Free chapter · Read without an account
AMRAH PART 22
by Hussain Yusuf · AMRAH
AMRAH
©Hussain Yusuf✍️
<<PART 22>>
Amrah ta zabura, ta tashi zaune da sauri. Idanuwanta suka kafe kan farin mutumin da yake tsaye a kanta. Tsoro da mamaki suka gauraya a fuskarta. Ko da yake ta san cewa ƙarfin ikonsa ya fi nata, amma kyawunsa ya ɗaure mata kai, kuma mararin da take ji a zuciyarta game da shi ya ƙi barinta ta bar wajen.
Hisham ya saki murmushi, wanda ya ƙara bayyana fararen haƙoransa. Ya ce da ita, cikin tattausan lafazi, "Assalamu Alaikum. Me ya kawo kyakkyawar yarinya irin ki nan wajen da babu kowa? Wannan wuri mai natsuwa bai dace da kasancewar wannan fuska mai yawan damuwa ba."
Amrah ta ɗaure fuska, ta tashi tsaye, sannan ta ɗan yi taku uku nesa da shi kaɗan, Ta ce da shi a fusace, "Kai wane ne? Me ya sa kake bi na? Kuma me ya sa ka zo ka dakatar da ni daga shirin ɗaukar fansa da nake yi a kan mutanen ƙauyen Kiyawa? Ka yi nesa da ni kafin na nuna maka asalin wace ce ni!"
Hisham ya yi shiru na ɗan lokaci, amma murmushin bai gushe ba a kan fuskarsa. Cikin sigar lallashi ya fara yi wa Amrah magana da kalamai masu sanyaya zuciya, "Amrah ni ba mai cutarwa ba ne a gare ki. Sunana Hisham bn Hashim. Na kasance ina neman mafaka da kwanciyar hankali a wannan wuri mai kyau. Amma da na iske ki a wajen, sai na fahimci cewa natsuwar da nake nema tana tattare da ke. Na ga baƙin ciki a idanuwanki, kuma na sani cewa wani abu mai zafi ne ya taɓa zuciyarki."
Ya matso kusa da ita a hankali, ya ci gaba da lallashinta da murya mai sanyaya zuciya. "Ki sani, wannan kyakkyawar fuska ba ta dace da zama fuskar baƙin ciki da burin ɗaukar fansa ba. Me ya sa kike son ɗaukar fansa, alhalin kyawunki ya isa ya haskaka duka wannan ƙauyen?"
Kalaman nasa sun fara shiga ranta, amma ta ƙi nuna hakan. Ta ƙara ɗaure fuska. "Ka manta da zancena. Ba ruwanka da rayuwata. Kuma ba na buƙatar komai daga gare ka!"
Hisham ya kalle ta kamar mai nazarinta daga bisani ya ce, "To, Amrah. Idan har ba kya so in shiga cikin rayuwarki, ba zan tilasta miki ba. Amma ina roƙonki da kyakkyawar zuciya ki kwantar da hankalinki. Na san za ki yi tunani a kan yadda za ki ci gaba da rayuwarki ba tare da baƙin ciki ba."
Ya ƙara kallonta sosai, ya ce, "Idan kin yarda, zan iya zama abokinki mai ɗebe miki kewa. Zan iya zama mutumin da zai mayar miki da murmushi a wannan fuskar taki, har sai kin yanke shawarar abin da ya dace ki yi da rayuwarki."
Amrah ta kasa ɗaga idanu ta kalle shi kai tsaye. Tana sauraron muryarsa mai daɗi, sai ta ji wani abu ya fara tsirowa a zuciyarta game da shi, amma sai ta tilastawa zuciyarta daurewa.
Ta kalle shi, "Zan yi tunani a kan maganganunka. Amma ka yi nesa da ni. Ba na son wani ya zo kusa da ni yanzu."
Hisham ya yi murmushi mai cike da fahimta. "Na fahimce ki, Amratu. Zan yi nesa da ke, amma ina ƙara tabbatar miki da cewa, a duk lokacin da kika buƙace ni, a shirye nake na kasance a kusa da ke."
Ya juya, ya hau dokinsa, ya ɗauki hanyar komawa ƙauyen. Amrah ta tsaya a wurin, tana kallonsa har ya ɓace a cikin daji. Ta kasa gane tausayawa da wani iko da suka tattara a jikin Hisham. Ta san cewa shawarar da za ta yanke yanzu tana da matuƙar muhimmanci ga rayuwarta.
A waya, Hamrah ta kira Daddy ta sanar da shi cewa ita da Jawad za su je yi wa Kamal barka matarsa Zeenatu ta haihu. Duk da ran Alhaji Kabiru bai so ba, tilas ya amince da bukatar ƴar tasa saboda Kamal ɗin yana da matsayi na musamman a wurinsa, mutumin kirki ne sosai, shi ya sa ya rabu da ita. Amma sai da ya gargaɗe ta cewa kar ta daɗe, kuma da zarar ta ga wata matsala ta yi gaggawar kiransa.
Godiya ta yi wa Daddy, sannan ta kira Jawad ta sanar da shi cewa Daddy ya amince ya fito yanzu su tafi su dawo da wuri. Kafin cikar minti talatin Jawad ya hallara a ƙofar gidan su Hamrah, kiranta ya yi a waya ta fito, ba su ɓata lokaci ba suka ɗauki hanyar zuwa asibitin.
Ƙarfe biyar na yamma suka isa Bilkisu Memorial Hospital. Sai da suka yi tambaya aka nuna musu ɗakin da su Zeenatu suke. Da sallama suka shiga, suka tarar da Kamal zaune kusa da Zeenatu wacce take kwance tana murmushi, jaririyarta a kwance kusa da ita.
Kamal ya yi murna matuƙa ganin Hamrah da Jawad. Ya miƙe, ya tare su da fara'a, sannan ya kalli Hamrah ya ce, "Hamrah! Ina godiya da wannan ziyara! Sannunku da zuwa."
Hamrah ta amsa gaisuwarsa, sannan ta nufi wajen Zeenatu da sauri. "Zeenatu, sannu! Na yi murna matuƙa da jin wannan labari mai daɗi. Allah ya raya mana baby girl, ya sanya ta zama yarinya ta gari."
Hussain Yusuf✍️