Free chapter · Read without an account

Chapter Nineteen (Aminci)

by The Healer's Pen · NI DA KANNENA

Miƙewa tayi tsaye ta kwantar da Junior akan cinyar sa, sannan ta nufi cikin gidan. Binta kawai yayi da kallon mamaki, duk wannan tsawon shekarun ta iya ɓoye wannan a zuciyar ta? Amma daga baya ya danganta hakan da rashin mahaifa musamman mahaifiya, don da suna tare da mahaifiyar su da tuni ta daɗe da fahimtar matsalar Nuratu.


Wani zazzafan hawaye ne ya fara zubo masa na tausayawa Nuratu, don a yanzu itace abar tausayawa. Su tunda suka taso bata taɓa bari sunyi maraici ba daidai dana kwana daya, ta tsaya tsayin daka iya karfin ta da sadaukarwa mai tarin yawa akn su, amma ita fa? Waye ya kula da ita? Waye ya tsaya mata? 


Tausayin ta ne yaji ya kara shigar sa. Ya mayar da hankalin sa kan Junior da yake kwance a cinyar sa, ya ƙura masa ido, ya sani sarai Daddy ya yayi kokari wajen bawa Nuratu kulawa da gata, kuma ya tabbatar da irin son da Ashraf yake mata saboda yana da guarantee akan hakan, kuma ya sani shi kaɗai ne zai iya kula da ita ya maye mata gurbin uwa da uba, ya zame mata bango majingina kamar yadda suma ta zame musu bango a rayuwar su. Amma babbar matsalar itace; wannan larurar ta Nuratu ta rufe mata ido ta kasa fahimtar hakan.


Numfasawa yayi cikin ransa sannan ya furta a fili: " Duk yadda zanyi zan samar miki mafita Ukhty, dai dai da rana ɗaya kema kiji abinda kowanne mai rai kuma mai lafiya yake ji, ko da zan rasa raina inshaAllahu." Da wannan tunanin ya miƙe ya saɓa Junior a kafaɗar sa ya nufi cikin gidan, zuciyar sa cike da ƙwarin gwiwa da alwashi.


Shigar sa palour ke da wuya, ya hango Nuratu daga nesa akan kujera ta ƙurawa TV. ido, kai da ganin ta kasan ba kallon take yi ba, matattakalar benen ya kama ya nufi ɓangaren su Ameerah ya kwantar da Junior tare da yi masa addu'a, sannan ya nufi ɓangaren sa domin ya watsa ruwa.


Ita kuwa bin bayan sa kawai tayi da kallo, zuciyar ta tana matsanancin bugawa, a tunanin ta furtawa Anuwar da tayi zai saka ta samu sauki, sai dai kash! wani yanayi take ji a jikin ta wanda bata taba jin irin sa ba. Kururuwa aka shiga yi mata a kunnen ta da wata irin murya mai tsoratarwa "Tun da kika faɗa kin shiga uku..." Haka ake ta maimaita mata. Take bugun zuciyar ta ya nunku, rawar da jikin ta yake yi ya sauya zuwa jijjiga, gumi ya lullubeta, duk da sanyin AC da yake kaɗawa a palour bai hana ta jiƙe sharkaf ba. "Har wanne lokaci zan kai ban furta ba, na furta ɗin, Innalillahi wa'ina ilaihi raji'iun!"


Wannan maganar data furta a zahiri ce ta jawo hankalin Baba Rabi da Ameerah, cikin sauri da tsananin tashin hankali Ameerah tayo kanta tana kuka tare da faɗin:


"Innalillahi wa'ina ilaihi raji'iun! Ukhty me yake damun ki na shiga uku!"


Haka ta rungume ta tana kuka. Ita kuwa Baba Rabi sauri tayi ta nufi kitchen domin ɗakko mata ruwa.


"Kiyi min addu'a Ameerah! Allah ya yaye min abinda yake damuna, ni kaɗai nasan me nake ji.."


Cikin kuka Ameerah ta jinjina kanta tare da faɗin:


"Allah ya baki lafiya.."


A daidai lokacin Baba Rabi ta ƙaraso, cikin sauri Ameerah ta karɓi ruwan ta fara tofa mata Ayatul Kursiy da Falaq da Nas, ta kai robar ruwan bakin ta, amma inaaaa gaba ɗaya haƙoranta sun datse, babu ta in da ruwan zai shiga, take ta kurma wani ihu tare da sanƙamewa.


Sakin robar ruwan Ameerah tayi tare da miƙewa tsaye ta ɗora hannun ta aka ta kurma wani ihu. Ita kuwa Baba Rabi jijjiga ta ta shiga yi tana faɗin "kirawo Anuwar mu kai ta asibiti." Da gudu Ameerah ta nufi sama, ta kusa hawa ɓangaren Anuwar ta zame saura ƙiris ta gangaro, amma haka ta daure ta ƙarasa ta same shi ya fito daga wanka daga shi sai towael, ta sanar masa da halin da ake ciki. Da saurin sa ya zira jallabiyya ya biyo bayan ta.


Yana ƙarasowa ya tallafo kanta, ya kama kunnen ta na dama ya fara yi mata kiran Sallah, amma ko gezau, yayi mata duk wasu dabaru amma abun yaci tura, take ya kira abokin sa Zayyan ya bashi duk wasu ayoyi da zai tofa mata a ruwa tasha amma ina bakin ta ya datse babu ta yadda wani abu zai iya shiga ciki.


Gefe Anuwar ya koma ya zubawa sarautar Allah ido, hankalin sa ya matuƙar tashi musamman ganin yadda Ameerah da Baba Rabi suke kuka. Kimanin awa guda suna fama, wata dabara ta faɗo masa, ya kalli Ameerah yace:


"Kije kiyi alwala."


Aikuwa babu musu ta tafi, bayan ta dawo suka miƙe gabaɗayansu suka yi sallah raka'a biyu sannan Anuwar ya ɗaga hannun sa ya fara addu'a:


"Ya Ubangiji ga baiwar ka nan, ka saukaka mata wahala, ya Allah ka saukaka mata rayuwa, ka warware mata duk wani ƙulli da ƙunci da yake bibiyar rayuwar ta, ka bayyana dukkan abinda yake ɓoye, domin kai ne mafi sani akan sirrikan sarari da na ɓoye. Ya Ubangiji dukkan abinda yake damun ta ka warware shi, ka bata lafiya, ka amintar da ita, ka sanya farin ciki da salama a zuciyar ta, ka ƙara mata hakuri da juriya ka faranta rayuwar t,  ka bata ikon cinye jarrabawar ta cikin sauƙi..."


Shima fashewa yayi da kuka, sannan ya miƙe ya ɗakko Al-Qur'ani mai girma ya miƙawa Ameerah shima ya buɗe ɗayan sannan ya kalle ta yace:


"Sauka zamuyiwa Ukty Ameerah yau ba bacci!"


Jinjina kanta tayi cikin kuka sannan ya sake kallon ta yace:


"Zanyi talatin ɗin sama ke ke kuma kiyi na ƙasa."


Haka suka duƙufa, suna karatu Baba Rabi tana yin nafila, kiran sallar farko suka sauke Al-Qur'ani mai girma. Sai sannan Anuwar ya waiwayi in da take, da mamakin sa yaga tayi nisa cikin baccin ta, babu wannan sanƙamewar da tayi. Hamdala yayiwa ubangiji sannan yacigaba sa tofa mata ayoyin Al-Qur'ani mai girma har zuwa lokacin sallar asuba, suka tashi suka gabatar da sallar.


Kasancewar a kwance take magashiyan a tsakar palour akan carpet ya saka tuni Ameerah ta ɗakko pillow da bargo ta lulluɓeta, sannan suka nemi waje guda suka zuba mata ido tana wani nau'in bacci mai abun tausayi.


Sai misalin karfe takwas na safe sannan Nuratu ta fara motsi, da sauri suka nufi kanta suna yi mata sannu. "Hasbunallahu wani'imal wakeel" ta fara ambatawa, sannan ta buɗe idon ta a hankali ta fara ƙare musu kallo. Wani irin hawaye ne mai ɗumi ya fara gangaro mata a idon ta, ta fara yunƙunrin miƙewa zaune Anuwar ya taimaka mata ta zauna.


"Yanzu shikkenan haka zancigaba da rayuwa da wannan larurar? Anuwar ka kaini asibiti na haukace bani da hankali wallahi..."


Basu kaɗai ba, duk wanda zai zo ya riske su a wannan yanayin sai ya zubar da hawaye, saboda yanayin da take magana abun a tausaya mata ne.


"Lafiyar kalau Ukhty, amma tashi na kai ki asibiti kinji, kanki ne kawai yake ciwo."


"A'a Anuwar ba ciwon kai ne yake damuna ba kawai, ban faɗa muku bane tuntuni...ni kaɗai nasan me nake ji kuma nake gani...".

Translate 


"Kiyi hakuri tashi mu tafi.".


Taimaka mata yayi ta miƙe, kanta taji yayi mugun sarawa, sannan taji wani jiri ya ɗebeta, banda Allah ya saka Anuwar yana kusa da ita da zata iya faduwa. Rungume ta yayi Ameerah ta dauko mata hijab suka nufi waje.


A hanyar su ta zuwa asibiti take ta bawa Anuwar labarin abubuwan da take ji ajikin ta, yawan raɗa da ake mata acikin bacci ko a zahiri, sannan muggan mafarkan da take yi, uwa uba ga ciwon kai, sannan jikin ta sai ta dinga jin kamar ana hura mata wuta musamman ida yamma tayi. Shuru kawai Anuwar yayi yana sauraron ta cike da ta'ajibi, sannan daga bisani suka ƙarasa asibitin.


Babban abinda ya bawa Anuwar mamaki shine; duk wasu gwaje-gwaje anyi mata amma babu wata alamar ciwo, babu hawan jini babu komai. Babban abinda yafi ɗaga masa hankali shine ƴan kwanaki ya rage ayi mata dashen ciki. Shin a haka Nuratu zatayi rainon cikin? Anya baza'a fasa yi yanzu ba?


Tambayar da ya shiga yi wa kansa kenan a daidai lokacin da yake zaune a gefen gadon da take kwance tana bacci, bayan allurar baccin da yayi mata, saboda ta sake samun hutu. Ya lura da ramar da tayi, da kuma wani haske da fatar ta tayi, sai yanzu ya fara tambayar kansa "anya akwai jini ajikin Nuratu?" Saboda shi kaɗai ne gwajin da ya rage ba'a yi mata ba, duk da sakamakon fertility clinic ɗin ya nuna lafiyar ta ƙalau mahaifarta a shirye take da daukar ɗa. Amma dole ya saka aka yi mata PCV ƙarshe dai sai da ya kwanta ta bada jini aka saka mata. Bayan ya kammala ya kuma dawowa ya zauna ya sake ƙura mata ido, ita kuma tayi nisa cikin baccin ta.


Wayar sa ce ta fara ringing, sunan Daddy ya gani, cikin ladabi ya dauka tare da karawa a kunnen sa:


"Assalamu alaikum warahmatullah!"


"Waalaikumussalam warahmatullah! Anuwar kana lafiya?"


"Alhamdulillah Daddy!"


"To Masha Allah! Kana ina haka?"


Kallon Nuratu yayi kawai ya kawar da zancen tare da faɗin:


"Ina asibiti."


Kasancewar Anuwar likita ne Daddy bai damu ba da jin yana asibiti, yacigaba da magana:


"To Masha Allah! Idan da hali kazo yanzu ina son ganin ka."


"To shikkenan gani nan inshaAllahu!"


Ya kashe wayar cike da mamakin wannan wanne irin kira ne na gaggawa haka. To haka ya bawa abokin aikin sa ajiyar Nuratu, duk da yasan zai yi wuya ta farka kafin ya dawo, sannan daga bisani ya nufi gidan Daddy.


A ƙaramin masallacin da yake harabar gidan Daddy ya iske shi shi da wasu baƙi mutum biyu, kana ganin su kaga cikakkun ƴan ƙauye fitik waɗanda suke cikin wahala, yunwa, kokuma aikin ƙarfi. Sallama yayi ya shiga, bayan sun gaisa Daddy ya kalle shi yace:


"Kasan waɗannan mutanen?"


Sai sannan Anuwar ya ƙare musu kallo. Ko da wasa bai gane su ba 


"Bangane su ba gaskiya, su waye waɗannan ɗin?"


"Kar dai ace Anuwaru ne wannan ya girma haka? Tirƙashi!"


Ɗaya daga cikin su ya ambata tare da kama bakin sa alamar mamaki. Sannan yayi sauri ya jawo hannun Anuwar na hagu ya ƙarewa hannun kallo.


"Tabbas Anuwaru ne wannan, wannan tabon na hannun sa nine nan nayi masa rauni da tsabga yana yaro, ba makawa shine, ikon Allah!"


Ya ƙarasa maganar yana kallon abokin zaman nasa. Shi kuwa Anuwar janye hannun sa yayi, sannan ya sake ƙare musu kallo yace:


"Malamai su waye ku? Kuma daga ina kuke?"


"Mu nan ƴan uwan ka ne, sunana Iro, wannan kuma abokin haihuwar ka ne Mailamma, ƴaƴan kawunka Ilu daga Bunkure, shin ina sauran ƴan uwan ka? Ina Nuratu matata?"


A fusace Anuwar ya ɗago ya dakatar dashi ta hanyar ɗaga masa hannu:


"Kai dalla malam dakata, bama son shashancin banza anan, ta yaya kawai za ku zo ku hau yi mana shirmen banza anan. Mecece hujjar ku? Kuma ta yaya kuka san nan har kuka zo?"


Murmushi suka yi, har sai da runannun haƙoransu suka bayyana yalaye shar abun ƙyankyami, sannan wanda yace sunan sa Iro ya saka hannun sa a aljihun rigar sa ya zaro wata baƙar leda. Hotunan passport ne guda huɗu suka bayyana na Nuratu lokacin da ƙuruciyar ta tana yarinya. Cikin hanzari Anuwar ya karɓa ya ƙarewa hotunan kallo. Tabbas wannan Nuratu ce. Ya miƙawa Daddy shima ya jinjina kai saboda kamannin Nuratu sam basu ɓata ba. 


"Yanzu kun gasgata ni ko? To bari kuji labari. Wannan ƙaninane da yake yin garuwa anan garin, watannin baya wani mara mutuncin mai mota ya kaɗe shi,  kaga ƙafarsa nan da ƙyar take takuwa. Sai wata baiwar Allah ce ta tsaya ta taimake shi ta hanyar bada kuɗi a kai shi asibiti. To bayan an kaishi naje duba shi ake ta labari sai na ƙuduri aniyar sai naje na yi wa wannan mata godiya. Haka muka koma daidai wajen da abun ya faru, wani mai caji yace ya santa da sun zauna unguwa ɗaya ita da ƙannen ta, amma yanzu bai san in da ta koma ba. Ana haka wani bawan Allah da yaji muna zancen,  yace a wannan ranar akwai wani ƙaramin ma'aikaci da yake aiki a ƙarƙashinta a wani kamfani yaji yana faɗar karamcin ta da kuma kirkinta, saboda haka zai haɗa mu dashi. Haka kuwa akayi, muna zuwa ya ɗakko wayar sa ya nuna mana hoton ta, nan kuwa na gane ta sarai, ai bazan manta Nuratu ba, da muka bukaci ya faɗa mana in da take sai yayi mana kwatance, da muka je sai wata budurwa ta fito tace mana bata nan, haka muka haƙura muka tafi. Daga bisani muka koma wajen wannan mutumin yace watakila ba gidan bane. Ni kuwa ban haƙura ba, muka bita wannan kamfani, haka muka dinga sintiri ba'a bar mu mun ganta ba. Haka muka haƙura muka tafi ƙauye noma, shine naci alwashin sai na gana da ita, na ƙullo kuɗi na, na ɗakko wannan hoton muka koma wannan kamfani bamu samu wannan ma'aikaci ba sai wani muka samu muka bashi kudi, yace bai san gidan ta ba, amma zai nuna mana gidan mai wannan company la'alla idan munzo mu ganta anan saboda suna da alaƙa mai ƙarfi. Da farko na ɗauka damfararmu yayi ashe da gaske ne, mun sha fama da masu gadi sai da mukayi sa'a Alhaji ya fito yaji na ambaci Nuratu daga Bunkure sannan yace a shigo damu. To kaji yadda komai ya faru, yanzu ina matar tawa take?"


Wata irin muguwar ƙuluwa Anuwar yayi, sarai yanzu ya gane su, amma ya danne tare da daka masa tsawa:


"Kai! Karka sake ce mata matarka, yanzu matar wani ce, kajini ko?"


Kallon kallo suka yi shi da ɗan uwan nasa sannan suka haɗa baki sukace:


"Matar wani kamar yaya?"


"Kamar yadda na faɗa maka har da ɗan ta."


Cikin tashin hankali Iro ya kalli Anuwar yace:


"Babu yadda za'a yi Nuratu tayi aure har ta haihu, sam ba zai yiwu ba inaaa..."


"Nine nan na ɗaura mata aure, kuma ɗana take aure."


Daddy ne ya katse shi. Sannan ya ɗakko wayar sa ya nuna masa hoton Nuratu da Junior tun suna London har zuwa yanzu. Wani irin gumi ne ya fara ketowa Iro ya saka gefen rigar sa ya fara fifita.


"Abinda mukayi fa babu yadda za'a yi ta aur..."


Dandanan ya kama bakin sa ya tsuke. Anuwar da tun ɗazu yake binsa da wani mugun kallo ya kalle shi cikin tsana yace:


"Ƙarasa maganar taka mana"


"A'a ba komai..."


Aikuwa a fusace Anuwar ya miƙe ya fara ƙoƙarin zare belt.


"Wallahi idan baka faɗa ba sai na tattaka ka a wajen nan"


Kafin ya sake cewa komai tuni Anuwar ya rufe su da duka da belt ko ta ina. Sai ihu suke, kafin kace me, securities ɗin Daddy sun cika wajen, da ƙyar Daddy ya iya tsayar da Anuwar yana ta haki ga dukkan alama ya sauke ɓacin ransa da damuwar sa akan su.


"Daddy wallahi idan basu faɗa ba a wuce dasu police station..."


"A'a zan faɗa kuyi mana rai zan faɗa..."


Iro ne yayi maganar cikin tsananin tashin hankali da tsoro yana ƙarewa kitika kitikan securities ɗin Daddy kallo. Daddy ya kalle su yace: 


"Muna jin ku, idan kuka yi mana ƙarya waɗannan zamu saka su dake ku iya duka."


"Ƙyale su Daddy Ashraf zan kirawo masa, ba yana iƙrarin matar sa bace, to zai haɗu da daidai da shi."


Ya ƙarasa maganar yana ƙoƙarin danna waya. Dakatar dashi Daddy yayi a dai dai lokacin da su Iro suke cewa "kuyi hakuri wallahi zamu faɗi gaskiya." 


"Wato magana ta gaskiya lokacin da Baffan Nuratu ya rasu, babana Ilu ya ɗaukeni muka tafi can wani jeji kan dutse, akwai wasu Maguzawa matsafa ne na gaske muka je akan ayiwa Nuratu asirin da babu wani namiji da ta isa ta aura a duniya idan bani ba, haka aka haɗa komai kwanan mu uku acan sannan naga an bawa babana wata tukunyar ƙasa aka ce mu binne a kufai, shine muka je wani ƙauye kusa damu muka haƙa kushewa kusa da wata bishiyar tsamiya muka binne. Wallahi babana yace idan na faɗa sai ya kashe ni. Shiyasa har ya mutu babu wanda na faɗawa."


"Innalillahi wa'ina ilaihi raji'iun!" Daddy da Anuwar suka shiga furta wa, Daddy ƙafafuwansa kasa ɗaukar sa suka yi, shi kuwa Anuwar gefe ya koma ya kifa kansa da bango ya fasa wani mugun kuka mai tsuma zuciya. Anuwar mutum ne mai taurin zuciya da jarumta zaiyi wuya yayi irin wannan kukan.


"Ya Allah ka saukaka wa Nuratu jarrabawa, ka saka wannan itace karshen jarrabawar ta mafi wahala."


"Ai Nuratu ta gaji mahaifin ta akan ƙarfin ruhi da addu'a, wallahi da bazata taba yin aure ba..."


"Yanzun kasan halin da take ciki ne? Kasan a masifar da kuka saka ta?"


Anuwar ne ya katse Iro cikib ƙaraji. Rarrashin Anuwar Daddy ya shiga yi sannan ya kalli Iro yace:


"Zaka gane wajen da akayi binnen?"


"Ƙwarai zan gane"


"Ku tashi mu tafi"

 

Daddy ya furta tare da kamo hannun Anuwar suka nufi wajen ajiye motoci. Kafin kace me,  Daddy ya ɗebi zugar securities ɗin sa sun nufi garin Bunkure bisa jagorancin su Iro.


Tafiya sannu sannu a hankali suka nufi wannan ƙauyen da yake maƙwaftaka da garin su. Sai da Daddy ya fara isa gurin mai gari suka nemi izini sannan aka ɗunguma har mai garin da limamin garin da sauran ƴan…

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol