Free chapter · Read without an account

PAGE 36-40

by SultyWrites · MATAR SADAM



Kusan 30mins ta dawo dakin seenah ta kalla dake kwance tana game tace aa seenah am lalle jiki yayi sauki .

tashi tayi zaune tana fadin alhamdulillah Kam naji sauki sosai whl 

mika mata ledar dake hannunta tayi tare da fadin "allah ya Kara sauki yanzu saiki dimanci shan ruwan Lipton akai akai hakan zai taimaka miki sosai 

Karbar ledar tayi tana tambayar "mai muka samu ne ?

" Gashinan bude ki gani mana ya Adnan ne da kwashe² wai kauye ya raka abokin sa shine aka hado su da wanna abun taura ne ko miye wai shi Bai iyaci ba shine yazo ya hadani da ita da abin kirki ne ai bazai nemeni ba .

wata shegiyar dariya seenah tasa ba shiri itama najwan ta kwashe da dariya tana fadin kingan ki ko kin farfado kuma zaki fara dazu ko hannu aka saka maki a baki baza ki ciza ba harda su sume sume .

" Naji ni karki damen tunda dai lpy ta samu ai sai a dora daga Inda aka tsaya bari ma ki gani in tashi in wanko wannan abin mu sha .

" Ku sha ke da wa mamana ? 

" Toh in dai ba aljanu ba najwa inaga ai mu biyu ne kawai dakin nan.

" ai kema kinsan da zan sha kafin na kawo maki sai na fara sha in ma kin samu na kawo ma kin kenan mikewa tayi tana fadin " oho kuma kin yiwa dan karamin kanki .

      Sai bayan an idar da sallar isha najwa tace kinga tashi mu sauka Kar a fara cigiyar mu

"ni whl kunya nake ji naj 

Dariya Najwa ta kwashe da ita harda buga kafa tace dadin ta mijin ki kika saukewa tsarabar

" Wace tsaraba ta fada ba tare data gane inda najwan ta dosa

" Heeee sannu tou baki ma san aikin da kikayi ba kenan , tho kin masa staining Kaya

Waro ido tayi da fadin "shikenan na shiga uku kowa kuma kallon da zai dinga min daban

Miqewa Najwa tayi tana cigaba da dariyar ta tace kema dai whl kawai ki waske abinki kowacce mace fa da kika gani a duniyar nan tana yi amma idan kikace wanna noke noken zakiyi to shine ma zakisa a fahimci wani abu dan haka muje kawai madam kiyi fuska abinki .

Tashi tayi ta bita suka fita a bakin step suka hadu Afnan tace yauwa najwa dama ku zanzo kira ku ake jira za'ayi dinner shine daddy yace in kiraku najwa ce tace eh ai gamu nan .

  Kowa na gidan ya hallara a dinning din su kawai suka rage seenah ce tace daddy baika da hutawa .

" barka dai mamanah ya jikin naki ? 

A Dan kunyace tace Alhamdulillah.

dagowa sadam yayi yana kallonta dariya maganar ta ta bashi wai baika sai kace irin wacce take koyon maganar nan murmushi yayi kawai ya maida kansa ga wayar dake hannun sa time to time yana satar kallon ta kasa² amma in ka kalleshi saika rantse da Allah hankalin sa duka na ga wayar da yake danna wa .

Nina tace baby ya jikin kasa tayi da kanta tana fadin naji sauki Nina .

" haka akeso ai Allah ya kara lpy kuma ku dinga kula banda ciye² cikin farin ciki ganin nina bata dago wancan zancen ba tace in sha allah zan kiyaye.

" to Ku zauna mana kwayiwa mutane tsaye aka umma ta fada tana watsa musu hararar tabe baki seenan tayi ta kalleta ta watsar cikin shagwaba tace Nina to ai yatsayemin kujeyay tawa ni a ina zan zauna.

" waye ne ?

A dan darare ta nuna emir tayi da hannu Wanda yayi kamar bai san mai ake ba.

" kai tashi ka basu wajen su koma can tare suke zama itada najwa, dagowa yayi yana fadin yanzu nina saboda allah baga wata kujerar can ba ita ta zauna mana sai lalle wadda nake Kai umma tayi charaf ta chafe da "to in ma banda rashin kunya emir bai girmeta bane in a haihuwar kaji ne ma ai ya haifi wanda suka fita amma tace saiya tashi ya bata guri saboda rashin da'a da tarbiyya kuma ace lalle abinda take so din zaayi.

   Ba karamin jin zafin maganar daddy da nina su kayi ba sai dai ba suce komai ba, to there biggest surprise kawai su kaga sadam din ya mike fuskar sa dauke da murmushin dashi kadai yasan ma'anar sa ya dubi seena yana fadin " zo ki zauna .

kallon sa tayi ta juya ta kalli umma zuciyar ta na zafi saboda maganar data gaya mata ta budi baki da niyyar magana dukda ba tayi niyyar cewa komai ba amma ganin su daddyn sunyi shuru yasa ita kuma ta kasa daurewa cikin sassarfa ya karasa gaban ta kaman zai ja kujerar ne ya zauna kasa kasa yace kikayi magana Allah sai na saka Miki hannu 

dan ja baya tayi kadan tana murguda masa baki ta sake Kallon umman tare da cizar lips din ta tana jin kamar ta rufe ta da duka sake maida kallon ta tayi ga sadam din lumshe idon sa yayi ya bude tare da jefa Mata kallon da saida ta hadiya wani yawu tana jin yan hanjinta na kadawa wuce wa tayi izuwa kujerar dan najwa har ta zauna .

kallon umma yayi suka hada Ido da sauri ta dauke kanta bacin ran daya kasa boyuwa kwance a fuskarta.

   Ana gamawa duk suka koma parlour aka zauna ana hira najwa tace emir ina tsarabar mu ?

" bankawo ba da sauri ta tashi daga kusa da seena ta koma kusa dashi tana fadin 
"Allah bazan yadda b kai fa kace wanna tafiyar zaka kawomin tsaraba tunda wancan baka kawo ba Adnan yace nima am min alqawarin takalmi daddy yace ni Kuma turare, dariya yasa " Kai daddy harda Kai toh kowa na kawo masa tsarabar sa saida safe zan bawa kowa nasa shikenan.

    Afnan ce ta wage baki da niyyar yin hamma ahhhhh faf sadam ya make bakin da sauri tasa hannunta ta rufe bakin idonta na kawo ruwa yace haka ake kawai ki wani wangale baki kamar kofar gari ke baki san manzan Allah (S.A.W) yace "idan hamma yazo ma dayan ku to yayi iya kokarin sa ya kawar da hamman, ya mayar dashi , saboda hamma daga shaidan ne" . 

Umma tace me haka wanna ai salon mugunta ne haka kawai Ka tashi Ka fasa Mata baki kallon umma yayi yace yanzu saboda Allah hajiya yara sunyi abu baza a gyara masu ba kuma ai bani na fadi ba in kuma kince ba haka bane toh ki duba sahih Muslim 2994.

"Tho tho dan masani Allah ya kawo mu kaifa Ka dawo Kenan zaka fara takura min yara murmushi yayi yace hajiya Kenan mutum da gidan ubansa ace bazai dawo ba kuma ya'yanki ai kanne na ne dasu da najwa duk daya suke a wurina yadda in Najwa tayi abu zan gwabeta ko na daketa haka su ma dole in naga sunyi ba daidai ba in gyara musu a matsayina na waliyyin su.

mikewa daddy yayi yana fadin ni dai saida safen ku zan hau sama inada ayyukan da zanyi emir idan Ka gama kazo kai da seenah kafin na shiga bacci ya amsa da tou daddy su najwa kuma suka bishi da good night!!.

  umma kuwa haushi ne ya kamata ganin daddy ya tashi ya shige wato da yake yau ya dawo dakin yar gwal shine zai wani fake da cewa aiki yake dashi wani tsaki taja, cikin dariya kasa² sadam yace sorry hajiya cikin hasala tace soron uwarka Kai Ka kiyayeni whl dan ni ba sa'ar wasan ka bace, kai gama ka raina kowa toh kaga wadda zaka zolaya nan bani ba sha sha shan yaro kawai ta karashe tana nuna nina da hannu tare da tashi ya kade zanin ta ta wuce bangaren ta.

Shi kuwa ko a jikinsa sai ma daga murya da yayi wurin fadin asuba ta gari hajiyar mu .

        Dakuwa Nina ta masa " wato emir ba zaka fasa jawomin abun magana ba ko, matar baban kace fa to whl ba ruwana kaci gaba Allah ya baka saa.

" to nina mai na mata kawai dan nace mata sorry , ba tare data sake magana ba ta tashi tabar parlourn itama.

     Ya rage daga adnan sadam seenah najwa nafisa sai Afnan, Adnan ne yace nikam Lolaki ba daddy bane yake kiran ku kike zaune harara ta maka masa 

" Allah ya adnan na gaya ma ban san wanna banzan sunan thom dariya yayi yana sake fadin wai lolakin ne bakyaso .

Ganin kallon da take aika Mata yasa Najwa kunshe dariyar ta tace wai ya Adnan Kai in mutum yace ma baya son abu kai kuma a lokacin ka samu abunyi Kenan .

"Tho al munafunfun kanwa uwar hadi tho ba da ita nake ba sai ki Kai gulmar taki wani wuri

itadai bata sake ce musu komai ba ta maida hankalinta kan Indian film din da akeyi Mai suna JUDWA 2 sosai take san film din saisa in dai taga shi akeyi to in ta zauna bata tashi sai an gama .

     Sadam ne ya mike tare da ajje tumbler din da ke hannun sa kan centre table ya nufi side din daddy da kallon gefen Ido seena tabi shi ai kuwa suna hada Ido da adnan ya kwashe da dariya najwa tace Kai kuma kalau kake cikin dariyar yace lpy ba lau ba.

dariyar da Afnan tasa ce ya sa su juyawa suna kallon ta kwashewa da dariya najwa tayi itama harda tafa hannu tashi seena tayi ganin an tafi talla ta kalle su tare da girgiza kai tace " gaskiya kuna bukatar check up whl dan inaga Kan wasu ya samu matsala Kar kuma a fara Kai duka .

Nafisa kuwa Ban da bin ta da harara ba abinda tayi tare da jan tsaki .

Da sallama ta shiga parlourn, daddy na zaune kan two seater sadam na gefen sa kan one seater, karasawa tayi kujerar da daddy ke zaune ta zauna tare da daura kanta a kafadar sa .

shafa kanta yayi yana murmushi yace maman daddy kin iso Kenan dama ke muke jira .

" ke tashi ki nemi waje ki zauna kika wani zo zaki sa kafadun sa suyi ciwo dan murguda masa baki tayi a fakaice tace to ina yuwanka zaro Ido yayi yace ni ? Kai din ta fada tana sake murguda baki tashi yayi ya nufo kujerar da suke kai da sauri ta tura kanta bayan daddy tana fadin wayyo daddy kaika bayi ya dakeni.

" whl kana tabata ina rama Mata koma ka zauna , kwafa yaja ya koma ya zauna.

mamana gyara zamanki magana nake son yi daku ba tare da ta dago ba tace Allah daddy duka na zaiyi mugu ne dazu ma ya fasawa Afnan baki .

" bazai dake ki ba ai na masa magana leqo da kanta tayi kadan sai kuma ta tashi ta gyara zamanta tare da fakaitar Idon daddy ta masa gwalo murmushi yayi kawai ya dauke kansa .
    
       Daddy ne ya fara fadin "da farko dai zan fara da neman afuwar Ka sadam akan wani abu da nayi ba tare da jin raayin kaba ko neman shawarar ka da sauri sadam ya tare shi da cewa
"haba daddy nifa danka ne bai kamata kana neman afuwa taba ai saboda kana da iko dani ne yasa kayi hakan kuma na san baza ka taba yin wani abu da zan cutu ba, murmushi daddy yayi yana kallon dan nasa cike da so da kauna sai sa yakejin sadam a zuciyar sa fiye da sauran ya'yansa ( wato lafazi ma mai dadi wani abu ne) .

Hakika sadam naji dadin wanna furuci naka gareni har bansan yadda zan misalta maka ba Allah ya maka Albarka ya haskaka rayuwarka Allah ya jibanci lamuran Ka , wato abinda ya faru shine ............ Kaf daddy ya kwashe komai ya fadawa sadam sannan ya dora da fadin dan Allah sadam ka riqe amanar seenah ka rungumi wanna auran naku da hannun biyu , haseena yarinya ce karama dole saika hada da hakuri , kuma auran ka da ita ba saki mutu ka raba kar naji Kar na gani nasan kuma Kai mai biyayya ne a gareni tun kana yaro ina da tabbacin baza Ka bani kunya ba,  a yanzu ba lalle Ka gane abinda nayi ba amma nan gaba kadan zaka san cewa gata na Maka in sha allah in dai kayi hakuri zakaga ribar biyayya, juyawa yayi ga seenah yace mamana wannan shine sadam yayanku kuma mijinki banda rashin kunya kada ki ga ko dan kina nan gida gaban mu ne kice komai zaki masa a a duk suna daya zai amsa na mijinki a yanzu da kuke gaban mu da kuma lokacin da zaki koma gidan sa Yana da iko dake a yanzu fiyeda kowa ki zama mai biyayya a gareshi kinji yar Albarka kanta a kasa tana Wasa da hannunta tace toh daddy in sha allah bazan yi abinda ranka zai baci ba.

Nina ce ta shigo parlourn hannun ta dauke da wani madaidaicin tray dakin daddy ta wuce ba jimawa ta fito ta nemi waje ta zauna mikewa daddyn yayi yace toh ni zan shiga daga ciki allah ya bamu alheri a tare seenah da sadam suka ce allah ya tashe mu...shuru seenah tayi tabar shi ya karasa sannan ta sake cewa have a pleasant night daddy harara sadam ya wurga Mata yana jan kwafa.

     Daddy na shigewa sadam ya sauko kasa wajen kafar nina cikin wani irin yanayi ya fara magana kamar zaiyi kuka " yanzu nina saboda Allah abinda akamin an min adalci Kenan wanna wani irin abu ne wai ni akayi wa aure sai kace a film ba shiri ba komai kuma ma arasa wadda za'a aura min sai wancan yar ficiciyar yarinyar sa'ar karamar kanwata in kaita ina kenan yanzu kawai sai mutane suji nayi aure in akace ina matar sai kawai nace wannan yarinyar ce Matata in auren ake so nayi a barni in kawo wadda nake so da kaina mana ko kuma a nema min daidai dani kawai dai salon asa yara su raina mutum wanna ai abun kunya ne.

"eh lalle ma emir wato da yake nika raina shine zaka zo ka tisani gaba Kana min korafi ina nan uban naka ya shige daki uffan baka ce ba hadda masa saida safe to ai bani zaka samu Ka fadawa wanna maganganun naka ba sai kaje kasamu shi mahaifin naka wanda ya dauro ma auren , sai shegen san girma kaman gyambo kuma da kake ta wannan maganganun wa yace maka yanzu za'a baka ita ai sai ta gama secondary school tukunna za'ayi bikin in kaga dama a lokacin ka sanar da mutanan naka in kaga dama ka barsu wanna ruwanka ne dan haka Allah ya tashemu da alheri tashi kaje Ka kwanta saida safe.

Tashi yayi yana fadin saida safe ya fice yanajin duk ransa ba dadi zuciyar sa na zafin da ya rasa dalilin hakan shi dai yasan daga zancen auren da daddy ya masa ne ya tsinci kansa cikin wanna yanayin da wannan zancen zucin ya isa part din su, yana shiga karamin parlourn su ya zube nan kasan tiles din yana ci gaba da tunane² da shi kansa be san na miye ba.

Nina kuwa da murmushi ta bishi tare da dan girgiza Kanta ta maida kallonta ga seenah wacce tayi shuru tana sauraran su, tasowa tayi ta dawo kusa da ita ta zauna tana fadin baby kin fara jin bacci ne murmushi tayi tace
"eh nina 

"to shikenan tashi kije ki kwanta Allah ya tashemu lpy da ameen ta answer tana mikewa ta fice .

Da kallo ta bita tana kara jin kaunarta a ranta a fili tace in sha allah sadam sai kayi alfahri da wanna auran.

     Ko da ta dawo parlourn bata samu kowa ba sai nafisa dake kwance akan doguwar kujera tana faman danne²a waya duba takai Kan agogon bangon dake manne a parlourn 10:03 tagani zama tayi dan cigaba da kallon sai dai bata fi 5 mins ba taji kallon ma ya gundure ta , tashi tayi da nufin barin parlourn ta tsinci muryar nafisa na cewa ke mikomin ruwa banza tayi da ita kamar bata jita ba taci gaba da tafiyar ta "keeee!! ta daka Mata tsawa ina magana kina tafiya saboda kece rasa kunya beran tanka juyowa tayi tare da watsa mata wani kallon banza tace ai kin san sunana dan bada ke aka rada min suna ba kuma da kike wani cewa kina magana ina magana wace ke ta dan dakata tare da tabe baki sannan ta ci gaba "mutum ce ke kamar ni kamar kowa dan haka ni ba najwa bace saiki dinga daukan kanki kamar wata uwar mu abinda baifi shekaru biyar zuwa shida bane tsakanin mu, kina da kafa ina da kafa dan haka idan kin matsu kina iya tashi kije ki dauko ruwan idan kuma baki Matsu ba kijira sai ruwan yazo ya sameki da kansa tana gama fadar haka tayi gaba tabar nafisa da tada jijiyoyin wuya sai faman zazzaga ruwan masifa take ita kadai .

Tana shiga dakin su ta hango najwa kan gado tana kallo har tayi shirin bacci , key ta sawa kofar ta karasa gaban wardrobe ta sauya kayan jikinta zuwa na bacci sannan ta wuce toilet , saida ta gama duk wani night routine dinta sannan ta hawo gadon tana warce tab din daga hannun najwa, tashi tayi ta zauna tana fadin kinsan mai odahalf ni wlh har na matsu mu shiga SS2 din nan ko daddy ya saya mana waya nagaji da wannan tab din da sai dai kayi game kawai yan class din mu har dariya suke min in nace bani da waya abun kunya whl.

" hmmmm toh allah ya kaimu lokacin 

"wai keda waye ne naga tunda kika shigo kaman ranki a bace .

" barni kawai naj ni da ya nafisa ne mana wai ni zata kira da ke sannan tace na miko mata ruwa tsabar ikon mulkin mallaka shine ni kuma na nuna mata bafa tsoron ta ake jiba gwara ma ta sani karta ga ba'a tanka mata ta dauka ko shakkar ta ake shuru² fah ba tsoro bane iya taku ne ah toh .

Kara najwa tayi tana tafa hannu "kaii amma whl kinyi bala'in birgeni odahalf amma gsky nayi missing ina ma banyi saurin shigowa, " dariya tayi tana fadin " kin cika gulma wlh .

" ke bari da a baka labari gwara ka bayar

" sannu toh yar jarida .

Kamar wadda aka tsikara tace yauwaaa baki bani labarin abinda ya faru ba.

" a ina kuma ?

  "da daddy ya kiraku mana ke da emir.

tabe baki tayi tace " toh gulma wuya ba abinda akayi

" Kar muyi haka mana dan Allah shakamin inji .

kwanciya tayi tare da janyo tab din, da sauri najwa ta warce tana fadin bansan wulakanci fa ni in baza ki fadamin ba in sani basai kin ja min aji ba.

cikin wani cool voice tace naj!!!! Plz mubar maganar nan, jikin najwan ne yayi sanyi tace odahalf wani abun ne ya faru dan Allah ki fada min kona samu peace of mind wanna yanayin naki ya nuna min akwai wani abu deep down.

biting lips dinta ta shiga yi ba tare data kalli najwan ba ta fara bata labarin abinda ya faru ba tare data boye mata ko daidai da kalma daya ba .

sosai najwa taga rashin kyautawar yayan nata wanna ai cin fuskane ya bari sai ta tashi mana amma a fili sai ta sakar mata murmushi tana fadin ke yanzu odahalf akan wanna har zaki wani damu , komai fa lokacine kuma ina mai tabbatar maki ya sadam will regret his words to you sai ya fito ya nunawa duniya ke a matsayin matar sa yana Mai proud da hakan karki ji komai kuma ki nuna ma baki san da zaman sa cikin gidan nan ba , wata yar gajeriyar dariya tayi tace thank you tawan Allah ya barmin ke.

wata hirar najwa ta dauko har saida taga seenan ta saki jiki sannan sukayi addu a suka kwanta.

Washe gari kuwa seenah bacci tayi sosai dan har najwa ta tashi tayi wanka ta shirya ta fice a dakin bata sani ba, saida najwan taga kowa ya fara fitowa ana shirin yin breakfast sannan taje ta taso ta dakyar harda su fada tukun ta tashi ta shige bathroom din, a gaggauce tayi wankan saboda yadda najwa ke azalzalarta akan tayi sauri.
       
      shiryawa tayi cikin armless gown English wear black mai dauke da stones golden daga gaban rigar sannan ta yafa dan karamin dark blue veil ta zura bedroom slippers dinta ta fara fesa turare da sauri najwa ta warce kwalbar tana fadin wai ke idan kika rike turare sai kinga bayansa ne hankalin ki zai kwanta duk kin kusa gamawa da turarukan nan .

Bata ce komai ba tayi waje biyo ta najwan tayi da gudu itama ta Kara a guje a haka suka isa dinning din suna dariya.

      Sun tarar da daddy harya gama abinda zaiyi ya wuce office kasancewar yanada meeting kafin a tafi masallaci da yake Friday short day ne .

zama sukayi suna gaishe da nina da umma sai najwa data gaishe da sadam ya amsa Mata ba yabo ba fallasa, ita kuwa seenah juyawa tayi wajen adnan suna magana kasa² , wani abu sadam yaji ya tokare masa a kirji shi fa abinda yake gudu kenan gashi tun daga yanzu raini ya fara shiga tsakani ko ta gaishe shi instead ma sai tayi kamar bata san da zubin sa awajen ba .

kasa² yake kallon su ji yayi gaba daya abincin ya fita a kansa amma kuma ya kasa tashi sai faman juya spoon yake a plate .

      Nafisa ce ta fara tashi tana fadin umma barin je in shirya yau inason zuwa gidan su sadiqa .

"nima zani ya nafisa Afnan ta fada tana mikewa, umman ce tace ohk idan zaku wuce kimin magana na baki sako ki kaiwa aunty surayya da toh suka answer suna barin dinning din.

     Kusan a tare umma da nina suka tashi suma , Adnan ne yace nima barin zo na wuce , seena tayi saurin cewa "ya Adnan ina zaka kuma?

" zan shiga campus ne akwai wani paper da zamuyi submitting kin san yan final year sai a hankali , dariya najwa tayi tana fadin " ko ba final year ba .

" oho miki dai amma ko banza nafi yar ss 1.

" eh anji bakomai there's time muma ai kamar yau ne in Allah ya yarda .

" Toh wai ya adnan alqawarin namu fa , 

" ummmm kinga seenah ki bari inna dawo ma yi magana .

"to please kaika dade, murmushi yayi yace "ke dai idan aka fada maki abu an shiga uku.

najwa tace " wai me ake kullawa ne bani , juyowa tayi karaf suka hada Ido da sadam dauke kanta tayi tana fadin " sai kinji ne nifa ban san shishiginarity .

" au yau ni din odahalf ba komai ai zamu gani .

shi dai Adnan tashi yayi yana fadin "bros barin dan shiga school amma ba dade wa zanyi ba, ba tare daya kalleshi ba yace adawo lpy.

      


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol