayi sannan tace:
"Sannu ya jikin naka?"
Idon sa kyar akan ta yace:
"Da sauki tun da na farka na ganki kusa da ni"
Murmushi ta sake yi a karo na biyu sannan tace:
"Allah ya ƙara afuwa."
Girgiza mata kai kawai yayi sannan ya mai da hankalinsa kan ruwan da ake ƙara masa, ya ɗago hannun sa ya ganshi a kumbure ya mayar ya ajiye sannan ya saka ɗaya hannun ya shafa gefen leɓen sa in da yaji shi shima a kumbure, sannan ya sake mai da hankalinsa kan Nuratu wadda duk ya bata tausayi yace:
"Don Allah meye tsakanin ki da Ashraf da har zai min wannan dukan saboda nace ina son ki kuma zan aure ki? Please kar kiyimin ƙarya Nuratu."
Silalewa tayi daga tsaiwar da tayi a hankali ta zauna akan kujerar da ke gefen gadon ta dube shi kamannin sa gaba ɗaya sun sauya, idon ta ya fara kawo ƙwalla tayi sauri ta kau da kan ta tace:
" Babu komai tsakanin mu"
Murmushin ƙarfin hali Auwal yayi ya gyara kwanciyar sa sannan ya kalleta yace:
"To yana son ki, so kuma sosai saboda naga hakan a idon sa, amma don Allah Nuratu ki dube ni nafishi buƙatar ki, tun da na rasa matata watan mu uku da aure ban ƙara jin inason ko wacce mace a duniya ba in ba ke ba, don Allah Nuratu ki taimaka min bana jin zan kai labari in babu ke!"
Cikin Murya mai abun tausayi ya ƙarasa maganar tasa. Ita kuwa Nuratu kan ta ne ya kulle ta rasa me yake mata daɗi zuciyar ta tana saƙa mata abubuwa da dama, tabbas tasan idan tace zata karɓi soyayyar Auwal yaudarar sa kawai zatayi saboda ta riga da tasan ba auren sa zata yi ba babu wani namiji da ta ke da hurumin saurara a yanzu.
Vibration ɗin wayar ta ne yasa ta dawo daga dogon nazarin da tayi, saƙo ta gani daga Daddy kamar haka:
" NURATU NASAN KE YARINYA CE MAI HANKALI DA TARBIYYA DA ILIMIN ADDINI, NA BAR KI NE KAWAI SABODA NA KAU DA ZARGI A IDON MUTANE, AMMA BA DON SON RAI NA BA INASO KI DINGA TINA MATSAYIN KI A KODA YAUSHE TARE DA KILLACE KANKI KAR KI SHIGA HURUMIN UBANGIJI KINJI!"
Ƙurawa saƙon wayar ido tayi sannan ta sa hannu ta goge ƙwallar da take ƙoƙarin gangaro mata, ta rasa me yasa wannan ya zama raunin ta a rayuwa, shi kaɗai ne yanayin da yake sakata kuka.
A hankali ta mai da hankalin ta kan Auwal da yake kallon ta zuciyar ta fal da tausayin sa, ta rasa wacce irin amsa zata bashi, zuciyar ta ta kasa yarda cewar Ashraf yana son ta ne, kawai tasan makirci suke ƙulla mata shi da mahaifiyar sa.
A hankali ta buɗe bakin ta tace da Auwal:
"Ka kwantar da hankalin ka, ita mace da kake gani rabo ce idan Allah yayi ni matar ka ce zamuyi aure mu rayu cikin farin ciki,idan bai ƙaddara ba bazai taɓa yiwu ba, haka zamuyi hakuri duk da ni a yanzu ba auren ba ne a gaba na amma hakan ba yana nufin nayi rejecting, abin da nake so da kai shine ka kwantar da hankalin ka kawai ka daina damuwa ka rasa matar ka ma ka rayu kai ta addu'a ita ce magani."
Ta ƙarasa maganar a ciki sigar lallashi. Duk da Ahmad ya fahimci in da ta dosa, gashi kuma ya haɗa takara da Ashraf amma dolen sa ya haƙura ya kwantar da hankalin sa amma hakan ba yana nufin ya hakura da ita gaba ɗaya bane.
Misalin 12:00 na dare Nuratu na zaune tana nafila ta juya ta kalli Auwal wanda yayi nisa cikin baccin sa sakamakon allurai da yasha, bata san me yasa yake bata tausayi ba, miƙewa tayi ta nufi fridge domin ta ɗakko ruwa, bayan ta ɗakko ta juyo kwatsam! kamar daga sama taga Ashraf a tsaye sanye da riga da wando na truncksuit baƙaƙe kan sa da hular sanyi.
Ba ƙaramin tsoratata yayi ba, hakan ya saka ta fara ja da baya, ganin halin da ta shiga ne ya saka shi rarumo hannun ta da sauri ya jawo ta suka fice daga ɗakin.
Haka ya dinga janta kamar wata ƙaramar yarinya ita kuma tana binsa a tsorace, tana tsoron tayi ihu ta sake haddasa wata fitinar, ba yadda tayi haka tabi bayan sa ta zubawa sarautar Allah ido.
Sai da suka nufi inda yayi parking ɗin motarsa sannan ya juyo har yanzu hannun sa riƙe gam da nata sannan yai mata nuni da ta shiga cikin motar, "nan fa ɗaya ta furta a ranta", haka tayi ƙememe taki shiga motar.
Ganin alamar da gaske take bazata shiga ba, ya saka hannunsa da ƙarfin tsiya ya juyo da ita dai dai jikin motar ya saka hannun sa ɗaya ya rufe mata baki ya haɗe cinyarsa da tata ya matse ta ajikin motar suna fuskantar juna idon sa cikin nata sannan yace:
"Me wancan banzan ya fini dashi da har zaki zaɓe shi sama da ni? to ina so ki sani ni bani da kishiya iyaye na ma ni kaɗai suka haifa a duniya babu wata mace da ta isa na so ta sannan ta haɗa ni da wani, saboda haka idan kinaso ya rayu lafiya ki rabu dashi don wallahi zan iya raba shi da duniya akan ki."
Numfashin ta sama sama ta zaro ido tana kallon sa gashi ya rufe mata baki numfashin ta ya fara fita daƙyar, tsoro ne fal a fuskar ta musamman da ta lura kamar ba'a hayyacin sa yake ba, kamar yasha wani abu.
Cikin sauri ta fara ƙokarin kwacewa iya ƙarfin ta amma tsananin matsar da yayi mata yayi yawa bazata iya ba saboda ba ƙarfin su ɗaya ba.
Hannunta guda ɗaya ta fara ƙoƙari kwacewa daga nasa amma ina abun yaci tura, tsananin azabar matsar da yayi mata ya saka ta fara hawaye bata sani ba, jin alamar hawayen ne ya saka ya sake ta, a hankali ta silale ta zauna a dandagaryar ƙasa duk jikin ta yayi sanyi, fuskarta tayi ja sosai hawaye ne kawai suke zubowa daga idon ta.
Zuciyar ta fal da tunani shin yau she zata samu sauƙi ne a rayuwar ta? ta yaya zata iya rayuwa da wannan wanda har yanxu bai gama nutsuwa ba? ga alamar shaye shaye nan ƙiriƙiri a tattare dashi. Tabbas tasan a yanayin da yake magana zai iya yiwa Auwal komai, hankalin ta ne ya koma kan sa tuni ta miƙe da shirin komawa cikin asibitin.
Caraf! ta sake ji ya riko ta ta baya ya fincikota ya haɗa ta da jikin sa, wani irin yana yi taji ta shiga, shi kan sa sai da yayi wata sanyayyiyar ajiyar zuciya.
Kicikicin kwacewa ta fara yi amma yafi ƙarfin ta zata yi masa ihu ya sa hannu ya rufe bakinta ya ɗauketa cancas ya nufi wajen mota.
Duk da zame zamen da take yi amma hakan bai saka ya kasa buɗe gaban motar ba ya saka ta aciki ya rufe ta sannan ya sunkuyo ta glass ɗin motar sai lumshe ido yake alamar a bige yake yace mata:
"Nayi rantsuwa baza ki kwana a asibitin nan ba idan kuma kika takura, in few minutes zan saka ayi poisoning ɗinsa wallahi."
Hannayen ta ta saka guda biyu ta toshe bakin ta cike da tashin hankalin maganar sa, hawaye tuni su gama jiƙa mata fuska, ba yadda zata yi haka ta haƙura ta fawwalawa Ubangiji.
Zagayowa yayi ya shiga motar ya jata da mugun ƙarfi.
Zuciyar ta banda bugawa ba abinda takeyi kuka ne ya sarƙe mata cike da tunanin halin da Auwal yake ciki, juyowa tayi tana kallon sa fuskarsa a ɗaure ba alamar rahma ko kaɗan tace:
"Don Allah kar ka cutar dashi bashi da laifi don Allah na roƙe ka!"
Ko kallon ta baiyi ba ya ci gaba da tukin sa kamar zasu tashi sama saboda gudu ga titin yayi shiru babu mutane sosai.
Ta lura bashi da alamar kulata hakan ya saka ta mai da kanta ta jingina da kujerar motar tana kallon hanya zuciyar ta sai bugawa takeyi ta rasa me zatayi, a hankali ta fara kiran 'Hasbunallahu wani'imal wakeel' acikin zuciyar ta ko zata samu sauƙin halin da take ciki.
Wani katafaren gidan gona ya nufa ya nemi wani waje yayi parking ɗin motar tasa, cike da hanzari ya fita daga motar, tana jin sa yana yiwa masu aikin wajen warning akan kar su faɗawa kowa yana nan.
Ita kuwa Nuratu gaba ɗaya ta sukurkuce, kan ta jingine da kujerar motar ta rasa me yake mata daɗi, ga wani sarawa da kan ta yake yi, gashi ko wayarta bata ɗakko ba ballantana ta nemi ceto.
Gani tayi ya buɗe murfin motar yana yi mata alamar ta fito, jikin ta a sanyaye ta fito tana laluben mayafinta can ta gama dubanta bata gan shi ba hakan ya saka ta haƙura tabi bayan sa kamar wata sokuwa.
Wani ƙayataccen palour suka shiga wanda akai masa ado da leather chairs ya tsaru sosai, jagwaf! Ashraf ya zauna a ɗaya daga cikin kojerun da suke palour ya jingina bayan sa ya lumshe idon sa kan sa na kallon sama, ita kuwa Nuratu tsayawa tayi ba tare da ta ƙaraso ba tana ƙarewa palour kallo, zuciyar ta ba sai an tona ba kowa yasan ba daɗi.
A hankali ya buɗe idon sa ya maida hankalin sa kanta, ya ƙura mata idanu, yana rayawa a ransa shi fa duk yana yin da take ciki birgeshi take yi, in ma tana kuka in ma tana murmushi, bai ga wata makusa a tare da ita ba, zuciyar sa sai azalzalarshi take yi akan ta, ya riga yasan ko waye shi akan abinda yake so babu abinda bazai iya aikatawa ba, wani zazzafan kishi yaji ya ƙara baibaye zuciyar sa da ya tuna da yanayin da ta shiga da yace zai cutar da Auwal, tabbas fa idan bata fita a sabgar sa ba Wallahi da gaske zai iya illa ta shi.
Miƙewa yayi yana haɗa hanya ya nufo in da take, duk da a tsorace take dashi amma ta daure zuciyar ta, ta ɗago kai ta kalle shi a dai dai lokacin da ya tsaya daf da in take, ya rarumo hannun ta, cike da ƙwarin gwiwa ta fizge, murmushi kawai yayi sannan yace:
"Kiyi haƙuri, bani da hakuri ne akan abin da nake so ban saba da hakan ba, a ko da yaushe nasara na sani a rayuwata ba faduwa ba, inaso ki kwantar da hankalin ki, sam bani da niyyar cutar da ke, infact na zaɓi na kawo ki nan ne saboda na kasa jure ganin ki zaki kwana da wani, bana so gari ya waye ina wannan yanayin saboda komai zai iya faruwa dashi."
Ya numfasa sannan ya ci gaba da magana:
"Nuratu kece mace ta farko da ta kafa min tarihi na farko da naji kin shiga raina a ƙanƙanin lokaci kuma nasan baki da hakki ne akan mu Ni da Mummy, bazan ɓoye miki ba mun shirya akan mu tarwatsa alaƙar ki da daddy ne ta hanyar bijiro muki da soyayyar bogi sai Allah ya kama ni naji kin shiga rai na fiye da kima."
A hankali ya durƙusa a gabanta idon ta sam ya soye babu alamar tsoro ko tausayin sa, ya durƙusa akan gwiwoyin sa ya riko hannayen ta guda biyu yace:
"Wallahi, billahi inason ki tsakani na da Allah bani da niyyar cutar dake, Nuratu ki taimaka min, a ƙasa da sati ɗaya na rasa in da zan saka kai na don Allah ki taimaka min kinji."
A cikin sigar tausayi da lallashi ya ƙarasa maganar.
Ita kuwa Nuratu sam bai bata tausayi ba, saboda sarai tasan makircin Mummy, fizge hannun ta tayi taja da baya ta fara murɗa ƙofar fita.
A kulle gam ta jita ko motsi bata yi, kifa kan ta tayi a jikin ƙofar zuciyar ta tana mata wani irin zafi, ga tambayoyi da takewa kan ta, "me zance ce da KANNENA? a wanne hali suke su da ɗa na? wace amsa zan bawa Daddy gobe? Shin wannan hali Auwal yake ciki? Karfa ya rasa rayuwar sa saboda ni."
Ji tayi ya rungumota ta baya sai wata ajiyar zuciya yakeyi mai ban tsoro, ya ɗora kan sa akan wuyan ta yana faɗin:
"Bana so na cutar dashi ki cire shi a ran ki Please!"
Ya sa hannu ya juyo da ita duk da fizgewar da take yi hakan bai hana ya fuskanto da ita gare shi ba yace:
"Muje na raka ki in da za ki kwanta dare yayi sosai."
Wani ƙayataccen bedroom ya nufa hannun sa riƙe da nata, ya zaunar da ita a gefen gadon sannan ya miƙe ya nufi ƙofar fita, sai da ya kama murfin ƙofar sannan ya juyo ya ce mata:
"Sweet dreams, I love you so much!"
Ya fada tare da ficewa daga ɗakin.
Cikin sauri ta miƙe ta ƙarawa ƙofar key sannan ta barshi a jiki yadda koda an saka key ta baya bazai buɗe ba, durkushewa tayi a ƙasa ta tura kanta tsakanin cibiyoyinta ta fara rubzar kuka ƙasa ƙasa, zuciyar ta kamar ta tsage, ta fara hasaso rayuwar da tayi a baya, bazata taɓa butulcewa Ubangiji ba kuma bazata taɓa cewa Allah ya karya jarabce ta ba saboda dai dai yake da tace Allah ya rabata da imanin ta saboda shi da kan sa ya faɗa muminai masu ƙarfin imani yake jarabta.
Da wannan tunanin yasa zuciyar ta ta sanyaya, gaba ɗaya taji kayan jikin ta sun dame ta, idon ta ta ɗaga ta kalli agogon da yake manne a bangon ɗakin misalin ƙarfe 1:45 ta gani na dare, miƙewa tayi ta nufi wata ƙofa da ke gefen bedroom ɗin tana tunanin toilet ne.
Ai kuwa toilet ɗin ta gani, ta mai da ƙofar ta rufe ta dawo ta zauna a gefen gadon, can zuciyar ta ta raya mata wani abu, ta miƙe da sauri ta nufi wardrobe ɗin da take ɗakin, da mamakin ta ta ga kayan bacci na mata da abayas da hijabs da kuma wasu dogayen riguna na materials na zaman gida, can kuma ta hango underwires duk sababbi don ko wanne da tag a jiki.
Juya kayan ta fara yi a hankali in da ta fara rayawa a ranta "wato daman ya shiryawa zuwa na nan" mai dasu tayi ta nufi toilet cike da mamaki, tayi wanka ta ɗauro alwala ta dawo ta nemi wata doguwar riga material mai saukin nauyi ta saka da dankwalinta saboda tayi alƙawarin baza ta saka nightdress din ko ɗaya ba.
Ta miƙe sosai akan lallausan gadon, ta lulluɓata ta kashe fitilar duk da tasan baza ta iya yin bacci ba, hankalin ta ya rabu gida gida ta rasa tunanin wanne ɓangaren zatayi, a zahiri tana tausayawa ƙannneta, ɗan ta da kuma Auwal, amma a badini ta san itace babbar abar tausayi saboda matsalar kowa mai sauƙi ce akan tata.
Duk da kokawar da take da bacci don kar ya ɗauketa sai da ta kasa controlling kanta, kasancewar ta gasa jikin ta da ruwan zafi ga gajiya kala-kala a tare da ita ga bashin bacci da taci kwana biyu bata san lokacin da bacci yayi awon gaba da ita ba.
Ta bangaren Ashraf kuwa, neman waje yayi a ɗaya daga cikin kujerun palour ya zauna, ya jingina bayan sa, ya ɗaga kansa sama daƙyar yake iya buɗe idon sa saboda ƙwayoyin da ya sha sunyi masa yawa, duk da ya rufe ko ina na gidan amma gani yake kamar Nuratu zata gudu.
Yau tsawon shekara biyu kenan rabon da ya sakawa cikin sa kayan maye saboda gudun lafiyar jikin sa amma gashi yau saboda sanadin Nuratu ya koma ruwa, tabbas idan bata amince da shi ba zai iya rasa rayuwar sa gaba ɗaya.
Want the next chapter?
ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol