Free chapter · Read without an account
Chapter Seven (KANNENA)
Haka motar tai ta tafiya damu, bamu san inda zata kaimu ba, nidai fatana koma ina ne muje amma banda inda aka san mu, ina ji ina gani na bar yankina inda al'umma ta take, mahaifata, inda iyayena suka rayu kuma suke a kwance a ƙabari, ban ƙara marmarin komawa wannan wajen ba har izuwa yau da nake baku labari.
Tsawon awanni kamar uku muka iso cikin gari, bansan me driver motar ya tsaya yi ba, nidai dana tabbatar da mun shigo birni kawai na lallaɓa muka sako daga motar Ba tare da wani ya lura da mu ba.
Dirar mu wannan waje ke da wuya na ci karo da wata irin al'umma, mai mabanbantan dabi'a da wadda na baro a abaya, kowa harkar sa yakeyi, ga wani irin ƙauri da yake a gurɓace a iskar da suke shaƙa, ga ƙara ta nau'in ababen abun hawa da injina, surutai barkatai sannan ga yawaitar tituna da ababen hawa.
Haka na ja KANNENA muka koma gefe muna nazartar wannan sabuwar duniyar da muka tsinci kanmu, inda muka tsaya kan hanya ne hakan ya saka ababen hawa da na mutane sukayi mana caaaa! akan mu matsa, saboda sautin horn ɗin ababen hawa daƙyar na iya samun gefen hanya na sukuya na toshe kunne na, saboda ji nayi kamar zasu fasamin kunne.
Ashe bani kadai ba Anuwar ma hakan, Ita kuwa Ameera kuka kawai ta saka ta rukunƙume ni, ganin hakan ya saka na sunkuya na zaro ɗaya daga cikin zannuwana na goyata, saboda Ameera bata da rigima sam, nasanta ba karamin abu ke sata kuka ba tunda daman can nice uwar rainon ta.
Kama hannun Anuwar nayi, nayi ta maza na karasa bakin titi, kasancewar naga tsallaken yafi wadataccen wajen zama, na rasa yadda zanyi na tsallaka, gashi na lura kowa harkar sa yake yi ba ruwan sa damu.
Sai can karatun da akayi mana tun a primary ya faɗomin, malamin mu na social studies yace mana idan muka kasa tsallaka titi ko muna tsoro to mu samu wani babba mai hankali ya tsallakar da mu. Da wannan dabarar yasaka na fara waige waige domin neman wanda zai tsallaka damu.
Can muna tsaye na hango wani babban mutum zai tsallaka, na ƙarasa kusa dashi nace masa:
"Don Allah Malam ka daure ka tsallakar damu"
Duk da yayi mamakin ganina da girmana amma na furta masa hakan, amma bai ce komai ba ya kama hannun Anuwar ni kuma na ƙanƙame shi muka tsallaka.
Bayan mun tsallaka naga ya shiga wani masallaci, saboda a dai dai lokacin an kira sallar magrib, haka nima na nemi buta mukayi alwala muka zagaya ta bayan Masallacin muka bi jam'i, duk yadda Anuwar yayi akan zai shiga Masallacin na hana shi.
Bayan mun idar Anuwar ya fara min kukan yunwa, naita waige waige ban ga abinci ba ko da na siyarwa, can na hango wata tana suyar awara na zaro Naira ɗari na bashi nace yaje ya siyo mana.
Bayan ya siyo ya dawo ya ajiye mana muka zauna muka ci muka sha ruwa a wani burtsatse da yake gefen masallacin, sai sannan hankali na ya ƙara tashi na fara tunanin inda zamu kwanta, ga Ameera tayi min bacci ga Anuwar ma yana layi.
Mikewa nayi na sake goya Ameerah a bayana, Anuwar ya ɗakko mana kayan mu muka nufi wani lungu da naga mutane suna shiga mukai ta tafiya kamar muna da wajen zuwa, sai da muka zo ƙofar wata primary sannan Anuwar ya cije shifa ya gaji ya fara min kuka.
Tsayawa nayi ina rarrashin sa, wannan dattijon da ya tsallakar damu titi ne naga ya fito daga get din makarantar yana shirin kullewa, nan fa na matsa kusa dashi ina rokon sa akan don Allah yabar mu mu shiga ciki mu kwana bamu da inda zamu kwanta.
Da farko dai yaƙi saboda yace doka ta hana yin hakan, amma ganin yadda Anuwar ke ta kuka nima inayi ya saka ya dudduba yaga babu kowa sannan ya buɗe mana muka shiga, ya sake buɗe mana wani waje da gani staff room ne na malamai saboda har da fanka yace mu kwanta anan amma karmu sake mu fito sai yazo. Cike da murna nace masa to nayi godiya ya fice.
Kayan mu na kwance na ɗakko ragowar zani na na shimfiɗa mana muka kwanta, can kamar minti goma da fitar mai gadin nan naga ya dawo hannun sa da maganin sauro da ashana ya miƙo mini sannan yace min ya ɗebo mana ruwa a botiki yana waje idan zamuyi amfani dashi.
Cike da farin ciki na karɓa nai masa godiya sosai, na miƙe nayi alwala nayi sallar Ishaa sannan na kwanta zuciyata fal tunanin iyayena, da dangina, bansan sanda kuka ya ƙwace min ba.
Sai da nayi mai isata, amma abinka da babu fargaba yau bansan sanda bacci ya daukeni ba.
Washegari tun asuba mai gadin nan ya shigo bayan an idar da sallah ya tashe ni nayi sallah sannan ya nemi kan wata kujera ya zauna ya kalle Ni yace:
"Meye sunan ki?"
Na kalleshi cike da girmamawa nace masa:
"Nuratu!"
Sannan ya kuma cewa:
"Ina iyayen ku? Sannan wadannan yaran ya kuke dasu?"
Nan fa na fara inda inda sannan can dabara ta faɗo min sannan nace:
"A hannun matar baban mu muke take musguna mana shine muka taho wajen yayan mahaifiyar mu kuma muka zo muka sunyi tafiya kuma bamu san kowa ba shine muke neman in da zamu zauna kafin su dawo.."
Girgiza kan sa yayi sannan ya sa ke kallo na yace:
"Kin ga zaman ku anan bazai yiwu ba saboda makaranta ce hakan ya saɓawa doka, saboda naga kuna bukatar taimako ne na bar ku, saboda haka zan kai ku gidan mai unguwa nayi masa bayani duk abinda ya yanke a kanku shikkenan."
Cike da farinciki na amsa saboda nima kai na nasan zaman mu anan ba mai yiwuwa bane.
Bayan gari ya gama wayewa wannan bawan Allah mai gadin ya siyo mana kayan karin kumallo koko ne da ƙosai, haka muka sha muka ƙoshi sannan ya umarce mu da mu fito domin zuwa gidan mai unguwa.
Bayan isar mu gidan mai unguwa ya labarta masa komai tun daga tsallakar damu titi da yayi har zuwa kwanan da muka yi.
Mai unguwa ya jinjina kai sannan ya kalleni yayi min tambayoyi na bashi amsa amma ba tare da na faɗa masa sunan garin mu da kuma asalin abin da ya rabamu da gida.
Can ya numfasa ya kalli Malam Habu maigadi (kamar yadda naji sun kira shi) yace:
"Na lura yaran nan suna bukatar taimako, kuma kaga yadda zamani ya sauya mutane an koya musu tsoro da rashin yarda, amma a maganganun ta na lura ba karamar wahala suke sha ba, amma babu komai zasu zauna a wajena har zuwa lokacin da kawun nata zai dawo daga tafiyar sai muji daga bakin sa."
Ƙirjina ya hau bugawa da jin wannan kalaman nasa saboda nasan babu wani kawuna a wannan garin hasalima bamu da kowa a nan hankali na ya tashi na fara tunanin kuma yadda zan ɓullowa lamarin.
Haka muka zauna a gidan mai unguwa tsawon sati biyu cikin kyara da tsangwama, kowa ƙyamar mu yake yi musamman amaryar sa Baba Mero, bata ƙaunar mu kwata kwata, ƙarshe ma ta fara kiran mu da Mayu saboda wani zazzabi da tayi ta kwanta wai sai mun tsallake ta.
Mutanen unguwa aka taru a kan mu ana zagin mu da cin fuska kala kala saboda sharrin da Baba Mero tai mana, shi kuwa mai unguwa bashi da tacewa saboda kamar tsoron ta yakeji.
Muna tsaye a ranar da tace sai na tsallaka ta mutanen unguwa sun taru sun mana caaaa! nikuwa nayi fafur naƙi saboda nasan ni ba mayya bace saboda ina tsoron sharrin mutane kamar yadda akayiwa wata a garin mu, idan na tsallaka ta miƙe tace ta warke kunga zargin maita ya tabbata kenan.
Daƙyar muka samu wani malami ya raba rigimar, Baba Mero ta watso mana kayan mu soro tace bazamu sake kwana a gidan ba, ganin dare yayi na roƙeta daƙyar ta barmu muka kwana a soro.
Washegari tun da duku duku na tashi na shirya su Anuwar na miƙe na goya Ameera a baya na, jikin ta zafi rau da zazzaɓi ta kwana, ga yunwa, da ita muka kwana, duk da ba samun isasshen abinci mukeyi a gidan ba amma dai yafi babu, rabon mu da abinci tun kokon da mukasha da ƙosai guda uku uku na jiya.
Gashi duk kudin hannuna sun kare a sai mana abinci saboda baya isar mu, haka na kama hannun Anuwar mukai ta tafiya bamu san in da zamuje ba, har muka iso unguwar Kurna muka nemi wata barandar masallaci muka zauna muna kallon mutane idon mu yayi zuru zuru saboda yunwa da azabar tafiyar ƙafa.
Hankali na na mayar kan Ameerah da taketa numfarfashin zazzaɓi, idon ta a rufe ruf ko buɗewa batayi, nan fa naji zuciya ta tayi rauni na fara hawaye, hakan Anuwar shima ya fara yimin kukan yunwa.
Na rasa yadda zanyi dasu, haka nace da Anuwar ya zauna da Ameerah ina zuwa, na miƙe na nufi bakin titi ina ta kallon mutane zuciya ta tana rayamin na roƙe su ko zamu samu abinda zamu ci na kai Ameerah ko da chemist ne, amma wata zuciyar tana gargaɗi na akan kar nayi babu kyau saboda karatun da naji Baffa na yayi akan nau'in azabar da za'a yiwa masu roƙo ranar alkiyama.
Haka na hakura na ci gaba da zagayawa, can na hango wata rumfar mai abinci alamajirai sun baibaye za'a yi musu sadaka, aikuwa haka na tsallaka naje na nemi waje na raɓe ina kallon su.
Bayan an kammala sadakar mai wajen abincin ta kalleni tace:
"Ke! ba an gama sadakar ba, ki wuce ki tafi, ko baki samu ba?"
"Eh! ban samu ba ni da Kannena."
"Ina ƙannen naki suke?"
"Suna can jikin wani masallaci."
"Jeki ki taho dasu."
"Toshikkenan"
Da sauri na nufi inda suke, na tarar da Anuwar yana ta gyangyaɗi, na tashe shi na goya Ameerah, sai da naji wani iri saboda zafin da jikin ta yayi sannan na kamo hannun sa muka tafi.
Muna isa ta kalle mu ta girgiza kai sannan ta ɗakko wata tasa mai faɗi ta zuba mana tuwon shinkafa da miyar taushe, baza taɓa mantawa da Baba Rabi ba.....
Haka muka zauna muka fara ci, na lallaɓa Ameera taci, ashe daman larurar tata da yunwa, Baba Rabi ta saka aka siyo mata magani tasha sannan ta kalleni ta fara mini tambayoyi akan dangina da iyaye na.
Ban faɗa mata gaskiya ba saboda nasan tabbas za'a ce za'a mayar damu, hasali ma sai da naja kunnen Anuwar, nasan dai nace mata iyayen mu sun rasu matar babanmu ce take gallaza mana muka gudo.
Baba Rabi tayi min faɗa sosai sannan tace idan zan iya sai na dinga yi mata wanke wanke tana bamu abinci.
Banyi musu ba na bata amsa cikin sauri cike da murna daman abinda nake buƙata kenan.
Haka muka ci gaba da zama da ita, ta bamu daki acikin gidan ta muka zauna, ni daman bani da ƙiwar aiki Innata ba abinda bata koyamin ba, haka zanyi mata aikin gida da na rumfar abincin ta babu ruwa na, babbar matsalata a yanzu shine ta yaya zamu koma makaranta.
Mun zauna a wajen Baba Rabi na tsawon wata biyar babu kyara babu ƙorafi ko tsana kullum cikin saka min albarka takeyi, ta saka Anuwar da Ameerah a makarantar allo sannan tai min alƙawarin idan an fara ɗiban dalibai duk zata mai damu makarantar boko.
Ba karamin daɗi naji ba, hakan ya saka na sake zage damtse nai ta kyautata mata ba dare ba rana, har na fara koyon yadda take girke girken ta na fara tayata, da lokacin fara ɗaukar ɗalibai yazo ta ɗauke ni mukaje kasuwa ta sai mana uniform da litattafai murna kamar me har kuka nayi.
A Safiyar wata Asabar ina zaune ina yin wanki da kayan mu da na Baba Rabi kawai wasu mata suka shigo ciki harda ƴan sanda tsakar gidan mu, da sauri na miƙe na nufi ɗaki ina ƙwalawa Baba Rabi kira saboda bata daɗe da fitowa daga wanka ba tana shirin fita rumfa.
A razane ta fito daga ɗakin sannan ta kalleni tace:
"Lafiya me ya faru?"
Nuna mata waje nayi sannan muka fito tare tana ganin su ta fara salati. Sannan tace:
"Hajiya Umma meya faru na ganki da ƴan sanda kuma?"
"Ba dole ki ganni dasu ba ai tare mukeyi"
" Tare muke yin me kuma?"
Baba Rabi ta faɗa tana kallon ta idon ta a waje.
Ɗaya daga cikin ƴar sandar tace:
"Malama ki wuce mu tafi police station Kya amsa tambayoyin mu acan."
Hannu na ɗora a kai na na fara rusa kuka tare da ƙanƙame Baba Rabi ina cewa babu inda zataje. Tsawa sukai min sannan suka fincike ta suka tafi.
Hankali na ya tashi matuƙa ga abinci mun gama girkawa, zamu fita, na rasa yadda zanyi, dabara ta faɗomin naje makarantar allon su Amuwar na ɗakko su na shirya su muka nufi rumfar sai da abincin mu.
Saboda kaifin ƙwaƙwalwa irin tawa haka na zage na dinga zuba abinci kamar yadda Baba Rabi takeyi, abu kamar wasa na kusa siyarwa mutane kuma kamar koro su akeyi, sai dai tambaya kawai da nasha na Baba Rabi Ni kuwa bata da lafiya kawai nake ce musu.
Haka na siyar da abincin nan Anuwar yana min wanke wanke, na tara kuɗin nan tim a hannu na, kulle ko ina na nufi kasuwa nayi cefanen gobe tun da daman ni take aika, zuciyata cike da begen ta sai dab da magrib muka nufi gida.
A zaune na tarar da ita tana ta gursheƙen kuka, da gudu na ƙarasa na fara tambayar ta:
"Baba me yake faruwa?"
Kallo na tayi cike da tashin hankali sannan ta buɗe bakin ta yana rawa tace:
"Hajiya umma ce aka kama ta tana safarar yara daga ƙauyuka tana kai su gidajen masu kuɗi aikatau shine tace wai tare mukeyi da ita, daman tuntuni tayi tayi da ni akan na bata ke naƙi saboda mu warware bashin da take bi na naƙi, shine tai min wannan abun, to da mukaje Allah ya taimaka yadda kika nuna ba kyaso a tafi dani ya saka suka yarda ba hannuna acikin bayan nayi musu ƙaryar cewa nasan mahaifiyar ku mun zauna tare amma bansan daga inda tazo ba ba'a san danginta ba da ta rasu na cigaba da riƙe ku, to shine bayan sun ƙyale ni suka kafamin sharaɗin da zai min wahalar ɗauka...."
Sake fashewa tayi da wani matsanancin kuka, hankali na yayi matuƙar tashi.
Na dubeta cikin tsananin ruɗewa nace:
"Don Allah Baba Rabi ki faɗamin me yake faruwa... don Allah kinji..."
Nima jikina rawa ya fara yi saboda ƙwaƙwalwata ta kasa ayyana abinda zata faɗa saboda tsananin tashin hankalin da na shiga saboda ganin yadda babba kamar baba Rabi take gurza kuka haka.
Haka ta sake kallona a karo na biyu ta sunkuyar da kanta ta kasa haɗa ido dani sannan ta buɗe bakin ta yana rawa tace:
"Nuratu... sunce lallai tun da haka ya faru ban san dangin ku ba dole na miƙawa gwamnati ku.. ma'ana su kai ku gidan marayu ku cigaba da rayuwa acan..."
Sake fashewa da kuka tayi. Ni kuwa neman waje nayi na zauna a ƙasa daɓas! Tunanina ya tsaya cak!
Can cike da kiɗima Baba Rabi ta kamo hannuna tace:
"Nuratu ki daure ki faɗamin daga inda kuke ko na samu sauƙi a zuciyata naje can wajen danginku na nemi alfarma kucigaba da zama dani saboda na riga da na saba daku bani da kowa Nuratu...."
Ta sake fashewa da kuka.
Ni kuwa kallo na bita dashi cike da ƙin yarda da shawarar ta, tabbas da na koma garin mu gwara nayi rayuwa a gidan marayu ƙarƙashin kulawar gwamnati a ƙalla nasan zamu sauƙi da tsaro a can, amma halaccin da Baba Rabi tayi mana a rayuwa ta saka bana son rabuwa da ita saboda banda iyayena da kakannina na wajen uwa Baba Rabi itace mutum ya gaba w duniya da muka samu sauƙin rayuwa a zama da ita.
Miƙewa nayi na zaro ragowar cinikin abincin yau na miƙa mata sannan nayi mata da nuni da cefanen da nayi sannan na miƙe don yin sallah tare da yiwa Kannena umarnin suyi Sallah su ma.
Kallon mamaki Baba Rabi ta bini dashi tare da juya kudin da na bata, na tabbatar da cewa ba da ban a cikin tashin hankali muke ba abun ta yaba min ne saboda cinikin da nayi a yau da yadda na iya tafiyar da komai cikin sauƙi, amma sai da tashin hankalin da muke ciki bai saka tace komai ba face wani kallo da naga ta bini dashi me wahalar fassarawa.
Bayan na isar da sallar Ishaa shimfida nayi mana domin mu kwanta, ran mu babu daɗi ciki har da Kannena saboda duk abinda mukayi a gaban su ne kowa yayi shiru na nemi waje na zauna a gefe na kasa kwanciya ba haɗa kai na da bango ina kallon Ameera da ta fara bacci Baba Rabi tayi sallama ta shigo.
Kusa dani ta nemi waje ta zauna, sannan ta kalleni tace:
"Nuratu alamun ki ya nuna cewar kina so ki tafi ki barni ko?"
Ƙasa kallon ida take nayi Saboda tsananin kunyar ta da ta kamani da tausayin ta saboda ina ji a jikina kamar ban mata adalci ba da har na bari ta gano ni.
Want the next chapter?
ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol