Free chapter · Read without an account
1
by Haruna Faisal · BAKAR RANA
Sanyin daminar da ke busawa a safiyar ranar Laraba na biyo don neman abin da zan kaiwa Sarki ya zame mashi kariya daga ƙulalan da ke kai masa naushi. Cike da nishaɗin da fuskata ta gaza wajen sakayashi na ke bin gefen titin da ya ratsa tsakiyar anguwar. Wasu tsuntsaye mace da namiji da ke faman shawagi a saman wata itaciya na bi da kallo, nishaɗina na sake ninkuwa sakamakon yadda nima abar ƙaunata ta tsefe zuciya da gangar jiki da zaƙaƙan kalamanta a wayewar garin. Duk da yanayi na damina da ake ciki ya yi daidai da irin lokacin da masoya ke nishaɗantuwa da shi. Na yi sallama da ita ba don mun gaji da juna ba sai don lokacin fita makaranta da ya yi. Ba don jarabawar da zan je rubutawa ba, babu abin da zai katse mini zuciyata daga samun nishaɗin da ta jima tana nema. A halayya ina daga cikin mutanen da ke nishaɗantuwa da yanayi na damina, nishaɗina da fara'ar fuskata na ƙara yalwata a duk lokaci makamancin wannan. Ko da yake 'Ba ka fushi' sunana da ya gama karaɗe unguwarmu ke nan, kuma hakan baya rasa nasaba da halayyata ta faran-faran da jama'a tare da ɗaukar damuwar mutane in azawa kaina, bana sassautawa har sai na tabbatar da raguwar damuwar. Ban kasance cikin jinsin kyawawan maza ba, amma, bana manta yadda Kakanmu ke yabon zubin halittata, tare da ba ni tabbacin fara'ar da ke ƙunshe a fuskata na janyo mini kwarjini a idanun jama'a. Ban ƙara sakankancewa da hakan ba sai da na kai munzali na fara cin karo da yadda ƴammata ke bunbuntowa domin kawo mini hari. Daidai lokacin da na ke ƙoƙarin tsallakawa gefen rumfar mai shayin, wata mota da aka rufeta da baƙin gilasai ta fara doka amsa kuwwa. Ganin ba ina kan titi ba ne yasa na ci gaba da tafiyata domin aiwatar da abin da ya fito da ni daga gida. Jin ƙarar sautin amsa kuwwar ya ƙi ya ƙare ne ya sa na waiwaya don ganin abin da ake wa wannan ɓaɓatun. Ga mamakina baƙin gilashin da ya lulluɓe motar aka rage, wani lafiyayyen hannu ya fito ana ya fitoni da shi. Ba tare da fargaba ko jin wani ɗar ba na doshi inda motar take, wani ɓangare na zuciyata na ayyana min cewa wataƙila tambaya mamallakin motar ke son yi. Bayan ƙarasawata, wannan hannun dai shi aka sake zurowa sai dai wannan karon yatsun hannun ne kawai suka bayyana a waje riƙe da wani ambulan wanda ban fahimci ko na mene ne ba. Fahimtar da na yi cewa ni ake miƙowa ambulan ɗin yasa na yi saurin fatattakar guntun tunanin da ke neman matsuguni a tare da ni, na sa hannu na amsa da nufin koro tambaya. Da amsar ambulan ɗin da na yi, da bawa motar wuta duk ya faru ne a matsakaicin lokaci. Amon sautin jama'ar da ke gefen hanyar ne ya sa na dawo daga duniyar tunanin da ya rumfaceni. "Kai kuwa Malam ina ka samo mai wannan motar haka da ko tunanin ƙananun yaranmu ba yayi yake ba mota wuta a cikin unguwa?". Murmushi kawai na yi na juya ina fuskantar magidancin da ke kwararo min tambayar. "Baba, kasan mutanen namu sai haƙuri, tun da Allah ya kiyaye ya fita layin dai kawai shi ke nan". Na juya na nufi inda na tunkaro tun asali. Ambulan ɗin da ke riƙe a hannuna na ke jujjayawa tare da kokuwa da ƙwaƙwalwata wajen son hasaso maƙasudin dangana ni da wannan saƙo ba tare da na san ainihin daga inda ya fito ba, sannan ban san in da zan kai ba. Ɗabi'ar mazan jiya na aro na yafa wanda hakan ya bani dama na yi ƙundunbalar farke ambulan ɗin, wata ƙaramar takarda ce ta faɗo. A firgice na miƙe tsaye ba tare da na shirya ba, zuciyata ta fara dukan uku-uku. "Innalillahi wa'inna ilaihir-raji'un. Hasbunallahu wani'imal wakil" Lokaci guda na tsinci kaina ina jero su ba tare da na shirya ba. Idan ba gizo idanuna ke yi mini ba saƙon da ake tura mini a wayata da aka sace satin da ya gabata, yanzu shi ne aka fara biyo ni da shi gida. "KA BI A HANKALI KA AIKATA ABIN DA MAI GIDA KE SO IDAN BA HAKA BA ZAKA MUTU!" Abin da ke rubuce a jikin takardar ke nan. Na fara samun wannan saƙon ta akwatin salula tun a kimanin watanni biyu da suka gabata, sai dai ban ɗauki abin da gaske ba domin na bar shi kan cewa wani ne ke ƙoƙarin razanani cikin abokaina duk babu irin wannan wasan a tsakanina da kowa. A yau tunanina ya canza, tabbas na fahimci akwai babbar matsalar da ke shirin tunkaro ni! Wane ne maigida? Wani irin aiki ne a ke yi min barazanar idan ban yi shi ba zan mutu? Rashin amsar waɗannan tambayoyin tare da tuno da jarabawar da ke gabana a safiyar yasa na tattara komai na ajiye har zuwa lokacin da zan kammala jarabawata. Bayan fitowar mu daga jarabawa ne na ƙara samun makamanciyar takardar ɗazu a maƙale a babur ɗina. Kafin in yi wani yunƙuri wayata ta fara tsuwwar neman agaji, ba tare da na duba mai kiran ba na ɗaga wayar. "Na san ka samu saƙonnina, na kira ne in ƙara tabbatar maka, ina tare da duk wani motsi na ka. A duk lokacin da ka yi gangancin sanar da wani game da saƙonnina zaka fuskanci hukunci mafi muni, idan kuma ka yi biyayya ga umarni na zaka zamo abun kwatance a cikin makarantar nan. Ka zama cikin shiri a ko yaushe aikinka zai iya farawa. Ka saka wannan a ranka, ko yaushe ina tare da kai ɗan saurayi" Wata siririyar murya ce ta gama zayyano min waɗannan kalaman. Kafin in samu damar furta wani abu ya datse wayarsa. Tashin hankalin da na shiga shi ya haifar min da rashin natsuwar zuciya da ruhi. Na kasance cikin ruɗu da rashin sanin makoma.