Free chapter · Read without an account

5

by Amina Abubakar Yandoma · KAFAR HAGU

*'KAFAR HAGU*

©️ Meenat A. 'Yandoma

Wattpad: Meenat_A_Yamdoma
Arewapen: @meenatyandoma

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

🅿️age 5
..."Ghali ka rufa mini asiri, kada kayi mini kisan kai a cikin gida." Magajiya ta fada tare da rirrike masa kafa. "Mun shiga uku! "Bushura ta fada lokacin da ta ga Gaga ya watsar da Farida sharaf! Tamkar kayan wanki "Magajiya kamar fa ya kasheta! Innalillahi wa'inna ilaihirajiun! Farida" ta hau girgiza Farida da ke yashe a kasa bata sam me ke faruwa ba. A guje Ɓurilli ta debo ruwa suka hau shafawa mata. Doguwar ajiyar zuciya ta sauke tare da miƙewa a rikice. Ganin Gaga ya duka kusa da ita sai da hantar Magajiya ta kaɗa, saboda bata san me zai biyo baya ba. "Wannan ɗanɗano jiran rabo ne nayi miki. Ranar da duk hannunki ya ƙara saura a jikin Rauda, ko da a ce da wasa ne. Farida zan shafe duk wani tarihin rayuwarki, sai na kafa tarihin da mata irinki za suji tsoron aikata makamancin abinda kika aikata."
Ya na kai wa nan, mikewa ya yi. Cikin zafin Nama Farida ta riƙe masa ƙafa. "Ina sonka ina ƙaunarka, kada ka ce zaka so wata Ghali mutuwa zanyi ka ji tausayina" da karfin gaske ya saka ƙafa ya hankaɗar da ita. Hannun Rauda da ke durƙushe ya kama ya kama suka shiga ɗaki. Kuka Farida ke yi tamkar wadda aka yiwa bushara da rasa iyaye. "zubar da mutumcin ya isa haka. Ki tashi mu tafi tun kafin wannan mahaukacin ya zamo ajalinki." 
"Aa 'yar nan. Ki yi shuru kada ya jiki ki janyo mana wata masifar da ba mu iya tarbewa." Ɓurilli ta faɗa. Tsoki Bushura ta yi ta kama hannun aminiyar Tata suka fice daga gida. Ganin zata shiga gidan Driver da sauri Bushuru ta shige ta tayar da motar suka bar wajen. Tunda suka fara tafiya hawaye ne ki bin fuskar farida. Kai Bushura ta girgiza cike da takaici."Farida! Anya kuwa kin daukarwa kanki hanya me bullewa? Yanzu a kan wancan ɗan dabar kika bijirewa iyayenki. Wai don Allah me kika gani a jikinsa da har kike wannan kukan." Da sauri ta taso da kanta data jingina a jikin sitiyarin motar. "Baki ganshi ba ne Farida kallo ɗaya na yi wa Gaga na tsunduma soyayyarsa. Ya na da kyau wanda duk wata mace in ta ganshi dole ta so Shi. Dole in mallakeka KO da zanyi yawo tsirara" ta karasa maganar tare da share hawaye da ke fuskarta. “Ban fahimci abin da kuke nufi ba" "ki ja mu muje wurin Boka". "Farida wurin boka kuma a wannan lokacin?"
"Kwarai kuwa! Ko ma me je zan bayar in dai har zan wulakanta waccan yarinyar in mallakesa." Bushura ba ta yi gardama ba, domin ta fahimci kawarta tayi nisa bata jin kira. Ba su dauki dogon lokaci ba suka karaso wurin bokan.  Tsakiyar jeji ne wanda zaka iya cewa ba zaka taba samun bil'adama a ciki ba. Kallo ɗaya za ka yi wa Bokan sai hantar cikinka ta kaɗa! Tsoho ne tukuf! Fatar jikinsa duk ta yamushe , ilahirin jikinsa gashi ne barbaje tamkar jikin dabba. bukkar cike take da kayan bokanci ne rataye Abin ƙyama.
Tamkar masu neman gafara haka suka zube suna kwasar gaisuwa. "Boka!" Farida ta fada. Ɗaga mata hannu ya yi, dole ta yi shuru suna kallonsa. Wani faranti me dauke da garin magani ya janyo tare da rufe idanunsa ya na karanta wasu ɗalasimai. Zaburar da suka ga Bokan yayi tare da bude idanuwansa ba shiri, sai da hantar cikinsu ta haɗa. A karo na biyu ya sake rufe idanunsa, a yanzu kam babu shiri ya budesu. "Boka lafiya kuwa?" Da sauri Bushura ta taɓa Farida alamar ta yi shuru tunda ba shi ya ce ta yi magana ba
Sai dai Farida ta yi nisa, saboda bata ji taɓota da ake yi ba. Doguwar ajiyar zuciya ya sauke ya kafe Farida da idanunsa daka-daka. "Buƙatar ki abu ne mai matuƙar wahala ta biya."
Rass! Gabanta ya yanke ya fadi tamkar zai yi tsalle ya faro kirkira ya fado. "Bo..boo..Boka me kake nufi" ta karasa maganar laɓɓanta na kyarma. "Mutuwa! Alamun mutuwa na ke hangowa a duk lokacin da na buga aikinku. Ke, ita ko shi tabbas ɗaya zai mutu" ba Farida kaɗai ba hatta Bushura sai da ta girgiza da jin wannan bayani. "Mutuwa kuma Boka? Ni da ke neman biyan bukata me ya haɗani da mutuwa?" "Bukatarki da kike burin cimmawa. Zata iya biya amma haɗarin da ke cikinta ya fi alheranta. A duk sa'in da na buga miki aiki duhu ne ke mamaye idanuwana. Tabbas bukata zata biya amma ki sani a cikin ku ukun jikina na bani ɗaya sai ya mutu, kin amince a yi miki aikin?"
Za ta yi magana Bushura ta yi saurin tarbar numfashinta. "Yanzu ke ana maganar mutuwar kuma cikinku ba a san waye zai mutu ba. Amma kike kokarin amsawa ayi miki. Farida wace irin soyayya ce ta rufe miki ido har take shirin kai ki ga halaka?" "Ki kyakeni! Ko da Ni ce ce wadda zata mutu na amince yayi min aikin Indai bukata ta mallakar Gaga Zata biya."
Jin abin da ta fada. Mahaukaciyar dariya Bokan ya kwashe da ita. Wata 'yar karamar laya ya mika mata"ki je, kome kika gani ki kuka da kanki?" Ya na kaiwa nan ɓat! Ya ɓace. Jiki a sanyaye suka taso ba tare da sanin me zata aikata da layar ba.
"Farisa kin mutu! A kan namiji ki tunkari mutuwa? Anya kuwa yaron nan ba mallake ki yayi ba?"
"Ni da ke cikin wannan yanayin Ni kadai nasan me nake ji. Da In rasa shi ƙara ta fashe kowa ya rasa, ke banƙi ba ayi mutuwar kasko, a mutu har liman. Marece ya fara mu yi kokarin barin jejin nan"
Babu yadda Budhura ta iya, zuba mata ido ta yi har suka karasa wurin motar. Tafiya suke tamkar za su tashi sama, motar tayi tsit! kowa da abin da ya ke saƙawa cikin ransa. Sun shiga cikin garin Katsina kenan birki ya kwacewa Bushura. "Farida babu lafiya fa. Motar nan ta kwace mini" a rikice Farida da ke gefe ta tashi zaune. "Farida kinga abin da nake fada miki ko? Ƙila ma mune za mu mutu" Bushura ta faɗa ta na kuka ganin motar ta yi kan wata ƙatuwar mota. Mutanen da ke gefen hanya lokaci ɗaya kowa yayi ta kansa, motarsu Farida hanya ta saki tare da bugun ƙatuwar jefayif wuntsilawa ta riƙa yi ta fadi can gefe. Tsabar tashin hankali mutane sun kasa ƙarasawa garesu, domin ta wuntsile ga fetur harya fara zuba akwai yiyuwar kamawarta da wuta a kowa ne lokaci. Da gudu wani bawan Allah yayi kansu ya na neman taimako...

YAU BUSY NAKE, A YI HAKURI DA WANNAN BA YAWA

***


Meenat A. 'Yandoma
***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol