Free chapter · Read without an account

Chapter Nine (Zulumi)

by The Healer's Pen · NI DA KANNENA

Ina tsaye ina kallon ikon Allah na rasa bakin magana jikina gaba ɗaya jin sa nake kamar ba nawa ba, ji nake kamar mafarki sam na kasa yarda da abinda yake faruwa har mutanen gida suka cika suka taru ciki kuwa har da Hajiya kowa sai tofin Allah tsine yake min.


Ban san ta yaya zan baku labarin wannan ɓangaren ba, bana so na tuna, ya kasance ɓangare mafi muni a tarihin rayuwa ta, yadda Hajiya ta kasa fahimta ta yafi komai ɗaga min hankali, bazan iya faɗar komai ba dole na taƙaita muku wannan al'amarin.


Duk da Alhaji bai mutu ba yana kwance magashiyan a wani babban asibiti a London, amma shari'ar mu sai da takai wata takwas anayi, saboda duk wasu dabaru da nau'in azaba na jure naƙi amsa laifina abinda ya bawa Kowa mamaki kenan ciki har da ni kaina amma daga baya nasan hakan yana da alaƙa da mutuwar mahaifana.


Duk sanin da ka yiwa Nuratu idan ka ganta ba ka isa ka gane ta a lokaci guda ba, na rame nayi baƙi tun ina kuka har na dai na, zuciya ta ta ƙeƙashe na daina tsoron mutuwa kuma naƙi yarda na amsa laifina, ga kuma babban tashin hankalin da nake ciki bansan halin da KANNENA suke ciki ba.


Idan kuka ga rashin tsoron Allah da ake yi a wajen Shari'ar mu wallahi sai abun ya ɗaure muku kai, saboda wasu irin mutane ake shigowa dasu kullum wanda ban ma taɓa ganin su ba suna bada shaidar zurrr akan wai ni nace zan biyasu su kashe Alhaji suka ƙi, har da murya ta aka kwailawaya a waya da wasu abubuwan da sam bana so na tuna ma ballantana na bada labari.


Abinda na sani kawai kuma na lura dashi tun daga kan alƙalin da yake shari'ar har zuwa lauyan da akace wai yana kare ni an basu cin hanci kawai saboda naƙi amsa laifi na ne ya saka suka rasa yadda zasuyi kuma aka gaza yanke min hukunci.


Akwai wata rana ina zaune acikin gidan yari ina bitar haddar Alkur'ani na saboda shi kaɗai nakeyi na samu sauki, ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan yari yazo yace nazo inji sabon lauya na.


Abin ya matuƙar bani mamaki, ni nasan bani da wani lauya, wancan ma shi ya ga dama yace zai tsayamin daga baya kuma na fahimci cewa duk shiri ne, kuma nasani tun da nake dashi bai yaɓa cewa yazo gani na ba, banyi gardama ba haka na taso na biyo bayan sa.


Isar mu ɗakin ganawar ke da wuya na iske wani matashi a ƙalla zai kai shekaru 37-40 yana zaune da shiga ta ya bini da kallon tausayi sanann na nemi waje na zauna ina yi masa kallon tuhuma.


Bayan mun gaisa dashi ya dube ni yace:


"Sunana Barrister Shamsudeen Rufa'i ni lauya ne mai zaman kansa, sannan ina aiki da wata ƙungiya ta tallafawa mata waɗan da suka tsinci kan su a halin da kike ciki a yanzu ƙarƙashin kulawar wani mashahurin attajiri da baya son a faɗi sunan sa."


Cikin natsuwa na ci gaba da sauraron sa ba tare da nace ƙala ba.


"To magana ta gaskiya da kansa wani uzuri ya shigo dashi wannan kotun ya iske ki kun fito daga zaman kotu, hakan ya saka jikin sa ya fara bashi cewar kamar baki aikata laifin da ake tuhumar ki dashi ba, hakan ya saka yayi mai yiwuwa don ganin case ɗin ya dawo hannnun ƙungiyar mu saboda mu taimaka miki, dafatan zaki bamu hadin kai domin samun nasara inshaAllahu."


Murmushi kawai nayi na takaici saboda ina tunanin wani sabon salon yaudarar aka zo min dashi hakan ya saka na ƙura masa ido na tsawon lokaci sannan nace:


"Duk wani maƙircin ku nafi ƙarfin ku ba kuma zaku saka ni na amsa abinda banyi ba ko da za kuci nama na ɗanye.."


Katse ni yayi cikin hanzari tare da fara yimin bayani yadda ya kamata domin na fahimci cewar baya tare dasu amma na gaza sauraron sa har lokacin da aka ƙayyade mana ya cika na miƙe na shige ciki.


Haka wannan lauyan yayi ta zuwa yana lallaɓani amma abun yaci tura na kasa yarda dashi na kasa yarda da kowa zuciya ta tayi tauri kamar dutse idanuna sun ƙafe idan kuka ga nayi kuka to na tuna dasu Anuwar ne kawai.


Tsawon sati uku yana zuwa naƙi sauraron sa, har ranar da za'a koma kotu ta zagayo muka je kotu sukayi ta sha'anin su son ransu ashe Barrister Shamsu yana kotun haka ya miƙe ya nuna kwarewar sa ta gogaggen lauya, yanayin yadda jikin su yayi sanyi da yadda ya nuna ƙwarin gwiwa ya saka na fara yarda da cewar da gaske taimako na zaiyi.


Hakan ya saka na fara sakin jikina dashi na bashi duk abinda yake bukata na bayanai kafin ranar komawa kotu ta kuma zagayowa ya samu ƙwararun hujjoji, wasu ma sun bani mamaki sosai yadda aka samu hujjoji na CCTV PORTAGE da kuma wasu ma'aikatan gidan Hajiya da suka shirya faɗar gaskiya.


Duk da Barrister yasha wahala matuƙa kafin ya samu wadannan hujjojin amma naji daɗi sosai, sannan daga bisani na roƙe shi akan ya binciko min inda KANNENA suke, aikuwa haka akayi acikin ƴan kwanaki ya gano cewar tun ranar da abun ya faru suna gidan su abokin Anuwar shi da Ameerah.


Nayi mayuƙar farinciki tare da yiwa Barrister godiya, a ko da yaushe sai dai yace na godewa Allah sannan nayiwa founder na kungiyar su addu'a domin duk abinda ya faru shine sila, nayi iya bakin ƙoƙari na akan Barrister ya faɗa min ko da sunan sa ne, amma yace min ba'a bashi umarnin yin hakan ba.


Ranar zaman kotun mu na ƙarshe wanda ya kai wata tara ana wannan Shari'ah naga abun mamaki, yadda aka din ga bankaɗo hujjojin tare da tone tone akan abinda ya shafi shari'ar mu da wanda ma bai shafe ta ba, mafi yawanci ta hannun Binta mai girkin Hajiya aka same su sakamakon samun sinadarin gubar da tayi amfani da ita ajikin battery wayar ta (keypad).


Wato abin da ya faru shine: Anty Mariya ta daɗe tana son ganin bayan Alhaji Babannan saboda daman saboda kuɗi take zaune dashi shine tayi amfani dani ta laɓe a baya na domin cimma manufar ta, wato babban abun mamakin shine wai har da aminin sa Alhaji Saminu aka shirya hakan saboda bakin su ɗaya.


Abinda yafi ɗaure min kai shine, yadda bincike ya tabbatar da cewar Bashir ba ɗan Alhaji Babannan bane na jini ɗa ne ga Alhaji Saminu suka haifa da Anty Mariya a ɓoye domin cimma manufar su ta samun dukiyar sa masu yawa.


Dalilin da yasa kuwa ta hana Alhaji aure shine likitoci sun tabbatar mata baya haihuwa tuntuni amma tayi amfani da kuɗi ta juya sakamakon tasan yadda tayi ta haihu, shiyasa ta bi duk wata hanya mai yiwuwa domin hana shi aure saboda kar asirin su ya tonu.


Saboda tsananin mamakin yadda abubuwa suke faruwa kamar shirin film kasa tsayuwa nayi, kuma ranar Hajiya ta halacci zaman kotu banda hawaye ba abinda take yi ta ƙura min idon cike da tashin hankali, ni kuwa acikin zuciya ta neman tsari nakeyi da sake rayuwa acikin wannan gidan da gwara kurkuku ƙiriƙiri dashi sau dubu.


Da yake kungiyar da ta ɗauki nauyin tsaya min tana da ƙarfi sosai, sun tsaya tsayin daka tare da taimakon jajirtaccen lauyan nan an nema min adalici sunyi matukar kokari musamman yadda aka canja alƙalin saboda hujjoji da aka gabatar a kotu na karɓar cin hanci da yayi kuma ya amsa laifin sa, haka ya saka cikin sauƙi kotu ta wanke ni tare da yankewa masu laifi hukunci dai dai da abinda suka aikata.


Bayan kammala shari'ar mu an sake ni na fito da gudu Anuwar da Ameerah suka taho muka rungume juna muna kuka mai tsuma zuciya gaba ɗayansu kuka sukeyi tare da furta:


"Ukhty haka kika zama?"


Haka muka ci kukan mu mai isar mu, da na hango Hajiya da mutanen ta sun tunkaro in da muke da saurin na kama hannun su Anuwar muka fice daga kotun muka dinga sauri tare da haɗawa da gudu har muka ƙule aka dai na ganin mu, sai bayan munyi nisa sosai sannan wannan lauyan da ya taimaka min ya faɗo min cewar banyi masa godiya ba, kuma ko sunan ƙungiyar ta su ban sani ba.


Jikin wata ƙatuwar bishiya muka nemi waje muka zauna, daman Ameera ta taho da ƴan kayan ta a jaka ta zaro min hijab na saka Anuwar ma da school bag a bayan sa, ya sakko da ita ya zuge zip ɗin ya zaro min snacks da lemo ya miƙo min fuskar sa cike da hawaye na karɓa na fara ci kamar wata mayunwaciya, ko da yake itan ce don rabo na da jin ɗanɗano irin wannan har na manta.


Nan fa na shiga yi musu tambayoyi akan abubuwan da suka faru take Anuwar ya fara labartamin:


"Lokacin da police suka tafi dake mun rasa yadda zamuyi Hajiya ta faɗi ta suma, masu aikin ta musamman Binta suka shiga bedroom ɗin ku sukai ta bincike tare da kwashe golds ɗin ki da na Ameerah da duk wasu kayan ku masu tsada, ganin haka ya saka na shiga sai da mukayi rigima da su na iya kwaso credentials ɗin ki na school sai kuma wannan zoben naki da kikace yayi miki yawa da Ameerah ta duba ta ganshi ta ɗakko."


Ya saka hannu ya ɗakko zoben gold a jakar sa ya miƙo mini.


Murmushin takaici nayi sannan nace:


"Daman duk abinda muka samu a gidan muka sameshi kuma mun barshi a gidan wannan ɗin daka ɗakko shine rabon mu don bazan yar ba, kaci gaba ina jinka"


"To bayan nan sai na fito muka tafi gidan su classmate ɗi na Saleem muka yiwa Mummy su bayani bayan Daddy su ya dawo ta faɗa masa muka cigaba da zama, inata bincike akan in da aka kaiki ban samu ba har zuwa lokacin da wannan Barrister ya binciko inda muke yace zai kawo mu wajen ki amma sai zaman court na ƙarshe shine yau da wuri yazo muka tafi na hado mana kayan da zamu buƙata, don Allah Ukhty mu bar garinnan."


Ya faɗa muryar sa a sarƙe.


Murmushi nayi sannan na kalleshi nace:


"Ai Anuwar ko baka faɗa ba a yau zamu bar gari nan Kano zamu koma."


Haka kuwa akayi, na shiga kasuwa na sayar da wannan zoben yayi daraja sosai na ƙulle kuɗi na muka nufi tasha muka hau mota sai Birnin Kanon Dabo.


Isar mu Kano ke da wuya muka sauka a tashar Unguwa uku, kasancewar yanzu kai na a waye yake ba kamar da ba na buƙaci da mu nemi hotel nan kusa mu zauna kafin na nemi gidan haya da zan kama mana.


Wani saurayi na samu yayi min kwantancen in da zan samu, yawon duniyar nan bamu samu ɗaki ba haka muka dawo muna tsaye wani matashi ya taso ya nufo in da muke tare da yi mana sallama.


Bayan mun amsa yake tambayar mu wajen kwana muke buƙata ne saboda ya lura baƙi ne mu, muka amsa masa sannan yace akwai ɗaki a gidan da yake idan babu damuwa zai kaimu mu gani idan yayi mana sai mu biya na adadin kwanakin da mukeso kafin mu tafi.


Haka murna ta kama ni nace masa babu komai saboda daman zaman hotel bashi da daɗi, haka ya wuce gaba muka bishi a baya muka isa wani babban gida mai ɗakuna da yawa, yawancin mutanen gidan ƙabilu ne, ya saka key ya buɗe mana muka shiga.


Ɗaki ne falle ɗaya amma ƙato ne sosai da toilet aciki da kuma wani wajen girki a gefe, sannan da fanka da katifa da dai ƴan ƙananun tarkace na abubuwan buƙata na yau da kullum, wajen yayi babu laifi, muka ajiye kayan mu sannan na tambaye shi kuɗin wajen na wata guda yace min basa bada wajen a daɗe aciki na ƴan kwanaki suke bayarwa.


Banyi musu ba mace masa babu komai ya karɓi kuɗin sati guda, sannan nace masa idan an samu ɗakin da za'a biya na shekara ko da kamar wannan ne muna so zamu zauna, ya amsamin da zai bincika.


Haka muka zauna a ɗakin, su Anuwar a ɗarare suke sun kasa sakewa, na zaunar dasu nayi musu nasiha, na tuna musu baya, na tuna musu asalin su da kuma inda suka fito, ita rayuwa babu yadda batayi da bawa nace dasu suyi haƙuri wata rana sai labari komai zai wuce, gaba ɗaya jikin su yayi sanyi suka hakura suka fawwalawa Ubangiji.


Tsawon kwana uku muna cikin wannan gida, bama fita sai idan wani abun muke bukata, mun kame kan mu, Abdurrazaƙ da ya bamu wannan ɗaki ya yaba da kirkin mu sosai har ya lamince mana da mu biya kuɗin wata shida kafin a samu wani gidan.


Haka kuwa akayi na bashi kuɗin, sai dai babban tashin hankalina kudin namu sun fara ƙarewa saboda Hausawa sunce: "zara bata barin dami."


Sai kuma tunanin inda zan dinga samun kuɗi ya faɗo min, banyi ƙauron baki ba na tambayi Abdurrazaƙ ko da zan samu aiki koda koyarwa ce a private school don na din ga samun kuɗi ga karatun Ameerah ya tsaya gwara ma Anuwar yayi candy.


Ai kuwa baiyi min mugunta ba yace zaiyi magana da CEO ta Company da yake aiki idan ta amince sai na fara zuwa, nayi murna sosai da farinciki da jin wannan zancen nasa saboda bana son mu wayi gari babu abinda zamuci.


Haka kuwa akayi bayan sati guda da maganar na fara zuwa aiki, aikin company akwai wahala sosai, company rarraba shinkafa ne aiki ne na lissafi da bin diddigi, duk ilimin mutum dole sai ya nutsu sosai ya koya, haka nayi haƙuri na jajirce na fara koyar aiki.


Tsawon Wata uku ina aiki a wannan company tun safe idan na fita sai yamma liƙis ko magrib, gaba ɗaya bana son aikin saboda idan na fita ban san halin da KANNENA suke ciki ba, gwara ma Ameerah na mayar da ita makaranta kuma ta shiga islamiyya, amma babban tashin hankali na Anuwar tun da ban san da suwa yake wuni ba.


Acikin wannan wata ukun na samu ɗaukaka sosai a wannan company, an ƙara min albashi daɗin daɗawa jinina ya haɗu sosai da Hajiya Turai mai company, tana ƙaunata sosai, saboda ƙwarewa ta da kuma amana, kuma tana bayyana hakan a cikin mutane, hakan ba ƙaramin jawomin matsala yayi ba.


A watan mu na shida a Kano muka samu haya a wani ƙaramin gida mu kaɗai, haka muka haɗa kayan mu muka tare gwanin sha'awa, saboda a hankali na dinga siya mana kayan amfanin gida daidai gwargwado, muna zaune cikin rufin asiri kafin Anuwar ya tsiro min da fitinar shaye shaye.


Saboda hankali na ya kasa kwanciya ya saka dole na samarwa Anuwar admission a Kano State Polytechnic ya fara karanta Laboratory Science, kullum zan bashi kuɗin mota yaje ya dawo da na abinci, kasancewar area tamu da mutane sosai ya saka na fara sana'ar zoɓo domin mu rage wasu abubuwan.


Ai kuwa sana'ar tayi ƙarfi sosai fiye da tunani, acikin ƴan watanni ta saka har fili na mallaka ƙarami saboda inada burin na gina mana mahalli namu na kan mu domin mu samu hankalin mu ya kwanta kamar kowa.


Yanayin yadda Anuwar yake dawowa daga makaranta bai yi min ba, hakan ya saka na fara tuhumar sa, tare da bincika shi saboda na tabbata ya fara shaye shaye, ranar da na fahimci hakan ji nayi kamar na mutu saboda baƙin ciki, haka muka haɗa kai ni da Ameerah mukayi kuka mai isar mu har gari ya waye, zuciya ta tana faɗamin "Na gaza."


Gabaɗaya na ɗaukewa Anuwar, na daina yi masa magana hakama Ameerah, tunanina hakan zai saka ya daina amma sai matsala ma da ya Hai far min.


Watarana ina wajen aiki gaba ɗaya hankali na yayi gida, na kasa haɗa lissafin yadda ya kamata, kuɗi na gani wajen million uku sun haura na rasa yadda akayi saboda hankali na baya jikina, ga matsin lamba da hassada da nake fuskanta a wajen aikin matsaloli sun min yawa tun da ƙuruciyata saboda har yau ban cika shekaru 25 ba.


Na fara tunanin yadda zan yi da kudin nan, saboda na sani ba ƙaunata ake yi a wannan company ba, idan na bawa wani ajiya za'a iya cutata tun da ban gama haɗa lissafi na ba, haka na yanke shawarar da na taho dasu gida kawai zuwa da safe sai na warware matsalar.


Jakar goyo na na ɗakko na cire food flask ɗi na da ƙaramin tea flask ɗina na fara jera kuɗin acikin jakar, bayan na kammala nayi complain akan zuwa da safe zan ƙarasa lissafin na wuce na nufi gida.


Isa ta gida ke da wuya na tarar da tashin hankali, Anuwar ya kama Ameerah yayi mata duka ya farfasa mata jiki da belt, abinda ban taɓa ganin yayi ba, nan fa zuciya ta ta hasala na hau dukan sa shima, ai kuwa ya kasa haƙuri nima yayo kai na zai dake ni da ƙyar na ƙwace, mukayi baran baran dashi, ƙarshe dai ya hau haɗa kayan sa yace yau sai ya bar min gidana.


Haka ya haɗa kayan sa a school bag ina gani ya fita Ameerah ta tafi zata bishi tana kuka na riƙo ta, ranar ana zabga ruwan sama Anuwar ya fice ya barmu, munyi kuka iya kuka, na fita na bi bayan sa banganshi ba ƙarshe dai haka na haƙura na dawo ruwa yayi min mugun duka ranar kwanan zaune mukayi.


Washegari na yanke shawarar bazan je wajen aiki ba, zan fita neman Anuwar ko Allah zai saka a ganshi, daga wajena aikin mu suka fara kirana na bada excuse akace babu matsala amma na faɗi in da na ajiye kuɗin za'a haɗa min lissafi na, sai sannan tunanina ya dawo akan kuɗi, tun da na shigo na riski rikinsu Ameerah na ajiye jakar a palour ban kuma bi ta kanta ba da na ɗakko jakar da shirin na kai musu kuɗin su na zuge ta me zan gani, kayan Anuwar ne da ya haɗa ya canja jakar sa da jakar kuɗin Company ya ajiyemin tasa.


"Innalillahi wa'inna ilahi raji'un"


Na hau ambato tare da zubewa a ƙasa na ɗora hannu na a kaina fasa wani gursheƙen kuka.


Na rasa me zan yi haka na nufi company iya bayani nayi musu amma abun yaci tura babban laifin da nayi shine tafiya da nayi da kuɗin, duk yadda muke da Hajiya haka akai ta ziga ta tace bazata yarda ba ƙarshe dai sai da muka dangana da kotu aka sake garƙame ni.


Wannan karon sati na biyu a gidan yari aka sake zama a kotun mu, yanayin da Hajiya ta ganni na bata tausayi, hakan ya saka ta sakko saboda alƙwarin bada takardun fili na da nayi domin rage asara kuma a hankali idan na fito zan dinga biya.


Hajiya taji tausayi na sosai, ta karɓi iya takardun filin duk da ko rabin kuɗin baiyi ba tace ta yafemin sauran duniya da lahira, amma sai dai nayi haƙuri ta koreni daga company ta, nayi farinciki sosai nayi mata godiya ni hakan ma da tayi ta yimin komai haka na koma gida na tarar da Ameerah baiwar Allah ita kaɗai gashi ba wanda muka sani ballantana taje wajen sa ga Anuwar ya tafi ya barmu.


Haka muka haɗa kai muka ci kuka mai isar mu sannan tunanin abinda zamu ci ya fara faɗomin ban da cinikin zoɓo yanzu babu abinda muke dashi, haka muka yi ta lallaɓa rayuwar mu.


Yau tsawon wata uku kenan babu Anuwar babu labarin sa, nayi neman har na gaji ƙarshe na haƙura na barwa Allah komai, bayan ƴan kwanaki na samu aiki a wani restaurant da suke abincin gargajiya, na fara aiki a wajen ana biyana albashi muna yin buƙatun mu dai dai gwargwado wanda wannan gidan abincin shine asali kuma silar samun junior.


Watarana ina kaiwa baƙi a abinci, saboda shifting mukeyi watarana kitchen wani lokacin kuma kai abinci, na fito ina kaiwa waɗanda sukayi order abinci ɗaya bayan ɗaya har zuwa lokacin da na iso table ɗin VIP in da naci karo da wani shahararren mutum, wanda da ganin sa kuɗi sun zauna sosai, na ƙarasa na fara jere masa abinda yayi order wato dambun shinkafa.


Bayan na kammala ya ɗago kan sa ya kalleni yayi murmushi sannan yace:


"Anan kuma kika fara aiki?"


Cike da ladabi da mamaki na amsa masa da "eh" kawai.


Gyaɗa kan sa yayi sannan ya fara yimin tambayoyi kamar dama can ya sanni.


"Meye matakin karatun ki?"


"First degree in Business Administration"


"Zaki iya aikin company?"


"Zan iya inshaAllahu."


"Ga complement Card ɗi na zuwa nan da sati biyu ki kirani zanyi tafiya ne, zuwa lokacin nasan na dawo inshaAllahu."


Hannu biyu na saka na karɓa nayi masa godiya ya dakatar sani, na juya tare da barin wajen cike da mamakin a'ina kuma wannan mutumin ya sanni?


Saboda ko sunana bai tambaya ba, kuma banga alamar yau ya fara ganina ba saboda yanayin yadda yake min tambayoyi da ƙwarin gwiwa.


"Shin wanene shi?"


Shine abinda zuciyata ta dinga maimaitawa.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.