Free chapter · Read without an account

Page-46

by 🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚 🖋️ · “SANADIN ƘADDARATA”

FASAHA WRITER'S ASSOCIATION*
     (*F.W.A)*©✍️
     ⭐⭐⭐

Ƙungiya masu aiki cikin salon hikima da fasaha gurin juya tunanin al-umma, kaifin alƙalumansu ya zarta takobi ©✍
___________________________________________________



بسم الله الرحمن الرحيم.
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد. 




❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁ 




Free book📓



By: _*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_




Page4️⃣6️⃣





"Ƙwarai Inna, Nuriyyah" muryar Halima na jinya, ta buɗe rarraunun idanuwanta masu nauyi, numfashinta na fita da shigowa da ƙyar.

Inna ta matsa kusa da ita, ta yi saurin kamo hannunta tana cewa, "yar gudalleta ya jikin na ki? Likita ya ce ya kamata ayi miki aiki, kuɗaɗen kuma da yawa, Halima ban san ina zan samo su...".

"Inna" Halima ta katseta da ambatan sunanta, kallonta Inna ta yi yayin da wasu hawaye su ka sauka à idanuwan, Halima ta ce, "Inna kar ki damu, da ni kin ji? Na san jaririn cikina babu rai à jikinsa tuntuni, ƙi... ƙila yau ce rana ta ta ƙarshe à duniya nima, kamar yadda mahaifiyar Nuriyyah ta rasu, wanda ita ce SANADIN ƘADDARAR, sai shima Abban, to nima yau ce ranar tafiyata".

"Me ki ke faɗa? Halima kada na sake jin wannan kalaman daga bakinki, kuma za ki tashi, za ki cigaba da rayuwa kamar baya da yardar Allah, yanzu zan je na kuma nemo kuɗi ko ta ya ya, ba zan iya jurar rasa ki ba 'yata", Inna ta yi maganar da kuka ta miƙe da niyyar ficewa, sai dai hannunta da Halima ta samu riƙewa ya sa ta ta juyo tana dubanta.

Sai da Halima ta rufe ido ta matso hawayen da ke ciki, domin yanzu haka ma ita kaɗai ta san abun da ta ke ji, kawai dai dauriya ta ke kwatantawa, ta fara fitar da magana cikin numfarfashi, "na haɗu da ke Inna na nemi yafiyarki, nagode Allah da ya ba ni wannan damar, sai dai yanzu babban abun takaicina shine, rashin haɗuwa da Nuriyyah, bare na nemi yafiyarta, ba mu san a ina ta ke ba, sai dai ina kyautata zaton tana raye, ina neman alfarma a gareki Inna, don Allah duk ranar da Allah yasa ki ka ci karo da Nuriyyah ko da kuwa a mafarki ne, don Allah ki nema min yafiyarta Inn...".

Ba ta iya kaiwa ƙarshen maganar ba, saboda ciwon da ya taso mata, ta wani ƙwallara ƙara mai ratsa kunne, wanda ya gigitawa Inna hankalinta, jijjiga Halima ta hau yi kamar an jona mata wutan lantarki, likitoci su ka yo kanta da gudu, da sauri Inna ta fice ƙirjinta na bugawa, don ta ba su damar yin aikinsu, hankalinta ya kai ƙololuwar tashi.

Zama ta yi magananta na ta fitar da ruwa, ta yi tagumi tunaninta ya yi nisa, "Madam!" Faɗin doctor bayan ya sameta waje, a razane Inna ta miƙe tana kallonsa, ya kuma cewa, "Madam ina mai baƙin cikin samar da ke... mun rasa majinyaciyar da ki ka kawo mana, Allah ya ba ki haƙuri".

Jikin Inna gaba ɗaya ya saki ko motsi ƙwaƙƙara ta ka sa yi, daga bisani ta sulale ƙasa hawayen ma ya tsaya cak, ji ta yi gaba ɗaya kunnuwanta sun ɗauke da ga ji kamar duniya ta tsaya, Likita ko ya wuce.

Ta ɗau 'yan seconds a haka, mutanen kusa da wurin suna kallonta haɗi da tausaya mata. Lokaci ɗaya Inna ta ambaci sunan Halima da ƙarfi, sannan ta miƙe ta nufi ɗakin da ta ke da gudu kamar ta zautu, tana shiga ta ga an rufe fiskar Halima, kuka Inna ta fara rerawa matsananci mai ratsa cikin rai.

Ta je tana jijjiga Halima kamar za ta ta shi idan ta yi hakan, "ke Halima, 'yar gudalleta ki tashi, tashi mana, ba na ce na yafe miki ba? To ki motsa mana! Ki yafe min nima, ba laifinki ba ne duk abun da ki ka aikata, laifi na ne, ni ce SANADIN!" Haka ta ke ta sambatu akan gawan Halima kamar mahaukaciya.

SADIYA. 

Nurse ta fara cewa, "ta shaƙi iskar sosai, ya yi mata illa da yawa, hakan ya yi sanadiyyar shiganta coma, sannan mun rasa ta ɗaya", sai da Faruq ya ja da baya kamar wanda hankalinsa ya yi nisa da shi, ba ma shi kaɗai ba, hatta su Baaba sai da numfashinsu ya dakata, su ka sa salati, ita ko Nusaiba juyawa ta yi, ta saki murmushi duk da zuciyarta ya ɗan taɓu da jin ta kashe rai.

"Nurse is not possible! Ba zai yu ba, babu abun da ya samu matata" faɗin Faruq ya durƙushe haɗi da fashewa da kuka, wucewa nurse ta yi tana tausaya masa, rarrashinsa su Malam su ka shiga yi, su Baaba suma kukan su ke, Malam ne kawai mai dauriya, Nusaiba a siɗaɗe ta bar wurin dama ba ganin zuwanta su ka yi ba. 

Faruq ya ƙi sassauta kukan saboda zafin da ya ke ji a cikin ransa kamar za ta fashe, me yasa Sadiya za ta tafi ta barsa haka kawai? Ba zai iya jura ba. 

Bayan wasu mintuna, doctor ta fito daga ɗakin, ta iso garesu tana dubansu ta ce, "bayin Allah don Allah ku yi shiru, wannan kukan da ku ke yi yana kawo mana matsala akan aikinmu".

Baaba ta ce da ita, "haba dakta, yanzu mu yi wannan babban rashi ki ke yi mana wanga magana?" Malam ya ce, "kin ga Talatu zancen likita gaskiya ne, ku yi haƙuri da wannan kukan" ya maida kansa ga Faruq ya kuma cewa, "ɗana ka yi haƙuri, wannan muƙaddari ne daga Allah, mu yi haƙuri Sadiya addu'a ta ke buƙata".

Doctor da ke shirin yin musu wata maganar, jin abun da Malam ya faɗa yasa ta dakatawa ta kallesu ta ce, "har kunsa mata suna ne?" Da rashin fahimta su ka kalli likita, Lantana ta kuma cewa, "kamar ya doctor? Matar ƙanin nawa ne ki ke tambaya har ansa mata suna?".

"Matar ƙaninki? To ai ba ita ce kuka rasa ba", ɗib Faruq ma ya tsaida kukansa, ya yi saurin miƙewa ya na duban doctor da neman ƙarin bayani, ko da ta lura da haka, sai ta kuma faɗin, "cikin 'yan biyun da ta ke ɗauke da shi..." "ciki? 'Yan biyu dakta?" Baaba ta tari numfashin doctor.

Sauran ma su ka fiddo ido, musamman Faruq har bakinsa na rawa, "kuna nufin ba ku san tana ɗauke da ciki ba ko me?" "Doctor yi mana bayani don Allah, wancan nurse ɗin ta ce mana mun rasa Sadiya, ke kuma yanzu kin zo da wani zance daban" faɗin Lantana.

Sauke numfashi ta yi ka na ta ce, "ba ku fahimceta ba ne, wacche ku ka kawo mai suna Sadiyar da ku ka anbata, tana ɗauke da cikin 'yan biyu, sakamakon chemical ɗin da ta shaƙa ya sanya ta rasa ɗayar", wani ruwan ya gangara da ga idon Faruq, cikin murna ne ko alhini bai san wanda zai yi ba, zuciyarsa na ba da sauti, ya ce, "kenan matata Sadiya tana ɗauke da ciki?".

"Kuma 'yan biyu amma ba mu sani ba?" Baaba ta ƙarashe, doctor ta kuma cewa. "Wannan haka ya ke, amma duk ba wannan ba, a yanzu mun gama yiwa Sadiya duk wasu aikin da ya kamata, sai dai tana cikin babban situation gaskiya, ta shiga coma, don haka za'a maidata fannin ICU don ba ta kulawa sosai, amma ɗayan jaririyar kam ba mu gaatsala ba" murna ta koma ciki, daga jin wannan batun na likita.

Faruq ya sauke kai wasu hawayen na zuba, doctor ta kuma cewa akwai buƙatan su biyota, ba musu Faruq ya bita da gaggawa, hankalinsa ya ƙara tashi jin matarsa na cikin hatsari, shi ya ma zan yi da ransa yanzu? Malam ma ya bi bayan Faruq.

Baaba zama ta samu damar yi a hankali Lantana ma ta zauna gefenta, "ashe yarinyar nan tana da ciki har na 'yan biyu, amma mu ka yi ta mata gori kala kala akansa? Kai Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, ya Allah ka tashi kafaɗar wannan baiwar ta ka, ya Allah ka ba ta lafiya, yanzu ta ina zamu fara sanar da iyayenta wannan mummunan labarin? Muna da buƙatan neman yafiyar Sadiya", sai ta kuma fitar da hawaye haka itama Lantana.....

Nusaiba ko ba ta koma gida ba, sai gurin Iya Mairo ta yi, "kee don Allah Nusaibata, Abun da ya faru kenan?" Faɗin Mairo tana kallonta. Sauke numfashi Nusaiba ta yi ta ce, "wallahi kuwa Iya, ni tsorona kada su gane ni ce na yi wannan aika-aikan, da kuma tsoron hankalin Faruq ya dawo".

Murmushin muguwa Mairo ta yi tana cewa, "sa ranki cikin ruwan sanyi, ki yi kamar ba ki ji kalaman da ya yi ba, ruɗewa ce kawai da kuma soyayyarsa da ita, amma ba abun da hakan zai canza, ba su ɗan lokaci, don aikin bokan nan ba na wasa ba ne, tun da har ya ce mana sai kin karya ƙa'dar yin magana kuma Faruq ɗin ya ji sannan zai karye abun duka, to haka lamarin ya ke".

"Amma dai Iya yakamata a koma gun bokan nan, don ya kuma duba mana da yin wani aikin, don kada a samu matsala, kuma kin ga mun yi asarar maganin nan", fadin Nusaiba, Mairo ta kuma cewa, "ya yi tafiya ai, sai dai mu jira in ya dawo, amma kamar yadda na sanar da ke kada ki sanya damuwa a ranki Nusaiba, ba abun da zai faru, ki yi sha'aninki kamar baya, ki sha kuruminki".

Nusaiba ta ji daɗin haka, ta miƙe tana mai yiwa Baaba sallama, akan bari ta koma ya kamata ta ga lokacin da za su shigo da gawar Sadiya, ba tare da ta san Sadiya na raye ba, sai dai tana cikin coma, sai dai kamar ƙafarta ɗaya na cikin rayuwa ɗaya kuma mutuwa....

MONDAY. NURIYYAH.

Mun shirya zuwa school, har yanzu ni da Asma'u ko sannu ba ya haɗa mu, bayan mun je makaranta ko wani ɓangare su ka fara jarabawarsu, sai dai ni gaba ɗaya hankalina ya kasa kwanciya, duk da na yi iya ƙoƙarina ganin na zana jarabawar yadda ya dace.

Da wuri na gama sanna na fito na zauna a ƙasan wani icche mai sanyi, tagumi na yi ina tunanin yadda zan yi, kwatsam sai maganar Abba ya faɗo min na jiya, ya tambayeni akan me ya ke damuna, domin shi karan kansa ya ga canji a tattare da ni.

"Ina son sanin duk wata matsalar da za ta sa ki cikin damuwa, ki sanar da ni domin na yi ƙoƙarin samar miki da mafita, ba jin daɗi a gareni idan ina kallonki haka, please let me know". Na ji daɗin kalaman nan na sa jiya, sai dai ban iya ce masa komai ba.

Amma a yanzu ina jin ya kamata na sanar da shi, zan iya samun mafita daga garesa, na san ya yarda da ni. Wannan dalili yasa na tashi daga mazaunin da na ke, na nufi side ɗinsu Wasila, ba su fito a nasu ba, don haka na juya kawai na nufi hanyar fita, mashin na tare na shiga, na sanar da shi inda zai kaini wato asibitin Abba.

Ko da na isa hospital ɗin ya min kyau sosai, duk da mun zo lokacin da aka buɗe. A ofishinsa na sameshi, farin ciki fal ransa da wannan bazata da na kai masa, bai tsammaci zuwana ba, gaisheshi na yi ya amsa da tambayata ya exams ɗin? Na sanar da shi lafiya ƙalau, "Mine, kewata ki ka yi ne ki ka kasa haƙura na dawo gidan?" Ya faɗi yana ɗaga min gira da murmushinsa mai kyau.

Nima martanin murmushin na mayar masa ina yin ƙasa da kaina, "imm I'm listen, Mine" ya kuma faɗi, ɗagowa na yi ina kallonsa da tunanin ta inda zan fara, matsawa ya yi kusa da ni yana ƙarewa fiskata kallo, da sauri na kauda kai gefe har na so manta me ya kawo ni, amma dai na ce, "Yayana daman... ina son sanar da kai wata magana, kuma ina fatan za ka fahimceni?".

"Of course, Mine, kawai faɗi kanki tsaye, ina tare da ke kin ji farin cikina?" Ya faɗi da sanyin murya. Hakan ya kwantar min da hankali, na ji cewa nan ne ya kamata na kawo kukana, ban sanar da Momy ba gudun kada ta shiga cikin matsala.

"Ihimm ina sauraronki my heart" kallonsa na ke yi kamar yadda shima hakan ya ke, sai fara'a ya ke min wanda hakan ya ke hana ni cewa komai, ƙarshe dai na daure zan faɗi, "Yayana jiya ka min tambayar abun da ke damuna, shine yau na ke son sanar da kai, daman abun da ya ke..." ban kai ga ƙarisawa ba saboda turo ƙofar da Sayyid ya yi.

Ya tsaya yana kallonmu yayin da ya ji wani abu ya soki zuciyarsa, muma kallonsa mu ke, sakin fuska ya yi ya iso bayan ya danne komai, yana faɗin, "a ah yau Amarya ce ta zo da kanta?" Murmushi na yi masa ina gaishesa, ya amsa ya kuma ɗaurawa da cewa, "masoyan asali kenan" Abba ya ce, "kewata ta yi shi ne ta zo dubani".

"Ah da kyau, masoya" ya kuma ɗaurawa da cewa, "Nuriyyah zan yi miki laifi fa" da mamaki na ce, "laifi kuma yaya Sayyid?" "Eh mana laifi, to akwai wasu mara lafiya da aka kawo, kuma ana da buƙatar angonki a wurin, kuma da alamu kina son tattaunawa da shi".

Miƙewa na yi ina murmusawa na ce, "Yaya Sayyid wannan ai ba wani abu ba ne, we’ll discuss it when he comes home" na maida kallona kan Abba da idonsa kaina. Sai wani jin daɗi ya ke kamar wanda aka ma albishir mai girma, "Yayana ka tashi ka je mutane na da buƙatanka". 

"Mu je na saki a mota toh" Abba ya faɗa, na yi saurin girgiza masa kai, na nuna masa ya je ya duba marasa lafiya kar ya damu da ni, a ƙarshe dai ya haɗani da Sayyid akan ya sa ni a mashin.

Bayan mun fito haraba Sayyid ya ce mu je kawai ya kai ni gida sai ya dawo, ban ƙi ba na shiga.....

Su Asma'u bayan sun fito ba su tadda ni ba, Wasila har ta fara nemana da damuwa, amma Asma'u ta ce su tafi, ko da Wasila ta fara cewa ya kamata su duba ko ina ciki, sai ta ce da ita, ita za ta wuce gida idan ya so Wasilar ta tsaya, ba ta ji daɗin kalaman Asma'u ba, haka kawai su ka dawo.

Yau ma Momy ta rufe Asma'u da faɗa, akan sun dawo ba tare da ni ba. "Wannan wani irin abu ne ku ka ɓullo da shi kwanan nan Asma'u? Akan wani dalili za ku dawo ba tare da 'yata Nur ba?!" Cewar Momy da masifa, Asma'u ta ce, "ba mu ganta ba ne fa, ba mu san ina ta yi ba, waya sani ko wani gurin yawon iskancin na ta...".

Marin da Momy ta yi mata ne ya tsayar da ita daga kaiwa ƙarshen batun, "wani irin yawo iskanci ki ke son cewa, to kar na ƙara ji kina ji na?! Na san 'yata, da ace ita che aka tashi ba ta ganki ba ba inda za ta je sai ta jiraki, ko kuma ta dawo cikin tashin hankali tana cigiyarku, amma ki ke sanar da ni wannan banzar maganar?! Idan kin samu saɓani da ita ba shi zai sa ki faɗi haka ba, ina lura da ku kwanan nan ai"

Idanun Asma'u su ka cika da ƙwallah, yadda Momy ke yi mata faɗa akan Nuriyyah, share hawaye ta yi sannan ta wuce ba tare da ta ce komai ba. Momy kuwa ta zauna akan kujera ta ciro wayarta za ta kirani, sai dai ni ba na zuwa da waya makaranta, ijje wayar kawai ta yi a gefenta tana roƙon Allah yasa lafiya na ke.

Ayusha fa ta gama jin komai ta ƙarasa shigowa, ta gaishe da Momy, sannan ta wuce inda Asma'u ta ke, bayan ta shiga ɗakin ta sameta zaune akan gado tana kuka, sai da ta murmusa na manufurcinta sannan ta ƙarasa haɗi da cewa, "Asma'u lokaci ya yi, kada ki dakata, ki je yanzu ki sanar da Momy komai, akan me saboda Nuriyyah wacche ki ka gane wace ita, za ki sha mari? Saboda haka, go and tell Aunty everything that happened".

Shiri Asma'u ba ta ce komai ba, ganin haka Ayusha ta kuma ƙarawa da faɗin, "idan har ki ka ƙi faɗar gaskiya, za ki yi dana sani mara adadi, tayu makircin Nuriyyah ba a iya haka ya tsaya ba, gwara ki yiwa tufkar hanci, I am with you, zan zame miki shadah!" Asma'u ta ɗago ta kalli Ayusha, ita ko ta giɗa mata kai alamar ƙwarai.

Da jin haka kuwa ta miƙe tana faɗin, "shikenan! Yau za ayita ta ƙare! Kowa zai san ɓoyayyen sirrinta, Momy ta mareni saboda ita! Don haka marin sai ya koma kanta, ita ba 'yar uwata ba ce!" Tana faɗi ta fice a ɗakin fiska a haɗe. 

Ayusha miƙa ta hau yi tana ɗage hannu cikin nishaɗi, sannan ta zauna akan gadon, "I'm so proud of my self, Nuriyyah your welcome!" Ta faɗi sannan ta miƙe don zuwa falon, kamar yadda ta ce ita shaida ce......


Last page
___________________________________________________


😭rayuwa kenan, yau kai ne gobe ga ɗan uwanka, na tausayawa Halima, ta yi dana sani n'a haƙiƙa, yadda ta tuba Allah ya sa ya zame mata sanadin shiga aljenna, masu wannan halin kuma ya ganar da su, mun yi rashin rai biyu, Halima da jaririnta. Shin S man ya ci bulus kuwa?.

Ga Sadiya, farin ciki zamu yi ko baƙin ciki? Ashe tana da ciki duk abun nan🥺 ga shi Nusaiba ta salwantar mana da ɗaya, ga Sadiya cikin coma, shin za ta tashi? Ya Nusaiba za ta yi idan ta ji ta da rai?.

Hmm Nuriyyah kuma, Ayusha ta sa Asma'u ta tafi faɗa, shin Asma'u za ta sanar da komai? Ya su Momy za su ji?.

Ya ku ka ji wannan page ɗin à zuciyarku?

Mu kasance da ku a next page idan Allah ya kaimu,





_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol