Free chapter · Read without an account
Chapter Fourteen (Junior)
Rayuwa da nayi da Mummy rayuwa ce mai cike da ƙayatarwa, kulawa da kuma tausayi.
Ta kula dani kamar ƴar cikin ta, duk wani motsina tana sane dashi, tana tausayamin matuka, hakan ya saka na saki jiki da ita sosai.
Mummy ba mutum ce mai yawan tambayoyi ko son jin ƙwaƙwaf, bata damuwa da yawan tambaya ta akan al'amuran da suka shafi rayuwa ta, sai dai kullum bani hakuri take yi akan rashin zaman mijina kusa dani kullum tana tausa ta.
Ni kuwa bana nuna mata ina damuwa, sai dai itama dana lura kullum cikin damuwa take yi da yawan sallar dare tana roƙon Ubangiji akan Allah ya bawa ɗan ta tilo lafiya.
Haka nima ta roƙe ni tace na dinga yi masa addu'a haka na duƙufa na dage na saka Ashraf acikin addu'o'ina ko ba komai domin kasancewar sa uban ɗana.
Watarana ina makaranta kamar daga sama naji ana kiran sunana, Juyowar da zanyi wa zan gani? Barrister Shamsudeen Rufa'i, lauyan daya taimaka min akan case ɗin sharrin yunƙunrin kisan kai ɗan gidan Hajiya a Kaduna.
Cike da mamaki da zaƙuwa nace:
"Barrister ya aka yi kazo nan?"
"Ke zan tambaya ai Nuratu"
Nan fa kunya ta kama ni na shiga bashi hakuri da godiya akan kokarin da yayi min a wancan karon ko tsayawa banyi ba ballantana nayi masa godiya.
"Babu komai Nuratu me kike yi anan?"
Nan fa na hau bashi labarin nayi aure ina zaune da mijina anan, shima yace min yazo ƙara karatu ne yana zaune a Manchester da matar sa nan yazo taya abokin sa murna ne ya gama PhD.
Take muka yi musayar lambar waya bani katin sa yace na daure na ziyarce shi nace babu komai bayan mun sha hirar duniya yayi min sallama ya tafi.
Haka na cigaba da rayuwa a London, cikina yaci gaba da girma, laulayin da nake yi ya ragu na samu lafiya sosai na maida hankali na kan karatu na a yanzu kam bani da wata matsala da ta wuce shaƙuwa mai ƙarfi da take shiga tsakani na da ɗan ciki na.
Lokuta da dama na kan miƙe cikin dare na kama cikina nayi ta kuka ba ƙaƙƙautawa, kasancewar na sani tabbas bazan rayu dashi ba ga kuma wata ƙauna da soyayya da take shiga tsakani na dashi.
Babu yadda banyi ba akan na cire wannan damuwar acikin zuciyata amma abun yaci tura, har watarana da naje awo sai da likita yayi min warning akan cewar jinjina yana barazanar hawa.
Shi kuwa Daddy yawanci makaranta yake bi na mu gaisa, yayi ta kwantar min da hankali yana bani shawarwari akan yadda zan kula da kai na sannan daga bisani yake faɗa min cewar lokaci yayi da zamu sanar da mutuwar mijina na bogi.
Duk da mutuwar ba ta gaske bace amma sai da naji gaba na ya fadi naji wani tsoro da firgici ya ziyarce ni. Tunanin halin da ƴan uwana zasu shiga da zarar sunji wannan labarin ne ya fara yawo a ƙwaƙwalwata.
Daddy ne ya katse min tunanina...
"Akwai wasu sojojin England da suka rasa rayukan su sakamakon fashewar bututun gas a yau zamuyi amfani da wannan damar domin isar da sakon mutuwar mijinki zuwa ƴan uwana ki."
Jinjina kai na kawai nayi a daidai lokacin na miƙe daƙyar kasancewar nayi nauyi cikina ya shiga wata na bakwai.
Bayan saƙon mutuwar mijina na bogi ya iske ƴan uwana sunyi kuka sosai sun tausaya min matuƙa don har Anuwar sai da ya buƙaci da yazo London amma na hana shi, duk da Daddy yaso yazo amma naƙi kasancewar bazan iya kallon idon Anuwar da wannan ƙatuwar ƙaryar ba gani nake kamar zai fahimci abinda yake faruwa.
Bayan komai na labarin mutuwa ya lafa, hankali na ya koma kan ɗan da na zan haifa, gaba daya hankali na ya tashi saboda a kullum sake shaƙuwa nake yi da abinda yake ciki na.
Mummy ma sai da ta fahimci halin da nake ciki, duk tunanin ta ina damuwa ne akan wahalar naƙuda, sai ta shiga lallashi na da bani hakuri, amma ni sam ba wannan bane a gaba na bukata ta ya yaya zan rayu da ɗana na har abada.
Ina zaune a makaranta wani tunanin ya faɗo min, "toidan na haihu na gudu da ɗa na mana, nayi nisa dashi sosai in da ko da wasa babu wanda zai sake jin labari na ballantana a ƙwace mini shi, tun da yanzu na tabbata ina da kuɗin da zamuyi rayuwa NI DA KANNENA da kuma ɗan da zan haifa anan gaba."
Da wannan tunanin naji zuciyata tayi sanyi, na fara tunanin ina zanje? Shin ko ƙauyen mu zan koma? Shin ta yaya zan bar birnin London ba tare da Daddy ya sani ba? Ina zan samu passport da Visa ba tare da sanin sa ba?
Waɗannan tambayoyin su suka fara karakaina acikin ƙwaƙwalwata, nan fa na fara tunanin yadda zanyi passport ɗi na ya dawo hannuna.
Da yammacin wata ranar Laraba na gama lactures munyi sallama da Ramla ta tafi gida na nemi wani garden da muka saba zama da Daddy mu tattauna acikin makaranta na ɗakko wayata na fara laluben lambar wayar sa. Bugu ɗaya ya ɗauka na buƙaci ganin sa yace min gashi nan ƙarasowa.
Bayan ya ƙaraso mun gaisa na sunkuyar da kaina na kasa magana, saboda ina tunanin ta yadda zan ɓullowa al'amarin ne. Amma na tabbatar da Daddy mutum ne mai matuƙar wayo da basira idan na tunkare shi kai tsaye zai fahimce ni dole nasan dabarar da zan ɓullo masa.
Ɗagowa nayi muka haɗa ido dashi naga ya ƙura min idon yana nazari na ba tare da yace komai ba. Take naji wani mugun kwarjinin sa ya kama ni, amma duk da haka na daure nace:
"Anuwar ya damu sosai akan yana so yazo ya ganni ni kuma bana son yazo shine na yanke shawarar idan da hali zanje na ganshi ko hankalin sa zai kwanta."
Jinjina kan sa Daddy yayi sannan ya kawar da kan sa daga kallo na ya miƙe ya nufi hanyar tafiya sannan ya juyo ya kalle ni yace:
"Ba yanzu ba sai kin haihu."
Ya kaɗa kansa yayi gaba.
Wani irin abu naji ya to kare min maƙoshi na saboda takaici, na rasa me zance sai hawaye ne kawai suka fara gangaro min a kunci na. Nayi hakan ne saboda nasan dole passport ɗina zai zo hannuna kuma ida na kuskure na saka ƙafa na bar London ba zasu sake gani na ba.
Haka naci gaba da zama a wajen har duhun magariba ya doso sannan daga bisani na miƙe na nufi gida.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya, cikina ya tsufa sosai har an saka min ranar da za'a yi min operation, hankali na kullum ƙara tashi yake yi akan rabani da ɗana da za'a yi, a kullum ranar haihuwa ta tana matso wa fargaba ta tana ƙara yawa.
Ƴan uwana a koda yaushe cikin lallashi na suke da tausaya min, musamman yadda kwanannan idan muna waya dasu kawai sai naji na fashe da kuka, tunanin su akan mutuwar mijina nake kukan amma basu sani ba tsoron rabuwa da ɗa na ne yayi min katutu.
Iya warning babu wanda likita bai min ba, ya lallashe ni har therapy program na fara amma duk a banza saboda na riga da nayi nisa bana jin kira, gabaɗaya imanina ya tafi akan soyayyar ɗana.
Ranar wata Asabar kwana biyu kafin ranar operation ɗi na wani matsanancin ciwo ya tirniƙe ni, da mamaki mu da muka isa asibiti aka tabbatar da cewar haihuwa ce.
Bayan nayi naƙuda ta tsawon awa biyu cikin ikon Allah na haifo ɗa na namiji.
Murna a wajen Daddy kamar me, duk da yana shayin ya nuna a gaban Mummy amma duk da haka sai da yanayin farin cikin sa ya bayyana ƙarara a zahiri har sai da Mummy ta magantu.
Daddy ma kenan ballantana kuma ni, duk da maƙudan kuɗin da ya kashe akan samun jikan nasa amma na tabbatar da bai kai ni farin ciki ba.
A wannan ranar bayan Mummy ta tafi gida na ɗakko ɗana na zuba masa ido na ƙare masa kallo, tuni naji wani masifaffen son sa da ƙaunar sa ya mamaye gaba daya duk wani sassa da jijiyoyin magudanar jinina, numfashi na da kuma bugun zuciya ta. Tabbas banga abinda zai rabani da ɗana ba a duniya.
Wani hawaye ne mai tsanani naji ya gangaro kumatu na, ba shiri ya fara ɗiga akan fuskar ɗana, na saka hannaye na na fara sharewa a daidai lokacin Daddy ya shigo ya same ni a wannan yanayin.
Kallo ɗaya yayi min sannan ya mayar da hankali sa kan jaririn ya karɓe shi ya fara yi masa addu'a, acikin zuciya ta kuma tana raya min cewar: "Da ace lokacin da kike da ciki ne yazo ya same ki a yanayin damuwa da rarrashin ki zaiyi amma da yake kin gama aikin ki sam bai damu da ke ba ta jikan sa yake".
Take naji wani mugun haushi Daddy ya kamani da kuma ƙarawa kaina ƙaimi akan aniya ta ta guduwa da ɗana in da ba zai sake jin ɗuriya ta ba kamar yadda na bar dangina da mahaifata.
Ɗagowa Daddy yayi ya kalle ni sannan yace:
"Wanne suna kika zaɓar masa?"
Wani yanayi na tsinci kaina mai wahalar fassaruwa, na rasa me zance masa, shin daɗi zanji kokuma naci gaba da jin haushin sa, take na fara tunanin wahalhalun da Daddy ya sha da gwagwarmayar da yayi domin ganin wannan yaron yazo duniya, uwa uba ga mazajen kudade da ya kashe, take naji zuciyata ta maye gurbin haushin sa zuwa tausayin sa.
Na kalle she a raunane nace:
"Ahmad!"
Cikin hanzari ya kalle ni, kafin yayi magana nace masa:
"Sunan ka na zaɓa masa Allah ya rayashi bisa sunnah!"
Jinjina kai Daddy yayi ba tare da yace komai ba, yayi masa huɗuba da suna 'Ahmad'.
Lokacin da za'a sallama ni daga asibiti Daddy yazo min da maganar cewa zan bar gidan Mummy domin Ashraf ya farfaɗo jiya yana cigaba da karɓar kulawa likitoci a asibiti Mummy tana kula dashi saboda haka zai sauya min masauki.
Duk da ban taba ganin Ashraf a zahiri ba kuma wata mu'amala bata taɓa haɗani dashi ba amma naji daɗin wannan labarin ko ba don komai ba don kasancewar sa uba ga sanyin idaniya na.
Haka na sake tarewa acikin wani ƙayataccen gida mai kyau wanda yafi wanda na fara sauka komai, wannan cike yake da kayan raino kala kala abun sai wanda ya gani, sannan ga wata nurse da Daddy ya ɗauka wadda zata dinga kula dani sannan da kuma mai aikace-aikace amma ita baƙar fata ce ƴar ƙasar Ghana.
Haka naci gaba da rainon ɗa na har mukayi kwanaki Arba'in. Ameerah kullum sai ta dame ni da in turo mata da hoton sa bata rabo da video call kullum zancen ta ina Junior (sunan da Daddy ya saka masa). Haka shima Anuwar a koda yaushe basu da babban burin da ya wuce su saka shi a idon su.
Ranar wata Litinin daddare nayi wani mummunan mafarki inda naga wata iska mai ƙarfi ta tafi da Junior a hannuna nayi iya bakin ƙoƙarina na ƙwato shi amma abin yaci tura.
Farkawa ta ke da wuya na miƙe cikin sauri na nufi baby bed ɗin da yake ciki na ɗakko shi na rungume shi ina tofa masa addu'a hawaye sun cika min fuskata, kirjina sai bugawa yake yi take naji wani tsoro da fargaba ya mamaye ni.
Haka na koma kan gado na ƙanƙame shi ina addu'a ranar kasa komawa bacci nayi.
Washegari bayan nayi sallar asuba na miƙe cikin hanzari na fara haɗa kayana da duk abinda zan buƙata na zuba a trolley na faki idon kowa na fice na bar gidan.
Tashar jirgin ƙasa ta Marylebone Station na nufa hannuna rungume dashi ga tsananin sanyi da ake zabgawa tare da dusar ƙanƙara daman nayi masa shigar sanyi mai kyau sannan na fito.
Ina isa tashar jirgin misalin 6:15 na safe na siyi ticket na hau jirgin na nemi wajen zama na zauna, a cikin zuciya ta garin Manchester na nufa wajen Barrister da niyyar naje na faɗa masa komai ko da zan samu ya taimake ni da samun wata mafitar kokuma yadda za'a yi na koma Nigeria .
Misalin 6:30 na safe daidai jirgin mu ya tashi, a zuciyata addu'a kawai nake yi tare da neman zaɓin Ubangiji sannan da wani ƙwarin gwiwa da nake ji musamman idan na kalli fuskantar ɗa na.
Misalin karfe 8:35 na safe muka isa tashar jirgin ƙasa ta Birmingham Moor Street, daga nan na sake siyan ticket na hau wani jirgin wanda zai sada ni direct da garin Manchester acikin garin England.
Misalin 11:00 na safe jirgin mu ya iso garin Manchester, passinger ana ta hada hadar fita sai sannan na tuna da ban kira Barrister ba, haka na ɗakko wayata na fara laluben number amma shiru, duk da haka ban damu ba na laluba jakata na ɗakko katin da ya bani na tabbata zan iya isa inda yake da kwatance.
Na ɗakko trolley na na ɗora Junior a baby carrier yana fuskanta ta sannan na fara yunƙunrin fitowa daga jirgin.
Fitowa ta ke da wuya da mamakina naga ɗaya daga cikin securities din Daddy a tsaye kamar daman jiran isowa ta yake yi.
Wata muguwar faɗuwar gaba naji take naji ƙafafuwana sun hau rawa na tsaya cak musamman da idanuna suka kai kan ragowar securities ɗin a ƙalla sun kai su goma.
Yin ta maza nayi na saka gefen mayafina na kare fuskata na fita na ɗau hanya ina ta wani mugun sauri kamar zan tashi sama na saka hannu na rungume Junior da yake ciki baby carrier na fara sassarfa tare da gudu sama sama musamman da na waiwaya naga sun biyo ni.
Wani matsakaicin layi na shiga mai ƙarancin mutane na fara ƙoƙarin ɓuya, banyi aune ba naga motoci guda uku sunyi min zobe, haka na tsaya cike da tsoro ina jiran abinda zai biyo baya.
Dr. Sabo naga ya buɗe ɗaya daga cikin motocin ya fito fuskar sa cike da wani kalar murmushi da na gaza fahimtar na meye, sannan ya nufo inda nake.
Take naji wani tashin hankali ya ziyarceni, yana tunkaro ni amma ji nake kamar zai ƙwace min junior, hannu bibbiyu na saka na ƙanƙame shi a jikina na fara kurma ihu ina faɗin "Wallahi bazan Baku ɗa na ba kar ka ƙaraso in da nake."
Tsayawa yayi cak! a in da yake ya naɗe hannaye sa guda biyu sannan ya kalle ni fuskantar sa a sake daga in da yake yace min:
"Shin kin san haɗarin da yake cikin abinda kike shirin aikatawa kuwa? Kin san jinin suwa kike so ki gudu dashi? Kokuwa kin san waye Alhaji Ahmad Maihula da zaki yi wasan yara da jinin sa?"
Cike da kuka da ƙaraji na kalle shi nace:
"Ko ma waye shi bai dame ni ba ni ɗa na kawai na sani kuma wallahi bazan baku shi ba."
Tsayawa yayi yana kallo na cike da mamaki sannan daga bisani wayar sa ta fara ringing, bayan ya ɗaga "OK" kawai naji yace sannan ya miƙo min wayar.
Ƙemagadas naƙi karɓa ina ta sharɓar kuka, ƙanƙame na junior, hankali na a tashe, ya ƙaraso dab dani sannan ya saka hands-free na fara jiyo amon muryar Daddy:
"Nuratu! Kiyi hakuri ki biyo su ku taho na rantse miki da Allah babu wanda zai rabaki da ɗanki kiyi hakuri ki kwantar da hankalin ki, bazaki iya guje min ba duk in da zaki shiga a duniya, munyi planting tracker a jikin ki babu in da zaki shiga ba mu sani ba."
Haka yaci gaba da bani baki tare da kwantar min da hankali, babu yadda na iya haka na haƙura na shiga motar muka tafi.
Tafiyar da muka yi ba tafi ta minti biyar ba naga mun iso wani katafaren hotel mai suna 'Dakota Hotel Manchester'. Duk da bana cikin hayyacina amma zan iya cewa ban taɓa shiga waje mai kyau da tsari irin Dakota Hotel ba.
Elavator muka nufa wadda ta sada mu zuwa sama, sam ban lura da number ɗakin ba saboda gaba daya hankali na ba'a jikina yake ba.
Dakatawa securities ɗin suka yi a ƙofar ɗakin sannan daga bisani ni da Dr. muka shiga.
A tsaye na hango Daddy ya juya bayan sa yana kallon window, har na shiga Dr. yayi min umarnin da na zauna a ɗaya daga cikin kujerun ɗakin Daddy bai juyo ba yana tsaye ya goya hannayen sa a bayan sa kamar wani shugaban sojoji.
Jim kaɗan naji Dr. yace:
"Zan wuce gida sai anjima"
Jinjina kan sa Daddy kawai yayi sannan shima Dr ya sa kan sa ya fice yana yi min wani irin kallo da na kasa fahimta.
Ni kuwa ina ɗosane akan kujera, na ƙanƙame junior kamar wata mahaukaciyar da za'a ƙwacewa ɗa, hawaye ya gaza daina zubowa daga ido na, na ƙurawa junior ido yana ta faman bacci a tasa duniyar bai san abinda yake faruwa ba.
Mun kai a ƙalla mintuna biyar da shigowa sannan Daddy ya juyo ya fuskance ni, duk da nesa yake dani amma hakan bai hanani ganin tsananin damuwa da tashin hankali a fuskar sa ba, take naji yanayina ya sauya tausayin sa ya kama ni naji har na fara nadamar abinda na aikata duk da nasan ba laifi na bane kowacce uwa zata iya yin abinda na aikata ko ma fiye da haka.
Want the next chapter?
ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol