Free chapter · Read without an account

17

by Rufaida Umar · ALWASHI 2

ALWASHI

   42

©Rufaida Umar

Adam kuwa a daren ya farfaɗo sai dai ba su sallame shi ba sai a washegari. Tun dawowarsa kuwa babu wanda ya cewa uffan cikinsu.  Shirunsa ya basu tsoro don har suka soma tunanin ko binciken ƙwaƙwalwa za'a yi masa. A nasa ɓangaren ko bai gama yanke matakin da ya dace ya ɗauka ba ne. Idan tunaninsa ya ba shi cewa ya je kawai ya tattara komatsansa ya shiga duniya neman Kubra, sai wata zuciyar ta kwaɓe shi, yakan ji kamar idan ya je ya binciko ta, to ƙarshen kashe ta wancan azzalumin zai yi. Duk da irin ɓoyon da yake yi, ko bai ci nasarar ganin fuskarsa ta yanzun ba, to ya taɓa ganin hotonsa a wurin Kubra. Bai san muryarsa ba, amma jikinsa na ba sa cewa shi ne Affan, don haka tabbas zai bibiye shi ya ga ko zai ga Kubra. A ganinsa neman Kubrar a wannan takin kamar jefa rayuwarta da na yaransa a hatsari ne, idan har binciken zai yi, sai dai ya saka wani daban, kuma ya yi komai a sirrance. Da haka ya ajiye komai gefe, sai dai kukan zuci kawai. 

***
 KATSINA...

A ɓangaren Nihla kuwa, tun ba ta ƙarasa kaiwa ɓangaren iyayenta ba ta sauya shawara baki ɗaya, tunanin da ta yi bai wuce na abinda zai je ya zo ba. Ba ta manta cewa Daddy Affan ya buga mata gargaɗi game da ɗaukar wani mataki kan alaƙarta da Areef ba ba tare da saninsa ba. Tsoron zuwa ta kai ƙarar Areef ta hana ta abinda ta yi niyya, ita kam ta sani faɗar ma ba zai jawo Areef ya ƙaunace ta ba sai dai ya ƙara tsanarta. Kawai sai ta zagaya cikin garden ɗin gidan ta yi zamanta ta ci kuka sosai ta share hawayen sannan ta koma ɓangaren Mami. Ta ci sa'a Mamin ba ta falon, don haka ta shige ɗakin ba ta kula Benazir da Afrah ba. Ta yi nadamar yanda ta tunkari Areef ta kasa ɓoye sirrin zuciyarta. Tsoronta bai wuce matakin da zai biyo baya ba.


  KANO

Tun a daren Laila ta samu saƙon Areef na zuwan da zai yi don su gaisa. A lokacin tsaki kawai ta ja, za ta so zuwan nasa domin ta ji dalilin da ya sa ya aikomata wasu tarkacensa sai ka ce an faɗamasa ba ta da suturun sakawa. Don haka a washegari ta tashi da shirin tarbarsa duk domin kawar da hankalin mutan gidan kada su kawo wani abu a rai. Yanda Haseenah ke faɗi tashin ba ta shawarar me ya kamata ta dafa da kuma kokarin taimaka mata da wasu abubuwan hakan sai ya sa ta ji dadi, ta ji inama auren soyayya ne za ta yi da irin farin cikin da za ta yi a jituwarnan da suke yi sai ya fi haka. 

***
Areef kuwa, tun misalin sha biyu da mintuna suka iso garin Kano shi da Fareed. Kai tsaye gidan Haj Falmata (Dada) suka yada zango. Babban gida kuma tsararre na Tsohon Sanata Alh Zubairu Ahmad. Da fara'arta ta tarbe su, duk da cewa ba su sanar da ita suna hanya ba, amma irin tarbar da aka musu na abubuwan ci da sha kai ka ce dama can an san da zuwan nasu. Yaranta mata biyar duk suna gidajen aurensu. Sai yaran ƴan uwa har huɗu da take riƙo. Uku daga dangin mijin nata, biyu kuwa daga can Katsina. 
  Sai bayan sun ɗan huta ne take mishi batun Laila. 

"Ai na ji daɗi sosai da aka ce min har biyu ras za ka yi, Allah ya ba ka ikon yin adalci tsakaninsu, ya kara horewa."

"Amin Dada, ai za ta shigo ma ku gaisa in sha Allah." Faɗin Areef din kenan yana ɗan murmushi. Itama Haj Falmata da har lokacin fuskarta a sake ta amsa.

"Masha Allahu, haka nake son ji. Ka ce nan kusa da mu take ko?"

"Eh."

Ta ƙara jinjina kai. 

"Masha Allah, Allah ya tabbatar mana."

Suka ƙara amsawa da amin, suna cikin hira wayar Areef ta yi ƙarar shigowar saƙo. Koda ya karanta kawai sai ya dubi Fareed. 

"Ya kamata mu je ko?" 

"Ina kuma? Tun yanzu?"

Faɗin Haj Falmata ba tare da ta jira cewar Fareed ba wanda ya hangame baki. 

"No Dada, wani abu ne ya taso game da kamfanin da muke kokarin buɗewa a nan. Ba wai can muka nufa tun yanzu ba."

"Toh na fahimta, Allah ya tsare. Sai kun dawo."

Suka amsa sannan suka fito. A mota Fareed ya dubi Areef wanda yasa waya a kunne yana tuƙi da hannu ɗaya.

"Ina zamu je?" 

Areef ya ɗan dube shi, bai kai ga amsa mishi ba ya maida hankali kan wayar da ya kira aka ɗaga daga can. 

"Ma'aruf, ina jinka."

Motar ta yi shiru, Fareed bai ƙara cewa uffan ba kawai yana kula da map din da Areef ya kunna bayan kashe wayar ya saita yana bi. A haka har suka iso wani gida, bai manta abin da Ma'aruf yace ba don haka ya tsaya nesa kaɗan da gidan. Kallon gidan kawai yake yi Fareed abin ya ɗan ba shi haushi ya dube shi. 

"Wai duk wannan tafiyar da muka yi, dama ƙarshenta don ka zo nan ne? Me ka zo gani toh?"

Areef ya dube shi gami da sauke ajiyar zuciya sannan ya mayar da hankali ga gidan. 

"Sorry, idan ba ka manta ba, na ba ka labari cewa na saka detective bibiyar duk wani motsin Daddy Affan, tun bayan zuwansa ƙasar nan ya fara gudanar min da bincike da sa ido a kansa. Dalili kuma bai wuce rashin yarda da shi da na yi ba tun haɗuwarmu a can abroad. A wannan gidan Ma'aruf ya tabbatar min akwai wani sirri da Daddyn ke ɓoyewa. Na farko dai ya biyo shi zuwa gidan, sannan koda ya shiga bai jima ba ya fice. A yanda Ma'aruf yace, mazauna gidan ƙabilu ne kuma ba ya tunanin ma musulmai ne. Ya cemin a daren dai ya ƙara zuwa gidan bayan mun yi waya da shi na ce masa ya je ya bincika unguwar ko zai ƙara samun wasu bayanai a kansu. A nan ne ya ga mota ta fito ta bar layin a guje. Shi ma kuma ya taka tasa motar ya bi bayansu. Doguwar tafiya aka yi har aka fita daga Kano aka keta ƙauyuka da garuruwa a ƙarshe suka yada zango a wani ƙauyen garin Yobe. Nan ne kuma ya ga sun fiddo wani mutum sun yar a wurin sun tafi. Ya ji tsoron zuwa wurin gudun me zai je ya zo don haka ya bar wajen. Koda gari ya waye muka yi waya ya sanar da ni, na ba sa umarnin ya yi gaggawar zuwa don ya ga waye mutumin da ya gani, sannan inda hali ya taimaka mishi ko Allah zai sa mu san wani abu game da Daddy Affan ta bakinsa. Sai dai koda ya koma ya iske wasu mutan ƙauyen sun sanya mutumin a mota suna shirin barin wajen. Haka ya bi bayansu har cikin gari, kai a ƙarshe har bayan napep ɗin da mutumin ya hau ta ƙarasa da shi wata unguwa sai da ya bi. Ya kuma ga gidan da mutumin ya shiga. Sai dai ban ba sa iznin tunkarar mutumin ba karo na biyu tunda ba mu san waye ba, ba mu san kuma kallon da zai mana ba. Amma jikina yana ba ni cewa Daddy Affan ba a banza ba ya riƙe mutumin nan, Ma'aruf ya tabbatar min cewa akwai alamun tsufa ko makanta ko ma dai wahala tattare da mutumin. Ina son faɗaɗa bincike, domin wannan ne gidan da lamarin ya faru. Ina son sanin ko su waye a gidan, wane aiki ne ya haɗa su da Daddy Affan. Duka ina son bincikowa."

A nan ne Areef ya dubi Fareed wanda ke sauraronsa, sai lokacin ya samu damar magana bayan shi ma ya bi danƙareran gidan da kallo. 

"Amma kuma duka mene ne namu a ciki?  Na ga mutumin nan babu abinda muka haɗa da shi face kawai abotar da suke da iyayenmu. Don rashin yarda, ni kaina ban yarda da yanayin mu'amalarsa ba, amma kuma tunda har ba surukata za'a haɗa da shi ko wani business ba, ba na tunanin duk waɗannan abubuwan suna da wani muhimmanci." 

Ɗan murmushi Areef ya yi, ya ɗan dubi Fareed, ya buɗe baki zai ce wani abu sai kuma ya fasa. Kauda fuska ya yi. 

"Duk abin da nake yi, akwai dalili ƙaƙƙarfa Fareed, ba za ka gane ba a yanzu, a gaba komai zai fito a gabanka."

"Ka fahimtar da ni, yaushe muka soma yiwa juna ɓoye-ɓoye? Tun alaƙarku da Laila?" 

Ya ƙarashe yana ɗan ɗaga masa gira a yanayi na rashin walwala. 

Areef dai bai ce uffan ba sai jan motarsa da ya yi suka bar unguwar. 

***
 Sai bayan sallar la'asar Laila ta ji shigowar saƙon Areef cewa yana hanyar zuwa gidansu. Guntun tsaki ta ja ta miƙe don dama baccinta ta sha, kiran sallah ne ya tayar da ita ta yi sallar. Ita kaɗai ce a ɗakin, kamar kada ta yi wata kwalliya haka ta ji, tun bayan azahar suka kammala girke-girken tarbar Areef ita da Haseenah. Har abinda ba ta yi niyyar yi ba sai da Haseenah ta saka ta yi ɗin, a dole ta biye mata gudun kar ta gano wata matsalar. 

 Kayan jikinta ta sauya bayan ta ƙara wanke fuskarta da face wash ɗinta mai ƙamshin lemon. A dole ta saka emblished holland gold atamfar da Haseenah ta zaɓo mata cikin saitin kayan sallarsu. Wani sky blue ne da ratsin  peach da black a jiki, sai ƙyalli yake. Ya karɓi fatarta sosai, ta shafa hodarta har da jan janbakinta sai kwalli da ta zirara a ƙasan fararen ƙwayoyin idanunta. Wannan ne karon farko da ta yi kwalliya a zuwan Areef, ba kuma dominsa ba, sai domin ƴan gidansu da gujewa duk wata ƙofar da za'a zargi alaƙarsu. Ta ɗauko peach ɗin  mayafinta medium size mai adon stones ta yafa. Yanayin yanda ta murza ɗaurin ɗankwalin har zuwa goshinta ba ƙaramin kyau ya yi mata ba. Tun tana shirin ta ji wayarta na ringing, ganin sunan Areef ya sa ta fahimci ya ƙaraso, sai ko ƙarar buɗe ƙaton ƙyauren gidan da ta ji Maigadinsu ya yi. Turare ta fesa kafin ta fito zuwa falonsu. Nan ta iske Haseenah da wata ƙawarta wacce ko zuwanta ma ba ta ji ba, suna zaune sun saka farantin wainar fulawa a gaba suna ci suna hira. Ganinta ya sa duk suka dube ta. Haseenah miƙewa ta yi gami da sakin ɗan ihu kaɗan tana ƙoƙarin ruƙunƙume ta, tuni Laila ta ja baya tana nuna hannun Haseenah. 

"Ke manja fa!"

Suka yi dariya. 

"Wallahi kin yi mugun kyau ne masha Allah, wai haka kika iya kwalliya dama? Shi ne don rainin hankali ba ki taɓa yi ba sai wani kwalli da lip gloss kawai da kike sakawa?" 

Laila ta yi mata wani kallo ta kauda kai tana ɗan murmushi da jan tsaki duka a lokaci guda, ta maida hankali suna gaisawa da ƙawar Haseenah wacce ba ranar ta soma ganinta ba. Hakan sai ya ƙara ba Haseenah dariya. 

"Wow! To wallahi kar ki yarda ki yiwa Areef wannan kallon don ina ga ba zai iya barinki ya koma garinsu ba a yau. Inyee! Ah sai fa na maki hotuna."

Aikuwa ba ta bar Laila ta fita zuwa falon Momi ba sai da ta kashe ta da hotuna a wayarta. Faɗi take,

"Sai na zo gaisar da ƙanin nawa."

Laila ta bi ta da toh ta yi gaba. 

Momi Fannah da ke zaune tare da wasu ƴan yara ƴan yawon barka da sallah ta washe haƙora.

"Kai masha Allahu la ƙuwwata illah billah, ko ba ki faɗi ba ya ƙaraso tunda na ji Abbas shiru daga aikensa ya duba ko direban gidan su Mujahid ya ƙaraso tafiya da su."

Ta yi murmushi kawai. Aikuwa ba ta kai ga cewa bari ta je ba, Abbas ya shigo da sallama ya dube ta. 

"Anti Laila, Yaya Areef sun zo, na kai su sittingroom ɗin."

Ya furta don dama tun ɗazu Haseenah ta saka aka gyarawa Laila ɗin aka saka turaren wuta mai ƙamshi. Jin Abbas ya ce sun zo, sai ta ji faɗuwar gaba. Yau kuma shi da wa ya zo? Wai shi koyaushe cikin saɓawa umarninta zai kasance? Meyasa yake nuna mata kamar shi ba mai laifi ba ne? Meyasa yake jin kamar ma an riga da an yafemasa zunubin da ya aikata musu? 

"Ki je mana Laila."

Maganar Momi Fannah ya maido ta hayyacinta, ta yi mata sallama ta fice. 

***
Areef da Fareed suna zaune suna ƴar hirarsu inda Fareed ke cewa ya ƙagu ya ga wace wannan da Areef ɗin ya mato a kanta har ya ɓoyemasa alaƙarsu haka, shi ko bai ce komai ba sai ɗan murmushi. Fatansa kar Laila ta ba sa kunya a gaban Fareed. Ya san hakan a wurinta zai iya zama laifi, zuwa tare da wani tattare da shi ba tare da ya sanar da ita ba. Ƙila hakan ba zai daɗaɗa mata ba tunda auren ba wai na soyayya ba ne. 

 Sallamarta ta katse mishi tunani, suka dubi ƙofar shigowa gami da amsa mata. Fareed ya ɗan saki baki yana kallonta, ya tabbatar koda ace Ubangiji S.W.T na ba wa bayinsa zaɓin halittar kansu da kansu, toh yana rantsuwa da Allah bayan hakan babu wani abu da Laila za ta ƙerawa kanta na kyau da kuma sura da zai fi wacce yake gani a yanzun. A ɓangaren Areef kuwa, kallonta kawai yake yi yana yaba komai na shigarta. Ya bi fuskarta da kallo, ya ambaci sunan Allah a ƙasan ransa. Kyau dai ta yi shi, ita kuwa kwarjini ta ga sun mata a yau. daga Fareed din har Areef da ta raina wayonsa. Sai ta nemi tsiwarta ta rasa, ta nemi harara da baƙaƙen maganganun da ta ƙullo a ƙasan rai da niyyar jifansa da su idan ta samu wata ƴar damar, amma kuma duk sai ta ɗan watsar. Ta saka a rai kuma albarkacin wanda suke tare ne da ba ta sani ba. Ta ƙi ba kanta cewar wai har da darajar Areef din, a wurinta sam ba shi da wata daraja ta a zo a gani ban da na kasancewarsa uban Haidar ɗanta. 

 "Barkanku da isowa, ya hanya da mutanen gida? Fatan duk suna lafiya?"

Maganarta ya katse Areef daga kallon ƙurillah da ya shagaltu a jifanta da shi, a ɓangaren Fareed dama tuni ya kawar da tasa fuskar don kaucewa shiga hurumin Allah. 

"Barka dai, fatan mun sameku lafiya ku ma?"

Ta ɗan dubi Areef din da ya wani ƙura mata idanu yana murmushi ta janye nata ƙwayoyin idanun, tana murmushin yaƙe. Ba tare fa ta ba shi amsa ba ta zarce da gaida Fareed. Fuska a sake ya amsa. 

"Amaryarmu ashe mai tsada ce masha Allah, shiyasa wannan ɗan duniyar ya ɓoye mana ita. To Allah ya sa a yi muna raye."

'Duk halinsu ɗaya ashe, abokin ɗan iska, shi ma ɗan iskan ne.' Ta yi furucin a ƙasan ranta don ita ba ta ga wani ma'ana a zancensa ba. 

Yanayin yaƙen da take yi, ya sa Areef saurin shiga zancen. 

"Afuwan, duk da na gabatar maki da shi, amma na tabbatar ba lallai ki canki ko waye ba ko? Sunansa..."

"Fareed?"

Ta yi zancen a yanayi na kamar tambaya, ya ɗan yi jim don ya kasa tuna sadda ya yi mata zancensa, sai kuma ya yi ƴar dariya ya dubi Fareed. 

"Ta gane ka. Yes Fareed ne, babban amini kuma ɗan uwa a gareni."

Ta jinjina kai tana murmushi. 

"Na san shi, komai da ya dangance ka na sani Areef."

Ta yi magana mai harshen damo, sarai ya fahimce ta, da ace babu Fareed zai so ƙarin bayani, amma kuma sai ya basar kawai hakan ba yana nufin kuma ya bar zancen ba gaba ɗaya. 

"Ina zuwa please."

Ta furta tana duban Areef har da wani narkar da fuska, ya gyaɗa kai. 

"Permission granted." 

Ta miƙe bayan ta sakar masa wani murmushin dole. Ta fita daga ɗakin. 

"Wow wow masha Allah, kai shegen, ashe shiyasa ka yi bakam ka ƙi kallon duk wasu ƴanmatan da ake kawo maka domin ka aura? Ba karya, na yabawa zaɓinka, kuma in sha Allah ina mata kyakkyawa zaton dacewa da kyawun ɗabi'a ta zuciya ba iyaka sura ko fuskar ba."

"Uhum." Kawai abinda Areef ya furta kenan da murmushi. Shima zai so alaƙar ta zama mai kyau ko don su yi rayuwa mai kyau. Ba zai ce wai ya taɓa jin soyayyarta ba gaskiya, ya san dai abinda ya aikata mata ya dame shi wanda har a yanzu tausayinta yake ji. Yana kuma jin cewa ya cutar da ita iya cutuwa muddin bai aure ta ba. 

Koda ta tashi dawowa da kayan motsa baki da kuma abincin da ta girka, tare da Haseenah suka zo. Fuskarta cike da walwala suka gaisa da Areef, suka kuma yi ƴar raha da Fareed. A ƙarshe ta ba Areef amanar Laila matsayinta na ƙanwarta kuma ƴar uwarta da take ji da ita. Abinta ma ya bar ɗaurewa Laila kai sai ƴar dariya kawai da ta yi. Areef dai sai da ya ji ba ya son wannan lokaci ya wuce, domin koda ace yaƙe Laila take, to ya kula a lamarin Haseenar nan babu yaƙe ciki. 

    Haseenah ya nemi alfarma wurinta kan yana so su saka rana ta raka Laila wurin ƴar uwar mahaifinsa da ke nan Kano unguwar Badawa Layout. 

 "Ba ka da matsala, in sha Allah zamu tambayi Daddy a kai mu. Idan muka saka rana, za ta sanar maka."

Haseenah ta amsa, Laila ko wani kallo ta ɗan watsa mishi, ya narkar da idanunsa a nata alamar ta yi haƙuri. Kauda kai kawai ta yi. 

Sai da suka yi sallar Magriba, Daddy Mu'az ya zo suka gaisa da shi har suka sanar masa da batun zuwan iyaye sati na sama, wanda ko a wasa Areef bai sanar da Laila ba. Ya yi farin ciki sosai da fatan alheri. Daga bisani suka yi masa sallama suka tafi. 

Washegari suka wuce garin Adamawa. Tarba mai kyau suka samu wurin ƴan uwa, Areef ya sha tsokana da kirari wai angon mata biyu. Kausar ma da ado da komai ta tarbe su. Ita dai akwai kunya masha Allah, kuma da girmamawa matsayin Areef na Yaya a wurinta, haka Fareed ya fahimta. Idan ka ɗauke Laila wacce babu wani haɗi tsakani face na soyayya a yanda ya fuskanta. Shi dai Areef ya ji shi ne kawai, murmushi kawai ya yi. Ya sani ba zai samu matsala da Kausar a zamantakewa ba tunda tana sonsa, shi ma kuma ya sani ta kwanta a ransa. A ɓangaren Laila yake ɗan shakku, bai san matsayin da ya ba ta ba, haka dama ya sani shi ba shi da wata ƙima a idanunta da har zai siye zuciyarta ta ƙaunace shi. Fatan alkhairi yake yi musu kawai. 

Kwana ɗaya suka juyo zuwa Kano, sai da ya bi umarnin Dada Falmata ya kai wa Zahra ziyara a gidan aurenta har ya yiwa ƴaƴanta alheri sannan suka wuce Katsina. 

Tun yana Adamawa ya ga saƙon Laila tana tambayarsa meyasa bai sanar mata za'a zo wani satin ba? Bai ce mata uffan ba, wannan ma ba shi da amsar ba ta kamar wancan tuhumar da ta yi mishi na dalilin zuwansa da abokinsa Fareed. 

 
Daddy Mu'az ya amincewa Haseenah da Laila zuwa wurin Dada Falmata don su gaidata. Snacks masu daɗi suka yi mata. A motar gida aka kai su, ta text ta sanar da Areef zuwan nasu, ya aikamusu kwatance. 

 Wani tunani da Laila ta yi ne ya sanya ta duban Haseenah dab da shigar motarsu farfajiyar gidan. 

 "Kar ki kusa ki ce ina da twin sister please Haseenah." 

Abin ya ɗan ɗaurewa Haseenah kai. 

"But why?" 

Ta nemi ba'asi, Laila ta girgiza kai. 

"Ko mene ne zan faɗamaki daga baya." Daga haka Haseenah ta jinjina kai ta ce Ok kawai. 

A kallo ɗaya Dada Falmata ta yaba da Laila ta kuma ji ta shiga ranta. Rungumeta ta yi ta zaunar a gefenta. 

 "Kar ki kusa ki ɗauke ni a suruka kin ji ko? Ki yi min kallon Uwa."

Laila na murmushi ta gyaɗa kanta tana wasa da warwaron hannunta. Kamar ta sani, haka Dada Falmata ta dinga jerowa Haseenah tambayoyi da ita kanta Laila din, suna amsawa. Game da iyaye, yan uwa da karatun Lailar ma. Ƴanmatan da suke gidan su kansu sun yaba da Laila, ga Haseenah da ta fi ta sakewa sam ba ta da baƙunta a wuri idan ta so. Duk yanda suka so su tafi, Dada Falmata tsaida su ta yi sai da suka cika ciki da abinci sannan ta sallame su da manyan ledojin da ba su san mene a ciki ba. Bayan zuwansu gida suka ga atamfofi ne masu kyau har huɗu da wasu lesuka biyu masu tsada sai ko sarƙa da agogo. Ƙwarai sun yaba da kayan. 

A ɗaki bayan sun yi shirin bacci ne Haseenah ta dubi Laila a nutse. 

"Ina jinki." 

Cikin rashin fahimta Laila ta ce,

"Da me?" Don  ita har ga Allah ta mance ma. 

"Meyasa kika hana ni na sanar da su ku ɗin ƴan biyu ne?" 

Ajiyar zuciya Laila ta sauke. 

"Oh wannan? Shi yace kar na faɗawa Dadar, ban san dalilinsa ba kuma. Amma zuwa safe zan tambaya don nima ina son sani."

Da mamaki Haseenah ta ce.

"Ba ya so ki faɗamata? Toh su a familynsu ba su son twins? Dama ana gudun ire-iren wannan kyauta?" 

Laila ta kawar da kai gami da ƙara basarwa. 

"Oho musu, ni kaina tambayoyin da ke yawo a raina kenan. Amma ki bari nace zan tambaye shi na ji dalili ai."

Jinjina kai Haseenah ta yi.

"Ikon Allah, ai shikenan. Ko mene ne ma ji."

Laila ta ɗan yi yaƙe. Kwanakin nan duk a kufule take da Areef, ji take kamar ta ɗura masa ashariya kusufa-kusufa ko ta rage takaicin abubuwan da ya ɗuramata a kwanakin nan. Idan ta tuna ma an kusa zuwa sanya ranar aurensu sai ta ji ƙirjinta na wani dukan tara-tara.  

***
  KATSINA...

Gidan ya yiwa Areef daɗi tun bayan tafiyar Daddy Affan da ahalinsa wanda aka yiwa kiran gaggawa a ma'aikatarsa na wani abu da ya taso. A bakin Afrah yake jin cewa wai Nihla ta sha kukan rashin sallama da shi har take ba Mami sallahun a jaddada masa tana sonsa. Tsaki kawai ya ja na wannan banzar tarbiyya ta Nihla. 

 Baba Dakta kuwa cewa ya yi ba zai koma ba duk uzurinsa sai ya je ya kai kuɗin ɗansa Areef. Adamawa Mami ta so a fara zuwa, amma sai Baba Dakta yace a'a ba damuwa idan an fara zuwa Kano tunda ya fi kusa kuma ai saka rana ba wai aure ba ne. Abba ya kwantarwa da Mami hankali da cewa kar ta damu wacce take so ɗin za ta shiga a uwargida. Kunya sai da ta kama Mami ta hau bori wai ita Abba bai fahimce ta ba, ba tana nufin Kausar ta fi so a kan Laila ba. Abba girgiza kai kawai ya yi bai ce mata uffan ba.

*** 
 KANO

  RANAR KAI KUƊI...

Tana zaune a ɗakinsu ta idar da sallar azahar, jikinta duka a sanyaye yake. Ta ma kasa tashi daga wurin da ta yi salla. Tunda Haseenah ta shaida mata isowar waliyyan Areef gidan ta ji ƙirjinta na dukan tara-tara. Salati kawai take ta faman ja, an kai mintuna talatin da zuwansu ba ta ji tashin wani zance ba. Kawai kamar a mafarki ta ji muryar Haseenah na faɗin,

 "Dagaske AN ƊAURA AUREN?! LAILA! LAILA!!"

Zumbur ta miƙe tsaye jiri na ƙoƙarin ƙwasarta... 



MU HAƊU BAYAN SALLAH IN SHA ALLAH. 

ALLAHUMMA BALLIGNA RAMADANA BIL IMAAN... AMEEEN

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol