Free chapter · Read without an account

16

by Hafsat mustapha · KISHIN MATA

KISHIN MATA

    Hafnancy...

Kishin ilimi, Kishin Jahilci, canfe-canfe, da kuma cin amana.

•Masu tambayar WhatsApp group ɗina ga link nan ku bi*

***

No.16

A cikin wannan daran aka tasa kʼeyar Gidado gaba zuwa gidansu Hafsa tamkʼar karamin yaro,dashi da Baba Munniru,Baba Haruna sai kuma Aliyu da abokinsa Sagir wanda aka nemoshi awaya babu shiri,abunda abokin nashi ya aikata sam be mishi dadi ba,suka hada kai shida Aliyu sunata zaginsa acikin mota,Aliyu yace''wallahi malam ka bʼata wayonka,gaka nan dai ana ganinka anga mai wayau ashe abun ba haka yake ba da sauranka..ʼʼ

Baya cikin mood dʼin cece kuce shiyasa kawai yayi ignoring dʼinsa,Baba Haruna ne ya masa jan ido ganin yafi kowa zakewa yace''wai kai Aliyu bazaka rufewa mutane baki bane..?ai gara dashi har mata biyu gareshi kaifa dayan ma ta gagareka ajjewa ka tsaya kana ruwan ido,karka bari in sake jin muryarka acikin motan nan idan ba haka ba zan mugun sassabʼa maka,kaima Sagir ka kama kanka banison shirmen banza da wofi.."

Ba shiri kowannensu ya kama kansa,Gidado kuwa tunda suka kamo hanya uffan bece ba har kawo lokacin nan,lumshe idanu yayi yana tunanin sabbin halayen Yumminsa da take gwada mishi wanda ada can ba haka take ba,akwai soyayya da mugun shakʼuwa atsakaninsu don kusan zai iya cewa tafi kʼaunarshi akan sauran yaʼyanta ammh tunda ya auri Jamila komi ya sauya zani,abu kadan saita rufeshi da fada tamkʼar dama jiransa take ya aikata ba daidai ba,tunda ya auri Jamila zai iya kirga iya adadin daya zauna gashi ga mahaifiyarsa suna fira cikin so da kuma kʼaunar juna wanda ada can kafin yayi auran bazai iya misalta iya adadin zama na aminci da sukayi ba da kuma kʼaunar juna dake tsakaninsu ba,ammh ayanzu why diz sudden changes..?kodai haushinsa takeji akan rashin haihuwa..?ammh idan hakan ne toh meyasa bata dauki zafi da sauran ba sai shi..?

Wani zafafan hawayen dayake ta kafewa ne suka samu damar zubowa,adaidai lokacin suka iso kʼofar gidansu Hafsa,agogo ya nuna 10:15pm,bayan hannu yasa yana share hawayen gudun kar wani ya ankara dashi yana kuka,kowa ya fito sai ya rage shi kadai aciki yana tunanin ya fito ne ko kuwa aʼah,be gama yanke shawara da zuciyarsa ba yaji Baba munniru na fadin''zaka fito ne ko kuwa mu koma..?don bazamu shiga ciki babu kai ba...ʼʼ

Dasauri ya fito yana gyara zaman rigarsa wanda kananan kaya ne ajikinsa ko bari ya canzasu baʼa bari yayi ba aka taho gidan surukai dashi ahakan,bubbuga gate dʼin gidan suka soma yi,baʼa wani jima ba mai gadi ya budʼe musu,suka mishi bayanin kansu yace bari ya nemo musu iso awajen masu gidan,su Daddy na falo duk an zuba uban tagumi ana jimamin wannan alʼamarin har ita Hafsan,sai kuka take rerawa ahankali,Daddy ya dubeta afusace yace''Zaki rufewa mutane baki ko kuwa saina tashi na tattakaki anan..!?tunda zaman gidan kikeso ai gashi nan saiki zauna da tushi banza mara albarka wacce tayo gadon uwarta...ʼʼ

Dasauri mami ta tari numfashinta''A'ah ban gane tayo gadon uwarta ba..?ka tabʼa ganin nayi yaji ne balle naje gida da sunan ka sakeni..?ʼʼ  wani irin wawan kallo ya kwasheta dashi yace''Ai don ina hakʼuri dake ne da kuma shanye abubuwan da kikemun inba haka ba daʼace wani ne bani ba inajin da tuni kun rabu Amina,ki sani darajan yaʼyanki kike ci har kika kai tsawon lokacin nan agidan nan,ga yʼarki nan ta kwashi halayenki kaf ta dorawa kanta kuma.....ʼʼ

''Daddy don girman Allah ku bari wai meyasa kuke haka ne..?ʼʼ Mukhtar ya katsesu cikin tsananin bʼacin rai,mami tayi shewa ta mikʼe tana kokarin magana sai ga Ayuba mai gadi yayi sallama hakan yasa tadan natsu ta koma ta zauna,aka bashi izinin shigowa,dukʼawa yayi yake sanar dasu bakin da akayi,daddy ya washe hakʼora cikin tsananin farin ciki yace''Toh toh masha Allah kai Mukhtar tashi kaje ka musu iso ciki..ʼʼ

Mukhtar shima ya mikʼe yana jin wani irin farin ciki na ratsashi don ko ba komi yanason ayi sulhu kʼanwarsa ta koma dakinta,suka fice shida Ayuba,mami kuwa wani tsalle tayi ta dire take fadi cike da masifa''Wallahi Alhaji tun wuri idan sulhu sukazo nema agaskiya bazamu kʼarbi kokon bararsu ba don lokaci ya riga da ya kure babu zancen maida hannun agogo baya,insha Allahu Hafsa ta gama aurenshi ya bata takaddarta kawai....ʼʼ

Jin abunda ta fada yasa Hafsa fashewa da uban kuka tace''mami don girman Allah kiyi hakʼuri ni inason mijina kaddarace tazo mana ahakan,wallahi nina hankalta zan koma nayi maneji da igiya dayan daya sauran mana...ʼʼ kwasheta da wawan mari tayi tace''In sake jin wannan maganar ta fito daga bakinki saina sa almakashi na yankeshi,kinsan da cewa kina sonsa toh meyasa kika bari hakan ta faru..?toh ki sani ko zaki koma wannan gidan ba yanzu ba sai shima dʼin ya gane kuransa,oya maza ku tashi ku shige ciki kafin su shigo..ʼʼ

Da gudu ta shige ciki adaidai lokacin ne kuma su Aliyu sukayi sallama suka shigo,mukhtar ne agaba sai sauran suka mara mishi baya,Gidado ne akarshe kan nan nasa akasa,Ganin manya ahadʼe yasa Daddy saurin mikʼewa yana musu maraba da zuwa cikin mutunci da kuma karramawa,mami kuwa ko kallo ma basu isheta ba,suka samu wuri suka zauna aka gaisa dakyau,daddy ya umarci Nabeelah data kawo musu ruwan sha,sukace aʼah abarshi kawai sun gode,

Nabeelah ta shige ciki don tseguntawa  Hafsa cewa ai tare akazo dashi Gidadon,Baba Haruna ne yayi gyaran murya ya soma magana bayan an natsu kasancewar shine babba,yace''Alhaji muna zaune sai ga kiranka donmu harga Allah bamu da masaniyar afkuwar wannan alʼamarin,kuma fa ana tare har shi dʼin ammh be gaya mana komi ba saida ka kira kake sanar da mahaifinshi,agaskia wannan abu beyi dadi ba ammh ya zaʼayi tunda kaddararsu ce tazo da hakan,sai muyi imani da cewa hakan bazai faru ba saida hukuncin ubangiji,ayi hakuri don girman Allah yaro yayi babban laifi shiyasa muka tasoshi agaba don ya nemi yafiyarku sannan kuma ya maida ita atake tun kafin mutane su ankara da halin da ake ciki...ʼʼ

Kallon Gidado yayi wanda kansa ke adukʼe yace''kai maza ka bada hakʼuri sannan kace ka maidata...!ʼʼ

Caraf mami ta cafe tace''Ai wallahi koya bada hakʼuri ba komawa zatayi ba sai lokacin da muka so...ʼʼ azuciye Daddy ya kalleta yace''wai ke Amina meyake damunki ne..?ya zakice bazata koma ba shin kece keda iko da ita koni..?maza shiga ciki kibar maza suyi magana...ʼʼ

Tsoki tajah sannan ta shige tana gunguni,daddy ya dafe kansa cike da takaicin yadda ta dizgashi gaban surukansa,Mukhtar shi kansa ji yayi tamkʼar ya rusa kuka ko zaiji sanyi aransa,su baba haruna kuwa sai jinjina rashin mutuncinta suke,suka sake tabbatar da cewa lallai kam biri yayi kama da mutum,halayenta ne kaf yʼar ta kwasa,Shi kanshi Gidado aransa yace''Ashe halayenki ta kwaso tsaf...ʼʼ

Daddy yace''Don girman Allah kuyi hakʼuri kunsan shaʼanin mata sai ahankali,badamuwa yarinya zata koma dakinta ayau dinnan basai gobe ba..ʼʼ har ya mikʼe zaibi bayanta sai Gidado yayi hanzarin dakatar dashi yace''Daddy karka matsa mata don Allah abi komi asannu kuma ahankali,ni abunda yasa na saki Hafsa ba don komi bane illah fusatani da tayi,ta nunamun cewa ban isa da ita ba tare da yiwa matata da sauran yanʼuwana gorin haihuwa........ʼʼ

''Yo! Kujimun zancen banza fa toh kʼarya tayi..?nace kʼarya tayi..?su dʼin ba juyayyu bane..?ka gayamun yaʼyan da suka fito daga tsatson mahaifiyarka acikinku akwai wanda ya haihu ne...?baka ma gode Allah cewa Hafsa ta aureka ba tare da nuna damuwa akan rashin haihuwar taka ba..?ita wancan wahalalliyar ita taga zata jure zama dakai ammh Hafsa dai bazata koma gidanka ba,dama kaddarace ta hadaku kuma kaddarar ta rabaku,alhamdulillah naji dadin hakan sosai,akarshe ina mai shawartarku daku hanzarta binciken mahaifiyarku don ina tuhumarta akan cewa dasa hannunta acikin rashin haihuwarku dukah....ʼʼ

Gabaki dʼaya kallonta ake cike da mamaki da alʼajabi,ashe da Daddy ya korata ciki labʼe ta musu,afusace Gidado ya mikʼa jikinsa na mugun shaking with running tears yasa hannu ya ciro wata farar takadda ya isa ga daddy ya mikʼe mishi yace''Daddy kuyi hakʼuri ga takaddar Hafsan ammh kamar yadda na fada afarko ayanzu hakan ma ina kan bakana ne donni nagartaccen mutum ne wanda baya tabʼa canza maganarsa,i always stand by my words,idan Hafsa ta hankalta kuma taga zata iya cigaba da zama dani da lalurar da mahaifiyarta ta zayyano toh ina maraba da ita...ʼʼ da rawar jiki shima daddy yasa hannu ya karba,kafin yayi magana tuni Gidado yasa kai zai bar falon ana kiranshi ko waigowa beyi ba,dasauri Aliyu da sagir suka bi bayanshi,Baba Haruna da Baba munniru suma suka mikʼe afusace suka sallami daddy suka fito,dasauri daddy da mukhtar suka bi bayansu ammh ina ko sauraransu basuyi ba,

Afusace daddy ya koma ciki yana nuna mami da yʼar yatsa''Amina saʼarki daya ni ba irin mazajen nan bane masu daga hannu su daki matayensu ba,daʼace ni irinsu ne da ayau kin yabawa aya zakinta,ammh kije ni *BILYAMINU AHMAD NA SAKEKI SAKI DAYA* sakamakon cin mutuncin da kikawa surikaina kuma surukanki,idan kinje gidanku kya musu bayanin hakan....ʼʼ yasa kai ya shige,

Mukhtar dasu Hafsa da suka fito suka shiga nanata kalmar innalillahi suna kuka gami da fadin'' haba Daddy haba Daddy meyasa kaima ka biyewa zugin shaidanʼʼ mami kuwa zubʼewa akasa tayi tana birgima har daddy ya dawo falon ya cillar mata fara takadda yana fadi cike da dacin rai''Amina na gaji da zama dake,ayau hakʼurina ya kʼare ga takaddar sakin nan arubʼuce sannan kuma gana yʼarki wanda mijinta ya bayar abata....ʼʼ ya fada yana sake cilla mata wata farar takaddar,su Hafsa sai kuka suke rusawa har Mukhtar,

Daddy ya shige ciki ya kulle kansa yana kuka,sam Allah be hadashi da mace ta gari ba,haka ma yaʼyansa ukun duk babu na kirkin gara gara Mukhtar yana da hankali sosai kuma baya biye biyen mata,shidai barshi da shaye shaye,

Can mukhtar ya nufi Hafsa ya shigeta da bugu yana fadin''shegiya yʼar iska ai duk kece kika jawo aka saki mahaifiyarmu kuma wallahi tun wuri ki dau damarar bautuwa acikin gidan nan,billahi azimu Hafsa babu tausayi ko rangwame atsakanina dake...ʼʼ kuka yaci kʼarfinsa ya cigaba da bugunta harsai da tayi laushi........

   *********

Bayan fitar Aliyu ya samu Gidado yana dukan mota iya karfinsa hadda shuri yana kuka gami da fadin''Yumma why..?ni dama na dade ina zargin dasa hannunki acikin rashin haihuwar yaʼyanki sabida tsanar da kike nuna mana musamman ni tayi yawa ammh shiru kawai nayi don aganina bazaki tabʼa iya aikata abunda nake zarginki akai ba,Yumma meyasa kika hana mana haihuwa...?wani laifin ne mukayi miki da muka cancanki girman hukunci makamancin wannan...?you need to ans my question Asap....

Ya fada yana kokarin bude driverʼs side,Aliyu wanda ya gama jin zancensa shine yayi saurin dakatar dashi yace azuciye''kai Gidado meye haka..?shin kayi hauka ne..?meyasa kake kokarin barin maganganun matar nan suyi tasiri ne acikin zuciyarka..?

Azuciye shima yace''Aliyu ka rabu dani ai gaskia ta fada,itace mutum na uku data fadamun wannan maganar,sauran da suka gayamun ban tabʼa daukar zancen serious ba ammh ayau na dauki na mamin Hafsa don ina ji ajikina mahaifiyata tana da hannu agame da rashin haihuwata da sauran yanʼuwana....ʼʼ

Girgiza kai Aliyu yayi shima din zuciyarsa ta shiga zarginta ammh sai ya daure yace ahankali''plsss Gidado ka binne maganar nan kar kowa ma yaji don ba gaskia bane ni ban yadda ba....ʼʼ kafin yace wani abu sai gasu Baba haruna sun fito rai bace tare da sagir wanda ya koma dakko agogonsa daya manta dashi,babu wanda yace da wani kala har aka isa gida,Jamila sai kiransa take tayi awaya ammh ya kasa dagawa,can ta kira Sagir shine yake fada mata cewar ta kwantar da hankalinta mijinta nanan tafe nan bada jimawa ba,

Sanda aka zayyanewa Tsoho labarin abunda mamin Hafsa ta fada sosai ya fusata ainun don kusan zan iya cewa baʼa tabʼa soya ransa kamar yau ba,sai jeka ka dawo kurum yake tayi ana kallonsa kowa ya zubawa sarautar Allah ido da kuma jiran irin hukuncin dazai yanke,Yumma kuwa sai kuka take ta sharbawa tamkʼar ranta zai fita ji da tayi na ashe mutane zarginta suke akan dasa hannunta agame da rashin haihuwar yaʼyanta,Gidado ma kin bari yayi ya hada idanu da ita,zukatan wasunsu suma din suna zarginta ne,Tsoho ya daga murya ya soma magana cike da zafi''Jibi idan Allah ya kaimu ina son gabaki daya zuriʼar tsoho manya da kanana,na nesa dana kusa kowa ya hallara agidan nan,abuga asanar da kowa cewa akwai gagarumar meeting din gaggawa,zan nunawa matar nan cewa baʼa wulakanta zuriʼar Tsoho sannan kuma azauna lafiya,saina tabbatar dana sa ta jishi ajinin jikinta daga ita har ‘yar tata...................ʼʼ

Wannan paid book ne, amma zan ɗan bada garabasar free pages. Maza ki hanzarta biyan 500naira kacal domin ki mori karatunki ta wannan asusun bankin ***,Palmpay, Hafsat Mustapha. Sannan a turo da shaidar biya ta *** ko kuma a garzaya kan arewapan.

To be continued…

#’Yar Mutan Naija#

***.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol