Free chapter · Read without an account
Chapter 5
RIYANN
Love and sexy story
Free page
Page 6
___________Ko da ta shiga kowa ya yi bacci, Salame na ɗakinta, saboda haka, kai tsaye ɗakin ta shiga, ta samu kujera ta yi zauna kusa ga katifar Salame kana ta sa ƙafa ta zungure ta bata tashi ba saboda Salame akwai nauyin bacci, saboda haka ta saka kyalle ta ɗaure mata baki, kana ta lafita mata ice, haukace Salmae ta falka, zata zunduma da gudu,
amma Riyann ta sa ƙafa ta bigita ta faɗi tim, janyo ta tayi, ta zaunar, kana ta ce "Ke bil Adama idan kika kuskuren ki ka matsa da ga wurin nan sai mun ba Dodo jininki, ya shanye." cikin azaba Salame ta ɗaga kai babu bakin magana, kana Riyann ta kunna fitalar da ke ɗakin, nan Salame ta saki fitsari, saboda sam bata gane Riyann ba ce, saboda gashin da ya rufe mata fuska, nan Riyann ta shaga suburbuɗar Salame sai birgima ta ke ƙasa babu bakin magana,
nan da nan fatarta ta farfashe saboda mugunta Riyann ta saka ma ta garin yaji, ga jiki, suma ne kawai Salame batayi ba saboda azaba, tayi fitsari batasan adadi ba,
cikin murya mai ban tsoro Riyann ta ce "idan ki ka kuskura ki ke koma haɗa muna goɗiya da Aljanu sai mun kawar da ke, ke ji abinda muka faɗa ko ya ya.?" Nan ma gyaɗa kai ta yi, kana Riyann ta kai mata naushe ga baki, sai da hancinta ya fashe, da jini, kana ta fita,
ta koma gida ta na fita Salame ta banye ɗaurin da Riyann ta yi mata ga baki, ta kurma ihun azaba ta fito da gudu ta na kiran "Nashiga uku Inna! Inna! Aljana zata kasheni!." Da gudu Inna ta fito da zane ga hannu, sai ga Malam Kabiru Baban Salame shima ya fito,
suka yi kan ƴarsu, dai-dai lokacin aka maida wutar nefa, salati suka shiga yi ganin yadda jikin Salame ya kumbure abinka ga farar fata, duk ta yi ja saboda azaba, Inna ta ce "Malam kamar garin barkono nike gani ga jikinta." Taɓawa ya yi kana ya ce "Shine fa ba kama ba ce,
Salame wai waye ya yi miki wannan ɗayan aikin, cikin kuka ta ce "Aljana ce Baba baka ganta ba gwanin ban tsoro gashi duk ya rufe mata fuska, ga baƙar riga ko ƙafafuwanta baka gani da hannuwanta." Inna ta ce "To Wai mekika yi mata.?" "Wai saboda na ce ma Riyann bata haɗa zuri'a da su ba, saboda abinda ta keyi." Nan ta kwashe komai ta faɗa mu su,
Malam Kabiru ya ce "Ko dai Aljana ko ita Riyann ɗin ba saboda komai zata iya yi." Fita ya yi zuwa gidansu Riyann, nan ya shiga bubbuga gida, Baffa ne ya taso cikin yanayin bacci ya buɗe gidan ganin Malam Kabiru ya ce "Malam Kabiru lafiya kuwa cikin daren nan.?"
"Ina fa lafiya Riyann na nan.?" Eh ta na ciki." Kotsa kai ya yi cikin gidan Baffa na bayansa cike da mamaki, ɗakinta Baffa ya nuna mai, ya shiga kwance ya ganta ta watse ƙafafuwanta, sai sharar bacci ta ke yi, sanye da riga da wando na bacci, ga alama ta jima da bacci,
sakin labulen ya yi, ya na cewa "Tabbas Aljana ce ta dake Salame ba Riyann ɓace.". Baffa ne cikin rashin fahimta, ya ce "Malam Kabiru ban gane abinda ka ke nufi ba me ya faru." Nan ya faɗa mai duk abinda Salame ta gaya mai, Salati ya saka lokacin Umma ta fito zata shiga bayi, taji abinda suke magana akai,
"Baffan Riyann ya kamata ka ɗauki mataki fa kar Aljanu su haukata ma ƴa." "Haka ne Malam Kabiru zuwa da safe zamuyi magana." Ya raka shi kana ya rufe gida, Umma dai batace komai ba ta koma ta kwanta saboda tasan da Riyann na da Aljanu da ta gane, kwai itace Aljanar kanta, sune basu gane ba,
sai da Inna ta yi Salame wanka da ruwan sanyi, kana aka bata maganin ciyon jiki ta kwanta,. washegari da safe,bayan sun gama karin kumallo, safe, Baffa ya kalle Riyann ya ce "Mamana." "Na'am Baffana." "Don Allah mekikayi ma Salame.?" Mai da mai da tambayar ta yi "Wani abu ne ya sameta.?" "Eh juya da daddare Babanta ya zo nemanki."
Nan ya kwashe komai ya faɗa mata, ita dariya Baffa ya bata da ya ke cewa ta ba Aljanunta haƙuri, don Allah karsu koma taɓa kowa, sai cewa ta yi to, kana ya fita kasuwa, Umma ta kalli Riyann ta ce "Takwarata don Allah kedena wannan abin nasan fa kece ki ka yi ma Salame dukan tsiya ki ka bata tsoro, haka mukayi da ke ba cewa ki kayi ke dena rashin ji ba.?"
Ɗan susa kai tayi saboda tasan Umma ta san halinta sarai fiye da haka ma zata aikata, toro ɗan ƙaramin bakinta ta yi gaba ta na faɗin "Umma ita fa ta haɗa ni da Aljanu shine na gwada mata, zahiri." "Haba Aminatu na ai yanzu ke wuce wannan ke da za ki tafi birni kizama ƴar boko, ga mijinki Naufal, ɗan gayu." Wani murmushin ta yi kana ta ce "Shikenan Umma zan dena."
"Yauwa ƴar Umma ta shi na aike ki gidansu, ƙawarki, Saude." To kawai ta ce kana ta saka jikan ɗin ta ya sha guga, saboda Riyann akwai tsafta sam bata da ƙazanta, shiyasa bata abota da ƙazamai, su Saude ne kawai abokanta, saboda su na da tsafta, ƴan matan ƙauyen da Samari su na sun ƙulla alaƙa da Riyann amma sam basu samu fuska ba,
sai Ilolo saboda shima ɗan gayu ne, kaf ƙauyen, shine ɗan wanka, hhhhhh to ta haka ne ya samu shiga wurin Riyann, zahirin gaskiya Riyann saboda gayunsa kawai ta ke son sa, Umma ce ta bata wasu kuɗaɗe ta ce ta kaima Babar Saude, anjima zata zo suyi magana, ta amsa ta fita, a hanya ne ta haɗu da Ilolo,
ya na ganinta ya canza tafiya sai da ya ƙaraso kusa da ita kana ya ce "My Riyanncy ina zuwa haka.?" Duk lokacin da Ilolo ya kirata da wannan suna bakarin daɗi ta ke ji ba, murmushi ta yi mai kana ta ce"Umma ta aikeni, gidansu Saude."
Writes by pinky Darling 👄
~Matar Jay~