Free chapter · Read without an account
5
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*KOMAI TSANANI*
*By*
*KANSA'U* *BELLO*
*(OUM FATIMA)*
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*PAGE 05*
*BISMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM*
★★★
*Washe gari*
Yau ta kama ranar da ake gudanar da wannan al'ada don haka ko wane gida suke ta shiri, gidan Alhaji Zubairu Manomi yana ɗaya daga cikin gidajen da suke yin wannan al'ada kasancewarsa mutum na ɗaya a manyan manoma dake cikin ƙauyen. Don haka gaba ɗaya yaran gidansa kowa doya ɗaya yake bashi ya kai inda za'a gudanar da wannan al'adar.
A ɓangaren Nanah an bata doyarta tamkar dai sauran yaran gidan, don haka da gudu ta nufi ɗakin Mama cikin farin ciki don nuna mata. Tana zuwa ƙofar ɗakin ta dakata daga gudun da take yi gudun shan faɗa wurin Mama don ta hana ta guje-guje, tace ɗabi'ar yara Maza ce. Sallama tayi ta shiga ɗakin a nutse sannan ta kira sunanta.
"Mama kinga nima an bani zan je wurin wasan." Ta faɗa fuskarta cike da fara'a alamar tana cikin farin ciki. Haka kawai Mama taji bata son zuwan Nanah wurin duk da cewa ta san tana son ganin irin waɗan nan al'adun. Kallon ta tayi cikin so da tausayinta tace.
"Ni kam Nanah da kun haƙura da zuwa wurin wasan nan don haka kawai nake jin rashin natsuwa da fitar taki." Shagwaɓe fuska sosai Nanah tayi tana kallon Mama tace.
"Don Allah Mama kar ki hana ni zuwa kin ga kowa fa zai je, kuma da an kammala zan dawo gida ba zan tsaya wasa ba." Ta ƙare maganar a shagwaɓe sosai tana marai-raice murya. Ajiyar zuciya Mama ta sauke tace.
"Shike nan tunda kin dage kina son zuwa, Allah ya tsare." Rungume Mama tayi tana mata godiya cikin farin cikin da take ciki.
"Tashin min daga jiki tunda baki san kin girma ba, ko Sulaimanu baya son jikin da kike yi." Mama ta faɗa tana ture ta daga jikinta. Dariya Nanah ta ƙyal-ƙyale da ita sanan tace.
"To Mama shi ai Namiji ne kuma Maza basa hawan cinya, baki ji yanda ake cewa ba duk ƙanƙantar Namiji a gaba yake da Mace ba, kuma kina jin yana cewa nice ƙanwarsa." Dariya suka saka gaba ɗaya a kan surutun Sulaimanu, yaron yana da wayo sosai da ƙiriniya don duka shekarunsa biyar ne amma in ya furta maka wata maganar sai ka riƙe baki don mamaki.
***** Da yamma aka gudanar da al'ada kamar yanda aka saba don haka duk inda ka wurga idonka doya ce ke yawo tsakanin gidaje da kuma masu ci a waje, haka ma ƴanmata da Samarin kowa ya kama wurin hira. A ɓangaren yara ƙanana ma duk sun kama wuri suna ta gudanar da wasannin su cike da farin ciki da nishaɗi.
Haka ta kasance a ɓangaren Nanah yayinda itama tabi yara dai-dai sa'anninta su Atika, sai dai koda ta bisu kowa sai ya dare irin abinda yara keyi in suka raina ɗaya daga cikinsu. Wato tabi wanda ta raina, ko wacce yarinya a cikinsu ji take tafi ƙarfinta saboda yanda su Aziza suka gama ɓata ta a wurinsu shi yasa kowa ya raina ta. Sosai ran Atika ya ɓaci da abinda suka yi mata don haka ita taje ta kama hannunta suka nemi wuri nesa da sauran suka zauna suna jiyo muryoyin su Aziza na yiwa Atika masifa a kan cewar ai sai dai ta bita su ware don ba zasu zauna wuri ɗaya da ita ba.
"Ku dai abinda kuke yi bai dace ba sam." Atika ta faɗa cikin jin haushin abinda suke yiwa Nana.
"Ke dalla can ki rufe wa mutane baki, ai duk kece kike jawo mana raini a wurin agolar nan har take jin cewar matsayinta ɗaya da mu.!" Aziza ta faɗa a fusace don tafi kowa tsanar Nanah a cikinsu sakamakon wanda take matuƙar so Salmanu ɗan gidan mai gari yace yana son Nanah, duk da cewar Nanah bata kula samari saboda Mama data hanata. Salmanu yayi iya yinsa ya shawo kan Nanah ta riƙa kulasa amma ta ƙiya saboda ita tsoro ma take ji, don kullum huɗubar da Mama keyi mata akan cewar har yanzu ita yarinya ce babu abinda ta sani, kar taga ƙananan yara a nan suna kula samari tace itama zata ɗauka ta riƙa yi, karatu shine kaɗai abinda ya dace da ita a wannan lokacin. Duk abinda Mamanta ta faɗa mata ta san cewa abu ne mai amfani wanda ba zai cutar da ita ba, shi yasa take bakin ƙoƙarinta wurin ganin ta kiyaye duk abinda tayi mata hani dashi.
Zaune suke ita da Atika sunyi shiru babu mai magana, sai zuwa can Nanah ta sauke ajiyar zuciya ta kalli Atika tace.
"In tambaye ki don Allah Atika?." Kalkonta Atika tayi cike da tausayinta akan abinda ƙawayen nasu keyi mata, duk da cewa duk sun ɗan girmeta a shekaru amma ba wani me yawa bane da zai sa su riƙa nuna mata irin wannan tsangwamar. Don kaf ɗinsu in aka duba shekarun su ba zasu zama ɗaya ba, dole wasu sun girmi wasu. Wasu bai fi tseren shekara ɗaya ba wasu kuma shekara biyu abinda suka bata, in an turza sosai ta kai uku don ko Aziza mai cika bakin shekara biyu da wani abu ne ta bawa Nanah.
"Ina saurarenki, Allah yasa na san abinda zaki tambaye nin." Atika ta bata amsa.
"Meye ma'anar agola da ake kira na dashi ne, shin wani mummunan abu ne da yake sawa a guji mutum a rinƙa tsangwamarsa a cikin mutane?." Tayi mata tambayar cikin rauni abinda ke nuni da cewar abin na matuƙar ci mata rai. Tausayinta sosai ya ƙara kama Atika don haka ta gyara zamanta ta fuskanceta da kyau tace.
"A gaskiya ni dai iya sanina shine in kika ji ana cewa mutum agola shine wanda aka auro Babarsa taje dashi gidan wani, abin nufi shine a haifi yaro a wani gidan kuma sai Babarsa ta fito daga gidan Babansa ta auri wani mutum da ban ta tafi da yaron. Kuma sannan ba wani mugun abu bane kawai dai wasu mutanen ke mayar da abin wani iri su riƙa yiwa wanda aka zo dashi ɗin gori tamkar dai abinda su Aziza dasu Babarmu suke maki." Atika ta bata amsa da iya abinda ta sani.
"To amma ai ni Mamana ba fitowa tayi ba, rasuwa Babanmu yayi amma suke kira na da sunan kuma suke wulakanta ni har da Mama ma!." Nanah ta faɗa cikin karyewar murya.
"Eh ai duk ɗaya ne ko mutuwa Babanka yayi ko sakin Mamanka aka yi in dai tayi aure take da kai wani gidan agola ake kiranka." Atika ta bata amsa.
"Amma ni miye laifina da ake min irin wannan abin, shin akwai wanda zamana yake cutarwa a cikin gidanku da yasa basa sona ko kaɗan." Nanah ta kuma faɗa cikin sanyin murya. Atika na ƙoƙarin yin magana aka yi sallama, Buhari ne saurayin Atika yazo don haka ta amsa masa sallamar tana sunkuyar da kai. Gaisawa suka yi da Nanah kafin ya samu wuri ya zauna kusa da Atika don suyi hirarsu kamar yanda suka saba, yana zuwa hira gidansu don har an riga an bashi ita shine wanda zata aura.
Tashi Nanah tayi tace ma Atika.
"Ni zan wuce gida sai kin taho dama Mama tace kar na daɗe."
"To ba matsala sai na taho ɗin." Atika ta bata amsa, hanya ta kama tana tafiya a hankali cikin natsuwa tana wuce ƴan hira jifa-jifa. A dai-dai ɗan lungun da zata bi ta fita cikin layin gidansu ba zato ba tsammani taji an yi sama da ita, ƙoƙarin ihu take aka toshe mata baki da ƙarfin tsiya don haka ta shiga shure-shure tana son a sauketa.
Ba'a sauke ta ba kamar yanda take ƙoƙarin ganin faruwar hakan har sai da suka shiga wani kangon gini da aka fara a bayan garin. Sakar mata baki da akayi ne ya bata damar magana cikin tsoro da firgicin data shiga ta fara cewa.
"Su waye ku? Me nayi maku? Ku rabu dani in tafi gida!." Ta ƙare maganar cikin kukan tsoro da tashin hankalin rashin sanin ko su waye suka kamata suka kawo ta wannan wurin. Dariya taji an ƙya-ƙyace da ita da muryar da tayi mata kama da wacce ta sani kafin aka haska fitilar ƙaramar waya haske ga bayyana.
"Salmanu!?." Ta faɗa cikin razani tsoronta na ƙara bayyana ƙarara.
"Eh ni ɗin ne dai, ba dai nayi ta binki kika ƙi kula ni ba saboda shegen girman kan ki. To ai yanzu sai muga wanda zai ƙwace ki a hannuna yarinya don sai na wulaƙanta rayuwarki a wurin nan babu wanda zai ƙwace ki, in yaso sai muga ƙarshen girman kai." Salmanu ya faɗa cike da mugunta yana ƙoƙarin kai hannunsa jikinta. Doke hannunsa tayi kuka na ƙwace mata ta shiga roƙonsa a kan ya rabu da ita, cikin kukan take cewa.
"Ka rabu dani don Allah kar ka cutar dani, babu abinda nayi maka, wayyo! Taimako jama'a!." ta faɗa da karfi tana fashewa da kukan tashin hankali. Dariyar mugunta Salmanu ya shiga yi yana faɗin.
"Duk irin kukan da zaki yi babu wanda zai jiki yarinya dole yau sai na cimma burina a kanki, kai Ilu kai tsare min bakin ƙofa inyi in gama mu wuce kar a sami matsala." Salmanu ya faɗa yana kallon abokinsa Ilu.
"An gama Salmanu, ai yau kana cikin alkairi dumu dumu." Ilu ya faɗa cike da shaƙiyanci yana nufar bakin ƙofa don tsare masa.
Salmanu gadan gadan ya nufi Nanah da niyar keta mata haddi don haka kokawa sosai ta kaure a tsakaninsu yana son ta ƙarfin tsiya sai ya wulaƙanta mata mutuncinta, yayin da ita kuma take ta ƙoƙarin kare kanta cikin jarumta don ba ƙaramin juriya take yi ba wurin jure mari da dukan da yake kai mata.
Tayi matuƙar galabaita wurin ƙoƙarin kare kanta da take don haka yaci galabar yaga rigar dake jikinta, wani azababben ƙara data saka shi ya janyo hankalin matasa guda biyu ƴan bautar ƙasa wato (NYSCE) da suke koyarwa a secondary suka tsaya daga ƙoƙarin wucewa da suke ta gaban kangon zuwa gidan da suka yi masauki wato gidajen Coffer dake can wajen makarantar.
"Kamar fa ihu nake jiyo wa a cikin kangon nan." Ɗaya daga cikin su mai siffar jarumta ya faɗa. Kallonsa abokinsa yayi yace.
"Koma miye bai shafe mu ba don haka zo mu wuce dare nayi." Abokin nasa ya faɗa. Wani irin kallo ya jefa masa ya ɗauke kai sannan ya nufi shiga cikin kangon kansa tsaye ba tare da wani tsoro ba.
Ƙwala kiran sunansa abokinsa keyi amma ko juyowa bai yi ba ya dannan kansa cikin kangon inda yaci karo da Ilu a bakin ƙofa ya babbake.
"Malam ina zuwa haka?." Ilu ya faɗa yana ƙoƙarin hanasa shiga. Kallonsa yayi yana ƙoƙarin magana ya kara jin sautin fitar wani ihun a galabaice, don haka ya hankaɗe Ilu ya shige ba tare da damuwa da faduwar da yayi ba yana sakin ashar.
Salmanu dake gab da cinma burinsa cikin ficewar hayyaci sai ji yayi an fisgo shi an jefar gefe tare da sauke masa tagwayen marukan da suka sa ji da ganinsa suka dauke na ɗan lokaci. Tasowa yayin a fucace yana faɗin.
"Har waye kai da zaka shiga gonata, ka san kuwa koni way..." Bai rufe bakinsa ba ya ƙarajin saukar wasu marukan hagu da dama, dukansa ya shiga yi sai da ya masa lilis kafin ya koma kan yarinyar dake kwance ta sume tsabar firgicin data shiga.
Jacket ɗin daya ɗoro saman kayansa ya cire ya rufa mata sannan ya ɗaukota ya nufi hanyar fita da ita, sai dai me yana fitowa daga kangon yaci karo da tarin jama'ar da Ilu ya gayyato ya kuma sanar musu da cewa Nanah ce agolar gidan Alhaji suka kama tana iskanci da bƙin Coffer ɗin nan, shine don sun yi musu magana ya musu duka shida Salmanu, shima da ƙyar ya tsira ya tafi sanar da mutane.
Ai kuwa dan da nan mutane suka yi caaa!!!! Suna ta Allah wadai da faɗar magan-ganu marasa daɗi wanda suka ɗaure kan ɗayan Coffer ɗin dake tsaye yana jiran fitowar abokinsa daya shiga taimako, sai kuma ga sharrin da aka ƙulla masa. Ƙoƙarin fahimtar da mutane ya shiga yi sai dai shima suka hau sa da zagi tamkar zasu dake sa.
Ido huɗun da suka yi da wanda ya fito ɗauke da Nanah yasa duk wani tsageran daya taho da abin duka jikinsa yayi sanyi ya noƙe ganin tsayayye kuma ingarman Namiji mai cike da kwarjini da haiba a gabansu. Don haka aka kasa samun wadai zai fara kai dukan sai ma ƙus-ƙus da aka fara.
Da sauri Atika ta shigo gaba tana kiran Sunan Nanah cikin tashin hankali. Kallon ta yayi a tsanake kafin cikin kamewarsa ya buɗe baki cikin dakakkiyar muryarsa.
"Kin santa ne?.".....