Free chapter · Read without an account

Page-51

by 🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚 🖋️ · “SANADIN ƘADDARATA”

*FASAHA WRITER'S ASSOCIATION*
     (*F.W.A)*©✍️
     ⭐⭐⭐

Ƙungiya masu aiki cikin salon hikima da fasaha gurin juya tunanin al-umma, kaifin alƙalumansu ya zarta takobi ©✍
___________________________________________________



بسم الله الرحمن الرحيم.
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد. 




❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁ 



Free book📓



By: _*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_




Page5️⃣1️⃣





Itama ta dakata da zaman da ta yi niyya ta tsaya tana kallona, fiskarta a haɗe ta furta "kee! Ke ce!" Take zuciyata ta ɗau gudu sosai na kuma yin ƙasa da kaina ina zare ido.

Da mamaki Haidar ya ce, "Ummee kin santa ne?!" Sai da ta zauna, khairat kuma ta yi gurin Haidar, shi ma Mu'azzam ya zauna sannan ta ce, "eh na santa, ita che yarinyar da na ce maka ta taimakeni wancan ranar, har na sanar da kai sunanta Nuriyyah".

Murmushi Haidar ya yi cike da murna ya maida kallonsa kaina, ni kuwa har lokacin kaina a ƙasa ya ke, sai a sannan na tabbatar da inda na ga matar, "dama ke ce ki ka taimaki mahaifiyata? Ina ta son samun yadda zan yi miki godiya, sai ga shi Allah ya kawo min ke cikin sauƙi, ashe sunanki Nuriyyah. Masha Allah, Nuriyyah godiyar da na ke son yi miki ba zai misaltu ba, ban ma san ta ina zan fara ba, kin ceci wancche na ke matuƙar ƙauna a duniyar nan, ba zan...".

Haidar ne ya ke wannan maganar cike da jin daɗi, na katse shi da cewa, "wannan ba komai ba ne, ba ka da buƙatar yi min godiya, abun da Allah ya ba ni ikon yi ne na yi" girgiza kai ya yi ya juya ya kalli Ummee su ka haɗa ido suna murmushi, Mu'azzam ya ce, "kin ji yadda Ummee ta ke yawan yi mana maganarki tun ranar kuwa? Har tana cewa ta ji haushi da ba ta tambayi inda ki ke ba don ta kai miki ziyara, sai ga ki yau a gabanta, ni ban san irin farin ciki da ta ke ji ba yanzu haka kina ganintan nan".

Kama kunnensa Ummee ta yi dama a kusa da ita ya zauna, nan ya saka ihun wasa yana faɗin "Ummee kunnen za ki cire min? IS SO HOT, Ummee" ni dai sai murmushi na ke yi, hakan ya sani nishaɗi, shima abun da Haidar ya ke yi kenan, ita ko Khairat sai dariya ta ke yi. 

"waya tambayeka uban baki?" Cewar Ummee sannan ta sakar masa kunnen tana hararsa da wasa. Khairat da ta samu dariyar ya lafa ta kalli Mu'azzam ta ce, "Unclui Mu'ajjam, idan Ummee ta cile maka kunne, aina ja ka ji idan anyi maka agana" sai da na kusa tuntsirewa da dariya saboda maganar yariyar da kuma yadda ta sarrafa shi.

Su kam sauran dariyar su ka yi Mu'azzam ya ce, "sai na rinƙa ji da na ki kunnen, ina ke ƙaramar Bobbina ce?" "To ai ni kunne na nan aya nan aya ne" khairat ta faɗi tana taɓo gefen kunnuwanta ta ɗora da cewa, "ka ga ni? Ba hutu ba ne da ce in baka biyu ka ca" kuma darawa su Ummee su ka yi Mu'azzam ya sassauta dariyarsa ya ce, "to Ummee kin ga gidan baki anan jikarki, amma ba ni ba".

Momy ta girgiza kai ta juyo inda na ke da nima sai dariyar na ke ina kallon Khairat da ke hannun Haidar, maganar Ummeen ce ta sa na juyo ina kallonta. "Yauwa ni kam Haidar a ina ka haɗu da Nuriyyahn ne?" Ya sanar da ita yadda aka yi ni kuwa na kuma yin ƙasa da kaina.

"Nuriyyah gaskiya ne na yi farin ciki sosai da ganinki a nan, dama ina roƙon Allah ya kawo min damar da zan taimaka miki kamar yadda ki ka min, don da ba dan ke ba haƙiƙa da yanzu ba ni, saboda haka ki sanar da ni abun da ki ke so, ni kuma zan yi miki shi yanzun nan da yardar Allah idan har ina da damarsa, idan yaso daga baya Haidar ya maida ki gida".

"A ah Madam, kamar yadda na ce Allah ne ya bani ikon taimaka miki, da bai bani iko ba nima ba zan iya ba, kar ki damu da sai kin mun wani..." "no 'yata, kada ki ji komai ni ce na tambayeki, don haka ki faɗa min duk abun da ki ke so, Allah ne ya bani wannan damar nima". Shiru na yi na mintuna sannan wani tunani yazo min, dama ba inda na san zan yi yanzu, na ce, "toh Madam... don Allah ina son ku ɗaukeni aiki... san... sannan na zauna a gidanku, ko da shara da goge-goge ne, koma dai wani abun". Na faɗi da rawar murya.

"Da mamaki dukkansu su ke kallona, "aiki kuma Nuriyyah?" Cewar Haidar, "eh ku min wannan alfarmar don Allah", Ummee ta sauke numfashi da alama yarinyar tana cikin damuwa sosai, ka na ta ce, "ba za ki zamar mana mai aiki a gidan nan ba!" Hawayen da ya cika a idona ya zuba bisa jin kalamanta, "ya zan yi yanzu kenan?" Na tambayi kaina, saboda a yadda ta furta na game ban samu wannan alfarmar ba.

Ummee ta kuma cewa, "amma kuma..." na share hawayena sannan na dakatar da ita da cewa, "a ah Madam, kada ki damu kin ji? Ba wani abu ba ne, hakan ma ai na gode muku sosai, kuma na ji daɗi" na faɗi ina murrmushin ƙarfin hali na miƙe, sannan na juya zan fita, dukkansu su ka miƙe, kallon Ummee Haidar ya yi cike da damuwa, zai yi mata magana kenan ta ɗaga masa hannu.

Khairat da gudu ta ƙarasa gurina ta riƙe min hannu, hakan yasani tsayawa ina kallonta, "ba na con ki tapi" ta faɗi itama tana kallona, jininta kawai ya haɗu da nawa, kafin na amsa mata Ummee ta ce, "me yasa ki ka tsayar da ni daga maganar da na ke son ce miki? To ki jini da kyau Nuriyyah, ba za ki zamar mana mai aiki a gida ba, amma kuma za ki zama tamkar 'ya a wurina" da wani irin sauri na juyo ina kallonta".

Su Haidar kuma su ka saki murmushi, "eh haka na ke son cewa, ke kuma ki ka dakatar da ni! Sai kace kin san me zan ce" ta yi maganar da masifa tana kallona, dariya mara hayaniya na yi, hawayen daɗi ya fara wanke min fiska, "a ah fa, ya da kuka kuma? Sai ka ce khairat?" Ummee ta kuma faɗi tana zuwa kusa da ni.

Cike da murna na shiga gode mata sosai, ta ce ba ta son godiya, idan da akwai abun da ya wuce haka na cancanta a gurinta, "yanju jamu jauna tale ko? Kin iya waca ja ki yi mun?" faɗin khairat da murna ita kanta abun da ya faru ya yi mata daɗi. Na durƙusa ƙasa ina dubanta na ce, "eh na iya, harda wasan langa ma, kin san wasan?" Ta giɗa min kai alamar a ah, sai na ce, "to harda shi zan yi miki".

Haidar ɗakinsa ya wuce, shi kuma Mu'azzam ya ce, "to Nuriyyah ni kuma dai me za ki koya min? Tun da dai za ki koyawa Bobbina langa" hannu Ummee ta kai kamar za ta mareshi ya ce, "Ummee ni fa gani na ke kamar ba ki sona, ni ne fa Autanki ki kina mantawa ne?", "eh mana yanzu ma shirin kaika bola na ke ja'iri". Ni dai dariya na ke yi kaɗan kaɗan ina kallonsu,, khairat kuwa har da cewa, "Unclui Mu'ajjam ja ka yi wali a bola".

"Kai amma Bobbina wallahi kina ɓata min suna, ka ji wai Unclui Mu'ajjam" cewar Mu'azzam yana jan hancin Khairat, Ummee ta ce, "a hakan ma ka gode Allah, don Khairat ɗina ta yi ƙoƙari", nan Ummee ta kaini wani ɗaki, mai kyau sosai da ya ke cikin sashin, ta nuna min cewa wannan ɗakin shine ɗakina yanzu.

SADIYA. 

Tana kwance a ɗakin da aka kaita cikin sashin Baaba, suna zaune dukkansu a gefenta, Baaba ta buɗi baki tana kallon Sadiya ta ce, "'yata Sadiya ina mai roƙonki, don girman Allah ki yafe min duk abun da na yi miki, ruɗin zuciya ne ya ja ni, na gane zaɓin Allah shine daidai, Allah ya nuna min izinarsa Sadiya, ki yafe min don Allah. Na san abun da mu ka yi miki ba abun da za ki iya yafewa ba ne da wuri, domin mun ci miki mutunci, mun ƙas-ƙantar da ke da yawa, amma daurewa za ki yi 'yata, na gane kuskurena wallahi".

A hankali Sadiya ta juyo tana kallonta ƙwallahn fari ciki ya cika mata ido ta ce, "Baaba na yafe miki duk abun da ki ka aikata min, kema da kanki kin ce ni 'yarki ce, saboda haka ba ki da buƙatar yin duk wannan. Kuma na godewa Allah da ya nuna min wannan rana, ranar da ko da yaushe na ke addu'a da tsumayin zuwansa".

"Allah sarki 'yar albarka, Allah ya baki kyakykyawan zuciya Sadiya, na gode miki Allah ya ƙara shiga lamuranki", cewar Baaba tana dafa Sadiya da tsananin murna tana hawaye kar yadda Sadiyar ta ke yi.

"Anty Sadiya muma ki yafe mana don Allah, wallahi haƙƙinki ya bi mu, ki yafe mana ko za mu samu mijin aure na gari" faɗin Fatima, sai da Sadiya ta ji abun Ban-baraƙwai jin ta kirata da Anty, nan dukkansu su ka shiga ba ta haƙuri sai kiranta Anty su ke, babu ɓata lokaci ta ce, "na yafe mu ku, Allah ya yafe mana baki ɗaya".

Haka akazo kan Lantana itama Sadiya ta yafe mata, sun yi farin ciki sosai har da yi mata addu'a, suka rungumeta sai da Baaba ta ce su rabu da ita ba su ga jikinta baya ƙarfi ba ne? Sannan suka ƙyaleta cike da jin daɗi. Aisha da tuntuni wannan lamarin ke ci mata tuwo a ƙwarya, amma kuma ta ji shiru ba wanda ya ɗauko maganar, ta dubi Sadiya ta ce, "ina son in tambayeki Anty Sadiya, abun ya ɗaure min kai, akan lamarin da ki ka tsinci kanki, amma ya aka yi ki ka samu gass haka?".

Dukkansu su ka maida hankali kan maganar da Aisha ta yi, tabbas yana da mahimmanci, kallo ya kuma komawa kan Sadiya da sai yanzu abun da ya faru ya dawar mata, "yadda aka yi?! Na shiga kitchen don ɗebawa Nusaiba gandar da ta sa indafa mata, to ina shiga na ji ƙofar ta kullu, na yi mamaki da hakan ya faru, sai dai ban lura ba a gani na ko nive na yi kuskure ban lura ba, sai dai da na zo fita na ji ƙofar a datse, daga baya kuma na fara jin warin, kafin na fara wani neman taimako kiɗar da Nusaiba ta kunna ya fara tashi, sai dai wannan karon ta ƙure volume fiye da yadda ta saba".

Kowa ya yi jugum Baaba ta ce, "anya ba Nusaiba ba ce ta yi wannan aikin? Amma idan ko ya tabbata wallahi wannan karon ba za ta sha a banza ba!" Sadiya cikin nazari ta ce, "ni ma abun da ya zo raina kenan, amma kuma zato ba kyau, zai..." "ba zato ba ne, ita ɗin ce! Nusaiba ce duk ta aikata komai" muryar Faruq ya ratsa ɗakin. 

Kallonsu su ka mayar kansa da mamaki. Ga shi hannayensa duka akan kansa sai sauke numfashin raɗaɗi ya ke, da sauri su ka miƙe cikin tashin hankali su ke tambayar me ya ke faruwa? Samu ya yi ya zauna akan kujera yana cewa, "Nusaiba ce SANADIN komai Baaba! Ita ce ta haifar da komai kuma ba zan barta ba! Sai na tabbatar da ta amshi hukuncin..." sai kuma ya kasa ƙarasarwa saboda ciwon da ya kuma taso masa.

Dukkansu sun shiga halin kiɗima sosai, Baaba ta ce akai shi asibiti, amma kafin nan Malam ya shigo, ko da lura da yadda Faruq ɗin ya ke yi da kuma maganar da ya samu faɗi akan Nusaiba, sai su ka fahimci maganin ba na asibiti ba ne, karyewar sihirin ne yasa shi cikin wannan halin. Malam bai tsaya jinkirtawa ba ya fara yiwa Faruq addu'o'i don samun taimakon ubangiji.

FAMILY HOUSE.

Abba tun bayan da ya shiga ɗaki gaba ɗaya ya kasa sukuni, duniyar ta yi masa tsanani sosai, ya rasa abun yi sai safa wal marwa ya ke ta zubawa a cikin ɗakin. A ƙarshe dai ya samu damar zama saman gado, ya dunƙule hannunsa akan katifa saboda tsananin ɓacin rai. Me yasa hakan zai faru da shi? Nuriyyah fa wacche ya ke tsananin so, itache za ta aikata masa haka? Me yasa? Me yasa?" Magan-ganun da suke yawo a cikin kansa, ga kalaman Asma'u a gefe, kai! Shi ina ma zai sa ransa?.

Da ƙyar ya yi dauriyar fitowa don komawa asibiti, ganin halin da Momynsa ta ke ciki. "Hmm wannan shine hanya mafi dacewa, kin ga da ta bar gidan yanzu ba komai zai tafi daidai ba? Shikenan kun rabu da Nuriyyah alaƙaƙai, "everything will be okay now" cewar Ayusha a falon, wanda maganar ya faɗa cikin kunnen Abba, ya zare ido cikin wani firgicin daban, kamar dai sai yanzu ne ya ji zancenkoran Nuriyyah.

Da sauri ya fita ba tare da ya ce wa kowa da ke falon ƙala ba, duk su ka bishi da kallo cikin tsananin mamaki, "ku tsayar da yaron nan kada ya je garin tuƙin mota wani abu ya sameshi" faɗin Hajiya Kaka da damuwa saboda yanayin yadda ta ga Abba ya fita hankalinta bai kwanta ba.

Su Dady kuwa ba sa falon dama tuni su ka koma asibitin, Ayusha ce ta ce bari ita za ta je ta tsaida shi, ko da ta fita lokacin Abba na ƙoƙarin fita daga gidan, bai ma yi inda motarsa ya ke ba, "Abba ya ka ke gaggawa haka? Ina zaka je? Are you going back to the hospital? Ba ka ɗauki motarka ba to" Faɗin Ayusha da ƙarfi tana nufan inda ya ke, bai tanka mata ba, sai ma ficewa da ya yi ya barta tsaye da mamaki".

Bayan ya fita ya rinƙa dubawa yana kiran sunanta, amma shiru babu Nuriyyah babu labarinta, tsayawa ya yi a wani wuri yana sauke numfashi, 'me yasa za ka damu kanka akan yarinyar da ta ke son kashe maka mahaifiya? Yarinyar da ka san gaskiyar halinta yanzu? Me ya rage maka kuma da har ka ke wahalar da kanka akanta? Ya faɗi a zuciyarsa, wanda hakan yasa shi juyawa rai ɓace ya yi hanyar gida don ya ɗauki motarsa ya yi asibiti.....

Kowa na gidan ya dawo shiru cikin damuwa, awa ashirin ya wuce amma har yanzu Momy shiru babu alamar farkawa a tattare da ita, masu kuka su ka na yi, masu addu'a da rarrashi ma haka, lokaci ya zo ya wuce shiru har aka ƙara kwana ɗaya Momy ba alama, sai dai har yanzu ba ta mutu ba tana raye. Ranar Sayyid ya ji duk abun da ya faru, cewa an kori Nuriyyah akan laifin da shi sam bai amince da ta aikata ba, to taya ma za ta sa guban da ta san zai fallasata da wuri idan da gaske ne? Amma fahimtar da su ba shi da wani amfani yanzu, tun da aikin gama ya riga ya gama.

Yana tsaye bayan ya haɗa kayansa gaba ɗaya wanda ya zo da su, Abba na tsaye yana binsa da kallo na mamaki ya ce, "kana nufin don Nuriyyah ba ta gidan nan shine za ka tafi kaima?" "Yes Abba! To me zan tsaya na yi anan ɗin bayan duk abun da ya faru? Kun kori yarinya ba bincike, ba ku da tabbacin ta aikata ko ba ta aikata ba, amma za ku yanke mata irin wannan hukumci haka?".

Faɗin Sayyid rai ɓace, shima Abba cikin ɓacin ran ya ce, "kamar ya bamu da tabbaci? Bayan komai ya fito a bayyane, ko dai kana sonta ne Sayyid?" Murmushin takaici Sayyid ya yi ya ce, "ni ba na son jin wani ƙarin bayani ko kuma wani zance irin haka Abba, kawai dai abun na ke son ce maka, Allah ubangiji ya ɗaga kafaɗun Momy, ya ba ta lafiya. Ni zan tafi, kuma a gaskiya ba zan sake dawowa gidan nan da niyyar wani aiki ba, amma ba zan yanke alaƙar da ke tsakanina da kai ba, kai abokina ne tun da daɗewa, nagode da duk wata kulawa da kuka bani, na barka lafiya".

Cewar Sayyid sannan ya ɗauki akwatinsa ya fice da shi. Sakin jiki Abba ya yi ya zauna akan gado, ya rintse idonsa ransa zafi ya ke masa, ga Momy har yanzu ba ta farka ba. Damuwa duk ya bi ya yi masa yawa, tashin hankali kullum a cikinsa ya ke, har rama ya kama shi. Sayyid kuma idan tafiyar zai yi ya tafi mana, me sai ya tsaya sanar da shi wasu kalamai haka? wanda ko kaɗan bai ji daɗinsu ba.

NURIYYAH. SATI ƊAYA.

Wannan sabon ahalin da na samu bani da wata matsala da su a gidan, ko wanne a cikinsu ɗaukata ya ke yi kamar 'yar gidan, amma har yanzu ba wanda na sanarwa wani abu da ya shafi rayuwata, ba wanda ya takura min akan sai na bada labarina, domin tun ranar da Ummee ta tambayeni, ta ga na shiga cikin wani yanayi ta haƙura da sanin komai.

Na shaƙu da Khairat sosai, domin so tari a wurina ta ke zama, idan ba wai makaranta ta tafi ba, da ga zarar ta dawo kuma tana tare da ni, ta yi ta min surutu tana cewa mu yi wasa, maganarta kaɗai ma burgeni ya ke yi, hakan da ta ke yi mun ya ke rage min zafin wasu abubuwa sosai, duk da har yanzu ciwon dai yana nan a cikin ƙirjina, ko da yaushe sai na zubar da hawaye, da tunanin halin da Momyna ta ke ciki yanzu, amma ba ni da damar sani. Sai dai ina yin addu'a Allah ubangiji yasa ta tashi, Allah ya ba ta lafiya, yasa kada wani abun ya sameta.

Duk da cewa ba 'yar aiki ba ce ni, amma ina ƙoƙarin taimakawa masu aikin yin abubuwa da dama, so tari ma yanzu ni na ke yi musu girki, kuma ina jin daɗin yadda su ke yaba abincin na wa, Haidar na cewa zai zo na koya masa girki saboda ya rinƙa dafawa khairat, har Ummee na cewa, ya dai faɗi gaskiya ko surkanta ce ya ke son taya girki?. Ina ƙoƙarin kulawa da Ummee sosai domin kuwa duk lokacin shan maganinta baya wuce ta, saboda ni da kaina na ke zuwa ba ta, gudun kada wani abun ya sake faruwa da ita, saboda ta sanar da ni yadda ciwon na ta ya ke....

Yau tun safe Ummee ta sanar da ni Alhaji wato mahaifin su Haidar zai dawo daga tafiyar da ya yi kusan wata biyu baya gida, suna ta shirye shirye, sai bayan magriba ya iso, babban mutum ne sosai, kasancewar Momy ta riga da ta sanar da shi wace ni, hakan yasa da fara'a ya amsa gaisuwa ta, a baya har na yi tsoron ko ba zai amince da ni ba, amma sai na ga saɓanin haka.

Bayan kwana ɗaya da dawowar Alhaji, Ummee na zaune a falonsa, bayan sun gama cin abincin da ni ce na kawo masu. "Alhaji akwai wani babbar maganar da na ke son sanar da kai, kuma na san za ka yi farin ciki da hakan".

Da fara'a Alhaji ya ɗago yana kallonta ya ce, "ina sauraronki Ummeen yara", "yauwa to, ka ga dai yanzu kusan shekaru uku kenan wannan yaron Haidar ya ke zaune ba mata, tun da Allah ya ɗauki ran matarsa a gurin haihuwa bai ƙara aureba, kuma kana sane duk faɗi tashin da mu ka yi akan ya nemo mata amma ya ƙi".

Saida Alhaji ya jingina bayansa jikin lallausan kujerar sanna ya ce, "ƙwarai Ummeen yara anyi haka, amma me yasa ki ke wannan maganar? Bayan na san har yanzu ba wai fito da matar Haidar ya yi ba?". "Eh haka ne bai fito da mata ba, amma ni na fitar masa da ita!".

Da mamaki Alhaji ya ke kallonta cikin rashin fahimta ya ce, "kin fito masa da ita? Wace ce ita?" "Nuriyyah!" Ummee ta faɗa tana kallonsa, Alhaji ya ɗaga bayansa daga jinginar da ya yi, shima yana kallonta sosai.


Last page
___________________________________________________

Toh fah! Me za ku ce akan wannan lamarin?




 _*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_sqي

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol