Free chapter · Read without an account

Page-48

by 🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚 🖋️ · “SANADIN ƘADDARATA”

FASAHA WRITER'S ASSOCIATION*
     (*F.W.A)*©✍️
     ⭐⭐⭐

Ƙungiya masu aiki cikin salon hikima da fasaha gurin juya tunanin al-umma, kaifin alƙalumansu ya zarta takobi ©✍
___________________________________________________



بسم الله الرحمن الرحيم.
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد. 




❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁ 




Free book📓



By: _*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_




Page4️⃣8️⃣






Dady gefe ya yi kamar zai faɗi Abba ya taroshi sannan ya zaunar da shi, Asma'u kam sosai ta ƙarawa kukanta sauti. "Ya jikin na ta yanzu? Zuwa yaushe za ta iya tashi?" Dady ya yi tambayar, Abba da gaba ɗaya ransa ya ke wani iri ya kallesa ya ce, "Dady muma ba mu da tabbacin lokacin farkawarta, sai dai... nan da awa ashirin mu ke sa ran tashinta", sai da kowa ya razana, wannan awanni ashirin sun yi musu tsawo kamar shekaru.”

Da damuwa Uncle Usman ya ce, "to idan ta wuce hakan fa?" "Ba mu san me zai faru ba kuma" Sayyid ya ba shi amsa. Miƙewa Dady ya yi kamar an tsikareshi yana faɗin, "inna lillahi wa inna ilaihi raju'un! Taya ma aka yi Rahama ta samu guba? Ya aka yi ma hakan zai far..." "cikin kunu!" Ayusha ta katsar masa da maganarsa, dukkansu su ka juyo suna kallonta, ba tare da sun kammala fahimtarta ba.

Ganin haka ne yasa Ayusha ta ja numfashi ta matso kusa har da share wai hawaye a idonta, sannan ta cigaba da cewa, "uncle idan kun fahimta, Aunty ba ta ci wani abinci ba sai kunun nan da ta sha, kuma tana kan shansa ne yanayinta ya fara sauyawa, to idan ba shi ba akwai abun da kuka san ta sha ne?".

Cikin rawar baki Asma'u ta ce, "kina nufin kunun da Nuriyyah ta yiwa Momy? A ciki poison ɗin ya ke?!" Gaba ɗayansu su ka kuma zare ido sosai musanman Dady da Abba, "no no no no no, it's not possible! Ba zai taɓa yuwa ba, sai dai wani abun daban Momy ta sha, no ba kunun nan ba ne" faɗin Abba da ƙarin shiga tashin hankalin.

Su Dady sun kasa cewa komai, Ayusha ta dubesu dukkansu, ganin ta samu dama sai ta ce, "kada ku yi mamaki Abba, uncle yarinyar nan ba fa kusanta ba, amma Asma'u ai ke kin san halinta na ainahi ko? Then tell them" Asma'u ta ɗago tana kallon Ayusha ba tare da ta ce komai ba.

"Asma'u listen! Kada ki kuma aikata wannan kuskuren a yau, ki duba ki ka ga abun da ya faru yanzu, ta aikata fiye da abun da ta yi miki, idan ki ka rufe baki na yau kuma, ba ki san me zai kuma faruwa a gaba ba, ki yi tunani mai kyau" ta yi maganar tana giɗawa Asma'u kai.

Duk ido ya koma ga Asma'u, yayin da zancen Ayusha kuma ya shiga jikin Asma'u, ta ke wani baƙin ciki da tsanar Nuriyyah ya ƙara karaɗe zuciyarta, musamman da ya zamana wannan karon mahaifiyarta aka taɓa, su Abba da su ke kallonsu kawai ba tare da sun fahimci inda maganar ya nufa ba, Dady ya ce, "akan me, ku ke magana akai?" "Tell them Asma'u" Ayusha ta kuma faɗi tana dafa ta da munafurci.  

Asma'u ta girgiza mata kai, ka na ta share hawayenta, ta sauke ajiyar zuciya, Ayusha ta kauda kanta gefe cikin zuciyarta ta ce, "kin ƙi sanar da kowa wancan lamarin cikin sauƙi, to ya kenan yanzu da wannan lamarin ya afku?" Ta ƙarashe da sakin murmushi, sannan ta dawo da fiskanta garesu da damuwa sosai.

Asma'u ba ta ɓata lokaci ba ta zayyanewa su Abba duk abun da ya faru a wancan ranar. Tun kafin ta kai ƙarshe Abba ya yi ƙasa zuciyarsa na rawa kamar za ta ɓallo ƙirjinsa ta fito, har sai da ya ji ƙwaƙwalwarsa ta tsaya, Sayyid da shima ta sa zuciyar ta ke a haka cikin tashin hankali ya yi ƙasa yana dafa Abba.

A wannan lokacin wasu nurse su ka zo da faɗin jikin wani majinyaci ya tashi, don haka da gaggawa Sayyid ya wuce don zuwa duba shi, duk da bai so barin wurin ba, shi a jikinsa yana jin tabbas akwai lauje cikin naɗi, amma bari ya gama da aikin gabansa kafin ya san ta inda zai fara.

Dady kuwa numfashinsa ne ya dakata, wannan kalaman sun girgiza shi matuƙa. Uncle Usman ma ya yi mamaki da jin haka sosai.

"Ban yi tsammanin halinta har ya kai haka ba, shiyasa na bar wancan maganar a ganina hakan shine daidai, sai dai ashe Nuriyyah ta riga da ta shirya kashe min mahaifiyata" faɗin Asma'u tana kuka sosai, Ayusha cikin salon munafurci itama kamar tana kuka ta ja Asma'u su ka zauna kan kujerun gefe, don ta gaji da tsayuwar.

"Nuriyyah? Neman maza? Kashe Momy? Da guba? Da gaske na ji duk wannan magan-ganun?" Cewar Abba da sassarfa ya furta numfashinsa na rawa, ai kuwa Ayusha ta miƙe tana zuwa kusa da Abba ta durƙusa tana cewa, "wannan ma ƙila kaɗan daga cikin abun da za ta iya yi nan gaba ne, you know what? A ƙasar UK na san mutane da yawa masu makamancin halin Nuriyyah, a ido idan ka gansu ba za ka taɓa yarda za su yi....".

Jajayen idanuwasa da ya ɗago ya watsa mata wani kallo da su, shine ya dakatar da ita daga zuba zancen da ta ke, ta miƙe ta kame bakinta ta koma gefen Asma'u, a hankali Abba ya miƙe daga durƙushen da ya yi, a daidai nan wayarsa ya hau ringing, ya ciro daga cikin aljihun na sa, don bai ma yi tunanin ya bar wayan a ciki ba.

Ɗagawa ya yi yana goge idanuwansa yayin da zuciyarsa ta ke ƙuna, daga wayar Hajiya Kaka da damuwa ya tarun mata ta ce, "menene ya samu Rahaman? Na yi ta kiran mahaifinka ashe ya bar wayar a gida, shi kuma Usman numbernsa ba ya shiga, ban san ko network ba ne, wai me ke faruwa ne? Faɗa min me ya samu 'yata?" Ta faɗi tana sharar ƙwallah.

Abba cikin wata iriyar murya ya ce, "muna zuwa gidan yanzu!" Kawai abun da ya faɗa ya sauke waya, "me ka ke nufin kuna nan zuwa Abba?" Faɗin uncle Usman, Abba ya dubesa ya ce, "zamu je, inji meyasa Nuriyyah za ta yi haka?" Kafin uncle Usman ya ce komai Abba ya wuce zuwa gurin Sayyid, ya ce da shi ya kula da Momy zai dawo nan ba da daɗewa ba.

Sayyid ya tambayeshi ina za shi me zai je yi? Amma Abba ya ce kawai dai don Allah ya ba mahaifiyarsa kulawa, sannan ya wuce, Sayyid ya shiga tunanin ina Abba zai je? Amma dai ya kamata ya yi masa uzuri, don ya ma yi ƙoƙari da ya yiwa Momyn aikin kuma cikin ƙwarewa duk da zuciyarsa ba a kwance ba.

Nan su Abba su ka fice dukkansu cikin fisata, Dady kam magana ma ya kasa yi, ran Ayusha kuwa fal farin ciki, don ta san za ayita ta ƙare! Yau ce ranar nasarar.....

Ina zaune a gefen Hajiya Kaka idona a kumbure sakamakon kukan da na sha yi, kamar mara lafiya na zama saboda tsoro da kuma fargaba haɗi da tashin hankali akan abun da ya samu Momy, addu'a irir iri ba wanda ban yi mata ba. Bayan Hajiya Kaka ta sauke wayar da gaggawa na ke tambayarta ina fitar da hawaye na ce, "me su ka ce Hajiya? Ta samu lafiya? Ko sun ma haɗaku kun yi magana?".

"A ah, sun dai ce suna zuwa" ta faɗi itama wasu hawayen na sauka a idanuwanta, ganin haka na hannu sa na share mata ina cewa, "ba abun da zai samu Momy kar ki damu, tun da su ka ce suna dawowa ƙila da ita ne, ki daina kuka Hajiya Kaka" rungumeni ta yi tana girgiza kanta alamar hakan na ke fata.

Lokacin su Mama su ka shigo sashin gaba ɗayansu sun shiga damuwa, sannan su ka zauna tun da itama Mama ta yi magana da Uncle Usman ya ce mata suna hanya. Zuciyata bugawa ke yi sosai na rasa me ya ke min daɗi, ban san takamammen abun da ke damuna ba, rashin lafiyar Momy ne ko ya haɗu da wani abun i don't know.

Muna zaune a haka kowa da abun da ya ke sakawa a cikin ransa, kawai mu ka ji sallamarsu, sai da zuciyata ya bada rass da jin shigowarsu, dukkanmu mu ka miƙe muna kallonsu yayin da su ke shigowa, ganin ba Momy a cikinsu yasa ni leƙa bayansu da fargaba.

Ko da su ka ƙaraso tsayawa su ka yi dukkansu suna kallona, ba tare da na lura ba, barin kallon ƙofa nai tun da ban ga Momyn ba, "Dady ya na ga kun dawo ku kaɗai ina Momyn ta ke me ya same ta?" Na jera musu tambayar ko numfasawa ban yi ba, Su Hajiya Kaka ma kamar wakiltarsu na yi, su ka tsaya suna jiran amsa, yayin da ko wanne a cikinmu ya kasa sukuni.

Buɗan bakin Asma'u sai cewa ta yi, "kin fi kowa sanin a halin da Momy ta ke ciki yanzu!" Kallonta na ke da mamaki sosai, "ni kuma? Me ki ke cewa? Dan Allah faɗa min what happened to my Momy?" "Ita ɗin ba Momynki ba ce! Shiyasa ki ka yi mata abun da ki ka mata". Asma'u ta kuma cewa, cikin fargaba na ke cigaba da kallonta, ban gane me ta ke cewa ba, na maida kallona gun Abba. 

Sai da gabana ya faɗi saboda ganin yadda ya ke yi min wani irin kallo, ina iya fahimtar kallon na da alaƙa da tsana, Hajiya Kaka da ta gaji da jin wani zance ba wanda ta ke son ji ba, ta fara faɗin, "wani irin magana ku ka tsaya ku na yi ne? Asma'u kina lafiya kuwa ki kewa 'yar uwarki irin wannan kalaman? Wai me ma ya samu Rahamar? Ku faɗa min inji".

Wannan karon Ayusha ce ta ce, "Hajiya Kaka kalaman da Asma'u ta ke faɗawa wannan yarinyar ta cancanci fiye da su ma, saboda ita che sanadin rashin lafiyar Aunty Rahama!" Da sauri na cire kaina da ga kallon Abba da na ke na maida shi kan Ayusha, me ta ke nufi da maganarta?. Mama ta ce, "ke Ayusha ku fito fili ku sanar da mu abun da ya faru mana, gaba ɗaya kaina a kulle ya ke, kamar ya Nuriyyah ce silar ciwon Rahama?".

Ayusha an kuma samun dama, ta kuma faɗin, "Mama, Anty Rahama ta shiga wannan rashin lafiyar ne sakamakon poison da ta sha, kuma ba a ko ina tasha wannan poison ɗin ba sai a cikin kunun da wannan Nuriyyahr ta ba ta!" Ta kai ƙarshe da nuna ni da yatsa tana kallona cikin ido. 

Ba ni kaɗai ba, hatta da sauran sai da su ka girgiza matuƙa da wannan batu, sai da na zare ido kamar zasu fice daga mazauninsu, saboda tsabar girgizar da zuciyata ya yi, poison? Kunu? Ni?, na furta cikin raina, da inda-inda na ke cewa, "mmm... me ki ke cewa? Poison fa? Kuma cikin kunun da na ba Momyna? No no no ba gaskiya ba ne, ba gaskiya ba ne, ba gaskiya ba ne".

Wasu sabbin hawaye su ka yi zaman dirshen kan fiskata, Hajiya Kaka dai ko motsi ta kasa yi, Dady sai yanzu ya samu damar buɗe baki, kamar daga sama na fara jin farucinsa a tsakiyar kaina, "me yasa za ki yi mana haka Nuriyyah? Me mu ka tsare miki? Shin mun taɓa cutar da ke a iya zamanmu da ke? Me Rahama ta miki da ki ke neman ranta? Ta riƙe ki kamar 'yarta, ta so ki matuƙa, ako da yaushe zancenta Nuriyyah yarinyar kirki, amma ashe ba haka abun ya ke ba? Ashe sakayyar da za ki yi mata kenan? Kasheta shine muradinki Nuriyyah? Kisa? Kisa fa".

Girgiza masa kai na ke ta yi tun da ya fara maganar, "a ah Dady kar ka ce haka, ba gaskiya ba ne, ko kyankyaso wallahi ban taɓa kashewa ba, bare Momy, Momyna ce fa, ta ya zan kasheta? A ah Dady ba zan kashe Momy ba" Dady da zuciyarsa ya ƙara harzuƙa ina gama maganar ya sauke min mari mai ƙarfi a kumatuna, da hanzari na kai hannuna gun kaina a ƙasa hawaye su ka zubo, na fara kukan da ba sauti, amma mai radaɗi.

"Kina ganin zamu yarda da wani kalamanki ne yanzu?" Na ɗago ido ina ƙara kallon Dady, ya cigaba da cewa, "kin riga da kin rusa duk wata yarda da mu ka ɗaura miki, kenan ita kaɗai ki ka yi niyyar kashewa, shiyasa ki ka hana kowa shan kunun ko? Rahama wacche ko da yaushe ba ta ganin laifinki ita ki ke son kashewa, wannan wani irin abun ƙyama ne haka?".

"Ah haf, ni dama na san lokacin nan yana nan zuwa, ko ba daɗe ko ba jima, gashi Allah ya kawo mu ranar, yanzu Nuriyyah kin ma wuce tunanin kowa har kisa za ki iya yi? Kuma wa Rahama matar da ta ke matuƙar ƙaunarki fiye da 'ya'yanta? Tir wannan abu da me ya yi kama?".

Na rintse idona ina cigaba da kuka, salatin da Hajiya Kaka ta yi ne yasa ni ɗagowa haɗi da juyowa ina kallonta, kame kanta ta yi yayin da ya ke juya mata sosai, da sauri na isa gabanta ina son kamata, amma ta yi dauriyar dakatar da ni ta hanyar ɗaga hannu, jan birki na yi na tsaya ina kallonta, Wasila da ke kusa da ita ta kamata ta ijje ta kan kujera, itama hankalinta a matuƙar tashe sosai, taya ƙawarta Nuriyyah za ta yi haka?.

Ƙarasowa gurinta na yi na tsugunna a ƙasa ina kama hannunta na ce, "Hajiya Kaka wallahi ni ban sawa Momy guba a abun sha ba, ni ban ma taɓa riƙe wani abu mai suna guba ba, ki yarda da ni don Allahu!" Na ƙarisa ina sa kuka mai sauti, janye hannunta ta yi da sauri tana hawaye, "karki taɓani" ta furta, na kuma miƙewa ina kallonta ina girgiza kai.

"Hmm tuntuni dama Allah ya riga ya nuna min, amma na yi ta magana aka maida ni mahaukaciya a gidan nan, gashi yanzu ta ma wuce tunanina" Mama ta kuma faɗi tana kallona da tsananin tsana, Nusaiba ta ce, "wallahi Mama ni ban yi tsammanin rashin imaninta zai kai haka ba, hmm ɗan adam kenan" Wasila dai ƙwallah ne ya cika a idonta, ta ma rasa me za ta ce akan wannan lamarin.

Nufan inda Abba ya ke na yi, duk da cewa har yanzu kallon ɗazu ya ke bina da shi, "Yayana kaima ka yarda? Ka amince ni zan iya wannan abun? Maganar kisa fa, ta ya ma ni zan kashe wani, kuma wai Momy? Ita ce fa kaɗai ta ke kirana da Nur, sunan da Ummata ce kadai mai ce min hakan, Momy mahaifiyata ce, akan me zan sanya mata guba? A ah, wallahi ban aikata ba, na san kai za ka yarda da ni ko? ".

A baya idan na ambacesa da Yayana har wani sanyi ya ke ji cikin ransa, amma sai dai yau ji yayi kamar na jefa masa mulmulen wuta cikin ran na sa, da tsawa ya ce, "akan me zan yar da ke!? Wani irin yarda zan yi miki? Bayan komai a bayyane ya ke? Kin bani mamaki Nuriyyah!" "No Yayana, ba zan iya aikata makamancin kisa b..." "amma za ki iya bin maza ko? Za ki iya lalata rayuwar 'yar uwarki ko?" Wani Sabon girgizan na yi jin kalaman da ya faɗa, yana magana akan sharrin da Sunusi ya min.


Last page
___________________________________________________

😭 mu haɗu gobe idan Allah ya kaimu.

Like, comment, and share please 🙏🏻



_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol