Free chapter · Read without an account
15
by Rufaida Umar · ALWASHI 2
ALWASHI
40
©Rufaida Umar
MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE
Yar uwa muna saida kowanne irin supplement na gyaran jiki wanda zaisaki fito fes kamar sabuwar Amarya, yar uwa shin kurajene suka dameki, ko matsalolin jikine kamarsu rama, ko kibace tayi miki yawa kikeso ki rage, bushewar fata ko karancin ni'ima ko budewa ne ko infection? Ko kuma so kikeyi fatarki tayi laushi ki dinga sheki kina haskawa wato kalar madara dai Haj to ki garzago
Yan uwa kusani duk wani supplement da zamu kawo muku sai munyi bincike mun tabbatar da ingancinshi, mun kuma tabbatar da cewa bashi da wata illa ga lfy
Akwai masu cewa sunsha supplement amma har yanzu basuga wani canji ba, to yar uwa kodai an baki fake ko kuma ba'a baki wanda ya dace dakeba, kokuma bakisha yadda ya dace ba, kisani yar uwa kafin ki fara shan supplement akwai ka'idoji daya kamata ace kin kiyaye kuma kin kula dasu matukar kinaso suyi miki aiki yadda ya kamata kuma cikin sauki ***
1. Akwai Supplements na gyaran jiki ciki da waje, munada set na uwargida dana Amare da masu jego
Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc
Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners da air wick, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number ***
***
Yana kwance a saman doguwar kujera a falonsa yana kallon tashar Saudia inda ake hasko Mahajjata. Bai jima da kammala shan ruwa ba, zuciyarsa fari ƙal da wani irin nishaɗi irin wanda kowane musulmi ke jinsa ciki a ranaku irin haka na ibada da kuma gabatowar ranar sallah. Yinin yau sam bai zauna ba sai a yanzun, dabbobin layya na gidan suka je karɓowa don Abba ya kwana biyu da siya. Sam ba ya son haɗuwa da Nihla tun sadda ya ga ta fito kusan rabinta tsirara tsabar haushinta da yake ji, ga uwa uba mahaifinta da yake kaucewa ya ƙi ba sa fuskar su yi wata magana. Kausar tuni Mamin ta sanya an maida ta garinsu ba don komai ba sai gudun kar Nihla ta fuskanci wani abin. Hakan ya sa ko lefe ma can gidan Adda Diyya ake haɗawa.
Wayarsa da ke hannun kujera ta yi ƙara ya waiwaya. Ganin sunan da ke yawo a jiki ya sa shi sakin ɗan murmushin gefen kumatu. Har ta katse bai ɗaga ba. Dama ya yi expecting hakan tun bayan da ya samu waya daga mai delivery cewa saƙonsa ya isa gidan. Shi bai ma san a na haka ba, ya san dai Fareed ne ya sanya shi lallai ya siyawa Kausar da ita ɗin, wai haka ake yi da sallah ka yiwa masoyiyarka kyautuka. Aisha ce za ta yi order, Fareed ya sa ta aikomasa different designs na mukhaweer da abayoyin har ma da komai da ya siyawa Laila da Kausar din, da kansa ya zaɓarwa kowaccensu don duka fararen ne masha Allah. Mami ya damƙawa na Kausar da aka kawo daga Kano. Amma bai gwada mata cewar har Laila ya siya ba ganin ba son maganarta take ba , ta kuwa yi farin ciki ƙwarai gami da sa mishi albarka.
Karo na biyu kiran Laila ya sake shigowa, ya sani a fusace take, dalilin da ya hana shi ɗauka kenan. Ba ya son ta haifar masa da wani zancen da zai sosa ransa a yanayin da yake ciki na walwala don haka ya yi burus, ƙarshe ma miƙewa ya yi ya shige ɗaki don watsawa jikinsa ruwan ɗumi.
***
A ɓangaren Laila kuwa, koda ta kira har sau uku ba'a ɗaga ba, hakan ya fusata ta ainun, ta san da gayya ya ƙi ɗaga kiran nata. Ƙwafa ta yi, kamar ta aikamasa saƙon text amma gudun kada ma ya raina ta kawai ta fasa. Kawai ta nemi wuri ta yi zamanta a ɗakin Gwaggon ta ƙi fitowa duk da tana tunanin ayyukan da suke kan cigaba da yi na abincin sallah da ma suya. Ƴar aikin Momi Fannah da wata ce bazawarar ɗiyarta mai taimaka mata suna kicin suna ta rage aikin.
A falo bayan tafiyar Laila, Momi Fannah ta miƙe ta nufi hanyar ɗakin Haseenah fuskarta a ɓace, ganin haka Gwaggo Samha ta yi kiranta.
"Zo nan Ummu Abbas."
Jin haka Momi Fannah ta dawo ta zauna.
"Ga ni Gwaggo."
Da ɗan murmushi Gwaggo Samha ke dubanta,
"Ki rabu da ita in dai Haseenah ce, ni zan je na same ta. Bakin uwa yakan zamewa ɗa bala'i da masifa, balle yanzu da kike cikin fushi da ita. Yi zamanki bari na je."
Gwaggo na kai wa nan ta miƙe yayin da Momi Fannah ta amsa da toh kawai tana jin har lokacin ba ta huce ba muddin ba hannu ta kai ta jibgi Haseenah ba ko za ta yi nasarar raba ta da wannan mugun halin da ba zai haifar mata da ɗa mai ido ba a rayuwa.
***
Sallamar Gwaggo Samha a bakin ƙofar falon me ya sa Haseenah ɗago kai daga wayar da take amsawa ta dube ta. Ta kauda kai gami da faɗin,
"Give me some minutes please, I'll call you back."
Daga haka ta ajiye wayar tana kallon Gwaggo Samha wacce tuni ta nemi gefenta ta zauna tana gyara zama gilashin idanunta. Ɗauke kai ta yi tana danne-dannenta a waya ta ce,
"Su Gwaggo yau kuma me na yi? Don nasan ba'a ganinki a nan idan ba wani laifin ake tunanin na aikata ba."
Gwaggo Samha ta kai mata ranƙwashi a tsakar kanta, sosai ya shige Haseenah, ta kuwa yi saurin sakin wayar a saman cinyarta ta riƙe kan tana sosawa.
"Kya faɗi komai ma tunda wuyanki ya isa yanka ai. Shashashar yarinya, ai duk wani abu da kike aikatawa a gidan nan kina sane. Mace mai shekarun da ta doshi ashirin ace ba ta san me duniya ke ciki ba? Ƙarya ne wannan. Kinga tun ina ganinki da gashi ki yakice wannan mummunar ɗabi'ar da ba'a san inda kika gado ta ba a ranki? Ki fita idona tun muna shaidar juna wallahi."
Ta ɗan turo baki tana duban Gwaggo.
"Wai toh me na yi ne?"
"Ƙaniyarki kika yi. Haba Haseenah, matsayinki na musulma? Ki rasa wacce za ki ɗorawa karan tsana sai ƴar uwarki? Ko ba ki san ƙarfin alaƙarki da yarinyar nan ba na ƙara jaddada maki? To ki sani kakanta matsayin yaya yake a gareni. Mahaifinki kuwa ɗan uwar mahaifiyarta ne. Ke a ture duka wannan ma, koda ace ba ƴar uwarki ba ce ta jini, ina ce musulunci ya haɗa ki da ita? Abin da kike fa nunawa Laila ya wuce iya tsana kawai, ya na juyewa zuwa hassada."
"Hassada kuma Gwaggo? Ta ya zan yiwa ƴar uwata kuma hassada?" Cewar Haseenah tana kallonta fuska a murtuke.
"Eh hassada dai da kika sani. Idan ba hassada ba, ina ce ko batun zuwa tambaya da za'a yi bayan sallah na Laila ba ki ce mata uffan ba, ba ki yi mata fatan alkhairi ba. Duk wani abin cigaba na alheri da zai zo wa wannan yarinyar ba kya taɓa buɗar baki ki yi mata fatan alheri. Ki faɗa min wannan hassada ce ko a'a? Ki yi tunani karan kanki, Laila ba ta yi maki haka, nan idan abu ya sameki na farin ciki, ina kula da yanda take tayaki murna a fili kina gwatsale ta, hakan bai hana gobe wani abin farin cikin ya ƙara samunki ta yi shiru ta kauda kanta. Amma ke fa? Toh ko ban fito nayi ta maimaita maki kalmar hassada ba, na sani kin fahimci haka. A musulunce kin aikata babban laifi ga Ubangijinki. Ki tsarkake zuciyarki, ki buɗe ta ki fahimci mene ne ainahin abin da Laila ta taɓa yi maki a rayuwa har kika ɗora mata karan tsana. Yarinyar da tun tashinta ba ta san komai ba face wahalar rayuwa? A kaf tarihin Laila wanne ne ba ki sani ba? Mene ne ba a faɗi a gabanki ba kin ji? Rashin imanin naki har ya kai haka? Zuciyarki har ta yi makantar da ba za ki iya tausayawa ƴan uwanki kuma jininki da suka faɗa mawuyacin hali irin wannan ba? Laila marainiya ce da ba ta buɗi idanu ta tashi ta gan ta gaban mahaifinta ba, yana raye ko ba ya raye, babu wanda ya sani. Ina mai tabbatar maki Haseenah, wallahi ba don mutuwa mai yankan ƙauna ba, da ba za ki kama ƙafar gatan da Laila za ta samu a wurin kakanninta ba domin kaf zuri'armu a lokacin can babu mai rigar arziƙi irin na Hammad. Allah ya yi mishi arziƙi mai yawa, kuma da Allah ya tashi, sai ya kasance Kubra mahaifiyarta ita ɗaya ce ɗiyarsa a duniya. Ki faɗa min, idan don arziƙin ubanki da kike tunanin tana ci ne, me za ki gwada musu ban da dai ƙaddarar da ta riga fata? To ina ba ki shawarar ki yi tunani mai kyau domin gyaran gobenki tun kafin watan jin kunyarki ya kama. Allah ya sa ki gane."
Tana kai wa nan ta miƙe ta bar Haseenah da sanyin jiki. Gaba ɗaya kalmar nan ta hassada da Gwaggo ta jingina ta da ita ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya yi ba. Ba ta san ma hawaye take ba sai da ta ji ɗigarsa a saman leɓɓanta. Shiru kawai ta yi tana ta nazarin maganganun Gwaggon da son tunano me ma Lailar ta taɓa yi mata a rayuwa na munanawa? Amsar ita ce babu. Daƙyar ta ja wayarta ta hau danne-danne amma fa jifa-jifa zantukan Gwaggo na mata yawo a kwanya, sam ta kasa sukuni.
Laila da ba ta san ma wainar da ake toyawa tsakanin Gwaggo da Haseenah ba, tana can ɗakin Gwaggon tana kwasar takaicin Na'eem da Zakiyya waɗanda duk ta sanar musu batun kayayyakin da Areef ya aiko amma suka nuna ba wani abu a ciki, kamar haɗin baki duka sun yi ƙoƙarin fahimtar da ita ƙila duk cikin son kawar da tunanin yan gidan ne kar su fahimci ba alaƙa da soyayya mai ƙarfi tsakaninsu sai dai sam ba ta riƙi hakan da suka ce matsayin wata hujja ba. Ta ja tsaki kawai.
"Meyasa ba za ki sanar da su Momi cewar ba ke kaɗai zai aura ba? Ba kya ganin idan kika yi shiru su hana auren a gaba?"
Tambayar da Zakiyya ta mata kenan. Ta girgiza kai kamar suna ganin juna kafin ta rubuta mata amsa.
"A'a, ba za su ji komai daga bakina ba, ban fa damu da wani aurensa ba Zakiyya kema kin sani. Ki bari a yanda na sanar da shi ya furtawa Daddy da bakinsa idan ya zo gaisuwar sallah kamar yanda muka tsara kafin a shigo tambayar. Hakan zai fi."
Zakiyya ta amsa da "Ok, hakan ma ya yi."
Nan suka sako hirar duniya abinsu kafin su yi sallama. Koda ta fita ma ba ɗakinsu ta yi ba, kicin ta bi Momi Fannah suka cigaba da aikace-aikace. Ana yi ana hira da dariya.
***
YOBE...
Zama ne na musamman aka shirya a falon Nene wacce gaba ɗaya jikinta ya yi mugun la'asar, kunyar duniyarnan na abinda ta aikata ya tarar mata. Ta ɗaga kai ta dubi yaranta, Ahmad Kibiya, Adam, Raihana, Zahra'u, Mahmud da kuma autarta Khadija. Yau ta sani tunda har Adam ya kira su duka, tabbas haƙurinsa ne ke neman ƙarewa game da son sanin inda iyalinsa suke. Maganar da ya soma ce ta karya shirun da ya ratsa falon na ɗan lokaci bayan gaishe-gaishe.
"Nene, ina neman afuwa bisa taron nan da na shirya a gudanar ba tare da neman izni ko shawararki ba. Kuma gaba ɗaya ina neman afuwarku bisa rashin haƙurin da na nuna dangane da abinda ya shafi iyalina."
'An zo wajen.' Shi ne abinda Nene ta ayyana a ƙasan ranta. Babu sauran ɓoye-ɓoye, dama ai ranar wanka ba a ɓoyon cibi, ta riga da ta saddaƙar yau dole allura ta tono garma. Wannan kunyar ma wai ta duniya kenan, sai neman kariyar Allah da ta lahira. Muryar ɗan nata mai tsantsar biyayya gareta ya ƙara cika ɗakin.
"Domin Allah, ina roƙonku ku tausayawa halin da nake ciki na jinya. Ban sani ba ko cutar nan ta ajali ce ko kuma zan warke a gaba ba, ni dai yanzu ba ni da burin da ya wuce ganin ƴaƴana. Nene idan sun ƙi su faɗa min, na sani ke uwa ce, za ki tausaya min a irin shekarun da na ɗauka ba tare da na sanya wani nawa a idanu ba, tun ina da ƙuruciyata har zuwa yau da girma ya cimma ni. Na godewa Allah haɗuwar da na yi da ku, Alhamdulillah. Fatana na ƙarshe yanzun shi ne na ga Laila da Sameera, ku taimaka min ku sanar da ni inda Kubra ke aure, zan je ne ba don tayar da ƙura ba, idan can ta zaɓi cigaba da zaman aurenta ba wurina ba, wallahi ba zan matsa akan lallai sai ta dawo gareni ba. Amma ina da damar da za'a ban na ga yarana. Ba kuma zan tursasa kan lallai sai sun dawo hannuna ba, a'a sam, ni dai na gan su kuma su gan ni matsayina na mahaifinsu wanda nake da tabbacin a duk zatonsu ba na duniyarnan."
"Adamu."
Nene ta kira sunansa, ya dube ta ba tare da ya iya amsawa ba saboda nauyin da ƙirjinsa ya yi, yanayin muryar da Nenen ta yi amfani da shi wurin kiran sunan nasa ya sa shi jin tsoron kar ta ce masa ƴan biyu sun rasu.
Nene ta sunkuyar da kanta ta soma magana hawaye na kwaranyowa daga idanunta.
"Ka yi haƙuri, don Allah duk abin da za ka ji daga bakina a yanzu, ka yi haƙuri ka yafe min. Na sani ƙila ban cancanci yafiyar ba, amma ka duba raunina a matsayin Uwa wacce ta tashi kawai ta ga ɗanta ya ɓace ɓat kamar wani kuɗi. Dole ce ta sa ni aikata wannan kuskuren ba a hayyaci ba. Na sani za ka ce bana son Kubra dama tun farko, za ka iya cewa tsanarta ma ya shafi na ƴan biyu. Amma wallahi yanzu ina cike da nadamar abin da na aikata."
Kan Adam ya ɗaure tamau, sai dai ya samu nutsuwa ta hanyar cigaba da maimaita ambaton Allah a ransa. Bai ce uffan ba kawai ya zuba idanu kan Nene yana sauraronta.
Nene kuwa hawayenta ta goge sannan ta ɗora.
"Babu sauran rufa-rufa, babh kuma amfanin na yi maka ƙarya don ban san me hakan zai ƙara haifar min a gaba ba. Adamu, bayan ɓacewarka na shiga halin ɗimuwa da baƙin ciki, koyaushe cikin nema da koke-koke muke ni da ƴan uwanka. Dalilin da ya ƙara haifar min da tsanar Kubra kenan, na ke jin cewa duk yanda aka yi ita ce silar ɓacewarka, aurenta bai amfane ka da komai ba balle mu. Wannan ya fusata ni na fita a hayyacina, na manta cewa Allah ke da ikon zartarwa kan bayinsa, na yi fatali da duk wata fatawar kirki da zuciyata ke tunkuɗo min, na kori Kubra daga gidanka. Na yi rantsuwar yanda ba a ganka ba, itama ba za ta rayu cikinmu ba. Na kore ta da zummar ta shiga duniya ita da abinda ta haifa don ta nemo min kai. Yanda ka ɓata itama ta ɓace min da gani. Wannan shi ne abin da ya faru, bamu san inda suke ba, daga baya Ahmadu hankalinsa ya tashi, bai ji daɗin abin da na aikata ba, neman duniya haka ya yi ta yi ko zai ga Kubra koda ba ta dawo ba ya karɓo yaran nan, amma ƙarshe na ce masa ma idan ya ƙara bincikarta, ban yafe masa ba. Haka ya haƙura. Ka yafe min don Allah Adamu, wallahi na yi nadamar abin da na yiwa Kubra. Na kasa daina mafarkinta, na kuma rasa ina ta shiga. Suna raye ko ba sa raye, babu wanda ya sani."
Ta dakata saboda kukan da ya ci karfinta, yaranta mata na taya ta. Adam Kibiya idanunsa tuni sun yi mugun kaɗawa, zafin da yake ji a ƙirjinsa ya fi ƙarfin ya misalta. A yau ya gane ashe lallai hawaye ma rahma ne. Zai so zubarsu sai dai ina! Abin ya ci tura. Ya buɗe baki ya kai sau biyar yana mayarwa ya rufe sakamakon kasa maganar da ya yi ba don ba shi da abin furzarwa ba, ko kaɗan, sai dai kawai domin zafin da yake ji a ƙirji. Ya dafe ƙirjin yana mai jan salati a zuciya, a zahiri idanunsa har lokacin suna kan Nene har lokacin amma kuma haƙiƙanin ganin nasa ɗaukewa yake neman yi. Ya dafe saitin ƙirjin, a hankali kuma da ƙarfin addu'a da ke saman harshensa, ya ɗan daidaita. Sai a sannan ya samu zarafin magana.
"Kenan Kubra ba tafiyarta ta yi ba kamar yanda na yi zato? Ba aurenta ta yi ta tare da ƴaƴana ba? Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Da ace mutuwa na yi Nene, za ki iya rufa idanu ki kori yarana biyu kawai da Allah ya min kyautarsu a duniya? Ashe duka zaku iya juyawa iyalaina baya bayan raina? Nene rashina ba zai sa ki rungumi Laila da Sameera ki dinga jin tamkar ni ɗanki Adamu ne a gefenki ba? Wane irin so kike min Nene, idan ba kya ƙaunar jinina?"
Kawai sai ya ji kuka ya taso mishi, ya shiga yi lokaci guda ƙirjinsa na tafarfasa. Mata masu rauni nan suka ƙara rusa kukan. Nene kira take ya yafe ta, ya mata aikin gafara. Shi kuwa Adam sai da ya yi mai isarsa yayansa Ahmad na tausarsa kafin ya share fuskarsa ya dube su.
"Kubra ba ƴar zina ba ce Nene kamar yanda kike yawan ambatonta a lokuta mabanbanta ba, ba kuma daga sama ta faɗo ba tunda Allah bai tsara hakan ga mu ƴaƴan Annabi Adam ba. Mace ce mai gata wacce mahaifanta suka rasu a hatsarin mota kamar yanda ta sanar da mu. Mahaifinta Hammad Yusuf sanannen mutum ne kuma tsohon ɗan kasuwar da aka tabbatar min da ya yi tashen kuɗi a zamaninsa kafin ya rasu. Akwai abubuwa da yawa da suka faru da ni bayan bari na wajenku, na zaɓi na yi shiru yanzu ne kawai saboda wasu dalilaina masu ƙarfi."
Ya ɗan ja fasali. Nene za ta yi magana ya tari numfashinta.
"Nagode Nene, ke mahaifiya ce a wurina. Ƙila na yi laifin take umarninki na auri Kubra ba don ranki ya so ba, amma lallai ba a kyauta min ba. An yi min ba daidai ba, duk da haka ina neman gafarar saɓawa umarninki da na yi na aurenta. Ba zan ƙara damun ɗayanku da zancen iyalina ba, matsala ce da ta shafe ni ni kaɗai yanzu. Ya rage nawa na binciko inda ahalina suka shiga. Yaya Ahmadu kai ma nagode da ƙoƙarinka, ban ga laifin bin umarnin Nene da ka yi ba, haka Allah ya tsara zai faru. Nagode dukanku, nagode."
Yana kai wa nan ya miƙe har jiri na son kayar da shi, da sauri Dakta Mahmud Kibiya ya riƙe shi. Adam ya ɗan ture shi murya na rawa ya ce.
"Bar ni Mahmud, tafiya zan yi. Ba kwa buƙatar Adam a jerin ƴaƴan Alh Yaƙub Kibiya, zan bi sahun iyalina."
Nan da nan duk falon kowa ya ruɗe. Nene ta miƙe jiki na rawa ta riƙe rigar Adam.
"Don soyayyarka da Allah da Manzonsa s.a.w kar ka yimin haka Adamu, kar ka tafi ka bar ni karo na biyu. Allah ma muna masa laifi ya yafe mana, don Allah Adamu kar ka ƙara bari na."
Inaa! Adam Kibiya tuni ya suma ya faɗa jikin Ahmad da ke a gefe. Hankula suka tashi. Dakta Mahmud ya buɗe masa maɓallan rigar kafin ya yi umarnin a fiddo mota a wuce asibitin. Nan da nan aka nufi asibiti da shi hankula duk a tashe.
***
WASHEGARI...