Free chapter · Read without an account
16
by Rufaida Umar · ALWASHI 2
https://arewapen.com/u/rufaidaumar
ALWASHI
41
©Rufaida Umar
KANO
Haseenah ce ta fito daga ɓangarensu a gaggauce don tuni kowa na gidan sun yi shirin tafiya masallaci sun fita zuwa wurin motar. Ta yi kyau itama cikin wani rose peach lace dinta mai kwalliyar red da blue flowers a jiki. Ta saka dogon jalbab ɗinta kalar leshin. Ta iske Laila wacce itama irin leshinta ne kawai bambancin colour ne, don na Laila skyblue ne da adon peach da dark blue a jikinsa. Suna hoto da Ilham da su Faruk. Daddy ma har shi a hotunan. Gaba ɗaya kowa cike yake da walwala. Daddy koda ya hango Haseenah sai ya dube su.
"Oya duk a shiga mota. Idan an dawo a ɗau pictures din kar mu makara."
Aikuwa a gaggauce Haseenah ta ƙaraso tana ɗan tura baki.
"Kai Daddy, sai da ka ga na fito? Ni dai gaskiya ban yarda ba sai an yi da ni."
Laila dai ta ja baya tana danna wayarta, da ace suna yabawa juna kwalliya, da za ta ce mata ta yi kyau abinta masha Allah. Tabbas Haseenah tana da kyau kawai dai a ganinta raina halittarta take ne don ita baƙa ce, wanda a ganin Laila abin da take aikatawa na kushe halittar da ko kiyashi ba ta isa ta halicce shi ba, zunubi ne babba.
"Laila." Kamar daga sama ko ko ta ce mafarki, ta ji Haseenah ta kira sunanta. Ta juyo ta dube ta da mamaki, ba gizo idanunta ke mata ba, murmushi Haseenah ke yi tana dubanta.
"Zo mu yi hoto."
Wannan karon hatta da Momi Fannah da yaran sai da suka sha mamaki, a ɓangaren yaran suma sun san ko zancen Laila suka yiwa Antin tasu ko tambayar inda take, tsawa take musu ko ta ja tsaki ta ce ba ta sani ba. Daddy shi ma murmushin kawai ya yi, koda ba komai Momi ke fadamasa ba, amma ya san da rashin jituwar diyartasa da Laila, yau da gobe dole idan kana tare da su za ka lura babu wata shaƙuwa ko sabo tsakaninsu.
Laila kuwa nuna ƙirjinta ta yi da yatsa.
"Ni?" Ta yi tambayar tana duban Haseenah domin ita wallahi dagaske gani take kamar ba ta ji daidai ba. Haseenah ta ɗan waske da harararta gami da ƙarasowa ta ja hannunta.
"Ke mana, ke kadai ce Laila ai. To ko ba kya ra'ayi sai mun ajiye tarihin hoton nan."
Aka yi dariya, Laila dai murmushi take. Momi Fannah baki yaƙi rufuwa sai hamdala a zuciya. Jira take su je su dawo ta tambayi Gwaggo yanda aka yi a wannan karon ta shawo kan jikarta ta.
Aikuwa sun yi selfie masu kyau a Iphone din Haseenah. Sannan aka yi gaba daya har Daddy Mu'az. Daga nan yace maza a tafi kar a makara. Haka duk suka shige motocin. Haseenah da Laila ji suke kamar an cire musu wani dutse mai nauyi a ƙirajansu. To fisabilillah mene ne amfanin gaaba? Koyaushe zuciyarka baƙiƙirin, kai kanka ba ka sake ka wataya ba, jifa-jifa dole mutum ya dinga faɗo maka a rai musamman idan ba ka saba da halayyar ba. Sai gaba ɗaya suke jin ransu wasai. Laila dai na ganin ikon Allah yanda Haseenah ke ta ƙoƙarin sanya ta a magana, koda aka je wuri guda suka zauna. Bayan an idar ta yi musu selfie tare. Haka suka komo gidan zuciyar kowannensu cike fal da annashuwa. Gwaggo Samha har ƙwallar farin ciki ta fitar ganin Haseenah da Laila tare sun biyo Daddy an shigo wurinta. Har hoto suka dauka da Gwaggon. Nan kuma Laila ba jinkirtawa ta tura ma Mama hoton don ta gani. Kusan rashin jituwarsu ma babu abinda Maman ba ta sanarmata ba daga baya. Ta kira mutanen Maidaguri ta saka aka hankaɗo mata hotunan wankan Haidar. Ta so kwarai ya zo Kano babbar sallarnan, sai dai tsoron kar su yi arangama da Areef ya sa ta fasa neman alfarmar hakan wurin Baba Barista.
Kusan dai wannan rana ita ce rana mafi kyau da annashuwa a wurin Laila. Ta saka ta a jerin ranakun da ba za ta taɓa mancewa ba. Ta ƙara yarda da cewa akwai alkhairi mai yawan gaske a cikin sulhu.
***
KATSINA...
A gidan Alh Sada Bilyamin kuwa, su ɗin ma kowannensu ya ci ado har ya gaji. Nihla tun fitowar Areef ta kasa sukuni, gaba ɗaya ta raina shigar da ta yi na wani tsadadden swisslace dinta da ya haura dubu ɗari kalar lemon green da adon baƙi a jiki. Ɗinki ne bubu da bai kama ta sosai ba, hatta Mami ta yabawa shigarta don sai da ta furta mata cewa ta yi kyau. Hakan ya yiwa Nihla daɗi sosai, sai dai yanzun ganin yanda Areef ya sha kyau cikin sky blue shaddarsa getzner. Gaba daya ta ji gaɓoɓinta sun sake, ta saci kallon kwantacciyar sumarsa ya fi sau a ƙirga, ita fa ta rantse tsananin buƙatar Areef da gangar jikinta ya ke, yana neman ya yi mata mummunan illah. Ta rasa ya za ta yi, duk dare idan ba ta sha magani ba ba ta iya yin baccin kirki. Zuwa yanzu ko ba a faɗamata ba abu ne da ta fahimta, Areef ba ya sonta ba ya son ganinta ma. Koda ta gaishe shi, sai ya kawar da kai zai amsa yana wani cin magani. Ta rasa wane irin kwantar da hankali Daddy Affan ke cewa ta yi, har yaushe za ta jurewa abinda ke ranta ta cigaba da ɓoyo? Zuwa yaushe ne zai kammala shirin da ya ce mata yana yi wanda zai saka mahaifin Areef da kansa ya aura mata shi? Gani take yi Daddynta kawai ƙarya yake mata, babu abin da zai iya domin ta gane shi ma iyayensa na son abin da yake so irin yanda nata iyayen ke sonta.
Koda suka dawo sallar idi suka sauya shiga domin yin yanka, leƙen Areef din ta dinga yi a gefe guda, yana sanye da jallabiyar da ta bi jikinsa ta kwanta luf. Tsaki ta ja ta wuce fuu zuwa ɓangaren da iyayenta suke. Ta ci alwashin muddin Daddyn nata bai shirya abin da yake cewa za ta ji daɗinsa ba, to a daren yau ba na gobe ba za ta kai kanta har ɗakin Areef ɗin.
Koda ta ƙarasa ɓangaren, kiciɓus ta yi da shi yana shirin fitowa zuwa farfajiyar gidan bayan shi din ma ya sauya kaya zuwa ƙanana. Ganin yanayinta ya dube ta.
"Meyafaru kuma?" Ya jefe ta da tambayar.
"It's love Daddy, it's love. Na gaji da jiran wani plan dinka. Ka bar ni na nemi soyayyarsa da kaina please. Na gaji."
Ya yi murmushi ya riƙo hannunta suka zauna a ɗaya daga cikin kujerun falon. Sosai ya dube ta da kulawa ya ce.
"Me kike ci na baka na zuba haka My Baby? Ki ƙara min lokaci kaɗan, kar ki manta alƙawari na ɗaukar maki ba zamu bar garin nan ba tare da na shawo maki kan lamarinki ba fa. Don haka ki zuba min idanu, kar ki yi gaggawar aikata wani abu da zai rusa tsarina, kin ji ko?"
Ta turo baki kawai ta ƙi amsawa, shi kuwa ya ɗan ja kumatunta kaɗan.
"Aush!" Ta saki ƴar ƙara kafin kuma su saki dariya a tare. Momi Inayah ce ta fito daga kicin, itama ta ci adonta cikin leshinta maroon, sai kawai ta saki baki tana dubansu.
"Ah, dama ba ka tafi ba?"
Ya miƙe har a sannan fuskar a sake.
"Ta ina zan fita na bar bebina cikin fushi? Ga ta ki kular min da ita. Bari na je."
Da sauri Nihla ta miƙe tana haɗe rai.
"No ni ba zan zauna wurinta ba, nima wajen Mami zan koma."
Kafin Daddy ya ba ta amsa ma tuni ta fice daga falon, suka bi ta da kallo. Daddy Affan ya yi dariya da duban Momi Inayah.
"Ki rabu da ita kawai, kin san dalilin fushinta a kanki ai ko? Ni bari na je."
Bai saurari komai ba ya fice ya bar Momi Inayah da jin zafin wannan banzan ɗabi'ar ta ɗiyarta da ma shi kansa mijin nata. Wato komai Nihla ta yi shi daidai yake a wurinsa? Babu kwaɓa babu tsawatarwa? Ita da ƴarta amma ba ta isa ta faɗamata gaskiya ba? Kawai ta girgiza kai gami da nemawa Nihla shiriya a ƙasan ranta.
***
Areef da Fareed wanda ya shigo gidan gaida Abba da yammacin ranar sallah kasancewar ba su haɗu ba, suna zaune a falon Areef din bayan kammala cin abinci kaɗan don kowanne cikinsu nama ya ƙosar masa da cikin. Fareed ya ajiye robar lemun coke da yake sha ya dube shi.
"Yaushe ka shirya mana shiga Kanon?"
Ya karkato kansa dake jingine jikin kujera ya dubi Fareed ba tare da ya dago ba ya murmusa. Shi wallahi ya manta da ita, ya san dai tun ɗagamata wayar da bai ba ne ya ba ta haushi. Ko gaisuwar sallah ba ta aikomasa ba kuma dama ya san ba zai samu ɗin ba. Kausar dai ta mishi shima ya gwada kyautatawar kiranta a waya tunda har barka da shan ruwa yana samu daga wurinta har dai azumi ya ƙare.
"Shirunka na nufin..."
"Zuwa jibi in sha Allah." Ya katse tambayar Fareed ɗin ta hanyar ba shi amsa kai tsaye.
"Hakan ya yi, Allah ya nuna mana."
Areef ya amsa da amin. Yana son yi mishi batun aurensu da Sameera Laila da kuma bayanin ma wace ce ita da zai aura, sai dai kuma ba ya so a samu matsala Fareed ransa ya ɓaci har ya sanar da iyayensu. Ba kuma ya son ɓata ran Laila a yanzun. Sai kawai ya basar gami da sanyo wani zancen daban.
"Mutumin nan fa na saka ana bibiyarsa."
Fareed cikin rashin fahimta ya ƙara dubansa.
"Wa kenan?"
Areef ya ɗago ya gyara zamansa sosai.
"Alh Affan. Sam ban yarda da motive ɗinsa na son zama kusa da Abba ba, yanayinsa a lokuta mafi sukan min kama da na rashin gaskiya."
Jinjina kai Fareed ya yi.
"Eh toh, ba zan ce haka bane ko a'a, tunda ka cemin ya ɗauki alwashin sai ka auri ƴarsa. Amma kuma ba ka ganin ya san abin da yake? Kalli matsalar da ta taso mana a ofis kwanaki kan kayanmu da muka yi shipping, a kira ɗaya fa ya magance mana matsalarnan. Ni sai na ga kamar kawai dai yana jin haushinka don ba ka son ƴarsa, bayan haka babu wani abu."
Ƴar dariya Areef ya yi ya girgiza kansa kawai, hannu ya kai ya ɗauki robar lemunsa mai sanyi da ya rage ya buɗe murfin ya ɗan sha.
"Alright." Shi ne kawai amsar da ya ba Fareed. Bai masa zafi ba don ya san babu wani bayani da Areef zai ƙara yi masa tunda har bai gamsu da abin da ya ce ba. Miƙewa ya yi yana jan guntun tsaki da harararsa.
"Ɗan duniya kawai, ni bari na tafi kafin Madam ta soma jero min kira."
Areef ya maida lemun ya ajiye. Shi ma mikewar ya yi har lokacin fuskarsa a sake suka fice.
***
BAYAN KWANAKI BIYU...
Mami ta ɗaure fuska tana duban Areef .
"Sai dai idan daga Kanon, ka wuce Adamawa don ku gaisa da ƴan uwa, a gane cewa kuma dagaske son yarinyarnan ka ke ba wai cushe na maka ba."
Amsar da ta ba shi kenan bayan ya zo mata da batun shiga garin Kano a gobe Alhamis. Ya yi ɗan murmushi.
"In sha Allahu zamu yi hakan Mami."
A lokacin kuma ta ɗan saki fuska. Dabara ta faɗo mata, ta dube shi.
"Ya dace ita kuma ta Kanon ka kai ta gidan Gwaggonku su gaisa."
Ya ɗan yi shiru, sai kuma ya amsa da toh. Daga nan kuma ta shiga ba sa bayanin an kusa kammala haɗa lefen Kausar ɗin. Ta ɗora da cewa ita za'a fara zuwa a yi tambaya kafin Laila. Nan ma dai toh din ya ce don ya sani idan ya nuna wani abu daban to fa zai samu matsala da Mamin. Shi da Lailar ma ba ta sonsa, balle ta wani damu da kishin zama Uwargida. Haka dai suka yi sallama ya fito daga ɗakin nata.
A falon ya yi arba da Nihla zaune tana danna waya, ta sauya shiga zuwa doguwar riga marar nauyi. Babu ko dankwali a kanta, gashin nan nata baƙiƙirin. Kallo ɗaya ya yi mata ya kauda kai ya nufi hanyar fita, ya kai ƴan baranda Mami bayan fitarsa a falon, bai yi aune ba ya gan ta a gabansa. Ya kalle ta fuskarnan a haɗe. Ita kuwa marairaice ta yi har idanunta na ciccikowa da kwalla.
"Please Yaya Areef, please ka ba ni dama ko sau ɗaya ne na nunamaka irin son da nake maka. Wallahi Yaya Areef ba zan iya auren kowane namiji idan ba kai ba."
Tuni hawaye sun wanke mata fuska. Ya kauda kai.
"Ban hanya na wuce."
Kawai sai ta fashe da kuka, bai kuma yi aune ba ya ji ta faɗo jikinsa ta cukwuikwuiye tana fadin.
"Yaya please, let’s be together… that’s the only way you’ll believe I’m pure. Wallahi ban taɓa sanin da namiji ba, ina..."
Shi fa gaba ɗaya mamakin abin da ta mishi ne ya hana shi motsawa, lokaci guda zantukanta suka maido shi hayyacinsa, ya kuwa dage ya ture ta kafin ya ɗauke ta da wani wawan mari. Jikinsa har rawa yake yi na tsantsar ɓacin rai da tsoron abin da ta aikata masa, babu abin da ya tariyo sai lamarin da ya afku shekarun baya a gidan nasu. Gigicewa gaba ɗaya Nihla ta yi gami da dafe ƙuncinta, ihun ma ta kasa balle kuka. Tunda uwarta ta haife ta ba a taɓa marinta ba sai a yau ɗin da mutumin da take masifar so ya dora yatsunsa biyar a gefen kuncinta. Da yatsa ya shiga nuna ta amma maganar ta ƙi fita sai kawai ya gifta ya wuce da rawar jiki yana waige-waige ko akwai wani wanda ya gansu a gidan, ya yi ta jan istigfari a zuciyarsa haka har ya shige ɓangarensa.
Zakari wanda aka yi komai a kan idanunsa lokacin da ya nufo sashin Mami don kawai fakewa da gaishe ta ya ga Nihla ɗin, daidai sadda Nihla ta fito ta tsaya sai kuma ya ga ta rungume Areef din, da sauri ya ɗauki video na abin har kan marin da Areef ya yi wa Nihla gami da barin wajen a gaggauce. A haka ya dakatar, yana kallon Nihla ta wuce a guje ta nufi ɓangaren da iyayenta suke ya koma da baya ya kwashe da dariya.
"Wannan wace irin sa'a ce? Oh my God! Alhamdulillah!"
Ya furta a fili cike da wani irin nishaɗi ya wuce ɓangaren Hajja.
***
Karɓa ta yi ta kalli bidiyon tsaf sai kuma ta saki dariya sosai shi ma yana taya ta. Wayarta ta fiddo ta miƙa masa.
"Aiko min. Ƙwarai zai yi mana amfani a gaba. Ba yanzu ne lokacin da ya dace mu sake shi ba."
"Sai yaushe?" Zakari ya yi tambayar na tare da ya karɓi wayoyin ba. Ta harare shi don har lokacin ba ta gama hucewa daga ɓacin ran da ya haifar mata ba a haihuwar Hadeeya ba wacce yanzu haka daga asibiti ta wuce gidansu amma dayake tana mugun kaunar Zakarin wai har sun shirya suna waya. Gidan ne dai bai samu fuskar zuwa ba saboda Uwarta.
"Babu ruwanka da sai yaushe, kawai ka saka min yanzun nan."
"Shikenan Hajjaju." Ya faɗi don lallaɓawa yake ko nan gaba za ta saka baki a zuwa bikon matarsa idan ta girgije ta gama jegon. Koda ya tura mata ta titse shi sai da ya goge na kan wayarsa sannan ta saki fuska.
"Areef ka ƙara shiga tarkona. Madalla da ke Nihla. Kaga idan mun tashi datsar bidiyon kawai zamu yi don aiki ya fi kyau."
Suka yi dariya.
***
YOBE...