Free chapter 路 Read without an account

Chapter 12

by ZAHRAA 路 Bayan Murmushi

Page 12馃挰鈱笍


 Bazan sami zuwa bikin Adda ba mamma bata da lfy ,nida sisters dina  zamu tafi Cairo gobe inshaAllah ,Muna dawowa Zan shigo abuja .nayiwa baba magana shima yace Muna dawowa zai tura maganar sa rana inshaAllah,message din da  farooq ya tura min kenan ta WhatsApp 

Voice note na masa Ina yi wa mamma Addua tare da fatan Allah ya bata lfy  na jaddada ina nan Ina jiransa.


Zaune yake  gefen gado sanye da cotton Kayan bacci sunyi luff a jikinsa yana sanye da medicated glass yana dube dube a laptop.sai kofin shayi a gefe,hanadi ce ta shigo tare da kwanciya a gefen sa ,Kallonsa tayi cike da soyayyah wato Ak zuma ne sai da wuta Yau kwana 4kenan basa magana ,idan  ta biye masa sai suyi wata a haka .darling har yanzu fushi kake dani?tana fada cike da shagwaba .Kallon ta yayi baice komai ba .Ka fahimce ni darling Sabida tarbiyar yaranmu nake gujewa zaman USA,Kaga mata ne duk tarbiyar da zamu basu suna fita zaa su hadu da yaran turawa a Rusa Musu tarbiya,kana ganin dawowar mu Nigeria kusan wata shida kenan amma har yanzu Kausar dabiar turawa take,bata son sallah ,bata son daura dankwali ,idan da a Nigeria ta taso na tabbata bazan sha wuya Kamar yanzu ba,darling Kausar bata da kunya kasani ,Ka Tina sanda muka mata Birthday din 8 years?daga na mata fada ta Kira min police Wai nayi harassing dinta ,Tinda ga lokacin na gane zamaan USA ba namu bane. kina nufin Nima ban da tarbiya kenan ?dan Kinfi kowa sanin rabin rayuwata a Chan nayi AK ya fada yana mai tsare hanadi da ido ,Aa darling zamanin ku ba daya bane  dana yanzu ,Ka fahimce ni dan Allah.kar ki damu na fahimta ya fada tare da ajiye laptop din a gefen sa ,yana janyo ta jikinsa .ajiyar zuciya hanadi ta sauke Nagode darling ,yanzu Yaushe zaka dawo Nigerian gaba daya ?Kina tunanin Zan iya zaman kasar nan ne?ay ni da Nigeria sai dai ziyara duk sanda na Sami time Zan dinga leko ki kuma Gasu yaya safiya da ramla duk suna abuja ,zasuyi keeping dinki company .to Darling Nagode da fahimta 


Abdulkadir Tahir tambuwal (AK) shine na 3 a gidansu ,yana da yayye mata biyu Safiyya da ramla  da kanne biyu  Abdulkarim ,da fadila autarsu .an haife shi a garin sokoto inda ya fara primary a Chan ,Bayan ya gama primary alhaji Tahir ya zama ambassador Nigeria to USA Sun tare a garin Massachusetts

 Inda ya fara Milton academy. Bayan ya gama zai shiga senior high school ,transfer din alhaji Tahir zuwa wata kasar ta fito haka yayi declining a cewarsa Sabida karatun yara ,kuma yanzu Sun riga Sun Saba da USA .


Sunzo hutu Nigeria idan suka sauka a gidansu na abuja ,idan an kwana biyu zasu qarasa sokoto .

 Hanadi saar Abdulkarim ne Wanda yake bin AK ,alhaji Tahir WA ne ga mahaifin hanadi uwarsu daya ubansu daya.mahaifiyar hanadi buzuwa ce daga nijar,hanadi kadai Allah ya mallaka masu shiyasa ta taso cikin soyayyah da gata.


Shigowa falon akayi a guje oyoyoyo nayi missing dinku hanadi ta fada tare da rungume yaya ramla Dama sunfi shiri .Nima nayi missing dinki hanadi .biggi kar ki karya yaya ramla mana cewar Abdulkarim yana mata gwalo ,Allah ya isa idan Ka qare ce min biggi ,ta fada Tana hararar sa, hanadi irin yaran nan ne masu kiba ,fara ce tas  dan har wani yellow yellow take ,Tana da dogon gashi irin na buzaye.sai a sanann ta jiyo yaya AK Ina yini ,sai yanzu kika ganni kenan ?kayi hakuri wannan rabbit teeth  din ne ya dauke min hankali ,wallahi biggi Indai biki Dena ce min rabbit teeth ba har abada bazan Dena ce miki biggi ba cewar Abdulkarim ,mommy ce ta sauko ,to mage da bera kun fara halin ko?sai kace masu ganin hanjin juna .


Sun kuma Massachusetts cike da kewan yan sokoto Wanda AK Allah Allah yake su bar Nigeria ,inda ya fara karatu a Harvard university tare da yaya ramla Wanda already yaya safiyya na gaba dasu .


Innallahi wa innaillahi rajiuun kalmar da AK yaji alhaji Tahir na maimaita wa kenan a waya.dawowar su daga school kenan ,daddy menene me ya faru?cewar ramla a rude suleiman ne da hafsou plane crash ya rutse dasu ,ya fada yana hawaye ,ba Wanda ya fado a rain AK irin hanadi rasa iyaye biyu a lokaci daya babban tashin hankaline,book a flight to Nigeria muryar daddy ne dawo dashi hayyacinsa ,Abdulkadir kai da ramla da safiya zaku zauna  nida Abdulkarim  ,fadila momynku zamu tafi Tinda exams kuke .


Bayan murmushi 

XahraB(Mrs )

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol