Free chapter · Read without an account

PAGE 11-15

by SultyWrites · MATAR SADAM

sau kusan uku tana haihuwa suna mutuwa biyu ba suzo da rai ba dayan kuma kwanan sa biyu a duniya shima yace ga garinku nan ,sai ana hudun ne tayi sa'a ta samu yarinya wacce taci sunan marigayiya wato haseenah dukda bata kasance yar fari ba Amma da yake itace kadai ta rayu a matsayin ta farko yasa fatima yi mata kawai ci irin na Fulani kwata ²bata janta a jiki ganin haka yasa hajjo dauketa ta koma wajen ta da Zama bata son abinda zai tabata komai take so shi takeyi hakan yasa ta taso da rashin ji ga tabara irin ta goyon Kaka.

Allah ya Mata baiwar karatun alqur'ani dan tunda kananun shekarun ta tayi sauka sosai ta samu kyaututtuka daga sarakuna da dama kasancewar ta yarinya ta farko a kauyen da tayi sauka a kananun shekarun ta, mahaifin ta bai barta ta zauna haka ba yace ta ci gaba da zuwa islamiyyar tana yin hadda da kuma sake sanin wasu littattafan.

WANNAN KENAN

A yanzu abida wacce suke Kira da  mahmah tana zaune a Kano ne a unguwar nasarawa yaranta hudu mace daya Maza uku Muhammad Asif  Nabil sai autar su wacce taci sunan Fatima , duk sunyi aure suna zaune a Kano Fatima ce kawai ke aure a Abuja saboda acan mijinta ke aiki .

Sai Hamza (daddy)wanda ya kasance shine minister man fetur na Nigeria a yanzu yana zaune a Abuja, ba yadda baiyi da hajjo su dawo Abuja ba Amma tace sam bata san zance ba inda aka binne mijinta itama nan za'a sata dan haka ba Inda zata je, ba yanda ya iya haka ya hakura ya kyaleta tare dasawa aka Kara yi Mata yan gyare² a gidan dan tace bata motsawa daga wanna gidan  .

Matan sa biyu ta farko yar governor Adamawa ce Mai suna nabila , sunsha fadi tashi kafin ya samu iyayanta su amince su bashi auranta kasancewar sa a lokacin mai rufin asiri ita kuma yar gomna . 

yaranta uku na farko sadam Wanda suke Kira da emir sai adnan da kuma auta najwa.

Sai matar sa ta biyu umaimah wadda ta kasance kanwa ce ga abokin sa , ya'yan ta biyu mata nafisa da afnan.

zaman gidan ya kasance zama ne irin na doya da manja domin umaimah kwata² bata son nabila mahaifiyar su sadam, saboda tun farkon shigowar ta gidan suka fara samun sabani da daddy akan nabila , dan fitowa yayi ya nuna Mata lalle in har tana san zama dashi toh dole ne ta mutunta nabila dan bawai baya santa bane yasa ya auro ta hakan ya nuna Mata lalle akwai soyayya mai karfi tsakanin su Wanda ya sata Jin kishi da kuma tsanar nabilan da yaranta fiye da tunani dan tasan ita ba auran soyayya sukayi da shi ba kuma tana da tabbacin ko rabin son da daddy kema nabila ita baya Mata.

Dadin dadawa kuma gashi kuma nabilan ce mai yaya Maza kuma har biyu Wanda ko yau daddy ya fadi ya mutu to gadon ta sai ya linka nata, hakan yasa ta sake daukan karar tsana ta dorawa sadam ganin shine babba kuma duk dukiyar mahaifin nasa tana karkashin kulawar sa ne saboda shi daddy aikin sa ma na office ya isheshi bashi da lokacin dazai iya raba hankalin sa Kashi² kuma yanzu a rayuwar nan amana tayi karanci dole sai kanada wani naka tsayayye akan dukiyar ka, Adnan kuwa karatu yake nan Nile university Abuja.
   
kwata ² nabila bata kula duk abinda umaymah zatayi Wanda hakan ba karamin Kara bata Mata rai yake ba domin ita so take nabila ta dinga biye Mata suna tashin hankali dan ta samu abinda take nema ta kuma ci nasara a kanta.

nabila bata taba nuna wa yaranta cewa akwai banbanci tsakanin ta da umayma, dukda ita a nata bangaren akasin hakan ne .

Saisa basu cika shiri da sadam ba domin shi ba zaiga yaro yayi ba daidai ba ya zuba masa Ido yanzun zaiji duka saboda saurin hannu irin nasa hakan kesa umaimah cewa ai nabila ce ke sashi yake cin zalin ya'yanta saboda sun tsane su, shi kuwa ko a jikin sa dan ko mai za tayi gobe ma in suka Kara ba shi zai hanashi sake ladabtar dasu ba .

Shekarar seenah 11 mahaifinta ya rasu hakan yasa mahaifiyarta tattarawa ta koma wajen hajjo, tunda dama tun daga Kan seenah Allah bai sake bata haihuwa ba kuma seenan a hannun hajjo take. 

Daddy ya nemi daukan seenah tun a wancan lokacin da mahaifinta ya rasu amma hajjo ta nuna bata yarda ba hakan yasa ya hakura .

BACK TO STORY

Mai gari na ganin su ya mike yanawa daddy sannu da zuwa 
" alhaji Kaine da kanka ashe ka shigo gari murmushi daddy yayi da fadin " wallahi kuwa yau mun kawo ziyara Malam ahmadu ya fama da jama'a ina fatan mun sameku lpy ?
" Alhamdulillah ya iyalin in ce duu kalau ko.

Kujera Mai gari yasa aka kawo , kallon hajjo daddy yayi da fadin hajjo ki zauna a kujerar mu nan ma ya isa ya karashe Yana zama kan carpet din dake shimfide awajen seenah na gefen sa.

    Bayan an gama gaisawa ne Mai gari ya nisa sannan yace alhaji wato abinda yasa na aika a kira su hajjo shine haseenah ce tafasawa wani yaro Kai da bokitin karfe a makaranta dazu shine mahaifin yaron yakawo kara nan gurina ya karashe da nuna mahaifin yaron dake zaune shi da dan nasa .

hajjo ce ta mike tana nuna mai gari "Malam ahmadu ina ganin mutuncin ka fa wato kai ma so kake ka shiga tawagar munafukan mutanen kauyen nan ko ka dubi wanna sangamemen saurayin uban su wane kakan su wance kace haseenah ta fasa masa Kai, shi dusa ne a idon sa da har zai tsaya ta fasa masa Kai yana kallonta wanna maganar ma ai hankali bazai dauka ba .

Ajiyar zuciya daddy yayi tare da cewa "hajjo dan Allah kiyi hakuri ki zauna ayi magana ta fahimta dakyar ya samu ya shawo Kanta ta zauna sannan ya juya wajen seenah dake raba Ido uwa shege a rabon gado yace "mamana wai haka akayi shin abinda aka fada gaskiya ne ke kika fasawa yaron can kai ?

Shuru tayi tana turo baki gaba , ya sake cewa " karki ji tsoro fadamin gsky kawai ,  daga masa Kai tayi tare da fadin "eh daddy amma shi ya fara shiga harkata don ni ban kulasu ba da aka gama exam suna ta wasan ruwa shine shi kuma wanna ya zubamin ruwa a jiki na ni kuma na kwada masa botikin na kuma mayeshi ta karashe tana watsawa yaron harara.

Girgiza Kai kawai daddy yayi yasa hannu a aljihu ya dauko kudi da bai san ko nawa bane ya mikawa uban yaron Yana fadin "Malam ga wanna sai a samu a kaishi chemis a ci gaba dai da hakuri kasan al'amarin Yara .

cikin sauri uban yaron yasa hannu ya karba " ai alhaji ba komai yarinta ne wataran sai labari mun gode Allah ya saka da alheri yaja hannun dan nasa yana cigaba da godia .

da harara hajjo ta bisu har suka bar fadar mai garin sannan ta juyo wajen seenah tana fadin "kema dai da karfin hali kike in banda karfin Hali irin naki ina ke ina wanna yaron dako daddagewa yayi saiya iya hadiyeki .

Sosai daddy yai ta raban kudi kamar yadda ya saba idan ya shigo gari kafin kace Mai mutane sun cika fadar kai kace wani shugaba ne a wajen, bayan ya gama ne yayiwa mai gari sallama suka wuce gida bayan ya ajje masa nasa rabon.

suna zuwa gidan seena ta wuce daki ta canja Kaya ta dauki gyalenta ta fito a zaune ta samesu da alama wata magana suke Mai mahimmanci karasawa tayi ta tsugunna gaban daddy tana fadin "amma daddy ba yau zaka koma ba ko ? 

" Yau zan koma mamana ai anayin sallar jumma'ah zan d'age da naso nayi weekend anan amma hakan bazai yiwu ba dan akwai wata tafiya da ta taso min urgently sai sa zan koma yau din , cikin rashin jin dadi tace toh daddy zanje gidan su kawata in dawo kafin Ka tafi.

" toh amma fah in kika dade tafiya zanyi kin san akwai nisa daga nan zuwa airport din ma, da sauri tace in sha allah bazan dade ba daddy , yan hamsin ²  sababbi da bansan ko na nawa bane daddy ya zaro a aljihun sa ya mika Mata, hannu biyu tasa ta karba tana godia yayi saurin katseta " kinga bana san godia addua kawai nake bukata murmushi tayi tana fadin in sha allah daddy I will include you in my prayers me kake so in roqa ma ko in roqa ma Allah ya rabaka da wa'ancan samudawan masu kama da yan dambe, daddy wai nikam basa takura ma ne naga tunda akace Ka zama minister tare kake zuwa dasu , whl daddy wa annan mutanan in suka shaqe mutum ko shurawa ba zaiyi ba.

Sosai daddy yake dariya har ta ida zancen sannan yace ke yanzu escort din nawane suka dameki Kenan ? 

dariya tayi itama da fadin Allah daddy toh ni amfanin me suke ma ne Kam? 

"saboda tsaro mana mamanah kin san yadda yanayin kasar ta mu yake akwai matsalar insecurity bare ma ni da nake matsayin minister man fetur, ku ma da ace a can kuke ai da sai da su zaku ringa yawo .

" Amma ni daddy nake ganin basu da amfani don in Allah ya nufa abu zai samu mutum ba wani dan adam da zai iya bashi kariya haka kuma in Allah ya Kare mutum ba wani abu da zai iya cutar dashi walau mutum ko aljan, addu'a kawai mutum zai sa a gaba a duk Inda yake, murmushi yayi yana fadin "Allah ya Miki Albarka mamanah Allah ya raya ki ya albarkaci ilimin ki , cikin jin dadin adduar ta amsa da ameen daddynah.

ummi tace yanzu sai ina kuma ke da bakya san zama wuri daya kamar kinci kafar kare ,turo baki tayi da fadin " ni ni fa ba dadewa zanyi ba yanzun zan dawo kafin daddy ma ya tafi gidansu saudat zani , hajjo tace kinga yi tafiyar ki a dawo lpy saura kuma ki sake tsokano wata rigimar daddy yace "ah ah hajjo in taga fah za'a zalinceta dole ta kwaci kanta .

"sai kuma Kayi ni dai na gaya maki na gaji da magana yauwa.

" tohm naji saina dawo ta fada tana nufar kofar fita a gidan.

Ko data fita bayan gari ta nufa dan dama nan ne wurin zuwan ta a ko da yaushe sosai takejin dadin iskar hadarin dake kadawa , tafiya take tana yan waqe waqenta harta karasa sosai tayi tafiya mai nisa amma ko a jikinta, can Kan wani dutse ta hau ta zauna tana kallon yadda wajen yake shiru sai kukan tsuntsaye da karar saukar ruwan dake zuba daga jikin duwatsu  .

Ba ko tsoro a tare da ita na ganin ita kadai ce a wanna jejin , views din wajen take bi da kallo tana murmushi cikin nishadi sai kuma ta tashi ta fara tsalle tana sauka daga Kan duwatsun cike da jin dadin weather wajen harta karasa sauka kasa.

Kan dan wani dutse marar tudu ta zauna idonta kan wani dan karamin gida dake wajen kamar a turai, da mamakinta taga kofar gidan a bude sosai gidan yake birgeta amma tana mamankin Wanda yake rayuwa a gidan dukda lokaci zuwa lokaci ne take ganin shi a bude dan ana jimawa kafin taga an bude shi jin jina karfin halin mai kwana a gidan take yanda zai iya bacci ba tare da tsoron abinda ke iya kawo masa hari cikin dare ba , wanna ko zaki ya ritsa mutum anan ai saidai buzun sa da sauri ta kawar da wanna tunanin ganin idan kuma itama yanzu zakin ya ritsa da itafa sai kuma tayi yar dariya still idonta na Kan gidan, duwatsu ta dauka tana cillawa a ruwa, ganin kamar ana kokarin fitowa daga gidan ya sata saurin tashi ta buya bayan wata katuwar bishiya .

   Wani matashin saurayi ne Mai matsakaicin shekaru ya fito rike da mug a hannun sa, sanye yake cikin sea blue jeans da red t shirt long sleeve ya tattare hannun rigar zuwa guiwar hannun sa, daya daga cikin kujerun robar dake wajen yaja ya zauna Yana kallon yadda hadari ke hadowa tare da kallon tsuntsayen dake shawagin su a wajen kusan 6 minutes sai kuma ya mike ya ajje mug din kan karamin table dinda ke gaban sa ya fito daga balcony din yana dan kalle² jikin sa ne ya basa kamar someone is starring at him amma bai ga kowa ba idon sa ne ya sauka Kan bakin rigar seenah dake boye a bayan bishiya dauke Kai yayi sai kuma ya sake kallon wajen kamar wani magnet ne ke janshi, fara takawa yayi Yana nufar wajen sai da yazo daf da bishiyar sai wayar sa ta dau ruri tsayawa yayi jim kamar Wanda akewa dole sai kuma ya zaro wayar a aljihun sa ya answer tare da karawa a kunne bakin sa dauke da sallama shuru yayi yana sauraren Wanda ke magana ta dayan bangaren can kuma naji yace amma daddy mai zaka yi da 400k daga wajena dan shuru ya sake yi yana sauraren mai maganar sai kuma yace shikenan tho daddy zan tura ma yanzu katse wayar akayi ta daya bangaren tsayawa yayi yana kallon wayar sai kuma ya maida Idon sa Kan bishiyar juyawa yayi ya koma cikin balcony din ya zauna kan kujerar daya tashi yana dan danne² a wayar sa .

Sosai seena ta gaji da tsayuwa hakan yasa ta tsugunnawa tana ci gaba da kallon sa .

   Sadam Kenan yaro da kudi abokin tafiyar manya,  tun Yana 20 years yayi graduation a Switzerland Inda ya karanci business administration kamar yadda mahaifinsa ya karanta, duk Inda ake neman handsome guy sadam yakai harma ya zarce komai nasa is unique, ba fari bane kuma ba za'a sashi sawun bakake kirin din nan ba Yana da colour Mai daukan hankali Wadda gyaran da take samu ya sa ta sake fresh gwanin birgewa , ga wasu shegun sexy eyes sai kyalli suke kamar Wanda aka shafa masu mai, girar nan kuwa cike take da gashi baki sidik kai Kace shaving dinta yake saboda yadda take a tsare , hanci kuwa kamar shi ya zana abin sa ga wasu cute lips dukda basu kasance pink ba amma kalarsu Is so attractive ga saje da gashin baki sunsha gyara kamar yadda gashin kansa ke kwance Kai kace balarabe ne , body structure dinsa kuwa kamar Dheeraj dhoopar shi ba dogo can ba ba kuma zai shiga sawun gajeru ba he's just every girls dream.

Duk yadda mahaifin sa ya dora shi kan ragamar komai nasa hakan bai sa ya dogara da dukiyar mahaifin nasa ba, a yanzu haka yana da company nasa na kansa guda uku yana da company a Paris dake sarrafa agoguna takalma airpod zobuna  e.t.c sai kuma company dake sarrafa duk wani kayan electronic a china kama daga Kan su computers da sauran su sai kuma companyn dake sarrafa Kuli Kuli da gyada domin fitar da Mai daga jikinsu dake nan Lagos Nigeria, he's a kinda person that like private life baya taba nuna wai shi wanine he's just living his life kamar kowa wanna Kenan.

Gaban sane ya fara faduwa tun yana cijewa har saida ya dafe kirjin nasa tare da lumshe ido yana sauraron bugun da zuciyarsa keyi kamar zata faso kirjin sa ta fito , wayar sa ce ta fara neman agaji sai da akayi kusan 3 missed calls sannan ya Mika hannu ya dauka ba tare daya bude Idon nasa ba yayi picking tare da Kara wa a kunne yayi shuru can kuma kamar Wanda aka matsa yace "ohk I'm coming , bude Idon sa yayi Yana tashi ya dauki mug din har ya juya zai shige gidan sai kuma ya sake juyowa ya kalli sama sai kuma ya maida idon sa kan bishiyar nan kusan seconds yana kallon wurin kafin ya juya ya shige.

Tana gani shigewar sa ta sauke ajiyar zuciya tare da fitowa da sauri ta hau Kan dutsen data fara zama ta zauna tana adduar Allah yasa ya sake fitowa kafin ta tafi .

yayyafin da aka fara ne ya sata daga kanta sama ruwan na sauka a fuskarta kadan² can kuma ta maida idon ta kan gidan ganin sa tayi ya fito dauke da blue jacket a hannun sa, idon sa sanye da spec baki sai da ya kulle gidan yasa key a aljihun sa sannan ya fito Ya daga kansa Yana kallon yadda garin yayi ja alamar za'ai iska Mai karfi , dan shafa kansa yayi sai kuma ya fara tafiya zuwa bayan gidan tashi seenah tayi ta fara binsa daga Kan dutsen har suka fita daga wajen duwatsun sosai wani babban dutse ta hau wanda zata iya ganin komai dake kasan, wasu black marcede Benz ta gani guda biyu pake a wajen, mutane hudu taga sun fito daga motocin sai wani Wanda kayan sa suka banbanta da na wa ancan hudun yana karasawa wajen ba tare da yayi magana ba ya mikawa wanna din mukulli tare da shigewa mota suka rufe sannan suma suka shiga tare da barin wajen suka bar dayan mutumin tsaye, sai a lokacin ta tuna da daddy cikin sauri ta cire takalmin ta sannan ta juya ta fara tafiya cikin sauri tana tsalle kamar wata barewa .

Tana karasawa kofar gidan taga wayam ba motocin daddy ba labarin su kamar za tayi kuka haka ta shige gidan da sallama jikinta a sanyaye,  hajjo ce ta amsa sallamar tana dorawa da " sai kuma kikaje kikayi zamanki har daddyn  ya tafi , ba tare da tace komai ba ta karasa Inda ummi da hajjo ke zaune ta zauna tana kai dubanta gaban su Inda taga huhunan goro dasu packet² na sweet da su chocolate kamar za tayi kuka tace da gaske daddyn ya tafi ?  yar dariya hajjo tayi wadda ke bayyana farin cikin da take ciki tace karki damu abinda daga ya dawo daga tafiya zai sake dawowa .

"da gaske zai sake dawowa kwana kusa ta fada tana washe baki hajjo tace ke dalla can da ina maki wasa ne, murguda baki tayi tana fadin na nawa kuma wai ance da kuturu Allah ya raba lafiya, mangara ummi ta kawo Mata tayi saurin kaucewa

"wai ke hajjon sa'ar kice ne bansan rainin wayo fha ki kiyayeni.......katseta hajjo tayi da cewa kinga fatima ba ruwanki munfi kusa ba'a shiga tsakanina da kawata zakiji kunyane ,ummi ta sake cewa gwara ma ki fara koyon zama waje daya dan nagaji da wanna shegen yawon naki ke kullum kina titi baki San zaman gida ba .

Bata fuska tayi  " toh ni ummi shikenan sai in ta zama gida ni kadai ba wani abokin hira ke kuma abu kadan kita masifa komai nayi abin fada ne .

" Amma ke dai akwai yar Albarka wato nice ma masifaffiyyar saboda ina maki fada in kinyi ba daidai ba ko ke baki san gata nake maki ba wasu suna can suna neman magayi ma sun rasa amma ke ana gyara maki saboda rayuwar ki kina cewa masifa to Allah ya shiryeki .

"ameen tace tana juyawa wajen hajjo tace hajjo sai fara'a ake an samu tsarabar goron birni.

"ke ni tashi ki mikomin ledojin can a kukkulawa makota tun wuri .

" na miye ne hajjo naji kina cewa a kukkulawa makota?

"na auran ki ne hajjo ta fada tana bude wani packet na alawa dariya seena tayi tana maimaitawa " wai na aurena a a kinman ta na haihuwata ne kefa hajjo wani lokacin sai a hankali tsufa ya fara Miki sallama ta fadi tana tashi ta dauko Mata ledojin .

Kunce bakin gyalenta tayi ta dauko kudin da daddy ya bata ta mikawa hajjo "gashi ki ajjemin kuma kika kashe whl saikin biyani ko na dauki goron na siyar tana gama fadin haka ta zari packet chocolate biyu da ledar sweet daya ta tashi da niyyar shigewa daki ummi tace ina zaki da wanna ai sun Miki yawa sai su sa kiyi ciwon ciki, turo baki tayi tana fadin " to ummi ai nasan duk wannan ni daddy yakawoma tsaraba goron ne kawai na hajjo amma shine wanna tsohuwar tace wai duk rabarwa zatayi ai bari ya dawo saina fada masa duk ta kwashe raba ma mutane Mai makon ma a raba masu ledar sweet din nan daya ko biyu amma tace wai duka tana gama fadin haka tayi shigewar ta daki, girgiza Kai kawai ummi tayi tana murmushi suka cigaba da abinda suke.

Tana idar da sallar Isha ta koma bakin gado ta zauna tana jiran hajjo ta idar da salla .

Tana sallamewa kuwa tace hajjo "ban kudi na zan tafi dandali .

" amma Haseenah bakya bari ba sai gobe kyaje tunda naga yau an sha ruwa.

" ni dai ah ah ruwan da tun laasar akayi shi ni kawai kiban in tafi.
Tashi tayi ta dauko ta Mika Mata, karba tayi ta tashi tana gyara daurin dan kwalin ta ta nufi kofa tana fadin hajjo saina dawo in ummi ta shigo kice Mata na tafi dandali kar tazo tana fada.

Kusan Karo sukayi da ummin a bakin kofa zata shigo ita kuma zata fita kallon seenan tayi sai kuma tace ina zuwa ? "dandali .

"tukun na ma sau nawa ina fada maki in zaki fita ki dinga yafa mayafi to maza wuce ki dauko gyalenki  , komawa tayi cikin dakin tana gunguni ta dauko gyalen dan tasan idan taki ummi na iya hanata fitar ma gaba daya , "kuma ki Kula Kar kiyi dare ina Kara jaddada Miki banda neman magana da to ta amsa tana wucewa.

    Karaso wa tayi ciki ta zauna tana fadin amma gsky hajjo bai kamata abar yarinyar nan haka ba ya kamata tasan komai ko dan ta rage wasu abubuwan data keyi tasan itama yanzu matar aure ce watakil hankali yazo Mata . 

Ajiyar zuciya hajjo tayi Sannan tace " ni a ganina nafi son a bari sai lokacin da Hamzan ya dawo sai asan yadda za'a Mata bayani cikin hikima ta yadda baza ta damu ba, wato fatima ki bar ganin wanna tsawon kafar na haseenah har yanzu bawani hankalin kanta ta mallaka ba du du du fa sai watan jibi zata shiga sha hudu kawai na yarda da wanna raayin na Hamza ne saboda dalilan da ya fada kuma nima na gamsu da hakan amma da badan haka ba gaskiya bazan amince ba, kuma nasan inada tabbacin zai Kula da ita kamar yadda zai Kula da sauran yayan nasa mata.

" haka ne hajjo , ni whl nayi farin ciki dan nasan ko ba komai zata nutsu ta kama kanta idan ta ga can ba kamar nan bane tunda anan din harda ganin idonki ke sa tana wani abun. 

"Hakane amma ki ci gaba da Mata addua Allah kuma yasa hakan shi yafi alheri , da ameen ummi ta amsa Mata suka cigaba da wata hirar.


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol