FreeArewaPen original
KISHIN MATA
- 1views
- 39chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · 1
KISHIN MATA. Hafnancy…Kishin ilimi, Kishin Jahilci, camfe-camfe, da kuma cin amana. No. 1 *Central Area Garki, FCT ABUJA….*Tangamemen gida ne wanda ya amsa sunansa da gida, ginin zamani wanda aka ginashi very simple and attractive. Kana sada kanka cikin wannan gidan,from ur first view, zaka tabbatarwa kanka da cewa wannan babban gida ne,sannan kuma a cike yake fam da mata,yan'uwa ne da kuma abokan arziki duk anzo taya *'DCP SULEIMAN ALASSANA GIDADO'* murnar ƙarin auren da yakeyi a yau.Ko ina kabi zaka ga duk mata ne dake yau ne ake yinin bikin,ansha anko kai kace ko bikin farko ne,da yawan matan sunyi gungun,anyi group group ana tsegumin zancen auren,kowacce da gutsiri tsomar da takeyi akan Jameelah wacce ta kasance uwargida sarauniyar mata agdn DPC Suleiman Gidado,Ramlah k'anwa ga DCP Suleiman wacce tafi kowa tsanar Jameelah tace da cousins dinta wa'enda suke kewaye da ita''Aini wlhy karku so kuga yadda nake cikin farin ciki da wannan auran da Hamma Gidad'o ya kara don atleast zai saka annamimiyar matar nan tasa nutsuwa da kuma yin ladab...''Da sauri wata meh suna Baddo tace''Ramlah wai nifa ban san dalilin dayasa kika tsani anty Jameelah ba bayan matar tana da kirki sosai,ki duba fa wlhy idan kaje gidanta na rantse da Allah sai ta rasa inda zata sakaka dan murnar taga yan'uwan miji,kyautatawar da zata maka kuwa abun har baa magana,idan zaka tashi tafiya haka zata sallameka da sha tara ta arziki,sannan kuma ku rabu amutunce cikin raha da kuma fara'a,nidai gsky matar tamun don haka bana tsammanin Hafsah zatazo ta fita samun matsayi awajen dangin miji idan akayi duba da yadda Jameelar ta riga ta siye zuciyoyin dangin mijinta.....''Ramlah data kai lomar abinci baki tayi saurin hadiyewa tare da kwasar Boddo da uban harara tace''Tadai siye zuciyoyinku amma banda nawa,sannan kuma ki bari ita Hafsan ta shigo mana kiga irin tata kalar kissar da kisisinar,ni na tabbata ma dole ta saukar da zamanin Jameelah aji kawai an bar yayinta,Allah i trust Hafsah bazata ta6a bani kunya ba.....'Wata Hanifa tace''Don tana yayar babbar kawarki ko?'' ta furta tana harararta,ta6e baki Ramlah tayi kan tace''Abar batun wai tana yayar kawata yasa na fadi hakan,maganar gsky Hafsah karshe ce,she's juz a wife material 100yards,ga iya girki da kwalliya,iya karairaya murya,infact kar kuso kuga yadda take bamu labarin irin yadda zata tarairayi mijinta da danginsa idan tayi aure tou dalilin daya sanya na hadata da yayah kenan don shi yafi dacewa ya mallaketa,sannan kuma nasan zata share masa hawayen daya dad'e yana zubarwa ta rashin ya'ya wanda waccen juyar ta kasa share masa.....''Dariya duk suka sanya su wajen biyar,Boddo ta cikon shiddan ce kawai bata yi ba illah takaicin Ramlar da take ji,tace''Ramlah wlhy kibi asannu don kema gidan wani zaki kuma idan dangin miji suka sanya...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.